Showing 99001 words to 102000 words out of 157890 words
shirin yin magana Mama Hafsa ta ci gaba da cewa, "Mun shafe sama da awa guda a unguwarsu Raihan amma gidanta ya ɓace mana sama da ƙasa babu shi babu alamarsa, hasalima duk wanda muka tambaya gidan da aka kawo amarya sai dai su ce ba nan unguwar ba ne." Mama Hafsa ta tsahirta cikin damuwa ta dubi Mama ta ci gaba da cewa, "Na san kin san ni ƙanwar Mahaifiyarta ce cikinmu ɗaya, hasalima tun kafin bikin nan muke zarya ni da Mahaifiyarta muna kai kayan jere. Gidan Raihan ba ɓoyayyen wuri ba ne ko a jiya da dare na je gidan mun kai yarinya amma a yau da nake yi miki magana babu gidan Raihan babu alamarsa. Hatta yarinyata a jiya da dare ta manta wayarta a gidan amma da suka koma tun a daren suka nemi gidan suka rasa, da take gaya min ban kawo komai ba na yi zaton dare ne ya sa ba su gane ba kuma abokin Huzaifa shi ya mayar da su. Shi ya sa muka ce bari mu zo mu ji yadda aka haihu a ragaya." A rikice Mama ta ce, "Ban gane ba a ga gidan Raihan ba kamar wani gidan tsuntsuwa, Hajiya wai me kike faɗa ne haka?" Mama Hafsa ta furta, "Abin da dai kika ji na faɗa Hajiya haka ne, mu kan mu muna cikin tsananin mamakin wannan lamarin." Mama ta fara ƙwalawa ƙanwarta Maryama kira, tana zuwa ta nuna mata wurin zama haɗe da faɗin: "Zauna Maryama ba zancan tsaye ba ne. Jiya ba ku kuka ɗauko amaryar Huzaifa ba?" Maryama da gyaɗa kai. Mama ta wara hannu tana faɗin, "To kin ji wai gidan Huzaifa ya shafe babu shi an neme shi an rasa." Nan take Maryama ta saka dariya don ita gani take kamar ma zolaya ce, ganin haka ya sa ran Mama Hafsa ya ɓaci nan take suka ɗauki abin da muhimmmanci don cewa ta yi dole su zo a je a ƙara duba gidan tun da sun ɗauki abin a zuwan wasan yara. Ba shiri Mama ta kira Mahaifin Huzaifa ta sanar masa halin da ake ciki tare da yayansa. Kusan mota huɗu suka yi har da ta su Mama Hafsa suka nufi unguwar su Raihan, Yayan Huzaifa ne ya kira Dr Hussain ya sanar masa halin da ake ciki, nan take shi ma ya zayyane musu abin da ya faru da su da dare na komawa da suka yi karɓo waya amma ba su ga gidan ba. Wannan magana ba ƙaramin sake ɗaga hankulansu ta yi ba, haka suka je unguwar su Raihan suka gama bulayi amma ko gida mai yanayi da na Raihan ba su gani ba. Mama Hafsa da tuni zuciyarta ta karye nan take fa fara kuka tana faɗin akan dole sai su Mama sun faɗi wurin da Huzaifa ya ɓoye musu Raihan, a ɓangare ɗaya kuma tana tsoron kada Allah ya sa ba Huzaifa aljani ne ya ɓatar da su ba ita da mijinta ba. Carko-carko suka yi a wurin da suke tsammanin nan ne daidai gidan Raihan, wani babban fili ne mai ɗauke da kangwaye sai wata ƙatuwar bola wacce da alama duka ƴan unguwar a cikinta suke zuba shararsu. Yara da manya na bakin layin ne suka fara kallonsu kowanne da alama mamakin ganinsu suka yi a tsaitsaye a wurin. Mahaifin Huzaifa ne ya ciro waya ya kira kambar Huzaif don duk cikinsu babu wanda ya yi wannan tunanin, da yake ya ware sifikar (Speaker) wayar nan take suka ji wayar tana shiga. Sai dai har ta katse ba a ɗauka ba yana shirin sake kira wayar Huzaifa da shigo, hannun Baba har rawa yake sannan ya ɗauka yana faɗin, "Huzaifa kana ji na..." Ƙit Baba ya ji an katse wayar gabaɗaya. A hanzarce Baba ya sake kiran wayar amma ɗif ya ji ta a kashe. Hankalin mutanen wurin har ya fi na koyaushe tashi, sunan tsaye saƙo ya shigo cikin wayar Baba da sauri ya shiga dubawa kamar haka haɗe da karantawa a fili.
" _Ku daina wahalar da kan ku akan sai kun nemo wurin da Raihan take domin tana tare da ni, kuma yanzu haka da ni da ita muna kallon duk abin da kuke yi, Ina kallonku a tsaitsaye wurin ƙofar gidana don haka ya kamata kowa ya kama gabansa kafin na ɓatar da ku kamar yadda na ɓatar da gidan tare da Amaryata Raihan. Ni kaɗai ni ne mamallakin Raihan ni ne mijinta na har abada HUZAIFA._"
Ɗago wa suka yi daga kallon wayar ilahirin jikinsu ban da rawa babu abin da yake yi. A ruɗe Baba ya ce, "Wai yaron nan yana da hankali kuwa an ya bai shiga ƙungiyar asiri ba? Kuna jin abin da yake faɗa kuwa?" Mama Hafsa ta sauke ajiyar zuciyar tana faɗin, "Tabbas akwai wata a ƙasa, yanzu dai kun tabbatar da abin da muke faɗa ko? Shi kenan ku dakace mu." Tana gama magana ta yi wa sauran mutanen da suka zo tare magana suka shiga motar suka wuce gida. Sai da suka kusa ƙarasa wa Mama Hafsa ta yi parking a gefen titi sannan ta ciro waya ta kira lambar Daddy, sai da ta kusa katse wa sannan ya ɗauka yana faɗin, "Maman Safna!" Mama Hafsa a sanyaye ta amsa, "Daddyn Raihan kana ina akwai maganar da nake son yi da kai." Da matuƙar mamaki Daddy ya furta, "Ni kuma? Me yake faruwa ba dai wani abu ne ya faru a gidan Raihan ɗin ba ko?" Mama Hafsa ta ce, "Ina son magana da kai da fatan baka kusa da Aunty Zainab." A gaggauce Daddy ya ce, "Kina ina yanzu ni fito wa zan yi yanzu dama." Mama Hafsa ta ce, "Muna kan titinku za ka ga motoci biyu a har tawa." Daddy bai jira cewarta ba ya katse wayar. Ko minti uku Daddy bai ƙara ba ya fito daga gidan saboda tashin hankali da fargabar abin da za a gaya masa ko mota bai fito da ita ba, Mama Hafsa ce ta fito daga motar tun bai ƙarasa wurinta ba ya ce, "Hafsa me yake faruwa da Raihan? Me ya samu mijinta ko shi ma mutuwa ya yi?" Mama Hafsa idanunta suka ciko da ƙwalla tana faɗin, "Daddyn Raihan mun rasa gidan Raihan hasali ma daga ƙarshe har wani saƙo Huzaifa ya turo wa Mahaifinsa a waya..." Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe sai da Mama Hafsa ta sanar wa da Daddy, a hargitse ya furta: "Huzaifaaaaa! Dama na faɗa sai da jikina ya ba ni wannan Huzaifan ba alheri ba ne."
Idanunsa ne suka kaɗa jawur rai a matuƙar ɓace ta dubi Mama Hafsa ya ce, "Ba ni key." A sanyaye ta miƙa masa ya karɓa ya shiga motar ganin haka ya sa sauran matan suka fito daga cikin motar suka yi carko-carko, cikin matsanancin gudu Daddy ya fita da gudun gaske. Mama Hafsa ce ta dubi su Hajiya Lawisa ta ce, "Tsaiwa a wurin nan ba za ta kaimu ba, mu ƙarasa gida mu sanar da Aunty Zainab don wannan ba maganar da za a yi shiru ba ce." Cike da gamsu wa da bayanin Mama Hafsa suka fara takawa da ƙafa don ƙarasawa, su Hajiya Shafa da suke cikin ɗayar motar suma suka rufa musu baya. Suna shiga cikin gidan mommy ta tare su fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin, "Wallahi ke dai Hafsa wayarki bata da amfani sam. Na kiraki ya fina a irga amma baki ɗauka ba." Mama Hafsa bata amsa mata ba a ƙoƙarinta na danne hawayen da yake son ziraro mata, ganin yanayinsu babu walawala ya sa Mommy ta ruƙo hannun Mama Hafsa tana faɗin, "Lafiya Hafsa me yake faruwa? Me ya faru da Raihan don Allah ki gaya min." Jin haka ya karya zuciyar Mama Hafsa ta faɗa jikin mommy tana fashe wa da kuka, a madadin Mommy ta sake tambayar abin da ya faru jikinta rawa ya fara yi nan take hawaye ya fara zubo mata, ta faɗa kan kujera daɓass ta zauna sannan ta iya furta, "Idan wani abu ne ya faru don Allah ku sanar da ni." Inno da shigowarta ɗakin kenan ta dafe ƙirji da hannuwa biyu ta ce, "Kuka wane iri nake ji da kunnuwana? Me ye kuma ake kuka kamar gidan mutuwa? Huzaifan shi ma mutuwa ya yi ne?" Shiru suka yi ba tare da wani ya iya furta komai ba, Mama Hafsa ta yi ƙarfin halin zama kusa da mommy sannan ta zayyane musu duk abin da yake faruwa. Salati mutanen ɗakin suka ɗauka Inno da Goggo kuwa tuni suka fashe da kuka, Mommy na zaune a wurin da take kasa motsa wa ta yi lokaci ɗaya ta ji kanta ya sara, wata irin juya na ɗaukanta ƙirjinta na wani irin buga wa da ƙarfi, ba su yi aune ba sai gani suka yi luuuuuu ta faɗa jikin Mama Hafsa a sume. Hankali a tashe Goggo ta faɗa kan Mommy tana kuka da sauri mutane suka janye ta aka shiga yayyafa wa Mommy ruwa amma ko kaɗan bata motsa ba, da sauri Mama Hafsa da sauran mutanen wurin suka taimaka aka fita da Mommy aka saka ta a mota, ganin wannan lamarin ya ƙara tsinka zuciyar Kabiru, duk da bai san abin da ya faru ba amma jikinsa yana ba shi wani abu ne ya faru da Raihan don ko a daren da aka kaita kwana ya yi bai yi bacci ba sai gabannin asuba, kuma ko da bacci ya ɗauke shi wani irin mummunan mafarki ya yi da ita. Jikinsa har rawa yake ya ƙarasa bakin falon bayan fitar da mommy daga gidan, jin kukan su Inno ya ƙara dagula lissafinsa har ya manta da matsayinsa na mai gadi ya faɗa cikin falon hankali a tashe yana tambaya. Inno sai da ta sharce majina ta ce, "Kabiru yanzu dama yaron nan Huzaifa azzalumi ne ba mu sani ba? Wai an nemi gidan Raihane an rasa ya ɓace da ƴar mutane ɓat kamar masu layar ɓata." Ƙirjinsa ne ya buga jikinsa ya fara karkarawa a firgice ya kuma tambayar halin da ake ciki, su Inno suka yi masa bayani dalla-dalla kamar yadda Mama Hafsa ta yi musu. Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka ya fice daga falon ya koma ɗakinsa ya zauna, shiru ya yi ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba nan take kansa ya fara juyawa lokaci-lokaci ya fara furzar da iska mai zafi.
Daddy ko da ya je ya shafe minti talatin a tsaye wayarsa ya ciro ya kira lambar Dr Hussain ko sallama bai yi masa ba ya ce, "Wallahi duk wurin da abokinka ya kai min ƴata sai ya fito min da ita, na rantse da Allah sai ya fito min da ƴata tun wuri ka gaya." Daddy bai jira cewar Dr ba ya katse wayar sannan ya kira D.P.O abokinsa ya sanar masa halin da ake ciki. Suna gama waya wayar Daddy ta fara ƙara Mama Hafsa ce a nan take sanar da shi halin da Mommy take ciki, da asibitin da suke ake bawa Mommy agajin gaggawa don har lokacin bata farfaɗo ba. Daddy bai gama jin abin da Mama Hafsa take faɗa ba ya katse wayar tare da shiga mota ya fita a guje, kafin Daddy ya ƙarasa asibitin saboda irin gudun da yake yi har sai da ya bige wani ɗan makaranta don ma Allah ya taƙaita yaron bai ji ciwo sosai ba. Yana shiga asibitin likitoci suna shiga yi masa bayanin zuciyar Mommy na gabda buga wa saboda matsananciyar damuwar da ta faɗa lokaci guda.
Raihan ba ita ta farka ba sai bayan da gari ya fara yin haske, kukan waɗansu tsuntsaye ne ya fara tashinta. A hargitse ta miƙe lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta fara hakaito mata da abin da ya faru, da sauri da fara dube-dube tana neman ta wurin da Huzaifa zai ɓullo mata sai dai babu shi babu alamarsa. Banɗakin ɗakin ta fara nema amma abin da ya bata mamaki ƙofarsa ta shafe tamkar ba a taɓa yin sa a wurin ba. Zarya ta fara yi a ɗakin tana neman ruwan da za ta yi alwala da shi, sai dai hatta ruwan jarkokin da Huzaifa ya kawo mata a daren ranar babu su ta neme su ta rasa. A hankali ta buɗe ƙofar ta fita zuwa falo, cikin sanɗanta ta fara dube-dube a cikin gidan amma sama da ƙasa da ta duba babu ruwa, kogin da ta gani a daren ranar ne ya faɗo mata da sauri ta ƙarasa wurin tana son buɗe ƙofar tsoro fal zuciyarta, ta jikin ƙofar ta leƙa amma sai gani ta yi kogin ya koma wawaken ƙaton rami. Dawowa cikin gida Raihan ta yi ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kuka ba zai kaita ba ya sa sake miƙe wa ta fita wurin ramin nan, da niyyar zura hannunta ta fara yin taimam. A ɗarare ta zura hannunta ta fara taimama tana shirin gamawa ta ji wani abu ya riƙe hannunta gam, a gefe ɗaya ga wani irin gurnani da yake tashi. Ƙara Raihan ta ƙwalla haɗe ta fisgar hannunta da ƙarfi, jini ne ya fara zuba sakamakon gefen ɗan yatsanta da wannan ƙanƙanuwar hallita ta kaiwa cizo. Jiki na rawa Raihan ta rufe ƙofa ta koma ciki, ganin jinin na zuba ya sa ta yaga ɗankwalinta ta ɗaure wurin. Zuciyarta na rawa ta gabatar da sallar asuba a lokacin tuni gari ya waye, wani abin mamaki har ta fara jin hayaniyar mutanen unguwar da yaransu. Tana nan zaune tunanin su Mommy ya faɗo mata da sauri ta ɗauki wayarta ta shiga kira amma fir ta ƙi shiga, hawaye ne yake bin kuncinta ɗaya bayan ɗaya, ga wata irin addababbiyar yunwa da take cinta kasancewar ranar ɗaurin aurenta ban da ruwan tea babu abin da ta iya sha saboda fargaba. Tana nan zaune ta ji turowar ƙofa da sauri ta matsa ta takure wuri ɗaya, Huzaifa ta ga ya shigo cikin ƙananan kaya ba ƙaramin kyau ya yi mata ba duk da tsoronsa ya riga da ya cika zuciyarta, amma da ta ƙare masa kallo sai take ganin kamar ba shi ne Huzaifan da yake son hallaka a daren jiya ba. Ƙirjinta ne ya buga da ya fara tunkarota, hannu ta ɗaga masa tana faɗin, "Don Allah ka mayar da ni gida." Murmushi ya sakar mata sannan ya tsugunna a ɗan nesa da ita ya ce, "Raihan!" Ɗagowa ta yi tana kallonsa ba tare da furta komai ba. "Kin san irin ƙaunar da nake yi miki kuwa? Ina yi miki soyayyar da ko iyayenki ba sa yi miki ita. Ni Huzaifa na rabu da kowa nawa akanki me ya sa ba za ki haƙura da su mu yi rayuwa mai ɗore wa cikin farinciki ba?" Huzaifa yana rufe baki Raihan ta fara jin alamar tsayawar motoci, waigawa Huzaifa ya yi ya saki wani shu'umin murmushi, karaf Raihan ta ji muryar su Mama Hafsa. A zabure ta miƙe ta fice falo haɗe da bankaɗe labulen window ta tura ƙofar windon da ƙarfi tana ƙwala mata kira.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
38
Ganin babu wanda ya waigo balle ya nuna alamun ya ji kiranta ya sa ta cire takalminta ta jefa a saitin wurin da Mama Hafsat take tsaye haɗe ta ƙwala mata kira, amma ko alamin juyo wa Mama Hafsa bata yi ba. Huzaifa yana daga wurin da yake tsugunne ya saki murmushi haɗe da cewa, "Da ma kin bar wahalar da kan ki domin babu wanda zai ji ki balle ya waiwayo gare ki, saboda wurin nan da kike yana da kamceceniya da dajin ƙare kukanka." A wurin Raihan ta durƙushe tana zubda hawaye mai zafi, Huzaifa yana son ƙarasawa wurinta amma wani irin turiri yake ji a duk lokacin da ya kusanceta. Takawa ya yi ya tsaya daga bakin ƙofar ya ce, "Kina da buƙatar abinci ne?" Cikin kuka Raihan ta girgiza masa kai haɗe da cewa, "Ka dubi girman Allah ka mayar da ni wurin iyayena." Guntun tsaki Huzaifa ya yi ya juya a fusace yana faɗin, "Idan na mayar da ke tabbas na san ta kowanne hali sai sun raba ni da ke ko kuma su hallaka ni, wallahi da na mayar da ke gara na hallaka ki kowa ma ya huta." Yana gama maganar ya fice daga wurin, jin maganar Huzaifa ta ƙara hargitsa tunaninsa cikin tashin hankali ta furta, "Innalillahi wa'inna'ilahirraji'un." Jin tashin motar su Mama Hafsa ya sa Raihan ta sake leƙa wa ta windo sai kawai ta kifa kanta ta wurin tana zubda ƙwallah. Raihan haka ta ci gaba da zama a wurin tana zuba wa sarautar Allah ido, don duk abin da yake faruwa a harabar wurin tana kallo har waɗansu yara ta gani masu buhu a hannu suna tsince-tsince a wurin gidan nata amma kiran duniya ta yi musu babu wanda ya amsa mata. Ta jima a wannan yanayin kamar almara bayan wani lokaci ta ji muryar Daddy, wannan karon a haukace ta ƙwallah ƙara haɗe da bubbuga ƙauren windon amma ko kaɗan Daddy bai ji ba. Tana ji tana gani Daddy ya ja motarsa ya bar wurin, wannan karon zama ta yi a wurin daɓas don tuni hawaye ya ƙauracewa idonta ta ji gara ma mutuwarta da rayuwarta.
Damuwa goma da ashirin ce ta mamaye zuciyar Daddy, ban da zarya a cikin asibitin babu abin da yake yi. sauƙin da ya ji da likitoci suka samu damar ceto rayuwar Mommy, amma sun sake jadadda masa zuciyarta tana barazanar bugawa. A ranar tawagar D.P.O suka ƙarasa unguwar su Huzaifa suka kwashe iyayensa domin zargi ƙururu ake yi akan Huzaifa na ɓatan Raihan. Duk ciwon da Raihan take da shi sai da Daddy ya zayyana wa D.P.O tas sannan ya bashi labarin yadda aka yi Dr Hussain ya rako Huzaifa har cikin gidansa, nan take zancen ɓatan Raihan da Huzaifa ya watsu a cikin garin Kano da sauran garuruwa daga ƙasar Nigeria. A