Showing 51001 words to 54000 words out of 157890 words
baki ba Mommy ta shiga office ɗin, tana shiga ta samu kan kujera ta zauna. A gaggauce mommy ta gaida Malam Usman, yana ganin yanayinta ya tabbatar da tana cikin damuwa. Duk abin da yake faruwa da Raihan da Mama Uwani sai da ta zayyane masa, ko kaɗan bai yi mamaki ba don wannan ba sabon abu bane a wurinsu kasancewar suna samun cases makamantan irin waɗannan har ma da waɗanda suka fi haka." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Tabbas ɗaukota a wannan halin da take ciki akwai babban hatsari sakamakon halin da take ciki. Amma zan haɗa ki da ɗaya daga cikin ma'aikatanmu..." Da sauri mommy ta haɗa hannuwa biyu tana faɗin, "Don Allah Malam ka taho mu tafi tare." Murmushi Malam Usman ya yi ya ce, "Hajiya don Allah ki kwantar da hankalinki wannan fa ba wani babban lamari ba ne a wurinmu, ina nufin zan haɗa ki da Malama Nafisa ku tafi zan shiga motata sai na riƙa bin ku a baya." Cikin gamsuwa da maganar Malam Usma Mommy ta miƙe tsaye tana faɗin, "To Malam Allah saka da alheri." Mommy na fitowa Malam Usman na biye da ita nan take ya sanarwa da Malama Nafisa abin da yake tafe da Mommy, Adaidaita sahun da Mommy ta zo a shi suka tafi da ita, motar Malam na biye da su tiryan-tiryan har suka ƙarasa ƙofar gidan Daddy. A kunyace Mommy kalli mai adaidaita sahun ta ce, "Don Allah bari na shiga na ɗauko ma kuɗin." Ganin abin da yake faruwa ya sa Mai ɗan sahun bai damu ba, don ya san lalura bata wuce kan kowa ba. Da ƙarfi mommya ta riƙa bugun ƙofar babu jimawa Kabiru ya buɗe mata, a gaggauce ta karɓi rancen dubu biyu a wurinsa tana miƙawa mai ɗan sahun ta juya suka shiga da Malam, Nafisa da Mommy.
Su Goggo na harabar gidan sun yi carko-carko Goggo na ganin Malam Usman kamar ta sanshi ta rangaɗa kabbara tana ci gaba da cewa, "Ka ga Ulama'u magada Annabawa." Inno ta ƙarasa gabansa ido ɗauke da ƙwalla ta ce, "Yaro ko wata biyu ba a yi da mutuwa Ƴata Hasiya ba yanzu ga Audullahi yana can ina jin tuni Aljanu sun riga da sun jajjage namansa." Malam Usman ya kalli Inno lokaci ɗaya ya ji ta bashi tausayi, cikin tattausan lafazi ya ce: "Insha Allah babu abin da zai faru da shi sai alkairi, bari na shiga ciki." Malam Usman ya yi gaba Nafisa da Mommy na biye da shi, daga Inno har Goggo babu wacce ta motsa ƙafarta don ta shiga cikin gidan.
Malam har ya je bakin ƙofar ya dubi Mommy ya ce, "Babu Famfo a kusa ina son na yi alwala." Da hannu Mommy ta nuna masa can gefe famfam da Kabiru yake amfani da shi. Sai da ya yi alwala sannan ya tunkari ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da addu'a, mommy na biye da shi amma ilahirin jikinta rawa yake tana tsoron abin da Raihan za ta aika da halin da Daddy yake ciki. Tsit cikin falon ya yi kamar babu kowa a ciki, Malam Usman ya kalli Mommy ya ce, "A ina yarinyar take?" Mommy ta fara waige-waige ta ce, "Ga dai ɗakinta can, amma lokacin da ta biyo mu a falon nan na barta." Jinjina kai Malam ya yi yana faɗin, "Za ki iya duba mana cikin sauran ɗakunan don mu san a wanne take?" Da sauri Mommy ta ce, "A'a Malam don Allah ka duba da kanka."
Lokacin da Raihan ta koma cikin ɗakinta wurin da Daddy yake ta tunkara a haukace tana faɗin, "Duk wanda ya nemi raba ni da matata sai na hallaka shi, Raihan matata ce mallakina ce babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da ita." Ilahirin jikin Daddy ban da rawa babu abin da yake yi, ga jinin da yake zuba daga jikinsa na ciwon da ta ji masa ga gumi tuni ya haɗu ya yi sharkaf, ya gama saddaƙar da rayuwarsa don gani yake tashi ta ƙare a kowanne lokaci Raihan za ta iya cimmasa, tun yana kukan zuci har ya fito fili ya fara kuka da hawaye shaɓe-shaɓe. Yana daga cikin banɗaki ya ji muryar mommy da Malam Usman suna magana, da ƙarfi ya ware murya yana faɗin, "Zainabu ku kawo mun ɗauki ina cikin banɗaki." Jin haka ya sa Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Malam ga Mahaifinta can yana ɗakinta." Da sauri Malam Usman ya nufi hanyar ɗakin sauna zuwa kai tsaye banɗaki suka ƙarasa Mommy ta ce, "Daddyn Raihan buɗe mu ne." Daddy da sauri ya amsa, "Zainabu kin tabbata ku ne kar na buɗe ta hallaka ni." Dariya ce ta so ƙwacewa Malama Nafisa, mommy ta ce, "Mu ne Daddyn Raihan tare muke da Malam." Daddy ya buɗe ƙofar yana zuro kai a hankali, sai da ya tabbatar da su Mommy ne sannan ya buɗe ƙofa. Yana fitowa Raihan ta shiga ɗakin a bakin ƙofa ta tsaya ta riƙe ƙugu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, da sauri Daddy ya juya zai sake faɗawa banɗaki Malam Usman ya fara takawa gaban Raihan, ko motsi Raihan bata yi ba cikib wata irin fusatacciyar murya ta fara magana.
"Malam babu ruwanka da ni, karka shiga hurumin da ba naka na, wallahi ba zan rabu da ita ba saboda matata ce na aureta halak-malak na biya sadakinta me ya yi saura." Malam Usman ya matsa gaban Raihan yana faɗin, "A ina ka taɓa jin aljani ya auri bil'adam? Nan ba wurin zamanka ba ne tun wuri ka kama gabanka." Raihan ta fara takowa cikin isa da ƙasaita ta ce, "Malam Ina ganin mutumcinka tun wuri ka kama gabanka don ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zan fita daga jikinta ba. Ni Huzafa na auri Raihan sama da shekara goma sha ta haifa min ƴaƴa, na santa farin sani na yi mu'amala da ita har ta fi matata ta jinsina gamsar da ni. Na shafe tsahon shekaru ina rainon abata, yanzu haka ina hanyata ta zuwa neman warakarta Mar'usa ta sanar da ni halin da ake ciki, kana ganin duk wannan wahalar da na yi za ta tashi a banza ne? Mahaifinta shi ya damƙamin ita shi da kansa ya bani aurenta akan me rana tsaka za ka zo ka nemi raba ni da matata." Lokaci ɗaya jikin Daddy ya hau tsuma baki na rawa ya furta, "Ni...Kuma? Yaushe na sanka da har na baka auren Raihan?" A zabure Raihan ta nuno Daddy tana cewa, "Ƙarya kake munafuki ni za ka ƙaryata a gaban jama'a? Na fi ƙarfin ka ƙaryata ni kuma ina ɗaga maka ƙafa ne saboda kana nunawa matata kulawa, baka cika saka mata ido ba kamar mahaifiyarta. Kun ga wannan." Raihan ta nuna Mommy sannan ta ci gaba da cewa, "Ta yi bala'in saka min ido kuma ba tun yau na so halakata ba don dai tana da yawan ibada, ta matsawa Matata Raihan kuma ga shi ita ce sanadiyyar bankaɗo sirrina." Malam Usman ya jinjina kai ya kallai Raihan ya ce, "Ba na son ƙarya don na san akwai maƙaryata da yawa a cikinku, ya aka yi Mahaifinta ya baka aurenta kana tunanin akwai uban da zai damƙa auren ƴarsa a hannun aljani ne?" Tuno idanun Mommy suka kawo ruwa ta kalli Daddy cikin kuka ta ce, "Dama ashe soyayyar da kake yi wa Raihan bata kai zuci ba, wanne abu kake aikawata a ɓoye da har za ka damƙawa aljani auren ƴata?" Daddy zai yi magana Malam Usman ya dakatar da shi da cewar, "Huzaifa kake ko wa? Na ji sunanka da alama kai musulmi ne to da farko zan haɗa ka da girman Allah ka fice daga jikin yarinyar nan ko za ka samu salama a wurina, matuƙar ka nuna min taurin kai sai na ƙoneka ƙurmus." Raihan ta koma jikin bango ta zauna sannan ta ce, "Malam ka bar haɗa ni da musulunci don ni ba Musulmi ba ne, ba don kar in watsawa Mahaifiyata ƙasa a ido ba da sai na ce hanyar da musulunci take ban biyota ba. Mahaifiyata da danginta Musulmai ne, mahaifina da danginsa duka kafirai ne. Zan yi maka magana ta ƙarshe, ba zan taɓa fita daga jikin Raihan ba, duk abin da za ka min sai dai ka yi amma zama a jikinta yanzu na fara domin yanzu ta zama cikakkiyar budurwa, na raineta tun bata zama wani abu ba sai da na fara ɗanɗana zumarta za ka ce na fita? Ɗan da muka haifa waye zai ci gaba da shayar da shi?" Malam Usman ya jinjina kai a fili ya ce, "Tabbas za mu kai ruwa rana da shi domin wannan yana cikin masu taurin kai." Nan take Malam Usman ya yi A'uziyya ya fara karanta surartul Baƙara, Malam Ya jima yana karatu amma Huzaifa ya yi shiru sai da ya ji azaba ta ishe shi ya ƙwalla wata irin razananniyar ƙara.
Inno na daga ƙofar ɗakin Kabiru ya saki dariyar farinciki ta ce, "Allah mai mutane da yawa, kai jama'a Allah na dawo Zinaru kin ji yadda Malam yake fata-fata da aljanin nan da ayar Allah?" Goggo ta sake baza kunne sannan ta ce, "Wuya mai sa Waziri shiga wandon Sarki ki ce da na tafi Albasu da na bar kallo."
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn 0706 206 2624
18
Kabiru yana daga ɗaki yana jin su Inno da har ya yi niyyar ya yi musu shiru sai ya ziro da kai yana faɗin, "Inno kar dai ku manta da ambaton Allah, don idan kuka yi sake ana cirewa daga jikinta za su iya faɗowa kanku." Inno tuni ta yi wuri-wuri ta ɗebi salati tana watsa wa Kabiru daƙuwa haɗe da cewa, "Gidanku ka ji ɗan nan, yoo ni me aljani zai yi da ni fata ta saki gijibgi duk ya sauko, kwarankwatsa ko da ina budurwa sai dai ya ganni ya ƙyale?" Goggo ta kalli Inno ta ce, "A'a bar faɗin haka wallahi tsaf za ki yi kyau da su ke dai mu roƙi Allah ya raba mu da su amma Aljanu suka haye mu na san Audullahi tarkata mu zai yi ya wuce Albasu da mu." Inno kamar mai nazari haka ta yi jigum cikin tsiro don har lokacin bata daina hango kammanin kofaton Mama Uwani a ƙafarta ba.
Malam Usman karatu ya ci gaba da yi babu ƙyaƙƙyautawa don ya san dama sai ya ɓullo masa ta haka za a samu mafita, sai da ya lura da Huzaifa ya yi lugub sannan ya sarara da karatun yana tambayarsa, "Za ka fita daga jikinta ko ba za ka fita ba?" A wahalce Raihan ta ɗago da kai dana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Malam ka dakata mu yi magana da kai ta fahimta don Allah ka daina ƙonani." Malam Usman ya zauna a kan kujerar ɗakin Raihan ya ce, "Babu wata magana ta masala da za mu yi da kai da ta wuce ka amince da abin da na umarceka." Raihan ta gyara zamanta sannan ta ƙurawa Malam Usman ido cikin rashin tsoro ta ce, "Malam ka faɗi wata buƙatar taka amma ba wannan ba, don ba zan taɓa rabuwa da ita ba saboda ita ɗin mallakina ce ban taɓa ƙaunar wata hallita kamar yadda nake ƙaunarta ba. Zan iya fansar da dangina tas akan ta, amma ka daina furta kalmar rabuwa a tsakaninmu." Malam Usman kalli Malama Nafisa ya ce, "Ba ni ruwan Addu'ar nan da garin maganin nan mai haɗe da habbatais sauda." Nan take Malama Nafisa ta ciro abubuwan da Malam ya buƙata a cikin wata jaka mai ɗauke da tambarin Waraka Islamic Chemist. Malam Usman yana karɓa ya ƙarasa gaban Raihan ya yi bismillah ya fara yayyafa mata, ya miƙawa Malama Nafisa garin maganin ya ce, "Ki tabbatar da ta shaƙi wannan garin maganin." Malama Nafisa ta tunkari Raihan tana tafe tana addua, ganin ta tunkarota ya sa Raihan ta yo kanta suka fara kokawa da ƙyar ta samu ta shaƙa mata maganin. Raihan na shaƙa ta fara sakin atishawa cikin fitar hayyaci, Malam Usman ya ƙarasa kanta ya fara yayyafa mata ruwa yana ci gaba da karatu, azaba goma da ashirin ce ta sa Huzaifa a gaba. Ban da ihunsa babu abin da yake tashi a cikin ɗakin, Daddy da Mommy suna gefe suna kallon ikon Allah. Lokaci-lokaci Mommy take wurgawa Daddy mugun kallo don har lokacin maganar Huzaifa ta tsaye mata a rai da yace Daddy ne ya bashi auren Raihan. Daddy duk jikinsa ya yi sanyi duk ya yi zuru-zuru kamar wanda yake bakin bindiga, suna cikin wannan halin suka riski muryar Huzaifa yana cewa, "Dakata! Dataka Malam zan fita." Malam Usman ya tsagaita da karatun ya ce, "Za ka fita ta ina?" Huzaifa ya sauke numfashi ya ce, "Zan fita amma sai ta gama shayar min da jaririn ɗana." Ran Malam Usman ya yi mummunan ɓaci ba ɓata lokaci ya ci gaba da karatu duk yadda Huzaifa ya kaiga roƙon Malam bai saurara masa. Yana cikin karatun ya ji wata murya ta canji ta Huzaifa da yin sallama, "Assalamu alaikum." Malam Usman ya koma ya zauna sannan ya amsa, "Wa'alaikas salam da wa nake magana." Cikin nutsuwa dattijuwar ta ci gaba da cewa, "Kana magana da Malama Fatima, ni ce mahaifiyar Huzaifa." Malam Usman ya ce, "Malama Fatima me ya sa za ki katse min aikina ina shirrin hallaka ɗanki Huzaifa."
Kafin mu ji amsar Mahaifiyar Huzaif mu koma waiwaye don jin Tarihin su waye Mommy da Daddy🥱
WAIWAYE...
Alhaji Abdullahi Muhammad Zango shi ne ainihin cikakken sunan Daddy, Mahaifinsa Marigayi Muhammad Zango asalinsu mutanen Daura ne cikin unguwar Zangon Daura. Su uku ne rak a wurin Mahaifinsu da mahaifiyarsu Alhajia Al'ƙasim shi ne babba, Marigayi Alhaji Haruna mai binsa sai Alhaji Muhammad Zango ɗan autansu wato Mahaifin Daddy. Ana kiransa da Alhaji babba sakamakon cin sunan kakansa na wurin Mahaifiya da ya yi, Mahaifinsu Marigayi Alhaji Babba riƙaƙƙen ɗan boko ne ya karanci fannin Law. Don haka Mahaifinsu Daddy gabaɗaya sun yi karatun boko mai zurfi, kuma dukkansu suna da rufin asiri. Alhaji Babba sun taso cikin gata da rufin asiri kasancewar Mahaifinsu yana haɗawa da harkar kasuwanci yana da rufin asiri sosai, Alhaji Ƙasim shi ya fara yin aure yana koyarwa a babbar jami'ar Sokoto sai da ya shekara bakwai da aure ƴaƴansa biyu sannan mai binsa Haruna ya yi aure, shi kuma yana aiki a ƙarƙashin hukumar kare hatsarirrika da ababen hawa (Road safety.) Bayan ya yi aure da wata biyar Mahaifin Daddy ya kammala bautar ƙasa shekara na zagayowa ya samu aiki a babban asibitin Katsina da yake fannin likitanci ya karanta. Rayuwarsu sun taso gwanin birgewa tare da haɗin kai a tsakaninsu, suna matuƙar mutumta junansu don haka akwai kyakkyawar alaƙa da soyayyar ƴan uwantaka a tsakaninsu. Mahaifin Daddy shekararsa uku da fara aiki ya haɗu da Inno, a lokacin ankwantar da Mahaifiyarta a asibitin da yake aiki bayan sallamar Mahaifiyarta Alhaji Babba har garinsu Inno ya je, Inno Bafulatanar ƙauyen Madaka ce bata yi karatun boko ba, sai dai ta yi makarantar allo da makarantar dare. Ita kaɗai iyayenta suka haifa gaba da baya, da sassafe suke fita kiwon shanu sai yamma ta doso sannan suke dawowa su huta su ci abinci wurin ƙarfe huɗu su tafi makarantar allo. Idan dare ya yi bayan magariba su tafi makarantar dare, da farko ƴan uwan Alhaji babba ba su so auren Inno da shi ba don a ganinsu me zai yi da ƴar ƙauyen da ko cikakkiyar hausa bata ji. Amma da suka ga yana so a kan dole suka yi masa addu'a da fatan alheri, kuma cikin lokaci ƙanƙani maganar aurensu ta kankama aka tsaida lokaci aka sha biki. Bayan biki Alhaji babba ya ɗauki matarsa ya tafi da ita cikin garin katsina ya yin da yake ziyartar ƴan uwansa lokaci-lokaci, dama kuma tun kafin aurensa da Inno ma haka yake yi.
An yi auren Inno da Alhaji babba da wata biyar Allah ya yi wa mahaifiyar su Alhaji babba rasuwa, wannan rashi ba ƙaramin taɓa su ya yi ba. Ana nan har Allah ya bawa Inno ciki sai dai cikin ikon Allah ta riƙa haihuwa suna mutuwa har sai da suka fidda rai da samun rayayyan ɗa. Kusan shekara goma da aurensu sannan Allah ya bawa Inno cikin Daddy a lokacinma ba su taɓa tsammanin zai rayuwa ba, amma cikin ikon Allah ya ɗore. Bayan haihuwarsa da shekara biyu Inno ta sake samun cikin Mama Hasiya bayan wata tara ta haifeta sai dai daga kansu bata sake samun haihuwa ba. A haka rayuwa ta ci gaba da gangara musu suka ci gaba da rainon ƴaƴansu cikin birgewa, kwatsam watarana aka wayi gari da rasuwar Mahaifiyar Inno ko kwana arba'in ba a yi ba shi ma mahaifinsu Alhaji Babba ya ce ga garinku nan. Wannan mutuwa ba ƙaramin girgiza su ta yi ba don kusan duka mamatan mutuwar faraɗ ɗaya suka yi.
Mahaifinsu Alhaji babba ya rasu babu jimawa Alhaji Ƙasimu ya samu ci gaba ya yin da ya samu koyarwa a wata babbar jami'a da ke ƙasar Ingila. Ƴan uwansa ba ƙaramin daɗin samun wannan ci gaban nasa suka yi ba, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya da daɗi babu daɗi har Daddy ya shekara goma sha biyu a duniya, ya yin da Hasiya take da shekara tara. Kwatsam wata rana Alhaji babba ya tafi Zangon daura yi wa Yayansa Alhaji Alƙasim barka da zuwa da yake ya zo hutu daga Ingila, a hanyarsa ta dawowa ya yi hatsari nan take ya rasu ko shurawa bai yi ba. Wannan mutuwa ta girgiza Inno saboda zaman lafiya suke yi ita da mijinta ba ƙaramin kulawa suke samu ita da ƴaƴanta a wurinsa ba, gawar Alhaji Babba zangon daura aka mayar da ita. Alhaji Ƙasim ya aika aka ɗauko Inno da yaranta, kowa ya ga halin da take ciki sai ya tausaya mata matuƙa. Lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta lalace