Showing 42001 words to 45000 words out of 157890 words

Chapter 15 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

174

wuya fuskar matashin saurayin nan ta faɗo mata a ƙwayar idonta. Ganin halin da take ciki ya sa Intisar murmusawa don ta fahimci abin da Raihan take buƙata game da Mr Samuel, a hankali ta ɗan zungurota tana cewa: "Wai yau lafiya Samuel yana lecture na ganki some how?" Muryar Raihan a raunace ta ce, "Ya tafi da zuciyata." Wata irin faɗuwar gaba Mugaza ta ji sakamakon jin magana Raihan, cikin ƙarfin hali ta wurga mata tambaya. "Wa kenan." Raihan ta manta shaf malami na ajin ta kwantar da kanta a kan desk muryarta na ci gaba da rawa kamar za ta yi kuka ta ce, "Kallo ɗaya ya yi min amma ya tafi da rayuwata, jin sa nake a ƙarƙashin zuciyata ta yadda duk bugun nufashi fuskarsa na walƙiya a fuskata. Sai dai kash..." Da sauri Intisar ta katse ta da faɗin, "Wanene shi? Ɗan gidan uban waye?" Ta yi wannan tambayar don so take ta ji daga bakin Raihan dukda zafin zuciyar da take ji a kanta, alwashi ta ci muddin Raihan ta furta waɗannan kalaman akan babban masoyinta Huzaifa za ta nuna mata iyakarta, don ta gwammaci ta halakata idan ya so ita ma su abar bauta su halakata kowa ya rasa. Raihan ta katsewa Intisar tunani da cewar, "Wani matashin saurayi ne, da alama shi ba kowa ba ne..." Nan take Raihan ta zayyanewa Intisar abin da ya faru tsakaninta wannan saurayin. Yanda Intisar take murna sai ka rantse da Allah ita ce mai saurayin, Raihan na shirin yin magana Dr Samuel ya hango su suna surutu. Da hannu ya nuno su yana kiransu, Raihan ko gezau haka ta miƙe ta nufi wurinsa Intisar ce take tafe jiki a sanyaye kamar mutuniyar kirki. Raihan tun bata ƙarasa wurinsa ba ya ce mata su fita, madadin ta yi takaici sai kawai ta bushe da dariya har sai ta bawa sauran ɗaliban mamaki. Tana fita Intisar ta bi bayanta suka zauna a dandamalin jikin block ɗin, Raihan na zaune ta runtse idonta nan take fuskar saurayin ta ci gaba da dawo mata. A fusace ta furzar da iska mai zafi, lokaci ɗaya faratan hannunta suka fara sauya launi, daga farare zuwa jajawur. Daga cikin lectura hall ɗin Dr Samuel ne ya fara jin wata irin juwa na neman ɗaukansa, cikinsa ya fara murɗa masa haka kawia ya ji kamar ana fusgar hanjin cikinsa. Tun yana iya daurewa har ya zage ya ƙwallah wata irin ƙara cikin fitar hayyaci, Raihan na daga waje ta bushe da wata irin dariya nan take hannuwanta suka fara dawowa daidai. Intisar ta dube ta cikin tsoron ƙarya ta ce, "Me yake faruwa Raihan?" Raihan bata kulata ba ta sauke idonta a kan wani narkeken jangwalagwada kamar tsuntsuwa tana tsaye ta cafe shi a haukace ta kaiwa kansa cizo, a daidai lokacin ɗaliban cikin block ɗin su suka fito da gudu sakamakon aman jinin da Dr Samuel yake yi, maza daga cikin ƴan Department ɗin su suka kama shi wasu suka wuce wurin hukumar makaranta don sanar da abin da yake faruwa. Carko-carko sauran ɗaliban suka yi dukda sun san Raihan na da aljanu amma ba su taɓa tsammanin za su ga tana gididdiba ƙadangare gida biyu ba, Wani irin huci ta fara yi mai ban tsoro haɗe da gurnani, tana yi tana tunkararsu ganin haka ya sa ɗaliban kowa ya fara yin ta kansu masu ciro waya suna yi mata suna yi daga nesa, Intisar ma wurin ɗaliban ta koma tana nuna tsoronta don duk wani abu da za a zarge tana ƙoƙarin kiyaye shi. Kafin wani lokaci tuni Malaman makarantar suka zo da motar makaranta aka ɗauki Dr Samuel sai dai tun kafin su je asibiti rai ya yi halinsa, amma ba su yi ƙasa a gwiwa ba sai da suka kaishi asibiti don tabbatar da haka daga bakin likitoci.

Raihan na tunkararsu ta fara fige ɗankwalin kanta, hannu biyu ta sa ya ɓark doguwar rigar jikinta don ma Allah ya sa akwai T-shirt a jikinta. Kasancewar rigar na da santsi nan take ta zuge ta faɗi ƙasa, Raihan daga ita sai ƙaramar riga da gajeren wando da ko cinyarta bai ƙarasa ba. Wasu daga cikin securities ɗin makarantar ne suka tunkari wurinta da niyyar kamata don su killace ta saboda suna gudun ta yi wa kanta tsirara a cikin jama'a. Ɗaya wanda ya kasance a kan gaba ya fi ɗayan kwari don na bayan yana da ƴan shekaru zai iya haihuwar Raihan, suna gabda ƙarasawa wurinta ta buga tsalle haɗe da wani kukan kura ta cafko kansa ta kafa masa haƙora a kunnesa. Kamar yadda kura take yagar nama haka Raihan ta yake masa kunne guda ɗaya, tana ɗagowa ta wurgar da fatar kunnen a ƙasa ta dubi saitin idonsa tana shirin kai haƙoranta Dattijon security ya kai mata ƙafa a ƙirji cikin shammata, a cen gefe ta faɗi kafin ta miƙe ya sungumi matashin securityn da yake cikin wani yanayi ya zuba da gudu, don tana yage kunnensa nan take ya sume.

Raihan kallon mutanen wurin ta riƙa yi a haukace tana shin-shine kamar sabuwar mayyar da ta yi tozali da jariri, duk girman makarantar an rasa wanda zai shawo kanta balle a samu a kaita gida. Gabaɗaya ɗalibai taruwa suka kowa da abin da yake furtawa, wasu ma tuni suka ɗora ayar tambaya akanta dangane da mutuwar Dr Samuel. Tafiya yake da ƙafafuwansa cikin nutsuwa, daga nesa ya hango cincirindon mutane wata zuciyar har ta raya masa ya je ya ga abin da yake faruwa don tun da ya ga wannan yawan jama'ar ya san ba na lafiya ba ne. Sai dai ɗayar zuciyar ta gargaɗe shi a kan ya yi tafiyarsa saboda yana da wurin zuwa, har ya ɗauko mashin ɗinsa daga wurin masu gadi kasancewar dama wurin wani malamai ya zo kuma bai same shi ba. Yana gabda wucewa ta hanyar ya ji wani matashi yana faɗin, "Kasan Allah surar yarinyar ba ƙaramin tafiya ta yi da ni ba, ban da ina tsoron wannan ciwon nata ba ai soyayya zan ƙulla da ita ko dan na ɗebi ganima." Na gefen hagunsa ya yi guntun tsaki ya ce, "A haka za ka ƙare kullin mata ne a gabanka, ni wallahi tausayi take bani. Dubi yadda aka zagayeta ana kallo kai gaskiya ciwon iskokai bai yi ba, yanzu da tana cikin hayyacinta yaushe za a ƙare mata kallo haka. Ni wallahi duk ji nake babu daɗi yanzu da ƙanwata ce fa haka za ta yi, gaskiya lamarin akwai tausayawa tun da take aljanu bata taɓa irin wannan ba." Al'amin yana niyyar wucewa ya ji sam ba zai iya ba, don maganar saurayin nan na ƙarshe ta taɓa zuciyarsa. A gefensu ya kafe mashin ɗinsa mai maganar yana ganinsa ya jinjina hannu cikin girmamawa yana faɗin, "Allah ya taimaki babban ƙwaro." Murmushi ya yi musu ya ce, "Hamza wai dama kune a nan." Tun bai ƙarasa maganar ba suka zayyane masa duk abin da yake faruwa, kafe mashin ɗinsa ya yi ya miƙawa Hamza mukullin, a hankali ya fara kutsawa don ganin halin da yarinyar take ciki. Da mamaki ya riƙa bin ta da kallo don gani yake kamar ya san inda ya taɓa ganin fuskarta amma ya manta sakamakon fuskarta ta yi kace-kace da jini, jikinsa ba ƙaramin sanyi ya yi ganin yadda ta yaga rigar jikinta kadan ya rage ta yage gida biyu. Bakinsa ya fara motsawa yana karanto ayoyin tsari yana ci gaba da tunkarar wurinta, cikin tashin hankali ɗalibai suka fara ihu waɗanda suka sanshi suka fara ƙwala masa kira. Kai tsaye ya tunkari Raihan ko waiwaye bai yi ba, tana kallonsa ta fara ja da baya hakan ba ƙaramin mamaki ya bawa kowa a wurin ba. Ƙirjinta ba ƙaramin bugawa yake yi ba duk yadda ta so zartar da wani abu akanta ta kasa. Yana ƙarasawa wurinta ya cafki kanta da hannuwansa biyu ya fara biya suratul baƙara da ƙarfi yana tofa mata, tun tana daga tsaye ta fara layi har ƙafafuwanta suka gagara ɗaukanta. Luuu ta faɗo kansa jikinta a sake cikin fitar hayyaci, kamar haɗin baki haka mutanen wurin suka ɗauki sowa fa tafi. A hankali ya kwantar da ita cikin ciyayin da ke ƙasa wurin sai da ya dubi hagu da dama sannan ya ciro mayafin da ya naɗe wuyansa ya rufa mata a jikinta. Ganin haka ya sa tsirarin ƴan department ɗin su suka fara ƙarasowa, kallonsu ya yi duk da bai san suwaya suke karatu da ita ba ya ce, "Su waye suka san gidansu yarinyar nan?" Cikin haɗin baki wasu samari suka ce, "Intisar."Sai dai duk yadda aka duba harabar wurin babu Intisar babu alamarta."

Tun zuwan Al'amin wurin a firgice Intisar ta ja da baya, yana fara karatu ta ɓace daga wurin don wani irin tiriri ya tasamma halakata. Cikin gajiyawa da kallon da mutanen wurin suke yi masa ya ce, "Ita kaɗai ta san gidansu?" Wani lectura da ƙarasowarsa kenan ya ce, "Mahaifinta ba ɓoyayyaye ba ne, ƴar gidan Alhaji Abdullahi..." Yana tsaka da magana wata budurwa ta ce, "A unguwar sharaɗa suke mun je gaisuwar ƙanwar mahaifinta." Al'amin ya ƙarasa wurin Malamin ya ce, "Ya kamata akaita gida Malam zamanta a wurin nan bai kamata ba." A tsorace Malamin ya riƙo kafaɗar Al'amin ya ce, "Ai ya kamata ka ƙarasa ladanka kawai." Ganin a tsorace Malamin ya ke ya sa Al'amin yin jim yana nazari, ɗagowa ya yi ya kalli yarinyar da ta faɗi unguwarsu Raihan ya ce, "Ina jakarta take." Da hannu ta nuna masa wurin da jakar take, yana ƙarasawa ya ɗauko wayarta ya cire layinta ya saka a wayarsa. Number iyayenta ya duba amma duk searching ɗin da ya yi bai gani ba, yana cikin dubawa ya ga ansa My Heart. Guntun tsaki ya yi a zuciyarsa ya ɗauka ko lambar saurayinta ce, yana kira ya ji muryar Daddy ya ɗauka yana faɗin, "My baby ya school?" Al'amin bai amsa ba masa ba ya zayyane masa abin da yake faruwa da Raihan tare da shaida masa wurin da take, yana gama maganar ko jiran ta bakin Daddy bai yi ba ya cire layin ya mayar mata cikin wayarta. Jakarta ya miƙawa matashiyar budurwar sannan ya raɓa ta gefe ya wuce don shi kansa sauri yake saboda uzurin da yake gabansa, uwa-uba kuma ga jikinsa da ya ɓaci da jini kace-kace.

A ƙasa da minti goma sha biyar Daddy ya ƙarasa cikin makarantar, ikon Allah ne kawai ya kaishi don yadda yake jin sa kamar zai tashi sama. Yana zuwa ya fara kutsawa cikin mutane, da hannuwa biyu ya ɗauke ta ya saka a mota ya figi motar da gudun gaske. Kai tsaye asibiti ya wuce da ita yana zuwa likitoci suka karɓeta sai dai dole sai da buƙaci ganin statement ɗin police, Daddy yana tsaye a wurin ya yi wa DPO ɗin unguwa uku waya ya sanar masa da halin da yake ciki, kasancewar abokinsa ne ya sa ba a samu jinkiri ba nan take ya turo da police officers guda biyu.

Ƙarin ruwa da allurai aka yi mata sai allurar bacci, ta jima tana bacci sannan ta farka a lokacin Mommy na zaune a gefenta. Kallon wurin da take ta yi ta kalli Mommy da mamaki ta ce, "Mommy me ya kawo ni nan me ya faru da ni na ga jini a jikina?" Mommy ta dafa kafaɗarta ta ce, "Ba na son tambayoyin nan haka Raihan, na taimaka miki ki shiga toilet ne." Kai kawai Raihan ta gyaɗa mata, mommy ta riƙe ta sai a lokacin ta lura da abin da aka rufa mata jiki da shi. Shiru ta yi tana kallon mayafin ajiyar zuciya ta sauke ta sa hannu ta janyo mayafin tana ƙare masa kallo, lokaci ɗaya zuciyarta ta buga ƙamshin turarensa ya dokin hancinta. Kamar zautacciya ta dubi Mommy tana cewa, "Wallahi wannan ƙamshinsa ne don Allah yana ina Mommy."


Intisar tsaye ta yi a gaban abar bauta bayan ta gama zayyane mata jawabin abin da yake tafe da ita, Abar bauta cike da farinciki ta ce: "Tabbas Huzaifa ya bata baya kamar yadda Jabbul-ƙasi ya shawartar da shi, amma ke kinsan wanene mijinki bai bar Raihan gabaɗaya ba sai don cimma burinsa. Tabbas ta faɗa tarkon ƙaunar wannan saurayin sai dai ina jiya masa uƙubar Huzaifa." Mugaza ta ɓata fuska tana faɗin, "Ina murna baƙo ya tafi ashe yana bayan gari, kenan a kowanne lokaci Huzaifa zai iya waiwayar Raihan?" Abar bauta ta jinjina kawunanta ta ce, "Faɗi ki ƙara domin tafiya ya yi domin ya dawo da shirinsa." Mugaza ta jinjina kai cike da takaici ta ce, "Menene abin yi a gare ni?" Abar bauta ta yi jim sannan ta ce, "Idan kin ga Huzaif ya rabu da Raihan sai an nema mata magani kuma sai dai ta auri namiji mai tsananin riƙo da ibada, ita kanta sai ta dage da riƙo da addini. Amma kina ganin muma za mu sha?" Mugaza ta girgiza kai cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane ba me ye haɗinmu da ita?" Abar bauta ta yi mata wani kallo sannan ta ce, "Kina nufin da ke da ni da sauran ƴan ƙungiya za mu tsira ne, muddin ta samu waɗannan abubuwan da na lissafa sai sun tarwatsa shirinmu da ni da ke da ƙungiya za mu halaka komai zai wargaje mana." Mugaza ta jinjina kai don lamarin ya sakata a tsakiya wannan shi ake cewa ga ƙoshi ga kwanan yunwa.


Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgn ta wannan number 0706 206 2624



15



Jikin Magaza ba ƙaramin sanyi ya yi ba amma gani take tana iya haƙura da komai ba Huzaifanta ba, a wurin da take tsaye ta durƙushe ta zauna tana shirin yin magana Abar bauta ta katse ta da cewar, "Yanzu dabara ta rage tamu, domin shi kansa Huzaifa matuƙar ya dawo da nasara ba zai bar mu ba. Ban san mai yasa abubuwan suke neman rikice mana lokaci ɗaya ba, a kodayaushe nasara nake gani a gabana amma wannan karan tana neman kubce min." Zumbur Mugaza ta miƙe tsaye ta ce, "Ki bar min komai a hannuna ni na san yadda zan ɓullowa lamarin." Da yake kan abar bauta ya kulle nan take ta amince da buƙatar Intisar, ga Hatsabibiya da ƴan tawaga sun tafi nemowa dakin arziƙi jinin da zai sha ya ƙoshi.

Kabiru tun fatar jikinsa na damunsa har abin ya fara zame masa jiki, watarana yana zaune a ɗakinsa bayan ya gama tulawar alƙur'ani, ya samu kofi ya karanta Ayatul kursiyyu bakwai falaƙi da nasi bakwai-bakwai sai ayatulkursiyyu da Amanarrasulu uku-uku kamar yadda ya saba kullin bayan ya gama tilawar alƙur'ani. Yana gama tofawa ya sha ya shafe jikinsa babu jimawa bacci ya ɗauke shi, ya jima yana bacci sai bayan wani lokaci ya farka kai tsaye ya ɗauki buta ya wuce banɗaki don lokacin har an fara kiraye-kirayen sallar Azahar, ba ƙaramin mamaki ya yi ba na bacin da yai mai tsawo, bayan ya idar da sallah kamar wanda aka cewa ya kalli mudubi sai gani ya yi jikinsa fayau babu wannan fatar macijin, farincikinsa ne ya ƙi rufuwa sai shafa jikinsa yake yana sake duddubawa. Nan take ya faɗi ya yi wa Allah godiya bisa ni'imar da ya yi masa ta yaye masa wannan lalurar da ya yi, kamar wanda aka yi wa bushara da gidan aljanna haka Kabiru ya riƙa shige da fice cikin farinciki. Washegari har mai ƙosai ya kaiwa kuɗi ta yi wa yara sadaka don nuna godiyarsa ga Allah S.W.A.

Da mamaki Mommy ta dubi Rain don ta yi tsammanin har lokacin Raihan na cikin ciwonta, tana nan tsaye Daddy ya turo ƙofa yana ganin Raihan a zaune ya washe baki cikin jin daɗi ya ce, "My baby." Raihan ta yi wa Daddy murmushi sanna ta ce, "Daddy ina me wannan abin?" Ta ƙarasa maganar tana nuna mayafin jikinta, hannuwa ya wara mata yana faɗin, "Ban san na waye na, ina jin na wata classmate ɗin taki ce..." Turo ƙofar da Intisar ta yi ya katse maganar Daddy, Raihan ta girgiza kanta ta ce, "Wannan ba na kowa ba ne sai na mijin da zan aura wallahi Daddy ina son shi." Lokaci ɗaya Mommy da Daddy suka zaro ido don wannan baƙuwar kalma ce da basu taɓa jin ta a bakin Raihan ba, ko a baya da samari suke nuna soyayyarsu gare ta ba su taɓa ji ko ganin ta nuna alamun soyayya ga wani ba. Daddy ya yi saurin cewa, "Wane ɗan baiwa mai rabon ne wannan?" Intisar da ke gefe ta furta, "Daddy wani mai rabo ne, don nima yau sai da ta yi min maganarsa." Mommy ta mayar da kallonta ga Intisar ta ce, "Au wai da gaske ne lamarin?" Raihan ta tura baki gaba tana faɗin, "Mommy da baki yarda da abin da na gaya miki ba?" Mommy ta sa hannu a baki ta kare ta ce, "Ina na isa na ce uwar maigari ta yi ƙarya." Gabaɗaya suka saka dariya, tiryan-tiryan Raihan ta yi masa bayanin yadda aka yi suka haɗu da Al'amin, sai da suka gama sauraronta Mommy ta ce, "To Yanzu Raihan daga haka ta haɗa ku da mutum bai ce yana sonki ba sai kawai ki fara son shi, shin ma ke kin tabbatar da wannan mayafin na shi..."

"Haba don Allah Zainabu yanzu ke ba murna za ki yi ba, kina gani duk saurayin da ya fitowa yarinyar nan ƙinsa take yi yanzu ba sai mu tayata so da neman yaron nan ba." Daddy ya katse Mommy cikin faɗa. Mommy ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta furta, "Daddy ka fahimci abin da nake nufi, shin shi yaron yana sonta ne? kawai daga haɗuwa bata san halinsa ba sai ta faɗa soyayya da shi?" Daddy ya ɓata fuska ya ce, "Ki bar batun soyayya idan kuɗi na magani zan nemar mata soyayyarsa a wurinsa, zan shi ga makarantar tasu na nemi wurin da yaron yake, ke kin tabbatar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login