Showing 138001 words to 141000 words out of 157890 words

Chapter 47 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

154

ya yi wa Al'amin akan Raihan amma ko ta kan tata ƴar da take kwance bai bi ba. Lokaci-lokaci take kallon wurin Ammi tana wurga mata harara, suna nan zaune wata Nurse ta ƙarasa wurinsu ta ce za su iya shiga wurin Sumayya amma bata buƙatar hayaniya.

Al'amin na zuwa gida a ɗarare ya shiga falon Mahaifinsa, ƙafa ɗaya ya saka Malam ya dakatar da shi da cewar, "Koma mu je gidansu Yarinyar nan za mu." Al'amin na son yin magana amma yana fargaba don yanayin Mahaifinsa ba ƙaramin tsorata shi ya yi ba. Al'amin ya yi tsammanin motarsa Malam zai shiga, amma ga mamakinsa sai gani ya yi ya buɗe ta shi motar ya shiga. Motarsa ya koma ya zauna sannan ya kunnata suka wuce gidansu Raihan, sai da suka je bakin gate sannan Malam ya ciro waya ya kira Daddy da yake ta zarya shi kaɗai a falon baƙi. Yana ɗauka Malam ya gaya masa suna ƙofar gida don haka da kansa ya je ya buɗe musu, Al'amin sai sunne kai ƙasa yake kamar sabuwar amarya. Falon baƙi ya kai su bayan sun sake gaisawa suka sake jajantawa juna abin da ya faru, sannan Malam ya ce sun zo ne su ba shi haƙuri don Raihan ta koma gidan Mijinta. Daddy da kansa ya je ya kira Raihan tana tafe gabanta na faɗuwa har ta shiga ɗakin, a can gefen ta rakuɓe ta gaida Malam ya amsa mata cikin tausayawa don kallo ɗaya za ka yi wa Raihan ka fahimci tana cikin matsananciyar damuwa. Raihan na daga tsugunne ta ji suna maganar komenta a hankali ta ɗago ta ce, "Daddy saki uku fa ya yi min." Daga Daddy har Malam buɗe baki suke yi haɗe ta yin salati, Malam ne ya fara faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Daddy ne ya dakatar da Malam yana faɗin, "Malam ba haka ake ba, yaron nan yau tsawon watansu nawa ko ƙara ɗayansu babu wanda ya taɓa kawowa, ya kamata aji ta bakinsa ba a rufe shi da faɗa lokaci ɗaya ba." Daddy ya ƙarasa maganar yana tambayar Al'amin. Sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya sanar musu iya abin da ya sani game da duk abin da yake faruwa a tsakaninsa da Raihan, sannan ya ciro waya ya nuna musu duk abubuwam da aka taɓa tura masa na Raihan da wani matashin saurayi. A razane Daddy ya miƙe tsaye ya furta, "Kabiru? Wannan cin amanar Kabiru zai yi min?" Raihan da a lokacin ta kai idanunta wurin ta zaro ido ganin Hotonta da Kabiru a maƙale da juna a yanayin da suke kamar ma'aurata, ko ma'aurata bai kamata su ajiye irin wannan hoton a wayarsu ba. Jikinta na karkarwa ta miƙe tsaye tana faɗin, "Wallahi-wallahi Daddy ban san komai ba Allah ba ni ba ce sharri aka yi min..." Raihan ba ta ƙarasa magana ba Daddy ya katse ta, ta hanyar zabga mata mari. A fusace ya shaƙo wuyanta yana faɗin, "A gidan uban wa yake yi miki ƙarya? Allah ya sani mun baki tarbiyya daidai gwagwado don haka..." Daddy bai ƙarasa magana ba, Malam ya riƙo hannunsa ya zaunar da shi da ƙyar ya ƙwace Raihan daga hannunsa. A gefen ƙafarsa ya zaunar da ita ya nemi Raihan da ta sanar musu da duk abin da yake faruwa. Nan take Raihan ta zayyane musu duk abin da yake faruwa tun daga farkon aurensu har lokacin da Al'amin ya saketa. Ba ƙaramin mamaki suka yi ba Al'amin tun da ya sunkuyar da kai bai ɗago ba saboda kunya, Daddy ya kalli wayar Al'amin da ke hannunsa ya kalli Daddy ya ce, "Waye Kabirun?" Cikin huci Daddy ya furta, "Shi ne yaron da na gaya maka rashin lafiyarsa." Murmushin takaici ne ya suɓucewa Malam, Daddy ya bishi da wani irin kallo yana shirin magana Malam ya ce, "Alhaji ka nutsu ka ba ni hankalinka a nan?" Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana wurgawa Raihan harara, sai dai a lokacin ya rage jin zafinta. Malam ya ci gaba da cewa, "Yau kwanan Kabiru nawa yana jinya?" Daddy ya yi jim sannan ya ce, "Zai yi wata ko fi ma ina jin." Malam ya jinjina kai ya kalli Al'amin ya ce, "Na ji ka ce wannan na jikin hoton shi ne wanda ya fito daga ɗakin Raihan ɗazu ko?" Cike da gamsuwa Al'amin ya gyaɗa kai ya ɗora da cewa, "Kuma wallahi ko Sumayya aka tambaya za ta faɗa don ba wannan ne zuwansa na farko gidan ba." Malam ya kalli Daddy ya ce, "Ban yi mamaki ba." Daddy ya dube shi da alamun tuhuma yana faɗin, "Kamar yaya Malam?" Malam ajiye wayar Al'amin sannan ya ɗora da cewa, "Huzaifa!" Ɗauuu! Haka Daddy ya ji maganar Malam har tsakar kansa, yana cikin nazari ya riski muryarsa yana ci gaba da cewa, "Tabbas Huzaifa ya ci kasuwarsa ya watse kuma buƙatarsa ta biya domin ba na raba ɗaya biyun wannan yana daga cikin kaidinsa. Alhaji ba sai na yi maka dalla-dalla ba tun da, da idanunka ka je ka gano Kabiru a garinsu ko magana baya yi sannan kuma ace har yana zuwa wurin Raihan. Shin tun da kake kiran lambar ka taɓa samun ta shiga? Ko kuma ka taɓa zama ka tambayi Raihan don ka ji ta bakinta?" Al'amin sai girgiza kai yake, Malam ya kalle shi sannan ya ci gaba da faɗin, "Ka ba ni mamaki Aminu da baka da dogon nazari da lissafi domin tun kafin ka auri yarinyar nan ban zayyana maka matsalar da take fama da ita ba? Ban ce maka duk wani abu da ka gani ba daidai ba ka sanar da ni? Kai fa mai ilimi ne ina tarin ilimin naka da ba za ka yi aiki da shi ba? Tun wuri ka dawo hankalinka domin muddin ka ɗore a haka soyayyar matarka za ta kai ka jahannama." Malam ya dubi Raihan ya ce, "Je ki ciki ƴar gidan Abba." Raihan ta miƙe kanta na sara mata ta wuce cikin gida, a tsawace ya dubi Al'amin ya ce, "Sakaran banza sakaran wofi, ka buɗe kunne ka ji ni da kyau. Dama matuƙar matarka ta warke ka cewa iyayenta su wuce gidansu da ita. Yadda na faɗa maka haka za ka shaida musu." A firgice Al'amin ya dubi Mahaifinsa. Malam ya nuna masa ƙofa ya ce, "Fice ka ba ni wuri." Kamar sabon munafuki haka Al'amin ya fice sum sum sum daga ɗakin gwiwarsa a sanyaye. Malam ya kalli Daddy ya ce, "Khalid Saleh wani amintaccen Aljani ne da mun ɗauki tsawon shekaru tare, a daren jiya ya sanar da ni ya gano wurin da Huzaifa ya samu mafaka, ban so gaya maka ba na so ace sai sun kamo min shi zan kira ka, amma tun da lamarin har ya kai ga haka a gobe ina da buƙatar ganin wannan Kabirun mara lafiya." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya furta, "Shi kenan Alhaji zan kira Mahaifiyarsa mu yi magana."Malam ya miƙe yana daɗa bawa Daddy haƙurin abin da ya faru, har ƙofar gida Daddy ya raka shi sannan ya nemi Malam da ya janye hukuncin da ya yanke akan Al'amin amma fir ya ƙi amincewa.



Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624


49


Jiki a sanyaye Daddy ya dawo gida wurin su Mommy, Inno na ganin Daddy ta ce, "Audullahi yanzu nake shirin zuwa wurinku ni fa ban gane ba." Daddy ya zauna akan kujera yana faɗin, "Da me fa Inno?" Da yatsa ta nuna Raihan sannan ta ce, "Yarinya nan ko baiwa ka siyo daga garinku sai haka, saboda Allah haka yaron nan zai zo ya tafi shi da Mahaifinsa salin-alin babu wani cin mutumci da ka yi musu balle ka sa hukuma ta kama su?" Ajiyar zuciya Daddy ya sauke ya ce, "Inno duk wannan abin da yake faruwa Huzaifa..." Da sauri Inno da Goggo suka katse shi cikin haɗin baki suna cewa, "A'uzubillahi minasshaiɗanir rajim." Goggo ta girgiza kai sannan ta ce, "Ka dubi girman Allah Audullahi ka bar ambatar sunan nan a gidan nan ko ma samu kurwarmu ta zauna lafiya." Daddy ya miƙe tsaye yana cewa, "Shi kenan Goggo." Har ya yi gaba ya juyo ya kira Mommy sannan ya shige cikin ɗaki. Nan take Mommy ta miƙe ta bi bayansa don ita ma bakinta cike yake da tambayoyin da take son yi masa. Mommy na wuce wa ɓangaren Daddy, Goggo ta dubi Inno ta ce, "Wai Audullahi ko haushinmu ya ji?" Inno ta taɓe baki ta furta, "Ni ma abin da zan faɗa kika riga ni, amma saboda Allah ina ce Huzaifa dai ba ƙanin Alhaji Babba ba ne?" Goggo ta kalli hanyar sashen Daddy tana cewa, "Baki ga ya kira matarsa ba, ko shawarar me za su yi oho." Raihan na jin maganganun su Inno sun fara damunta ta tashi ta wuce ɗakin Mommy, tana shiga ta haye gado ta kwanta ta shiga tunanin matsalolin rayuwarta. Hawaye ne ya zubo mata saboda tausayin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki, tuno abubuwan da suke faruwa da ita ta fara yi tun tana ƙarama. Tun bata san kanta ba take wata irin wahalalliyar rayuwa gashi har ta girma bata samu sassauci a cikin ta ba.

Mommy na shiga ɗakin Daddy ya nuna mata gefen gado, ganin haka ya sa ta zauna jiki a saluɓe tana shirin yin magana ta riski muryarsa yana cewa, "Tsugunne bata ƙare ba." Mommy ta kalle shi ta furta, "Da aka yi yaya?" Wayarsa ya ciro ya fara lalubar lambar Baffan Kabiru sannan ya dubi Mommy ya furta, "Huzaifa ya taka muhimmiyar rawa akan mutuwar auren yarinyar nan domin yanzu haka saki uku Al'amin ya yi mata." A hargitse mommy ta furta, "Saki uku fa?" Daddy ya gyaɗa kansa sannan ya kanga waya jikin kunnensa nan take ta fara shiga, ba a jima ba ya ji Baffan Kabiru ya ɗauka suka gaisa cikin mutumci sannan Daddy ya sanar masa da dalilin kiransa akan kawo Kabiru wurin Malam. Sanin halin Fula ni da mutanen karkara ya sa Daddy ya tabbatar masa da kafin ɗaukan Kabiru zai yi magana da jami'an tsaron garinsu, Baffa ya fahimci abin da Daddy yake nufi don haka ya yi dariya ya furta, "Alhaji yanzu ai babu wannan a tsakaninmu domin mun san ba za ka taɓa cutar da mu ba, Kabiru ai ɗanka ne Allah ya nuna mana gobe da rai da lafiya." Daddy ya ji daɗi don haka ya amsawa Baffa sannan ya tambayi jikin Kabiru, Baffa ya tabbatar masa da yadda yake kullin haka yake har wannan lokacin baya ummm baya umm-umm. Suna gama waya Daddy ya dubi Mommy ya sanar mata da duk abin da ya faru tun daga zuwan su Malam har tafiyarsu. Lamarin ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba, tausayin Raihan ya mamaye zuciyarta ta dubi Daddy ta ce, "Daddyn Raihan an ya Raihan na da rabon aure kamar kowacce cikakiyyar mace kuwa? Ta yiwu haka tata ƙaddara take ƙila mu muke ta abin mu..." Daddy ya katse Mommy da cewar, "Haba Zainab ke fa kike ƙarfafa min gwiwa ta yaya za ki furta irin waɗannan kalaman, Raihan Allah ne ya ba mu ita kum shi zai yaye mata duk wasu matsaloli da ke tattare da ita, duk wanda kika ga bata zauna da shi ba dama can Allah ya rubuta adadin zaman da za su yi da lokacin rabuwarsu, ina kika bar yaron nan Salim wa ya taɓa tsammanin ba za su yi zaman aure da Raihan ba? Wannan abin da ya faru da Raihan da ma can Allah ya ƙaddara mata sai dai mu yi fatan Allah sa haka ne ya fi zama alheri, ta yuwu mijinta yana gaba ta yuwu kuma akasin haka amma duk abin da Allah ya yi mai kyau ne." Jinjina kai Mommy ta yi ta ce, "Tabbas haka ne shi ya sa tun lokacin da yarinyar nan ta ƙwallafa ranta akan yaron nan nake yi mata faɗan ta nemi zaɓin alheri ba son zuciyarta ba, domin ba kowanne abu ne idan muka so shi muka a lokacin yake zame mana alheri ba. Kuma ba komai muke nema a rayuwa mu samu ba don haka a komai ake so ɗan'adam ya riƙe neman zaɓin Allah domin shi ne zaɓin da ba a yin kaico ko nadama a ciki." Daddy ya ajiye wayarsa sannan ya furta, "Wannan gaskiya Allah ya zaɓa mana abin ya fi alheri ." Gabaɗaya suka amsa da Amin.

Tun a cikin daren Daddy ya kira Direbansa ya sanar masa da tafiyarsu zuwa Shanono, gari na wayewa suka ɗauki hanya sai dai kafin tafiyarsu tun asuba Malam ya kira Daddy ya bashi wasu addu'o'in tsari daga shaiɗanu, sannan suka yi sallama. Tun da suka fara tafiya Daddy ya sa aka ware sautin Alƙur'ani mai girma a cikin motar, don haka zuciyarsa wasai yake jinta babu tsoro ko fargaba a zuciyarsa a haka suka shafe doguwar tafiya har Allah ya kai su rugar su Kabiru lafiya. Cikin mutumci da karramawa su Inno wuro suka tarbi Daddy, duk yadda ya ƙi yarda ya ci abinci sai da Inna wuro ta dama masa fura ya sha. Yana gamawa ta yi masa iso wurin Kabiru da yake zaune a ɗakinsa shi kaɗai. Daddy yana shiga ya kalle shi a hankali ya furta, "Allah sarki, Allah ya baka lafiya ka ji Kabiru." Kabiru bai ɗago ba kuma bai tanka masa ba sai Inna wuro ce ta je ta kamo hannunsa, kamar raƙumi da akala haka Kabiru ya bi bayanta har suka ƙarasa wurin Daddy ta damƙa shi a hannunsa. Ba don Baffa ya so ba Daddy ya tilasta masa akan sai sun tafi tare an yi komai akan idonsa, da farko Baffa cewa ya yi shi Daddy ya wadatar a yi komai amma Daddy ya nuna sam ba zai yiwu ba. Kabiru da ƙafarsa ya ƙarasa ya shiga motar sannan su Daddy suka shiga Musa Driver ya fara tuƙi suka ɗauki hanya. Ba su suka shigo cikin garin Kano ba sai bayan sallar Magriba, kai tsaye Daddy ya sa aka wuce da Kabiru wurin Malam. A ɗaki mai lamba biyar aka bawa Kabiru gado, sai da suka saka shi ya gabatar da Alwala ya yi sallah sannan Malam ya sa aka kai masa abinci . Daddy da Baffa suka wuce gida a cewar Malam sai wayewar gari da safe zai fara yi wa Kabiru magana tun da ya lura jinnun jikinsa musulmi ne baya hana shi yin ibada. Baffa na zuwa ya saki baki yana kallon irin dukiyar da aka narka a gidan Daddy, ɗakin da aka kai shi na saukar baƙi kaɗai ya isa abin kallo, ɗakin da Auwalu ya nuna masa da sunan na shi ne gani ya yi har ya kece na Gunduman garinsu. Mamakin irin sauƙin kan Daddy yake don idan kana mu'amala da shi kamar ba shi ne mai tarin dukiya haka ba, abinciccikan da aka ajiye masa kuwa kasa cinye su ya yi sai da gari ya waye aka kwashe wasu.

Lokacin da Al'amin ya fita daga gidan yana shiga mota ya kifa kansa akan sitiyarin mota, haka kawai ya tsinci kansa a cikin nadama bai san dalili ba. Tausayin Raihan ya ji don ya san a zamantakewar da suka yi ba ƙaramin cutar da ita ya yi ba, ji ya yi yana dana-sanin rashin neman yafiyarta don ya san akwai tarin haƙoƙinta akansa da bai sauke ba. A haka ya kunna motarsa ya nufi asibiti yana cikin tafiya ya ga wayarsa na haske, sai a lokacin ya tuna da ya saka ta a slient tun tuni. Misscall ya gani rututu na mahaifiyarsa da Mahaifiyar Sumayya sai kuma na Sumayya da baƙuwar lambar da ake tura masa hotunan tsirancin Raihan, alamar gajeren saƙo ya gani don haka da sauri ya gangara gefen titi ya shiga yana dubawa. Wannan lambar ce da aka saba yi masa magana yana shiga ya ga saƙon kamar haka:

_Ina taya ka murnar rabuwa da Matata da ka yi domin wannan shi ne samun kwanciyar hankalinka, Raihan tawa ce ni kaɗai har abada babu wani lusari da ya isa ya zauna da ita a inuwar auratayya. Ka gode Allah duk irin cin kashin da kake yi mata ban ɗauki fansa mai tsanani akanka da iyalinka ba, daraja ɗaya ka ci shi ne Azkar ɗin da kuke yawan yi, shi ne ya katange ni da ku amma ban ƙyale ka haka ba indai ina numfashi kai da haihuwa sai dai ka ga wasu suna yi, don dama cike nake da mahaifinka saboda abaya ya so halaka ni akan iyalina Raihan. Tun da har Mahaifinka ya gano lagona zan sake tabbatar maka da komai, domin ni Huzaifa ba na tsoro komai ka ga ya faru Raihan ba ta da masaniyar akai, kuma mahaifinka ya yi ƙarya ya sa a kamo ni matuƙar ina numfashi._" Takaici, baƙinciki da ɓacin rai ne ya mamaye zuciyar Al'amin a fusace ya daki sitiyarin motarsa sannan ya fisgi motar da gudun gaske cikin ɗacin zuciya. Yana zuwa Ammi ta riƙa jero masa tambaya sai dai babu wacce ya ya amsa mata don cewa ya yi ta wuce gida zai zo da safe ya same ta. Mahaifiyar Sumayya kuwa saboda ɓacin rai ko ƙurarsa bata kallah ba, yana shiga Sumayya ta kalle shi haɗe da yin guntun tsaki ta ɗauke kanta gefe. Mahaifiyarta ce ta miƙe ta fita sannan Al'amin ya samu damar janyo kujera gaban gadon Sumayya, yana shirin magana Sumayya ta furta, "Tafi ka koma gidansu. Don Allah ka rabu da ni tun da ta fini muhimmanci a wurinta." Al'amin ya haɗiye yawu mai ɗaci don har lokaci ransa a ɓace yake sannan ya ce, "Ya jikinki?" A daƙile ta furta, "Ciki ne ya riga ya fita me ya yi saura, ai dama na san matsiyaciyar matar nan ba za ta bar ni haka ba. Kwartonta ya sa na yi amma ka saka ƙafa ka tafi gidansu, na san ko limamin garin nan za ka kawo aure ne kai da ita ya ƙare tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login