Showing 93001 words to 96000 words out of 157890 words

Chapter 32 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

164

ba komai ta nuna ta damu da shi sannan ya ce, "Da gaske ne abin da kike faɗa fillo kin yi kewata?" Kabiru ya tambaye ta kasancewar ya gane me kalmar missing take nufi. Raihan ta taɓe baki cikin zolaya ta ce, "Wai fa har ka ji daɗi ko? To ni ma zolayarka nake yi." Ƙarasa maganarta ya yi daidai da zuwansu wani ƙofar gida da yara suke ta atisaye da ƙasa. Kabiru yana shirin aika yaro don ayi sallama da Dije Raihan ta dakatar da shi tare faɗin ita za ta shiga ta fito da amarya da kanta. Da sallama ta shiga cikin gidan, lokaci ɗaya suka tsaya suna kallonta saboda daga shiga da sautin muryar Raihan duk ta bambamta da ta su. Bayan sun amsa mata Raihan ta ce, "Ina Amarya Dije." Dije na jin haka ta mayafi ta rufe fuskarta, saboda tsananin kunyarta. Ras Raihan ta ji gabanta ya faɗi wani irin abu ya turniƙe zuciyarta. A hankali ta ƙarasa wurin ta ce, "Tare muke da angonki yana ƙofar gida mu je yana jiranki." Dije ƙin buɗe fuska ta yi sai ƙyar Raihan ta samu suka fito suna zuwa ƙofar gida hasken farinwata ya haske fuskar Dije. Wani abu ne ya sake taso wa Raihan amma sai ta kawar da kanta ta ci gaban da zolayar amarya da ango. Don ita kanta bata san dalilin da ya sa take jin haushin Dije ba, duk da wannan ne haɗuwarsu ta farko. Sun jima suna hira sannan Su Raihan suka yi mata sallama suka koma gida. A washegarin wayewar garin Juma'a aka ɗaura auren Kabiru da Dije akan sadaki Dubu hamsin, Daddy ne ya bayar da kuɗin bayan an gama abin da za a yi suka ɗauko hanya suka nufo garin Kano.

Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da gangarawa, har Kabiru ya gama rayuwar amarcinsa da amaryarsa ya koma bakin aikinsa na gadi, a lokacin bikin Raihan saura bai fi sati biyu. Daga ɓangarorin nan biyu duka kowanne shirye-shiryen biki suke yi, Daddy shi kansa ya dage sai sayayya yake haka daga ɓangaren mommy abin ba a cewa komai. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har aka shiga satin bikin Raihan.



Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624


35


Tun da bikin Raihan ya ƙarato kullin cikin ɓacin rai Kabiru yake, har sai da Raihan ta gagara haƙuri ta same shi a harabar gidansu. Wannan karon ma ɗaure fuska ta yi tamau kamar wata uwarsa ta nuna wata farar kujera da hannunta ta ce, "Zo ka zauna." Ba musu Kabiru ya ƙarasa ya zauna jiki babu ƙwari. Hannuwa biyu ta haɗa ta zabga tagumi tana zura masa ido sannan ta ce, "Fillo!" Yadda ta ambaci sunansa har tsakiyar kansa kallonta yi ba tare da ya furta mata koda kalma ɗaya ba sannan ta ci gaba da cewa, "Fillo me yake damunka?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Tabbas ina cikin damuwa, zuciyata na azalzalata domin furen da nake ƙoƙarin bawa ruwa ya bushe. Na jima ina ƙoƙarin ganin na mallaki ɗan itaciyar amma tuni bakin alƙalami ya bushe domin sama ta yi wa yaro nisa sai kallo sai hange daga nesa. Ki taya ni roƙon Allah da ya cire min sonta a cikin zuciyata domin babban goro sai magogin ƙarfe." Ran Raihan ba ƙaramin ɓaci ya yi ba a fusace ta dube shi ta furta, "Yanzu akan wata kake ɓata ranka a banza, ba na gaya maka ka cire ta a ranka ba tun da kullin cikin cewa ka rasa ta kake yi." Muryar Raihan ce ta fara rawa idanunta suka ciko da ƙwallah cikin rawar murya ta ci gaba da cewa, "Wacece wannan da ba za ka iya rabuwa da ita ba? A ina take? Me ya sa za ka takura rayuwarka a kanta, ka cire ta daga zuciyarka ko dole ne sai ka so ta?" Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan wanda ita kanta bata san dalilin zubarsa ba, jiki a sanyaya Kabiru ya kai hannunsa saitin zuciyarsa da take buga masa da sauri-sauri sannan ya furta, "Da ina da halin cire ta a raina da tuni na cire na huta da azabtacciyar soyayyarta, kamar yadda na gaya miki ki taya ni da addu'a shi ne mafita." Raihan ta miƙe a sanyaye sannan ta ce, "Shi kenan Allah ya kyauta." Taku biyu ta yi Kabiru ya ce, "Wai Fillo dama haka kike ji da ni? Gaskiya zan yi kewarki idan kika tafi." Raihan ta juyo ta taɓe baki sannan ta ce, "Kar ka min sharri haka nace maka?" Raihan na ƙarasa maganar ta wuce cikin gida. A ranar haka Raihan ta wuni duk jikinta ba daɗi, zuciyarta a dagule daga baya da ta rasa dalilin fushinta akan Kabiru sai da watsar da lamuransa ta ci gaba da harkokin gabanta.

Washegari kamar kullin Kabiru yana zaune a harabar gidan gefe ɗaya ga rediyo tana ta aiki ita kaɗai, a yadda ya nutsu za ka rantse da Allah sauraron ma'aikatan gidan redio yake amma a baɗini sam ba haka ba ne, hankalinsa da tunaninsa sun tafi duniyar tunani daban. Raihan ce tsaye a kansa ta kira shi ya kai sau uku sannann ya yi firgigit ya ɗago haɗe da sakar mata wani yalwataccen murmushi. Guntun tsaki ta yi ta ƙarasa ƙofar ɗakinsa ta janyo kujera ta zauna suna fuskantar juna, yana shirin yin magana Raihan ta ɗaga masa hannu fuska babu walwala ta ce, "Don Allah idan zancen wannan budurwar taka za ka min na yafe, tun da baka da aiki sai na begenta. Kuma wallahi idan ka cika ni zan kira ƙanwata Dije na gaya mata halin da ake ciki, don ba zai yuwu ka aje min ita a can Shanono ba ka zo kana begen wata." Da ido Kabiru ya bi Raihan yana kallon yadda take sauke kowacce kalma ɗaya da bakinta, ganin irin kallon da yake yi mata ya sa ta juya masa ido haɗe da tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Fillo don Allah ba wannan ba, zuwa na yi kaban shawara game da bikin nan ka ga saura kwana huɗu, kuma Barrista ya ce yana son a yi dinner da wacce uwa ni kuma yanzu duk waɗannan abubuwna ba sa gabana." Raihan ta jim sai kuma muryarta ta fara rawa idonta ya ciko da ƙwalla ta ci gaba da cewa, "Ban sani ba ko za mu yi doguwar rayuwa da Barista don gabana faɗuwa yake ina jin tsoron kar wani abu ya faru da shi kamar yadda ya faru da Salim, Fillo soyayyar Salim a jinina take har yau na saka cire shi a zuciyata. Ranar ɗaurin aurena da take tunkaro ni a kullin na tuna sai gabana ya faɗi ina fargabar kar wani abu ya sake faruwa tun da shi ma na riga da na saki jiki da shi." Ba ƙaramin tausayi Raihan ta bashi ba, sai dai duk da yana jin zuciyarsa na ɗaci a game da aurenta bai hana shi ya lallasheta ba saboda yana matuƙar san ganin farincikin Raihan. Har cikin zuciyarsa ya ji baya ƙaunar aurenta da Barista Huzaifa amma ba shi da wata hujja ko wani dalili da zai sa ya furta wannan maganar, ta wani fanin kuma yana ganin kamar ya so kansa da yawa idan ya ce baya son Raihan ta yi aure domin rayuwar mace taƙaitacciya ce, kuma shi bai furta mata kalmar soyayya ba ai baya rugeje mata tata soyayyar ba.

Kamar yadda ta saba masa a duk lokacin da ta fahimci yana cikin damuwa haka ya yi mata, miƙe wa ya yi tsam ya shiga ɗakinsa ya buɗe ɗan ƙaramin firjinsa ya ɗebo mata ruwa mai sanyi, har lokacin da ya koma bata motsa daga yadda ya bar ta ba. Sai da ya tsiyaya mata ruwa a kofi ya miƙa mata sannan ya zauna a kan kujera ya furta, "Fillo!" Ɗago wa ta yi ta kalle shi bata san dalili ba sai ji ta yi hawaye na zuba. Kawar da kansa gefe ya yi yana jin kukanta har cikin zuciyarsa miƙe wa tsaye ya yi ya bata baya sannan ya ce, "Idan kina son mu yi magana don Allah ki daina barin hawaye na zuba daga idonki." A hankali ta sa hannu ta goge ƙwallar idonta, juyo wa ya yi mata hararar wasa ya ce, "Ga wata nan a gefe." Ya faɗa yana nuna gefen fuskarta. Ita ma harar wasa ta sakar masa ta ce, "Ai dole ka ga makwancina Fillo tun da ina hawaye a gabanka." Kabiru yana shirin yin magana suka ji ana buga gida. Da sauri Kabiru ya ƙarasa wurin ya leƙa don ganin mai buga wa nan take ransa ya yi mummuna ɓaci, sai da furzar da iska mai zafi sannan ya dubi Raihan murya a daƙile ya ce, "Kin yi baƙo!" Da mamaki ta dubi Kabiru ta ce, "Baƙo kuma? Waye haka?" Ta yi maganar cikin mamaki don ko kaɗan ba su yi hirar zuwan Barista Kano ba. A hankali Kabiru ya zare sakatar ƙofar Barista Huzaifa ya shiga yana watsa wa Kabiru kallo, haka shi ma daga ɓangaren Kabiru wani ƙasƙantaccen kallo ya watsa wa Barista sannan ya shige ɗakinsa ba tare da ya tanka masa komai. Raihan na ganin Barista ta faɗaɗa fara'arta haɗe da faɗin, "Amini kai ne a gari? Gaskiya ka iya suprise me ya sa baka gaya min ba?" Fuska babu walwala Barista Huzaifa ya ce, "Dole ki ce haka tun da kina wurin mai gadi kuna hira, na kira ki ya fi sau shurin masaƙi baki ɗauka ba." Raihan ko kaɗan bata ji daɗin kalmar da ya gayawa Kabiru ba don haka ta nuna masa kujerar da Kabiru ya tashi, yamutsa fuska ya yi ya ce: "Wannan ba mahallina ba ne ki bari wanda ya fi cancanta da ya zauna idan na baku wuri sai ya zauna, ku ci gaba da hirarku. Amma fa ki yi haƙuri na katse muku jin daɗi don na san ba haka kuka so ba..." Tun bai rufe baki ba Raihan ta katse shi da cewar, "Haba Barista me kake faɗa haka ne, wai baka san waye Kabiru ba?" Tana rufe baki Barista ya rufe ta da faɗa Raihan tun tana kare kanta har ta ja bakinta ta yi shiru, duk da ta san Barista na nuna kishinsa akan Kabiru bata taɓa tsammanin abin nasa ya kai haka ba. Kabiru na daga ɗaki ya ji ba zai kasa daure ba don haka ya fito a zafafe ya kalli Barista ya nuna masa ƙofa haɗe faɗin, "Malam zo ka fice idan ka gama." Da mamaki Barista ya kalli Kabiru sai ya saki dariyar takaici ya ce, "Lallai mai gadi ya samu wuri..." Raihan ta ƙarasa gaban Kabiru ta furta, "Me kake yi haka Fillo ka na cikinn hayyacinka kuwa? Mijin da zan aura ne fa me ye naka a ciki?" A hargitse ya ɗago ya kalli Raina don maganganunta ba ƙaramin ƙara masa ɗaci a zuciya suka yi ba, Barista ta naɗe hannunsa sannan ya ce: "Da baki ba shi damar ya min haka babu yadda za a mai gadi ya raina mijin da za ki aura." Raihan ta dubi Kabiru ta ce, "Fillo ka bashi haƙuri." Wannan karonma kallonta ya yi ba tare da ya furta komai ba, sai da ta sake maimaita abin da ta faɗa yana shirin yin magana ta katse shi da cewar, "Ba na buƙatar jin komai ka bashi haƙuri na ce." Kabiru ya ƙarasa gaban Barista suka yi ido biyu sannan ya waiga ya kalli Raihan ya ce, "Komai zan yi saboda ke ne don kina ɗaya daga cikin mutane masu muhimmanci a gare ni." Babu musu ya bashi haƙuri sannan ya koma ɗakinsa. Barista ya jima Raihan tana bashi haƙuri sai daga baya ya sauko sannan suka ci gaba da tattauna akan lamuran da ya shafi bikinsu. Duk yadda Raihan ta so kauce wa yin wata bidi'a a bikin sai da Barista Huzaifa ya shawo kanta ta aminci, za su yi Dinner da Kamu amma daga haka sai ɗaurin aure. Duk abin da yake faruwa Kabiru yana daga ɗaki yana jin su, sai dai gabaɗaya zuciyarsa a dagule take. Sun jima suna hira sannan Barista ya yi mata sallama ya wuce gida, Raihan duk da yadda zuciyarta ta kai ga azalzalarta yi wa Kabiru magana haka ta danne don ta san kowaye aka yi masa abin da Kabiru ya yi ba zai ji daɗi ba, don haka tana raka Barista ta wuce gida.

Sannu a hankali haka suka ci gana da rayuwa Kabiru na fushi da Raihan ita ma tana yi don ko fita wurinsa ta daina yi, Raihan tuni aka shiga yi mata gyaran jiki kala-kala ban da ƙamshi babu abin da take yi. Hatta kaya idan ta cire ƙamshi suke yi saboda yadda turare ya ratsa jikinta. Ranar laraba aka yi kamun amarya a cikin gidansu Raihan, wani ɗinki aka yi mata da atamfa ba ƙaramin kyau ta yi ba. Kowa ya ganta sai dai ya ce masha Allah saboda yadda aka zane hannunta da ƙafarta da jan lalle, ga kwalliyar da aka yi mata daidai misali ta yi mata kyau. Washegari Alhamis aka yi dinner ɗin Raihan da Barista a Nihal Event center, wurin ba ƙaramin ƙayatuwa ya yi ba. Haka aka yi dinner aka tashi wannan karon su Inno ba su je ba, a cewarsu wurin zuwan yara ne ba na su ba. A haka aka tashi daga taro gwanin birge wa, don sun yi taro lafiya sun tashi lafiya kowa yana santin yanayin bikinsu.

Ranar Juma'a kamar yadda sanarwa ta gabata aka ɗaura auren Raihan da Barista Huzaifa akan sadaki dubu Ɗari, saboda tun kafin lokacin bikin Daddy ya nuna baya buƙatar kuɗin sadaki masu matsanancin yawa, ya fi buƙatar albarkar abin musamman da ya ga irin manyan akwatunan da Barista ya dire wa Raihan har saiti biyu. Wannan karon su Goggo har mai kiɗan ƙwarya suka ɗauko, haka mata suka cashe su kaɗai Raihan kuwa tana ɗaki tana tunanin lokacin bikinta Salim da irin shagulgulan da aka sha. Zuciyarta ce ta karye, a hankali ta miƙe jiki ba ƙwari ta nufi sashen Mommy kai tsaye ɗakinta ta nufa ta ci sa'a babu mutane da yawa tana shiga ta faɗa jikin mommy ta saka kuka. Mommy bata hana ta ba don ta lura tun da bikin Raihan ya matso take cikin damuwa, sai da ta yi mai isarta sannan ta: "Mommy tsoro nake ji kar wani abu ya faru an jima ba na son na rasa Barista ina ji..." Da sauri Mommy ta rufe mata baki haɗe da cewar, "Ki sawa zuciyarki kin yi aure ne na tsakani da Allah, don Salim ya rasu a daren aurenki bashi yake nuna Barista zai tafi ba." Mommy ta jima tana yi mata nasiha mai ratsa jiki sannan ta miƙe ta fice daga ɗakin. Kimanin ƙarfe takwas saura motocin ɗaukan amarya suka kafa da'ira a ƙofar gidansu Raihan. Sai da aka yi mata nasiha mai ratsa jiki sannan aka damƙata a hannun Goggo da Inno suka shiga mota da ita, kamar wancen karon sai da aka fara kai Raihan gidan Iyayen Barista sannan aka wuce da ita katafaren gidanta da ke unguwar Maidile, kasancewar Barista ya ɗauki hutun wata biyu don haka za su zauna Kano bayan sun cinye hutun su wuce garin Kaduna. Dr Hussain shi ne babban abokin ango duk wani shige da fice da shi ake yi, don haka baya zaune baya tsaye. Bayan an kai Raihan gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi, jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don ta gama saddaƙarwa jira take ta ji wani labarin daban. Tana nan zaune ita da su Safna ta ji muryar su Barista da abokansa suna yi masa tsiya irin ta abokan angwaye. Bayan sun shigo sai da aka yi siyan baki sannan su Dr Hussain suka ɗauki su Safna za su mayar da su gida. Barista Huzaifa har bakin gate ya raka su sai da ya ga fitarsu sannan ya tura ƙofar haɗe da bushewa da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci ɗaya ya murtuke fuska sannan ya furta, "Alƙawari na ɗaukar wa kaina Raihan tawa ce ni kaɗai, ni ne mallakinta daga ni babu wani Namiji da zan lamunce ya mallaketa bayan ni. Ni Huzaifa duk wata hanya da zan bi na faɗa sai na bi ta don ganin na Mallaki matata." Huzaifa yana gama maganar ya wuce cikin gida wurin Raihan. Su Dr Hussain har sun fara tafiya Safna ta ce, "Kai! Dr wallahi na yi babbar mantuwa." Da mamaki ya tambaye ta nan take ta gaya masa wayarta ta manta a kan gadon Raihan. Dr Hussain magana ya yi wa sauran Abokan tafiyarsa da farko har sun ce ya je ya rakata su ɗauko, kasancewar dare ya fara yi ya ce su bari ya kira wayar Barista amma ɗif ya ji ta a kashe. Juya motar ya yi zuwa hanyar gidan Raihan amma duk yadda suka kai ga dube-duben su sun nemi gidan Raihan sama ko ƙasa sun rasa.


🤣 Ina masu cewa suna Allah-Allah Barista ya mutu🤣🤣🤣 To dai yanzu how market?🤣 Mu je zuwa Huzaifa kana wuta ina bin ka da fetir💃🏼


Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624


36



Ganin zagayen da suke yi ya yi ya wa ya sa Safna ta dubi Dr Hussain ta furta, "Dr ni fa kaina ya kulle, wai da za mu taho ba ta wancan layin muka biyo amma na ga mun yi zagaye ya kai sau huɗu ban ga gidan ba." Dr Hussain tuni shi ma kansa ya ɗaure a cikin zuciyarsa ya furta abin da Safna ta faɗa a don shi ma ba ƙaramin mamaki ya yi ba, yana jin ta yi magana cikin sauri ya ce: "Wallahi kin rigani a fili na riga ki a zuci." Munira da ke kujerar baya ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin, "Ya kamata mu wuce gida idan ya so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login