Showing 96001 words to 99000 words out of 157890 words
gobe in Allah ya kaimu ba sai mu dawo ba, tun da yanzu fa dare ya fara yi kar a ga mun daɗe..." Maganarta ce ta maƙale sakamakon wayarta da ta fara ringing ganin lambar Mama Hafsa ya sa ta ɗago fuskar wayarta tana faɗin, "Kun ga abin da nake gudu ko? Safna ga Mommynku tana kira." Miƙa wa Safna wayar ta yi jiki a sanyaye Safna ta ɗaga tana faɗin, "Mommy muna hanya wallahi wayata na manta..." Daga can ɓangaren Mama Hafsa ta katse Safna da cewar, "Ba na son sakarcin banza kin san ƙarfe nawa yanzu? Maza ku dawo gidan idan har ba ranki kika manta a gidan ba ai kya bari da safe ki koma ki ɗauko." Mama Hafsa na gama maganar ta katse wayar, jin irin faɗan da aka yi wa Safna ya sa Dr Hussain ya ja akalar motarsa ya juya hanyar gidan mommy. Ba su jima ba suka ƙarasa gidan, tare da yi wa Dr godiya sannan suka buga gida Kabiru ya buɗe musu.
A lokacin da Huzaifa ya tafi raka su Dr sauke ajiyar zuciya Raihan ta yi tana jin wani irin farinciki yana ratsata, ƙaunar Huzaifa ta ji na ratsa cikin zuciyarta ita kaɗai ta saki wani malalacin murmushi. Tana jin alamar shigowarsa ta ƙara jan mayafinta ta rufe fuskarta, lokaci ɗaya ta ji gabanta na tsananin faɗuwa ga wata irin matsananciyar kunyarsa da take ji. Wannan yanayi da ta tsinci kanta a ciki ya sa ta faɗawa duniyar tunani don ta tabbata rashin saboda tun da hakan bai taɓa kasancewa da ita ba ne, ya sa take jin gabanta na faɗuwa. Tana nan zauna ta ji shigowarsa ras! Ta sake ji gabanta ya sake faɗuwa har sai da ta sauke ajiyar zuwa. Babbar rigarsa ya cire haɗe da ajiye wa akan gado sannan ya ƙarasa bakin gadon yana faɗin, "My happiness bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida." Murmushi ta yi ba tare da ta furta komai ba, a hankali ya zame mata mayafin kanra haɗe da rungumota jikinsa. Shiru Raihan ta yi tsigar jikinta na tashi sakamakon jin sabon lamarin da take fuskanta daga wurinsa. Ledojin da ya ajiye ya ɗauko ya buɗe a ƙasa sannan ya kalli Raihan ya ce, "Sauko my baby." A kunyace Raihan ta ce, "Na ƙoshi." Murmushi Huzaifa ya yi ya furta, "Ashe kuwa zan ɗauko ki cak daga wurin nan." Da sauri Raihan ta sauka ƙasa ai kuwa me zai yi mata ba dariya ba, ya lukuce kumatunta tare da faɗin, "Baby kin fiye tsoro why?" Shiru Raihan ta yi tana murmushi, a hankali Huzaifa ya riƙa yagar naman kazar yana saka mata a baki. Raihan tun tana jin kunya har ta fara sakin jikinta tana karɓa suna ci Huzaifa na sake janta da hirar soyayya. Huzaifa ya iya sace zuciyar mace da kalamai don haka suka ƙara tasiri a zuciyarta Raihan ta ƙara jin wata matsananciyar ƙaunarsa ta malale birnin zuciyarta. Sai da suka ci suka yi ƙat sannan Huzaifa ya kwashe kayan wurin ya kai su cikin kitchen, Raihan na rakuɓe a gefe fargaba fal cikin zuciyarta Huzaifa ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi ya riƙo hannunta. A sanyaye ta bishi ya zauna akan gado ya tallafota jikinsa haɗe da fara shafa jikinta yana faɗin, "I really miss you wifee." Murmushin yaƙe Raihan ta yi don har lokacin gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi, tun tana ɓoye tsoronta har ya bayyana a fili don saƙwanni Huzaifa yake aikawa Raihan zafafa. Ganin duk ta firgice ya sa Huzaifa ya ja ta har tsakiyar gado, tana biye da shi tamkar raƙumi da akala. Sauka ya yi ya kashe ƙwan fitilar da ke cikin ɗakin sannan ya kunnawa musu night lamp, kallon Raihan ya yi ya fara ƙoƙarin cire rigarsa. Raihan na ganin haka ta runtse idonta jikinta na karkarwa, tana cikin wannan yanayin bata yi aune ba ta ji Huzaifa a gefenta yana yunƙurin rabata da kayan jikinta. Muryarta na rawa ta dube shi ta ce, "Hubby ba mu yi sallar nafila ba." Cikin wata irin kasalalliyar murya ya furta, "Wacce irin sallah kuma?" Huzaifa bai san ya yi wannan maganar ba domin tuni ya fara fita daga hayyacinsa. Raihan ta fara ƙoƙarin kare jikinta ta ce, "Sallar Nafila." Huzaifa ya saka hannunsa cikin jikinta haɗe yawo da su cikin sassan jikinta. Yarrr ta ji tisgar jikinta na tashi, shi kuwa Huzaifa tuni ya yi nisa gabaɗaya ya fita a hayyacinsa saboda ƙamshinta da yake sake rikita tunaninsa. Kai hannunsa kan ƙirjinta ya sake ruɗar masa da lissafi haɗe da sauke ajiyar zuciya akai-akai. Jikin Raihan sai rawa yake don haka ta kai hannunta da niyyar dakatar da shi cikin yanayin fitar hayyaci ya furta, "Kar ki dakatar da ni don Allah, domin ke mallakina ce." Hawaye Raihan ta fara yi a hankali ta furta, "Don Allah ka bari sai gobe."Sannu a hankali Huzaifa ya fara neman kusantar Raiha nan take ta ji wani irin abu yana sukarta, tun bata tanka ba har ta ji ba za ta iya shiru ba domin abin na ƙoƙarin illatar da ita. Cikin tsananin azaba Raihan ta fara ja da baya a firgice tana faɗin, "Hubby don Allah ka bari wallahi ciwo nake ji me ye a jikinsa yake sukata." Huzaifa bai bi ta kanta ta sake fisgota da ƙarfi don babban burinsa ya ga ya cimma manufarsa. Wata irin azaba ce ta riƙa ratsa cikin jikinta da sauri ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara, ta tattare ƙarfinta wuri ɗaya ta hankaɗe shi tana ja da baya haɗe da takurewa wuri ɗaya. Ta dishi-dishin hasken da bai gama garwaye ɗakin ba ta hango wasu irin gajerun gashi masu kaifi kamar ƙayoyi na tsirowa daga jikinsa. Ƙirjinta ne ya buga tsoro ya fara kamata, tana cikin wannan halin ta riski muryarsa yana faɗin: "Me ya sa kike son hana ni halalina?" Raihan na daga gefe a zaune ta ce, "Wallahi wani abu ne yake fitowa a jikinka sukata yake yi." Hannunsa ya kai ya kunna ƙwan lantarkin ɗakin, nan take haske ya garwaye ko ina. Ganin haka ya sa Raihan ta fisgo mayafinta ta rufe jikinta a kunya ce. Kawar da kanta ta yi daga kallonsa don kunyarsa take ji. Tana zaune bata yi aune ba sai jin ta, ta yi tana yawo a sama mayafin jikinta ya faɗo ƙasa. Dariya Huzaifa ya saka ba shiri Raihan ta dubi wurinsa tana faɗin, "Hubby mai yake faruwa wayyo Allah na." Suna haɗa ido gabanta ya faɗi ganin waɗansu irin baƙaƙen gashi masu tsini suna tsirowa daga jikinsa, tana shirin yin magana ta ji ya sake cewa, "Ke matata ce don haka a yadda kike haka nake son ganinki." Yana rufe bakinsa waɗansu irin Manyan ƙaho ƙwaya biyu suka fara hudowa ta tsakiyar kansa, runtse ido Raihan ta yi a firgice tana cewa, "Waye kai Dama kai matsafi ne ka aure ni ban sani ba." Tana rufe baki ta bayanta ta ji an fara shinshinarta, a hargitse ta juya baya nan take ta ci karo da shi. Wata irin gigitacciyar ƙara ta ƙwalla jikinta na rawa ta fashe da wani irin matsanancin Kuka, dafe kansa ya yi da hannu biyu sannan ya furta: "Ba na son ki riƙa dagula lissafin rayuwarki, don ko kaɗan ba zan cutar da ke ba. Ni mai ƙaunarki ne har abada don haka ki kwantar da hankalinki mu yi rayuwar farinciki." Cikin kuka Raihan ta ce, "Ni wallahi na fasa aurenka don Allah ka mayar da ni wurinsu Daddy." Huzaifa ya bushe da wata irin dariya mai haɗe da kuka, sai da ya jima yana yi sannan ya ɗaure fuska kamar bai taɓa dariya ba ya ce, "Idan kina wannan mafarkin tun wuri ki daina domin ni da ke mutu ka raba, babu wurin da ya fi miki cancanta da zama kamar nan don haka ki daina tunanin akwai ranar da za ki koma wurinsu." Wannan magana ta sake ɗugunzuma hankalin Raihan a firgice ta sake fashe wa da kuka, luuuuu ta ji ta faɗa kan katifa tana kwanciya babu jima wa ta ga Huzaifa ya faɗo gefenta cikin wannan mummunar surar.
Hannuwa biyu Raihan ta sa ta kare fuskarta tana ci gaba da kuka jikinta sai karkarwa yake kamar mai jin sanyi, Huzaifa bai damu da ganin halin da take ciki ba ya ci gaba da kai hannunsa masu ƙayoyi yana shafar fatar jikinta. Duk shafa ɗaya idan ya yi mata sai dai ta ji kamar yana zane jikinta da ƙananan allurai, ganin bata da Mafita ya sa Raihan ta sadaƙar rayuwarta ta gama zuwa ƙarshe, tana jin hannunsa ya sauka a gabanta jikinta ya ci gaba da ɓari zuciyarta ta sake tsinkewa. Huzaifa wannan karon har ya fi karon baya rikicewa don haka ya tasamman kusantarta ta kowanne hali, Raihan na ganin haka ta runtse idonta hawaye na zuba ta fara karanto duk wata addu'a da ta zo bakinta don ubangiji ya kawo mata ɗauki. Jin shiru kamar an yi ruwa an ɗauke ya sa ta buɗe idonta da mamaki take kallon ɗakin, ganin Huzaifa baya ciki zumbur ta miƙe cikin sauri ta fara laluben kayanta. A can gefen gado ta hango su hannunta har rawa yake ta yi sauri ta saka su tana waige-waige amma ko motsinsa bata ji ba, ɗaukwali kawai ta iya ɗaurawa ko mayafi bata bi ta kansa ba ta yi maza ta buɗe ƙofar ɗakin ta fara zabga gudu don fice wa daga gidan, don a yanda ta ayyana ko a ƙafa ne za ta ƙarasa gida matuƙar ta samu ta fice daga gidan. Tana zuwa bakin ƙofar da za ta sada da gate ta ci karo da tashin hankalin da ya fi na baya, tana buɗe ƙofar da niyyar zuwa gate ta ga wani ƙaton kogi tsayuwarta keda wuya wasu tafka-tafkan kadoji suka ɗago haɗe da buɗe mata baki tamkar za su haɗiye ta. Da sauri Raihan ta yi baya ta rufe ƙofar ƙirjinta na bugawa, babban abin da ya fi bata mamaki yadda aka yi cikin gidanta ya shafe da ruwa wanda a daren ranar da aka kawota ba haka ba ne. Su Daddy ne suka faɗo mata a rai, da gudu ta faɗa cikin ɗakin ta fara laluben jakarta. Daga can jikin bango ta fara jin numfashinsa sama-sama wannan ya sake ɗaga hankalinta hannu na rawa ta ɗago waya ta nemo lambar mommy, amma wayar duniya da ta yi bata shiga. Haka ta riƙa bin lambobin wayar mutane tana kira amma babu wacce ta shiga balle ta saka ran za ta ji an ɗauka.
Huzaifa da yake daga jikin bango ya dubi Raihan a ƙufule yana faɗin, "Akan wane dalili za ki yi addu'a ko kina son na haike miki ta dole." Raihan bata kalli wurinsa ba tana daga zaune ta cusa kanta cikin cinyoyinta nan take fashe da wani irin matsanancin kuka. Tana cikin kuka nasihar Mommy ce ta faɗo mata da take yawan gaya mata a duk lokacin da ta ganta cikin damuwa ta yi sallah ta yi addu'a ta kaiwa Allah kukanta, a hankali ta ɗago ta share hawayenta lokaci ɗaya ta ji tsoron komai ya fita daga ranta. Miƙe wa ta yi ta taka ta kan gado don ko kallon Huzaifa bata son yi balle ta bi ta ɓangarensa, banɗaki ta shiga bakinta ɗauke da addu'a ta ɗauro alwata. Tana fitowa Huzaifa ya fara nunata da hannu yana faɗin, "Kar ki yi abin da kike shirin yi, na gaya miki kar ki yi." Da farko tsoro ne kama Raihan har take ganin kamar Huzaifa zai iya yi mata wani abin, saboda ko kaɗan bata kawo Huzaifa ba mutum ba ne. A tunaninta yana daga cikin ƴan ƙungiyar tsafe-tsafe ya aureta ne don ya tsaface ta. A ɓangare ɗaya kuma wata zuciyar na azalzalarta akan ta je ta gabatar da nafila ta roƙi Allah ya kawo mata mafita a rayuwarta, tun da ta lura addu'a ta yi tasiri akan Huzaifa. Daga gefe ta raɓa ta fara sallah, tana sallah tana kuka a sujjada tana kaiwa ubagiji kukanta. Raihan ta yi salla ta fi a irga bayan ta idar ta zauna tana addu'a, daga gefenta ta ji Huzaifa ya zabga ƙara daga nan ba ta sake ganinsa ba. Bata saurara ba ta ci gaba da addu'a sannu a hankali ɓarawon da ya fi kowa iya sata ya yi awon gaba da ita.
Washegari.
Tun da sassafe wasu daga cikin baƙin da suka hallaci bikin Raihan suka fara haɗa kayansu, don yawanci a ranar suka ce za su tafi. Mommy zuciyarta fari ƙal da ta wayi gari da tunanin Raihan ɗin ta tana gidan mijinta, har tana ayyana a wannan lokacin tuni ta riga da ta zama cikakkiyar mace. Shi kansa Daddy zuciyarsa fes ya wayi gari da ganin an yi komai lafiya an gama lafiya ba tare da wani abu mara daɗi ya faru ba. Ko babu komai zuwa wannan lokacin hankalinsa ya kwanta tun da ya aurar da Raihan, don haka yake jin sa wasai kamar ba shi ba. Su Inno da Goggo sai hidima ake da baƙi suna yi suna masifa don ko abu kaɗan mutane suka yi ba daidai ba sun rinƙa faɗa kenan. Wani lokacin Mommy har kunya take ji har sai ta ja su ɗaki ta yi musu magana, amma suna fitowa duk irin faɗan da Mommy ta yi musu za su zayyane shi a waje. Kimanin ƙarfe goma wasu daga cikin tsirarin da ba su je gidan Raihan ba suka shirya tare da Mama Hafsa da wasu sauran waɗanda aka je da su da dare, Mommy ce ta ɗauko waya ta nemo lambar Raihan don ta kirata ta gaya mata ga baƙi nan za su ƙaraso gidanta. Sai dai a kiran farko aka tabbatar mata da wayar a kashe. Bata kawo komai ba don haka su Mama Hafsa kai tsaye suka shiga mota suka wuce unguwar Medile, Su Mama Hafsa sun zagaye unguwar da suka kai Raihan ya fi sau biyar amma ko mai fasalin kama da gidanta ba su gani ba, ganin haka ya sa suka fara jajantawa a junansu daga ƙarshe suka yanke shawarar tambayar wani Mai shagon aski, da yake sun gane shi shagonsa a farkon layin gidan Raihan yake. Sai da Mama Hafsa ta yi masa sallama sannnan ta jefa masa tambaya, "Ƙanina don Allah gidan wata amarya da aka kawo jiya muke tambaya." Ɗan jim ya yi sannan ya ce, "Amarya kuma a nan layin? Kai gaskiya ƙila ba a kwatanta muku daidai ba, amma nan kusan wata guda kenan ba a kawo sabuwar amarya ba." Mama Hafsa jin maganarsa ta ji kamar har da rainin wayo a ciki, don haka ta yi masa sallama suka ƙara gaba. A can gefen wata ƙatuwar bola ta yi parking ɗin motarta, ta dubi Hajiya Lawisa ƙawar Mommy ta ce: "A daidai wurin bolarce wallahi nake ganin kamar jiya nan nan ne daidai wurin da gidan Raihan yake." Hajiya Lawisa da ta cika da mamaki ta ce, "Ba kama ba ce, wancen shagon telan shi yake kallon gidanta kuma ga shi nan a yadda yake yanzu ma haka yake, tun da jiya har magana na yi da shi kafin mu tafi na ce zan kawo masa ɗinkin wani les. Tabbas jikina yana ba ni akwai matsala." Mama Hafsa ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Matsala babba ma kuwa, amma mu fara zuwa Fagge gidan Iyayen Huzaifa kafin mu koma gida." Tana rufe baki ta tayar da motarta kai tsaye suka wuce unguwar Fagge sauran motoci biyun da suka taho tare suka rufa mata baya.
Littafin Kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
37
Mama Hafsat tana tafe zuciyarta fal fargaba da tashin hankali, zuciyarta ce ta shiga wassafa mata tunane-tunane ban da saƙa da warwara babu abin da take yi, lokaci ɗaya zuciyarta ta karye tsora ya dirar mata tana fatan kada Allah ya tabbatar da abin da take zargi. Shiru motar ta ɗauka babu mai iya furta komai, don lamarin ba ƙaramin ɗaure kai gare shi ba. Suna tsaka da tafiya wayar mommy ta shigo wayar Mama Hafsa, gabanta ne ya faɗi ta rasa ya za ta yi don ta san idan ta ɗauka baya wuce ta ce a bata Raihan su yi magana, tun da dama kafin su taho ta gaya mata idan ta je gidan ta haɗa su za su yi magana. Ajiyar zuciya ta sauke ta ajiye wayar ba tare da ta ɗauka ba, idonta ta mayar kan titi haɗe da furta, "Hasbunallahu Wani'imal Wakeel." A ƙofar gidansu Huzaifa suka yi parking ɗin motocinsu, jiki a sanyaye Mama Hafsa ta kashe motar tare da fita tana gaba suna biye da ita, suna shiga suka ci Karo da Mahaifiyar Huzaifa ta rako baƙin da za su tafi tana yi musu su gaida gida. Ganin su Mama Hafsa ya sa ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa, ku shiga ciki kafin na shigo." Mama Hafsa yaƙe ta yi ta amsa sannan suka shiga ciki aka yi musu masauki a falo. Jigum-jigum suka yi suna nan zaune aka kawo musu ruwa amma babu wanda ya iya ɗauka ya sha. Mahaifiyar Huzaifa ce ta shiga ɗakin fuska ɗauke da fara'a tana faɗin, "Hajiya sannunku ya gajiyar hidima da jama'a?" Mama Hafsa ta yi murmushin da bai kai zuci ba ta ce, "Alhamdullah." Sai da ta gyara zamanta tana kallon Mahaifiyar Huzaifa ta ci gaba da cewa, "Hajiya dama wata magana ce tafe da mu." Mahaifiyar Huzaifa ta tattara hankalinta wurin Mama Hafsa ta furta, "Ina jin ku Hajiya." Mama Hafsa ta kashe wayarta ta jefa jaka sannan ta ce, "Yanzu haka daga unguwar su Raihan muke, mun tafi domin raka bayin Allahn da ba su samu damar zuwa jiya sun ga ɗaki ba." Mahaifiyar Huzaifa ta saka dariya haɗe da cewa, "Allah sarki ya ƴarta tawa da fatan sun tashi lafiya?" Mama Hafsa ta kalleta ta ce, "Gaskiya ba ƙalau ba." Gaban Mama ya yanke ya faɗi tana