Showing 39001 words to 42000 words out of 157890 words

Chapter 14 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

180


Da mamaki Daddy yake bin wurin da kallo don hanyar babu hatsaniya kasancewar magriba ta fara kawo kai, horn ya fara yi a hankali a tunaninsa ko wata lalurar ce tasa yarinyar za ma a kan titi. Sai dai ko gezau bata ɗago ba duk da yana tafe yana ci gaba da danna horn ɗin motarsa har ya kusa ƙarasawa wurinta. A hankali ya gangara da niyyar yin parking wayarsa da take ringing ta katse shi, number Dr ya gani ya sake kiransa da sauri ya ɗauka ya kanga a kunne yana faɗin, "Hello Dr ga ni na taho wurinka." Daga can ɓangare aka amsa da cewar, "Alhaji ka yi haƙuri ɗazu arashi aka samu wani ƙanina ne ya ɗauki wayar ya maganar tafiya Indian?" A fili Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana lumshe ido ya ce, "Ni dama na yi mamaki da jin irin maganganun da aka yi ɗazu, yanzu kana ina?" Daga can ɓanagaren aka amsa da cewar, "Yanzu ka jira ni a gida zan zo na same ka." Daga haka suka sallame wayar, Daddy na ajiya wayar ya ɗago da niyyar ci gaba da Driven ya hangi saman titin fayau babu yarinyar babu alamarta. Da mamaki ya fara kallon wuraren don ko kaɗan bai lura da lokacin da ta tashi daga wurin ba, cikin rashin damuwa ya ci gaba da tafiya yana saƙa yadda tafiyarsu za ta kasance.

Yana komawa gida har ɗaki ya je ya samu su Inno bayan sun gaisa ya ɗan sosa kai ya ce, "Inno dama zuwa na yi da wata magana." Goggo ta miƙe tsaye tana gyara zaman hijabinta ta ce, "Audullah don Allah ba ka cewa na baku wuri za ku yi sirri? Allah ya sani ba zan zauna na ji sirrin ɗa da uwa ba." Daddy ya yi murmushi yana faɗin, "Goggo ba fa wata magana bace, dama gobe idan Allah ya kaimu za mu wuce ƙasar India wurin duba lafiyar Raihan, sai kuma maganar sake gida da za mu yi." Inno ta yi kasaƙe tana kallonsa sannan ta ce, "Ita dai Raihanu ba zan hana ka nema mata lafiya ba, amma saboda Allah Audullahi me ye aibun gidan nan?" Goggo ta wara hannuwa tana faɗin, "Ta ya ni gani kuma wallahi ko a Albasu babu ƙerarran gida kamar wannan." Daddy ya zauna sosai yana cewa, "Zainabu ce ta buƙaci haka tana ganin kamar nan ya muku girma idan muka tafi, dukda zan sa a kawo wacce za ta ci gaba da taya ku zama." Goggo ta ɓata fuska ta ce, "To yanzu fusabillahi ƴan zaman makoki haka za mu riƙa gantalin gaya musu mun sauya gida daga wannan zuwa wannan, Allah ya sani ƙawayena na Albasu rankatakaf sun ce za su zo sadakar uku haka za su riƙa bilayin nemanmu?" Inno ta taɓe baki ta ce, "Bar shi Zinaru, Audullahi so yake ya nuna mana yawan arzƙinsa to Allah ya sani daga gidan idan ka matsa min sai na koma wani wurin zan bi zinaru mu koma Albasu." Daddy ya yi shiru don yadda ya ga sun rikice masa da wuya idan zai shawo kan tsofaffin, ganin ya yi shiru Inno ta leƙa fuskarsa ta ce, "Amma dai ba haushina kake ji a zuciyarka ba ko Audullahi?" Daddy ya yi murmushi ya ce, "Haba Inno kawai ina tunanin wacce zan ɗauko ta taya ku zama ina ga a samu budurwa da Dattijuwa ko?" Inno da Goggo suka washe baki suna faɗin, "Eh haka ya yi Allah ya yi albarka." Daddy ya amsa da Amin sannan ya fice daga ɗakin. Yana zuwa ya sanar wa da Mommy yadda suka yi da su Inno, Mommy ta so a sauya musu gida amma babu yadda ta iya haka za ta haƙura. Sai dai ta bawa Daddy shawara a kan ya kirawo malamai su zo su yi saukar karatun alƙur'ani. Kuma a ranar dangin Mahaifin Daddy na nesa suka zo, ita ma mommy ta yi wa wata ƙanwarta Hajiya Hafsa magana akan ta zo gidanta ta zauna kafin ta dawo daga tafiya.


Su Abar bauta na tafiya Raihan ta miƙe tafara zaga lungu da saƙon da ke cikin tsibirin ƙungiya, daga can bayan wani dutse matatar jini ce a daskare. Hannuwan Raihan ne suka fara fidda wasu manyan farata, tana ƙarasawa wurin ta kafa hannuwanta a kan daskararran jinin da ya daske tamkar ƙanƙara, da hannunta ta fara kankararsu tana sakawa a baki tana shanyewa. Sai da ta sha ta yi ƙat sannan ta miƙe daga wurin tana yin gaba ta faɗi a wurin bacci ya yi awon gaba da ita. Raina ba ita ta farka ba sai yamma liƙis tashi ta yi zaune tana mittsika idanu, kai tsaye banɗaki ta faɗa ta fesa wanka sannan ta fito ta zauna a gaban mudubi tana shafa mai. A hankali ta wayarta ta fara ringing, daga ita sai ɗan ƙaramin towel ta ƙarasa ta ɗauki wayar, ganin baƙuwar lamba ya sa ta yi guntun tsaki ba tare da ta ɗauka ba. Ɗauko wayar ta yi ta ajiye a kan mudubi tana ci gaba da gyaran gashi da yake ta wanke kanta, tana tsaka da taje kai ta sake jin wayar ta sake ringing a hankali ta kai hannu ta ɗauka sai da ta yi kamar ba za ta ɗauka wata zuciyar ta bata umarni akan ta ɗauka. Cikin sanyayyar murya ta ɗauka tana furta, "Hello!" Sai da aka ɗauki ƴan sakanni sannan aka amsa da faɗin, "Assalamu alaiki." Taɓe baki ta yi bata amsa ba ta furta, "Da wa nake magana?" Daga can ɓangaren aka bata amsa da cewar, "Yin sallama ko amsata samun lada ne ga duk wani musulmi." Raihan ta yi tsaki a fili tana faɗin, "Idan baka da abin yi ni ina da shi." Bata jira cewarsa ba ta katse wayar." Duk da tana cikin ɓacin rai hakan bai hana ta sakin wani malalacin murmushi ba, a fili ta furta: "Wai ni zai nunawa muhimmancin sallama hmmm." Miƙewa ta yi ta ɗauko doguwar rigar atamfa mara nauyi ta saka don ta jima bata saka atamfa ba, haka kawai ta ji tana sha'awar saka su. Kan katifa ta koma ta kwanta ta buɗe Data ta shiga kafofin yanar gizo. Tana nan zaune Mommy ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, murmushi Raihan ta yi mata ba tare da ta amsa sallamarta. Mommy na tsaye daga bakin ƙofa ta ce, "Raihan yau duk wuni guda ban ji motsinki ba, an ya yau ko abinci kin ci kuwa." Raihan ta shafa cikinta tana cewa, "Mommy wannan cikin nawa ai har zuwa gobe ba lallai na buƙaci abinci ba." Hararar wasa ta yi mata ta ce, "Saboda kin cinye abincin gidan?" Raihan ta yi dariya ta ce, "Allah mommy na ƙoshi abincina na musamman ne." Mommy ta jinjina kai tana faɗin, "Allah ya shirya min ke wannan rashin cin abincin nan naki sai na nemar miki magani." Wayar Raihan ce ta sake ringing ta ja guntun tsaki za ta ajiye Mommy ta ce, "Ba kiranki ake yi ba." Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Wallahi mommy wani sakarai ne zai dame ni a waya." Mommy ta yi girgiza kai tana faɗin, "Kika sani ko classmate ɗinki ne ta yuwu ma gaisuwa za su yi miki tun da na san Intisar za ta sanar da su." Ba don son ranta ba Raihan ta ɗauki wayar tana faɗin, "Ya aka yi?" Daga can ɓangaren aka bata amsa da cewa, "Ina neman Saleem ya aka yi na ji number sa mace ta ɗauka?" Raihan cire wayar ta yi daga kunnenta ta ƙurawa lambar ido takaici ya rufeta, tana tsaka da nazarin irin baƙar maganar da za ta caɓa masa ta ji ya ci gaba da cewa, "Na rasa rawar kai irin na wasu yaran idan baya kusa in ya zo ki ce masa Salman ya kira, amma don Allah ki ce ya koya miki darasin sallama da amsata." Yana ƙarasa maganar ya katse wayar, cikin masifa Raihan ta dura wani uban ashar. Da sauri Mommy ta kai mata duka tana faɗin, "Wai me yake damunki ne Raihan?" A zafafe Raihan ta sanarwa da Mommy abin da ya gaya mata, Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce: "Hala sakarcin da kika saba kika yi masa." Raihan ta zumɓuri baki gaba ta juya ta yi kwanciyarta, Mommy ta zagayo ta gabanta tana faɗin, "Raihan ki haɗa kayanki idan Allah ya kaimu gobe za mu wuce india akwai wani Dr da za a haɗa mu da shi." Raihan tana daga kwance ta ce, "Tuni na riga da na san da tafiyar, abin da ya rage mu ƙarasa." Mommy bata kawo komai ba ta fice daga ɗakin.

Duk wani shirye-shiryen tafiya da ake yi Huzaifa yana sane da tafiyarsu Raihan, don lokacin da Dr ya yi waya da Daddy waya suna gamawa Huzaifa ya sake shafarsa, a nan take wurin ya faɗi bacci ya yi awon gaba da shi. A daren ranar ya dawo gidan su Raihan cikin surara Mama Uwani, Mommy ta yi mamakin ganin Mama Uwani don sun gama magana akan kwana za ta yi amma da ta ce musu mai jiki da sauki duk babu wanda ya kawo komai a ransa.

WASHEGARI.

Tun da safe su Mommy suka kammala shirinsu tsaf, Raihan ma ta shirya cikin riga da wando. Hannunta saƙale da baƙar jaka ba ƙaramin kyau ta yi ba, wayarta ce ta fara ringing tana ɗaukota ta ga number Intisar. Murmushi ta yi ta ɗauka da sallama tana faɗin, "Intisco baby." Daga can ɓangaren Intisar ta amsa mata da cewar, "Besty ya kun tashi ko yaya? Kin san yau muka yi da ƴan Department ɗinmu za su zo miki gaisuwa." Raihan ta yamutsa fuska ta ce, "Yanzu za mu ƙarasa airport ayya ke gaya musu dalilin tafiyata amma ai ina jin bai fi mu yi two weeks ba." Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama.

ƘASAR INDIA

Tun daga Nigeria Daddy ya sanarwa da wani abokinsa da ke aiki a cen maganar zuwanci, da farko sun so sauka a hotel amma Alhaji Yusuf ya nuna sam sai dai su sauka a gidansa. A ranar da suka sauka Daddy na sanarwa da Alhaji Yusuf asibitin za su ziyarta ya yi jim don ko a gidan talabijin bai taɓa cin karo da sunan asibitin ba, da mamaki ya dubi abokin nasa ya ce, "Abokina wai har yanzu wannan matsalar dai ita ce?" Daddy jiki a sanyaye ya ce, "Abu ɗaya muke fama shekara da shekaru." Alhaji Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Shi kenan babu abin da yafi ƙarfin Ubangiji. Zan kira wani abokina don shi ne mai kula da asibitocin kuɗi masu zaman kansu na ƙasarnan, duk yadda muka yi zuwa safiya za ka ji ni amma lamarin ciwon nan nata akwai ɗaure kai."

Duk tattaunawar da ake yi Huzaifa na laɓe a ɓoye yana jinsu, babban kuskuren da ya so aikata wa shi ne na rashin kautar da tunanin Abokin Daddy, lokaci ɗaya dabara ta faɗo masa a daren ranar ya sace abokin Daddy zuwa tsibirinsa tare da buɗe masa ido da sabuwar India a wurin hatta iyalansa duk na bogi ya saka masa.

Abin da Huzaifa bai sani ba tun ranar da su Raihan suka zo ƙasar India aka ajiye masa jabun Raihan, Raihan ta koma cikin ɗakin arziƙi da zama. Duk wannan shirin na abar bauta ne, don ta ci alwashin aiwatar da komai cikin shiri ba tare da Huzaifa ya fahimci wani abu ba. A yanda Huzaifa ya so, ya so ace ya jinkirtar da rahin Raihan dukda Jabbul-ƙasi ya sanar da shi babu wata dabara ko hikima da ta rage masa game da Raihan matuƙar bai kai ziyara ga Burtultika ba, amma kafiya da taurin kai irin nasa ya sa ya jarraba kawo ta ƙasar India domin a nan babbar da'irarsa take. Sai dai duk wannan abin da ake ciki daga Daddy har mommy babu wanda ya fahimci shirin Huzaifa, saboda ya kaisu babban asibitin kuɗi da asibitin da likitocin duk na buɗewar ido ne da Huzaifa ya yi musu, gabaɗaya ba mutane ba ne har suka gama zaryar asibitinsu kuma a ganinsu buƙata ta biya don tun da suka zo babu wani abu da Raihan ta sake yi na tsoratarwa. Kwanansu goma sha biyar suka tarkato suka dawo ƙasar Najeriya zuciyar Mommy da Daddy fes, musamman Daddy da yake jin kamar an yi masa bushara da gidan aljanna.

Kwanansu biyu da dawowa Kabiru ya ƙarasa cikin Falon ya miƙawa Daddy wata farar takarda, a cewar Kabiru Dr Muhsin ne ya kawo masa don ya kira wayar Daddy ta daina shiga. Daddy na karɓa Kabiru ya juya ya fice, don har lokacin jikinsa a naɗe yake saboda baya son ko kaɗan wani ya fahimci halin da yake ciki. Buɗe takardar ya yi cikin mamaki yana faɗin, "Ni fa kaina ya fara kullewa ya za a yi ace min Dr Muhsin ya riƙa zuwa nemana bayan ya san da tafiyarmu." Daddy ya ƙarasa maganar yana buɗe letter hannunsa, a fili ya fara karantawa Mommy na sauroronsa don ita kanta komai ya fara kwnace mata. Takardar ta ƙunshi ban haƙuri da Dr ya ke yi ga Daddy akan ya nemarwa Raihan wani likitan saboda rashin ƙwarin jiki da baya samu, daga ƙarshe ya ƙare maganar da cewar ya yi ta kiran wayarsa baya samunsa. Mommy ce ta riga Daddy maganar da cewar, "Tabbas akwai wani ɓoyayyan al'amari domin lamarin akwia rikitarwa." Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ni kaina al'amuran sun fara sha min kai." Sun jima a wurin suna tattaunawa daga ƙarshe Daddy ya yanke shawarar zuwa ya samu Dr Muhsin har Office ɗin sa.

Bayan Wasu Kwanaki.

Raihan ce shirye tsaf cikin doguwar riga kayan ba ƙaramin kyau suka yi mata, hannunta ɗauke da jakar makarantarta don tun dawowarsu daga India suka shiga first semester level 300 sai dai ba ta samu ta halarci makarantar ba. Da kanta ta ƙarasa wuri parking space ta ɗauki motarta, sai da ta je bakin gate ta fara zabga Horn. Da sauri Kabiru ya ƙarasa jiki na rawa ya buɗe mata ƙofa, da gudun gaske ta fice daga gidan ta ware sauti na tashi a cikin motar fuskarta ɗauke da ƙaton glass baƙi. A kan titin shigarta gate ɗin makarantarsu bisa tsautsayi motarta suka yi taho mu gama da wani matashin saurayi da ke kan babur ɗin lifan, sai dai Allah ya rufa asiri ba wata buguwa suka yi mai ƙarfi ba. A zafafe Raihan ta fito daga mota cikin masifa tana faɗin, "Kai wanne irin mutum ne da baka lura da gabanka..." Muryarta ce ta maƙale sakamakon tozali da ta yi da kyakkyawar fuskarsa, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wacce ta dawo da saurayin daga tunanin da ya faɗa na firgicin abin da ya faru. Bai tanka mata ba ya fara ƙoƙarin saukowa domin ɗauko wayarsa da ta faɗi can gefe, da sauri Raihan ta tsugunna ta ɗauko masa tare da sa gefen mayafinta ta goge masa. Tana shirin miƙa masa ta riski muryarsa yana faɗin, "Na gode." Ya yi maganar yana karɓar wayarsa, har zai tada mashin ɗinsa ta furta, "Ka yi haƙuri." Raihan ta samu kanta da furta waɗannan kalaman, murmushi ya sakar mata sannan ya ce, "Ba damuwa." Raihan ta gyara tsayuwarta tana lumshe ido sakamakon jin yadda muryarsa take rikitata, tun da take bata taɓa tsintar kanta a cikin wannan yanayin ba. Mutane da dama sun nuna suna soyayyarsu a gare ta amma babu wanda ya taɓa yi mata balle ta ji wani abu daga gare shi. Tana tsaka da tunani ta tsinkaye shi ya kunna mashin ya yi gaba abin sa, firgigita ta ɗora idonta a kan katafaren gate ɗin makarantarsu. Tana nan tsaye har ta ga shigewarsa cikin, hannunta ta sa ta dafe gefen ƙirjinta ya yin da ta ji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, tana nan tsaye cikin duniyar tunani ƙarar horn ɗin motar da ke bayanta ta dawo da ita daga duniyar tunani.


ALLAH YA SA HUZAIFA YA BARI SOYAYYAR TA ƊORE😂


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624


14


Kamar wacce aka zare wa laka a jiki haka Raihan ta fara takawa a hankali ta buɗe motarta, tana shiga ta bata wuta da ƙarfin gaske. Duk yadda ta so cimma matashin sai dai kamar an yi ruwa an ɗauke haka ta neme shi ta rasa sama da ƙasa, daga gefen hall ɗin da suke da lecture ta yi parking ɗin motarta. A kasalce ta ziro ƙafarta ta fara takawa kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, ɗaga kanta ta yi tana ɗan waige-waige don har lokacin bata cire rai da tsammanin ganinsa ba, a haka har ta ƙarasa bakin hall ɗin tana tafe tana saƙa da warwara. Zuwanta ke da wuya ƴan Department ɗin su suka fara yi mata ta'aziyya sakamakon mafi yawa daga ciki basu halarci gidansu ba, Raihan yaƙe ta riƙa yi musu amma sam hankalinta baya wurinsu. Tana nan tsaye Intisar ta ƙaraso sanye da coffee ɗin hijabi, kalarsa ba ƙaramin karɓarta ya yi ba. Ta baya ta rungumo Raihan tana faɗin, "Oyoyo Besty." Hararar wasa Raihan ta yi mata tana faɗin, "To ƙarasani ki huta kin ji." Hannuwa biyu Intisar ta sa a daidai kunnuwanta tana cewa, "Tuba nake na ƙaryaki ina na kama." Gabaɗaya suka saka dariya tare da rankayawa cikin block ɗin sakamakon zuwan malamin da zai yi musu lectures, Mr Samuel shi ne lectural da yake ɗaukansu Oral Engilsh ɗalibai na ƙaunarsa sosai sakancewar ya iya koyarwa, yana shiga ajin ya yi tsit saboda a dokarsa matuƙar kuna surutu nan take zai yi test a kan topic ɗin zai koyar a ranar, kuma matuƙar ya ɗauka yana amfani da shi. Tun shigowarsa Raihan ta kafe shi da ido lokaci ɗaya ta ji ta kawaɗaita da shi, sunkuyar da kanta ta yi ƙasa tana son aiwatar da manufarta a kansa runtse idonta ke da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login