Showing 111001 words to 114000 words out of 157890 words

Chapter 38 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

150

yi mai isarta sannan Malam ya miƙa mata wani hankici ta karɓa ta goge hawayenta. Ido ya zuba mata yana sake karantar yanayinta ya ce, "Me yake damunki?" Raihan ta sake goge hawayen da ya zubo mata sannan ta furta, "Babu abin da yake damuna Abba, haka kawai nake jin ɓacin rai sai na yi kuka nake jin daɗi." Jinjina kai Malam ya yi ya ce, "Yaushe kika fara jin haka?" Shiru Raihan ta yi kamar mai nazari ta ce, "Na ɗan kwana biyu." Karɓar katin hannun Raihan ya yi da kansa ya wuce ya haɗo wa Raihan magunguna masu yawa ya dawo ciki ya bata, kowanne sai da ya yi mata bayaninsa dalla-dalla. Godiya Raihan ta yi har ta sake miƙe wa ta zauna ta ce, "Daddy babu teller..." Katse ta ya yi da cewar, "Gidanku kin ji Raihan, fice ki bani wuri kar na karye ƙafarki." Dariya Raihan ta yi sosai ta fice daga office ɗin don babu yadda za a yi ka haɗu da Malam baka yi dariya ba saboda shi mutum ne mai barkwanci. Tana fito wa ta ji shi ma ya fito yana ƙwala wa Al'amin kira, ƙarasowa ya yi wurinsu Raihan. Malam ya dubi Raihan ya ce, "Za ka raka ta gida duk da a motarta ta zo, amma ban lamunce ta tafi ita kaɗai va saboda bata jin daɗi. Idan za ka dawo sai ka hau Napep." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Daddy da wuce wa gida zan yi fa." Malam ya wuce ƙofar Office ɗin sa sannan ya ce, "Ni dai na ce ka raka ta gida. Dududu minti nawa ne ka kaita gida ka dawo." Al'amin wuce wa ya yi wurin motar ba tare da ya furta komai ba, a sanyaye Raihan ta ƙarasa wurinsa. Hannu ya miƙa mata sai kawai ta tsaya tana kallonsa don bata fahimci abin da yake nufi ba. Ganin ta yi shiru ya sake harzuƙa shi ya dube ta ya ce, "Ko ba da key kika tuƙo motar ba?" A duburburce Raihan ta fara duba jakarta hannu na rawa ta miƙa masa key, da sauri ya buɗe motar ya shiga. Jikin Raihan na rawa ta buɗe motar ita ma ta shiga, da gudun gaske ya figi motar suka fice daga harabar wurin. Gaban Raihan ban da faɗu wa babu abin da yake yi, sai dai duk abin da Al'amin yake yi ko kaɗan bata ji haushinsa ba hasalima sai ta riƙa jin haushin kanta don gani take kamar ita ta yi abin da ya harzuƙa shi. Suna hawa kan titi ta ji ya furta, "Ta ina za mu bi?" A rikice Raihan ta riƙa kwatanta masa saboda muryarsa ba ƙaramin rikita masa lissafi ba, suna zuwa ƙofar gidansu Raihan ya faka motar ya fito ba tare da ya furta mota komai ba. A tunanin Raihan ko fita yin wani abu zai yi, jin shirun ya yi yawa ya sa Raihan fitowa daga motar sai dai tana fito wa ta hango Al'amin a can ƙarshen layinsu har ya kusa zuwa titi. Wani irin gwauron kuka ne ya zo mata ta kafa kanta a jikin motarta tana rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Kabiru na daga cikin ɗakinsa da farko ya ji tsayiwar mota a tunaninsa Raihan ce ko Daddy, amma jin shirun ya yi ya wa ya sa ya yi tsammanin ko wuce wa aka zo yi. Jin kuka sama-sama ya sa ya tako a hankali ya zare sakatar gidan, turus ya yi yana kallon Raihan sannan ya fito yana waige-waige jiki na rawa ya furta, "Waye ya taɓa ki?" Sai a lokacin Raihah ta ɗago fuskarta har ta yi jawur saboda kuka, ganin yanayin da Raihan take ciki ya sake ɗaga hankalin Kabiru. Jin irin tambayar da ya yi mata ya sa ta sake rushe wa da kuka, takawa Kabiru ya fara yi yana dube-dube amma unguwar shiru take ko tsuntsaye babu. Dawo wa ya yi gabanta a fusace ya buga mata tsawa yana faɗin, "Na ce miki waye? Wanene ya taɓa ki." Zaro ido Raihan ta yi don tun da take da Kabiru abin da bai taɓa yi ba kenan, ko magana mai ƙarfi baya yi mata balle ya buga mata tsawa. Tsoro ne ya kamata don haka lokaci ɗaya ta haɗiye kukanta, ajiyar zuciya Kabiru ya sauke don ya lura da halin da take ciki. Tausasa murya ya yi ya buɗe mata murfin motar ya ce, "Shiga!" Ba musu Raihan ta shiga ya rufe motar, ya ƙarasa ya buɗe mata gate ɗin gidan ta shige da motarta. Yana ganin ta shiga ya rufe ƙofar ya ƙarasa bakin motarta, Raihan na fito wa daga motar da sauri za ta wuce Kabiru ya sha gabanta fuska a haɗe ya sake tambayarta, "Waye ya saka ki kuka?" Wani hawayen ne ya ziraro mata sai dai bata jin za ta iya gaya wa Kabiru saboda ta lura ko hirar mijinta na baya son ta riƙa yi masa. Cikin muryar kuka ta ce, "Babu komai kaina ne yake ciwo." Haɗe fuska ya yi ya ce, "Ƙarya ba halinki ba ne tabbas akwai wani abu da yake damunki daga ina kike?" Harara ta watsa masa ita ma ta haɗe fuska ta ce, "Fillo wai me ya sa ka raina ni ne?" Bai tanka mata komai ba ya kafe ta da ido, ganin haka ya sa Raihan ta shammace shi ta yi cikin gida a guje. Ba ƙaramin dariya ta bashi ba don har sai da ya murmusa sannan ya wuce ɗakinsa, amma kukanta ya tsaya masa a rai saboda ya tabbata ruwa baya tsami banza.

Mommy da su Inno suna zaune a falo Raihan ta shiga da gudu tana dariya, don haka kawai idan tana tare da Kabiru ko a cikin fushi take sai zuciyarta ta yi wasai. A tsakiyar falon ta tsaya tana mayar da ajiyar zuciya haɗe da riƙe ƙugu, Goggo ta riƙe baki tana cewa, "Kai gaskiya wannan yarinya baki da ɗabi'ar aziƙi saboda Allah baki da aiki sai na gudu kamar kin yi wa sarki ƙarya ya sa a kamo ki?" Mommy ta dubi Raihan ta ce, "Raihan kedai bakya girma, so kike Muhammad ya taso ki koya masa wannan guje-gujen naki?" Zama Raihan ta yi a kujera sannan ta ce, "Wallahi Mommy Fullo ya raini." Mommy ta yi salati haɗe da kai wa Raihan duka a baya ta furta, "Yanzu saboda Rashin kunya Kabirun za ki ce ya rainaki." Inno ta yi guntun tsaki haɗe da banka wa Raihan harara ta ce, "Wannan sakarcin da kike yi ba Kabiru ba nan gaba Muhammadu sai ya rainaki." Raihan ta miƙe tsaye tana murguda musu baki ta wuce ɗakinta haɗe da cewa, "Allah ya kiyaye wallahi duk ranar da ya min fitsara sai na yi masa Walmukalifatu." Mommy ta yi dariya ta ce, "Ji sakarcin banza yanzu MD kike gaya wa haka kamar wani sa'anki." Raihan na shiga ɗakinta ta faɗa gadon haɗe da lumshe ido nan ta tuno fuskar Kabiru ta yi lokacin da ya tsare gida yake tambayarta, murmushi ta yi haɗe da furta: "Fullo! Fullo ka ga makwancina da yawa wallahi " Al'amin shi ne abu na biyu da ya faɗo mata, nan take ranta ya sake ɓaci musamman da ta tuna irin ɗiban karan mahaukaciyar da ya yi mata haɗe da kalaman da ta riske shi yana faɗa a waya. Uwa-uba kuma wayar Malam da ya yi ita ta sake tsinke igiyar da ta yi shanyar kwanciyar hankalinta akai, lumshe ido ta yi tana furzar da iska mai zafi nan take hawaye ya fara bin idonta. Filo ta janyo ta rungume a hankali ta furta, "Ba ni na ɗora wa kaina ba soyayyarka ta dira a zuciyata tamkar dirar mikiya. A duk bugun numfashi wutar ƙaunarka ƙara ruruwa take a cikin raina sai dai ga dukkan alamu babu ni a zuciyarka, don Allah ka so ni ka ƙauna ce ni idan ba haka ba zuciyata za ta iya buga wa a kowanne lokaci." Haka Raihan ta ci gaba da surutai ita kaɗai ganin damuwa ta yi mata yawa ya sa ta ɗauko wayarta ta shiga dandalin sada zumunta.

Washegari da daddare su mommy suna zaune suna hira Daddy ya shiga bakinsa ɗauke da sallama, Mommy na ganinsa ta miƙe ta tarbe shi tana cewa, "Daddyn yara yau ka daɗe tun magriba nake saka ido." A gajiye ya zauna Raihan ta yi masa barka da zuwa, su Inno ya fara gaisarwa sannan ya ce, "Wallahi a gajiye nake. Ni ba na manta Malam ya ce za mu kai gaisuwar Al'amin gidansu yarinyar da yake nema ba, wallahi sai ɗazu ya kirani to mun yi niyar zuwa da rana sai kawai muka yanke shawarar zuwa da dare. Mun je an saka ranar yaron wata uku, ashe wai ya jima yana jiran yarinyar sai da ta kammala karatu." Tun da Daddy ya fara maganar Mommy take kallon Raihan ƙasa-ƙada gabanta na faɗuwa, don tun Raihan na ɓoye soyayyar Al'amin har sai da watarana ta sanar wa Mommy, sai dai tun a lokacin mommy ta yi mata nasiha akan ta cire soyayyar Al'amin daga zuciyarta. Mommy na shirin yin magana sai ji suka yi Raihan ta fashe da kuka, ta tashi da gudu ta wuce ɗakinta. Mamaki ne ya kama Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Lafiyar Yarinyar nan ko ciwonta ne ya dawo?" Mommy jiki a sanyaye cike da tausayin Raihan ta ce, "Babu ko ɗaya Daddyn Raihan, wallahi ba tun yanzu ba yarinyar nan ta ƙwallafa ranta akan wannan Al'amin ɗin, ko kwanaki dai da ta yi min maganarsa na ce mata ta fita daga harkarsa amma ta ƙi. An taɓa soyayya dole ne tun da shi bai taɓa nuna yana sonta ba..." Katse ta Daddy ya yi ta hanyar ɗaga hannunsa sama ya ce, "Dakata Zainab! Yaushe aka yi haka ban sani ba? Me ya sa baki gaya min ba tuntuni na yi wa Malam magana?" Ganin Daddy na son rufeta da faɗan da bata da laifi a ciki ya sa ta ce, "Idan ka gaya wa Malam, shi zai aureta ya zauna da ita? Daddyn Raihan kai fa namiji ne ka san yadda halin maza yake mace tana son su ma ya aka cika balle ita ta tsaga billenta ta nuna tana son shi. "Shiru Daddy ya yi ba tare da ya furta komai ba, ya miƙe ya nufi ɗakin Raihan da yake jiyo shasshekar kukanta tun daga waje. Yana shiga ya tsaya daga jikin gadon Raihan ya furta, "Raihan!" Shiru ta yi ta ɗago tana goge ƙwallar idonta, sake ambatar sunanta ya yi sannan ya ci gaba da cewa, "Tun yaushe kike ƙaunar yaron nan baki gaya min ba." Hawaye na zuba Raihan ta ce, "An daɗe amma mommy ce ta hana ni." Daddy ya jinjina kai sannan ya ce, "Kin Makara Raihan saboda Mahaifin yaron nan ya ɗauke tamkar ɗan uwansa yanzu me kike so naje na gaya masa, tun farko da kin gaya min zan iya gaya wa Malam idan ya so sai a gaya wa yaron inkun daidaita shi kenan. Amma gaskiya a yanzu ina jiye miki wulaƙancin namiji saboda yana da wacce yake so, hasalima ya shafe shekara huɗu yana jiranta yanzu kina ganin za ki shiga zuciyarsa kamar waccen ne? Ki yi ta addu'a Raihan har Allah ya canza miki da wanda ya fi shi, a kullin zaɓin Allah shi ne zaɓi." Daddy ya jima yana yi wa Raihan nasiha sannan ya fito daga ɗakin, ai kuwa yana fita ta sake rushe wa da matsanancin kuka don har ji take zuciyarta na wani irin raɗaɗi kamar za ta hudo ƙirjinta.

Tun bayan faruwar wannan al'amarin Raihan ta yankar wa kanta tikitin zaman ɗaki bata da aiki sai na kuka da tunani, tun Mommy na fushi da ita har ta watsar ta fara rarrashinta amma duk a banza don ko abincin kirki Raihan bata ci. Lokaci ɗaya ta zabge ta rame ta yi baƙi idan ka ganta sai ka rantse ta jima tana jinya, Kabiru tun yana saka idon ganinta har ya daina. Kuma a wannan lokacin bikin Al'amin bai fi saura wata ɗaya ba, har lokacih Daddy ya gagara sanar wa Malam halin da ake ciki, dom gani yake kamar ya so kansa da yawa. Wannan lamarin ba ƙaramin damunsa ya yi ba har sai da ya gagara wataran ya tambayi Daddy ita, Daddy shi kansa abin na Raihan ya fara ɗaga masa hankali don ko kaɗan baya ƙaunar wani abu da zai iya salwantar masa da rayuwarta. Sai dai Daddy yana jin daɗin irin kulawar da Kabiru yake bawa Raihan don haka ya ƙara shiga ransa, bayan ya bawa Kabiru amsa yana shirin tafiya Daddy ya kira shi da wata irin mura sannan Kabiru ya dawo. Cikin girmamawa ya russana Daddy ya ce, "Kabiru wani hukunci na yanke amma ban sani ba ko zai yi maka daɗi, amma na ce sai na fara jin ta bakinka duk da harkar ƙaruwa ce...


Eheeeem 🌚 na ce ba! To wai meye harsashenku? Barkanmu da juma'a bayin Allah🌚


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

42


Cike da ladabi Kabiru ya jinjina kai yana cewa, "Babu komai Daddy na amince duk da ban san akan abin da ka yanke shawara ba, amma ina fatan ya zame min alheri domin na san ba za ka yi min zaɓen tumun dare ba." Murmushi Daddy ya yi saboda nutsuwa da ɗabi'un Kabiru na matuƙar birge shi, dafa kafaɗar Kabiru ya yi sannan ya ce, "Allah ya yi maka albarka na gode da wannan karramawa da ka yi min. Da ma ba wani abu ba ne na yake shawarar canza maka wurin aikine, ina son na kai ka kamfanina ku riƙa aiki da sauran yarana saboda na yaba da ƙwazo, hankali da riƙon amanarka. Tun da nake babu mai gadin da ya jima yana yi min aiki kamar kai, Kabiru jin ka nake tamkar ɗan cikina saboda irin girmamawar da kake yi mini da girman da kake ba ni. Idan baka manta ba na sha gwada ka na zubar da kuɗi a harabar wurin nan don na ga yadda za ka yi da su, amma sai ka yi sallama da ni ka dawo min da abina. Allah ya yi maka albarka Kabiru ya jiƙan mahaifa." Kabiru ba ƙaramin daɗi ya ji ba har ƙasa ya tsugunna ya fara yi wa Daddy godiya, ɗago shi Daddy ya yi ya ce, "Na hana idan na yi maka wani abu ka fara yi min godiya. Sannan wani hanzari ba gudu ba, na ce mai zai hana ka dawo da ƙaninka autanku ya maye gurbin aikinka idan ya so su Inno wuro sai a gyara musu ɓangaren da yake kallon na su Inno su zauna." Kabiru na jin haka ya fashe da kuka tare da ruƙo hannun Daddy yana cewa, "Ba ni da bakin gode maka Daddy domin ka yi min komai,har na rasa mai zan ce maka Allah ya saka da alheri ya ja ran tsohuwa ya jiƙan mahaifi, Ubangiji ya biya maka buƙatunka na alheri duniya da lahira." Daddy ya yi murmushi ya amsa da "Amin." Motarsa ya buɗe ya shiga Kabiru ya buɗe gate sannan Daddy ya fice daga gidan, Kabiru cike da murna ya faɗa ɗakinsa ya ciro wayarsa ya kira Inna wuro ya sanar mata. Ita kanta ba ƙaramin farinciki ta yi ba, Kabiru saboda farinciki haka ya fara kai kawo a ɗaki. Raihan ita ta faɗo masa a rai yake jin ina ma tana cikin ƙoshin lafiya, da bayan Inna wuro ita ce mace ta farko da zai fara sanarwa. Sai kuma ya sauya fuska cikin damuwa domin ya san ba ƙaramin ciwo ne zai sa Raihan ta daina fitowa wurinsa ba, hasalima ya kira wayarta ya fi a irga amma koyaushe zai jita a kashe. Maryama ya kira ya sanar mata hukuncin da Daddy yanke da kuma ci gaban da suka samu, ita ma ba ƙaramin daɗi ta ji amma amma a yadda ya ayyana su Inna wuro ba za su dawo ba har sai Allah ya sauki Maryama lafiya saboda cikinta ya kai kusan wata bakwai. Yana son ya yi sallama da Mommy don ya duba jikin Raihan kuma ya yi mata godiya game da abin da Daddy ya yi masa, amma ya rasa yadda zai yi don haka ya yi ta maza ya yi sallama a ƙofar falon lokacin shiru falon da alama ba bu kowa a wurin, a daidai lokacin Raihan ta ɗauko Apple akan Dianning saboda bata iya cin komai, shi ma sha'awarsa ta yi shi ne ta ɗauko za ta wuce ta ji sallamar Kabiru. Tana tafe tana dafa bango saboda jirin da yake ɗibanta ta ƙarasa muryarta can ƙasa ta amsa masa, da ido ya kafe Raihan saboda tsananin mamakin irin lalacewar da Raihan ta yi lokaci ɗaya. A sanyaye Kabiru ya ƙarasa wurinta ya furta, "Me yake damunki haka Raihan? Kin ga yadda kika koma kuwa?" Kamar ya tunzurata ta ji zuciyarta ta sake rauni hawaye ya ciko idonta, a hankali ta jingina da bango jikinta har rawa yake saboda yadda yunwa ta ci ƙarfinta, ga rashin ƙwarin jiki da tsananin ciwon ƙirji da take fama. Lumshe idanu ta yi ta furta, "Ka ta ya ni addu'a Fillo saboda rayuwata na cikin wani yanayi." Hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya sake yi ba, har ji yake ina ma yana da ikon taɓa wani ɓangare na jikinta da ko ba komai ya ruƙo hannunta ya lallasheta domin ya ji ainihin abin da yake damunta. Takawa ya yi zuwa gabanta ya ce, "Gaya min abin da yake da mun ki ko ina da ikon taimaka miki." Girgiza masa kai ta yi hawaye na zuba ta ce, "Za ka iya taimaka min da addu'a fillo domin ita kaɗai ce abin da za ka iya tallafa min da ita." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce, "Zan yi ƙoƙari matuƙa na yi miki addu'a daidai bakin gwargwadona amma a dukkan lamuranki ki riƙa neman zaɓin ubangiji, domin shi ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login