Showing 78001 words to 81000 words out of 157890 words
wuce ɗakinta ta turo ƙofa, kan gado ta faɗa lokaci ɗaya ta saki wani irin marayan kuka. Sai da ta yi mai isarta ta tashi zaune ta takure wuri ta fara ayyana irin rayuwar da suka yi da Salim, ta jima ita kaɗai a zaune gabaɗaya rayuwarta ta yi mata zafi. Lokaci-lokaci take share hawayenta tana yi wa Salim addu'a. Tana nan zaune ƴan jarida suka yi wa gidan Iyayenta ƙawanya, duk yadda mommy ta so hana su naɗar rahoton Raihan abin ya ci tura sai da suka yi mata hikima har ta amince musu. A falo Raihan ta same su a zaune suna ganinta kowanne ya fara gyara abin naɗe sautinsa tare da faɗin, "Sannu Hajiya ya ƙarin haƙuri." Da ido Raihan ta bisu hawaye na zuba, nan take suka fara jero mata tambayoyin abin da yake tafe da su. Sai da ta share hawayen idonta sannan ta ce, "Tabbas na yi babban rashi saboda Salim yana ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da shi ba, na yi rashin masoyi na rasa Salim a lokacin da nake tsananin ƙaunarsa. Ni na san irin abin da nake ji a zuciya har yanzu gani nake kamar tatsuniya ake gaya min akan mutuwar Salim, kunnuwa na jiyo min sautinsa amma mutane gaya min suke Salim ya mutu, gabaɗaya na rasa wanda zai ce min Salim yana raye ko na ji daɗi har kuma kuna ganin Salim ya rasu ko..." Raihan bata ƙarasa magana ba kuka ya ci ƙarfinta da sauri ta faɗa ɗakinta. Kalaman Raihan ba ƙaramin sanyaya musu jiki ya yi ba, daga haka suka yi wa su Mommy gaisuwa sannan suka kama gabansu. Haka taron gidajen bikin ya koma gidajan zaman makoki. Kullin sai Mommy da ƴan uwanta sun je gidan su Salim dukda bata jimawa saboda ba ta son barin Raihan ita kaɗai a gida.
Sannu a hankali kwanaki suka riƙa shuɗewa har aka yi sadakar bakwai ɗin Salim, Sai dai har a lokacin Raihan bata daina zubar hawaye akan mutuwar Salim ba. Ta rame sosai idan ka ganta sai ka rantse kwanciya ta yi matsananciyar jinya, hatta abinci sai da Mommy ta yi mata da gaske sannan Raihan take ɗaukan ruwan tea ta sha. Bata da aiki sai zaman ɗaki don kodayaushe tana ɗaki a kwance, sai dai idan mommy ta ji shirun ya yi yawa sai ta shiga ɗakin ta riƙa janta da hira don kore mata damuwa. Kamar kullin tana zaune a ɗaki ta idar da sallar Azahar tana zaune tana jan lazumi wayarta ta fara ringing. Kallon lambar take don bata san da ita ba, amma sai ta yi tunanin ko masu yi mata gaisuwa ne. Murya ba kuzari ta furta, "Salamu alaikum." Sautin muryar da ta ji an amsa mata ne ya sa ta sakin carbin hannunta, zumbur ta miƙe tsaye baki na rawa ta ce, "Don Allah kaine? Salim muryarka nake ji." Daga can ɓangare aka yi dariya kamar yadda salim yake ma'abocin fara'a sannan ya ce, "Kina mamaki ne Cutie ni ne man ko baki yarda ba." Jiki na rawa ta ciro wayar daga jikin kunnenta tana kallon lambar sannan ta fita da gudu tana ƙwala wa Mommy kira. A lokacin Mommy na kan dianning tana cin abinci jin kiran Raihan ya sa ta miƙe wa tana faɗin, "Lafiya Raihan?" Da sauri Raihan ta miƙa wa Mommy wayar ta ce, "Salim ne ya kira ni wallahi Mommy muryarsa na ji." Rass gaban Mommy ya faɗi, don ta san duk wanda ya mutu ya mutu har abada ba zai sake dawo wa ba, ganin har lokacin wayar na harbawa ba a katse ba ya sa mommy ta karɓi wayar jiki a sanyaye ta kanga a kunnenta. Kai wayar kunnenta ya yi daidai da ta ji muryarsa ta ce, "Cutie ba na jin ki sosai bari na sake kira." Gabanta ne ya sake tsinkewa ya faɗi sakamakon jin muryar Salim raɗau a dodon kunnenta, hannun Raihan har rawa yake ta fisgi wayar a hannun Mommy ta sake kira ta kara a kunne amma fir wayar ta ƙi shiga. Da sauri ta kalli mommy ta ce, "Don Allah mommy muryar wa kika ji idan ba Salim?" Hawaye ne ya fara zubo mata ta ci gaba da cewa, "Wallahi dama na faɗa muku Salim bai mutu ba Allah muryarsa ce." Lokaci ɗaya Raihan ta rikice wa Mommy ban da kuka babu abin da take yi, Mommy daskare wa ta yi a wurin saboda ita kanta abin ya girmewa tunaninta. A jiyar zuciya ta sauke ta ja hannun Raihan zuwa Falo ta zaunar da ita, sai ta da kalli Raihan sannan ta ce: "Raihan ki kwantar da hankalinki. Na fahimce ki amma ki bari Daddynki ya dawo za mu yi magana da shi, tabbas ni ma muryar Salim na ji." Da sauri Raihan ta fara gyaɗa kai tana faɗin, "Mommy kin dai yadda da magana ta ko?" Mommy ta bi Raihan da kallon tausayi don ta kwantar da hankalinta ya sa Mommy ta gyaɗa mata kai haɗe da cewar, "Na yadda Raihan shi ya sa na ce ki kwantar da hankalinki." Inno da take gefe ta kalli Mommy ta riƙe haɓa ta ce, "Alkazzibu ƙarya dai haramun ne." Lokaci ɗaya Mommy da Raihan suka waigo wurin Inno, Inno ko a jikinta ta watsa musu harara ta ce, "Gaskiya Zainabu kin ba ni kunya. Yanzu saboda Allah ki zauna ki jirkice wa yarinya ƙarya, ta ina matacce yake iya dawowa? Ni kam ko lokacin da Alhaji Babba ya rasu na kusa shekara kullin sai na yi mafarkinsa amma ko kaɗan ban taɓa tunanin zai dawo ba." Raihan wani ƙululun baƙin ciki ya kamata ta dubi Inno a ƙufule ta ce, "Don Allah Inno ki fita a harkata, yanzu dai ban sa da ke ba." Inno ta wara hannuwa sannan ta ce, "Ko ki sa da ni ko karki sa da ni ke kika sani, amma ni da kika ganni babu abin da zai hana ni nema miki magani don na lura mutuwar yaron nan so take ta zautar da ke. Saboda Allah mutuwar miji bata da daɗi amma keda ma baku shaƙu ba, ko zaman dare fa baku yi ba ni da nake miki fatan nan da wasu ƴan watanni Allah ya kawo miki wani mijin ki yi aurenki." Raihan na jin haka ta fashe da kuka cikin ɓacin rai ta ce, "Wallahi ba zan sake aure ba kuma wallahi kika kawo min wani maganin sai na matse ki kin shanye shi tass." Mommy ta rufe mata baki cikin raɗa ta ce, "Don Allah ki daina biye maganganun tsofaffin nan kamar ba ki san halinsu ba?" Raihan ta share hawayenta tana shirin yin magana suka riski muryar Goggo tana faɗin, "A yau ba sai gobe ba dama na yi niyyar zuwa Albasu don na karɓo wa Yarinyar nan taimako, tsorona Allah tsorona kar yarinyar nan ta fara gane-gane na shiga uku." Shiru ne ya biyo baya mommy ta faɗa nazari don ita kanta ta fara zargin akwai lauje cikin naɗi, don babu tantama mutuwar Salim na son jefa Raihan cikin wani yanayi. Miƙe wa ta yi ita da Raihan suka wuce suka bar su Inno suna ta zancen su akan nema wa Raihan magani.
Da daddare bayan Daddy ya dawo yana tsaka da cin abinci ya dubi Mommy ya ce, "Mommyn Raihan na fahimci akwai abin da yake damunki tunanin me kike yi haka?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Daddyn Raihan ka gama cin abinci magana nake son mu yi." Ajiye spoon ɗin hannunsa ya yi ya zuba mata ido a nan ya sake karantar irin damuwar da take ciki, ganin irin kallon da yake yi mata ya sa ta saki murmushin yaƙe don ta san matuƙar ta sanar da shi abin da yake faruwa ya bar cin abincin kenan. Tana tsaka da tunani ta riski muryarsa na cewa, "Me yake faruwa Zainab?" Murmushi ta sake yi a karo na biyu ta ce, "Alƙwari na ɗauka sai ka kammala komai zan sanar da kai, kuma karka ɗaga hankalinka don ba wani abin damuwa ba ne." Daddy har lokacin kallon Mommy yake don kar ya yi mata musu sai kawai ya ci gaba da cin abincin ba don yana jin daɗinsa ba saboda yanayin da ya gani a tattare da ita. Bayan ya kammala cin abinci Mommy ta dube shi ta ce, "Daddyn Raihan! Don Allah Salim yana da ɗan uwa ne?" Da mamaki Daddy ya dube ta ya ce, "Kamar yaya ɗan uwa?" Mommy ta gyaɗa masa kai tana kallonsa. Girgiza mata kai ya yi sannan ya ce, "A iya sanina Salim shi kaɗai ne namiji a wurin Mahaifinsa amma me ya sa kika yi wannan tambayar." Wayar Raihan da ke gefe ta ɗauko ta fara dubo lamabar da aka kira Raihan da ita ta miƙa masa ta ɗora da cewa, "Ɗazu wani ya kira Raihan a wayarta mai irin muryar Salim kai hatta irin kalaman da Salim yake mata sai da ya furta." Murmushi Daddy ya yi ya ajiye wayar Raihan ba tare da ya kalli lambar ya ce, "Haba Zainab na ɗauka ke za ki riƙa kwantar wa yarinyar nan hankalinta amma sai kike ƙara ɓullo hanyar da za ki tayar mata da hankali."
"Ba da wasa nake ba Daddyn Raihan saboda tun ina ƙarama na san mutuwa na san zafinta, duk wanda ya mutu ya tafi kenan har abada ba dawowa. Da kunne na ji abin da nake gaya maka ba Raihan ce ta sanar da ni ba, da ita ce kasan ba zan taɓa yadda ba." Da sauri Daddy ya ɗauki wayar Raihan ya ƙurawa lambar ido yana kallo, lokaci ɗaya ya danna kira amma fir taƙi shiga. Miƙe wa ya yi tsaye ya fara kaiwa da kawowa a dakin, Mommy ta ƙarasa wurinsa ta riƙo hannunsa sannan ta ce, "Ni ina ganin mai zai hana ka yi report wa ƴan sanda idan ya so sai su bibiyi layin don ganin wanda yake aikata haka." Lokaci ɗaya ya aminta da maganar Mommy har ya ciro waya zai kira D.P.O. abokinsa, sai kuma Malam Usman ya faɗo masa, don tun ranar da za a sallami Raihan ya ke sanar da su duk wani abu da za su gani na almara ko ɗaure kai su sanar da shi. Lambar Malam Usman ya kira ba a jima ba aka ɗauka, sai da Malam ya sake yi masa gaisuwar rashin Salim sannan Daddy ya zayyane masa duk abin da yake faruwa. Malam Usman jim ya yi sannan ya ce, "Tun bayan rasuwar yaron shin tana yin wasu abubuwa ko tana ganin wasu abubuwa na ban al'ajabi." Daddy ya yi shiru yana nazari sannan ya ce, "Eh to, tana yawan ce mana tana jin muryar Salim ya yi mata magana amma bayan haka babu wani abu da take gani ko ji sai yau da wannan kiran ya shigo cikin wayarta." Malam Usman ya ce, "Babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji, insha Allah akwai magungunan da zan sake haɗa mata, amma duk da haka sai ta sake dage wa da Addu'a kuma a daina barinta a cikin kaɗaici ko ta riƙa keɓewa wuri ɗaya. Idan da hali a riƙa yawan zama da ita kuma tana yawaita sauraron karatun alƙur'ani." Daddy da Malam Usman sun jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama akan zuwa wayewar gari Daddy zai je ya amsowa Raihan maganunguna.
Sannu a hankali duk wasu abubuwa da Raihan take ji sai suka fara ja baya, Mommy na bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta kawar wa da Raihan damuwa. Inno da Goggo kowaccensu sai da ta karɓo wa Raihan turare da maganin sha da wanka. Sai da Mommy ta yi da gaske sannan Raihan ta karɓa don ba ƙaramin haushin su Inno take ji ba, musamman idan ta tuna zancen sake wani auren da suke yi mata. Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da gangarawa kwanaki suka riƙa wucewa watanni suka shuɗe, Raihan ta rage damuwar da take ciki sosai tana walwalarta kamar kowa sai dai lokaci-lokaci Salim yana faɗo mata a rai. A duk lokacin da ta tuna shi tana jin ba daɗi sai dai ta yi masa addu'a, amma har lokacin gani take babu wani namiji da zai iya maye gurbin Salim don haka ko maganar yin aure bata son ji. Zumunci mai ƙarfi ne ya sake shiga tsakanin gidansu Raihan da gidansu Salim, ƙannensa na matuƙar ganin girmanta suna ganin mutumcinta. Lokaci-lokaci sukan kai mata ziyara musamman Farida da ta ƙwallafa ranta a kan Kabiru mai gadi.
Bayan shekara biyu.
Abubuwa da dama sun faru ciki har da auren Fatima ƙanwar Salim, Raihan ta haɗa mata sha tara ta arziƙi don su Fatima ba su yarda ita ba. Ranar da suka je Dinner bikin su Fatima ita kaɗai ta riƙa kallonsu tana tuna lokacin ta su dinner, hawaye ta ji ya zubo mata a fakaici ta goge idonta jiki babu ƙwari ta miƙe ta je ta yi wa su Fatima liƙi sannan ta wuce gida. A ƴan kwanankin haka ta yi ta fama da tunanin Salim sai daga baya ta watsar da komai ta fauwala wa Allah lamuranta. Azumi saura sati ɗaya Daddy ya biya musu zuwa Dubai daga nan za su wuce umara ƙasa mai tsarki, don Raihan da kanta ta yi wa Daddy magana akan za ta fara sarin kaya daga Dubai zuwa Nigeria, bai hanata ba don ta nuna masa zamanta haka ba daɗi kuma aikin gwamnatin da ta ci buri a baya duk ya fice mata a ka. Tare da su Inno suka tafi gidan sai Kabiru kadai suka bari, kwanansu biyu a ƙasar Dubai da daddare Raihan da Mommy sun fita zuwa wani store don yin siyayyar abin da ba a rasa ba, kwatsam suna gabda fitowa kamar almara Raihan ta ganta hannunta ɗauke da wasu ƙananan yara biyu mace da namiji. Cikin tsananin mamaki ta furta, "Intisar!" Ke nake gani ko idona ne?" Intisar cike da mamaki ita ma ta dubi Raihan ta ce, "Raihan ke ce?" Rungume juna suka yi Mommy ta ja hannun yaran wanda da alama ƴan biyu ne mace ba za su wuce shekara ɗaya da rabi-rabi ba. Raihan ce ta fara ɗagowa ta dubi Intisar ta ce, "Yanzu Intisar kina duniyar kika guje ni an ya amintaka ta ce haka?" Intisar ta yi murmushi ta ce, "Raihan ba za ki gane ba, abubuwa da dama sun faru bayan rabuwarmu labari ba zai yuwu a nan ba sai mun zauna." Raihan ta juya wurin yaran Intisar ta rungumo su tana jin wata irin ƙaunarsu, ido ta ƙura musu tana son sanin inda ta san fuskarsu amma ta kasa. Ɗaukan macen ta yi ta ce, "Amma twins ne ko Intisar?" Intisar ta yi murmushi ta ce, "Su uku ne Salma na hannun Daddynta." Kafin Raihan ta yi magana wani sihirtacen ƙamshinsa ya doki hancinta, waigawa ta yi don ganin mai wannan ƙamshin da ko a mafarki ta ji shi ba za ta manta ba. Karaf idonta ya sauka akansa wanda ya yi daidai da faɗuwar gabanta har ya sa jikinta ya ɗauki tsuma kamar mazari. Bakinta na rawa ta furta, "Salim! Don Allah kai ne?" A lokacin Mommy ta kai idon wurin cikin tsananin mamaki take bin sa da kallo don ko makaho ya shafa zai tabbatar da wannan Salim ne ko tantama babu.
Salma da ke hannunsa ya miƙawa Intisar ba tare da dubi wurin da Raihan take ba ya ce, "Cutie kin san Salma ta fi kowa rigima kika haɗa ni da ita." Intisar karɓar Salma ta yi tana murmushi ta ce, "Hubby ga aminiyata Raihan da nake gaya maka, yau Allah ya yi mun sake haɗuwa." Da murmushi ya dubi Raihan wacce ta kafe shi da ido ya ce, "Hey Aminiyarmu ina kika shiga kullin Cutie sai ta min hirarki." Hawaye ne ya fara zarya a fuskar Raihan ta furta, "Salim baka gane ni ba ne?" Da mamaki ya dube ta Intisar ma ta kalle ta sannan ta ce, "Salim kuma? Waye kuma Salim? Daddynsu Salma ne fa Raihan ko kin san shi ne." Kuka ne ya kwace wa Raihan ta ce, "Wallahi mijina, don Allah Salim ka gaya mata."
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
30
Mijin Intisar da ke tsaye cikin mamaki ya ce, "Mijinki kuma? Cutie kin ji me take faɗa kuwa?" Da sauri Mommy ta riƙo hannun Raihan ta ce, "Raihan ki nutsu me yake damunki kina hauka ne?" Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Don Allah mommy kin gani ko maganaina ne suke yi mini gozo? Kina ganin abin da nake gani ke ma kin ga Salim ko?" Intisar fuska ɗauke da damuwa ta ce, "Mommy don Allah me yake faruwa waye kuma Salim." Ganin mutane sun fara kallonsu saboda hayaniyar da Raihan ta fara yi ya sa mommy ta ce, "Mu fita waje don kar idon mutane ya yi mana yawa." Ba musu Intisar ta riƙe hannun yaranta Maigidanta ya riƙo mata ɗaya Raihan kuma tana riƙe a hannun mommy. A wurin motarsu Intisar suka tsaya har lokacin Raihan bata daina kallon Mijin Intisar ba, Mommy ta ciro wayarta ta nunawa Intisar hotunan auren Raihan ta ce, "Salim da kika ji Raihan tana faɗa yana tsananin kama da mijinki amma suna da bambamci saboda Salim yana da siririn tsagu a goshinsa. Haka Allah yake lamarinsa ya yi mutane masu kamanni iri ɗaya kuma mazauna wuri mabambamta." Tun daga farko har ƙarshe sai da Mommy ta bawa Intisar labarin abin da ya faru a auren Raihan, Intisar na gama jin labarin ta fara ruwan hawaye. Intisar ta dubi Raihan fuska ɗauke da hawaye ta ce, "Bestie a ranar da abin nan ya faru da ke a ranar na samu waya daga gida cewar Mahaifina ba shi da lafiya. Ban yi ƙasa a gwiwa ba na wuce garinmu don yananyin ciwonsa ance yana jin jiki. A ranar sa na je a ranar Allah ya yi