Showing 123001 words to 126000 words out of 157890 words

Chapter 42 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

159

da ba su gano ɗaki ba. Mamaki ne ya kama ta ganin yadda Al'amin yake gaida su cikin mutumci fa girmamawa yana sunne kai ƙasa, suna shigo wa da sauri ta ɗane Mama Hafsa tana murna. Ita ma rungumeta ta yi cikin farinciki don ta ji daɗin ganin Ƴar ƴar'uwarta cikin ƙoshin lafiya, sai a lokacin ta baje musu kajin da Al'amin ya kawo mata, kaɗan suka yi suka saka mata sauran a firji. Babu ƙofa ɗaya da Raihan ta buɗe musu da take nuna tana cikin damuwa don haka sai santin ɗakinta suke yi, sai da suka leƙa sashen Sumayya suka gaisa ta amsa musu cikin mutumci sai yabon sauƙin kanta suke Raihan ban da murmushi babu abin da take yi, daga ƙarshe suka koma ɗakin Raihan suka yi mata nasiha mai ratsa jiki, akan ladabi da biyayya sai juriya da haƙuri. Sun yi mata nasiha sosai akan yadda za ta kula da mijinta ta ɓangaren kissa da tarairaya Mama Hafsa na gaya mata har kunya take ji, ba su wani daɗe a gidan ba suka yi mata sallama suka tafi. Lokacin da za su tafi har da ƙwallarta ta raka su bakin gate tana ɗaga musu hannu, ɗakinta ta koma ta ɗauki waya ta kira wayar mommy. Sun jima suna hira da mommy duk a game da baƙi ne da sauran ƴan biki, bayan sun gama ta kira Daddy cikin farinciki ya amsa mata bayan sun gaisa suka taɓa hira sannan suka yi sallama.

Sannu a hankali haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Raihan na zaman haƙuri da kai zuciya nesa, kusan kullin sai sun yi waya da Mommy amma bata taɓa gaya mata halin da take ciki ba saboda ta fahimci abin da mommy take guje mata, kuma gani take da kunya ta faɗi irin zaman da take yi. Tsakaninta da Al'amin daga gaisuwa sai saka aiki bayan wannan babu wata hira da take shiga tsakaninsu, tana ji tana gani suke shan soyayya tsakaninsa da Sumayya har sai da ta ji ina ma ita ce yake riritawa haka. Idan ta ga abin zai ɓata mata rai sai dai ta koma ɗakinta ta ɗauki waya ta shiga Whatsappa, mostly ta fi sha'awar karanta littafan Ameera Adam don ba ƙaramin birgeta suke yi ba musamman na barkwanci don ko ranta a ɓace yake sai zuciyarta ta yi wasai, wani lokacin idan tana karantawa tana dariya har falo Sumayya take jiyo dariyarta, wannan lamarin ba ƙaramin tunzura zuciyarta yake yi ba. Hakan ne ya sa wataran ta tura ƙofar ɗakin Raihan ta gaggasa mata magana, uffan Raihan bata gaya mata ba sai ma ta ci gaba da dariyarta don ta zo wurin da Ɗan tsoho mai buhu ya zuba ihu haɗe da wurgar da buhun hanunsa ya nausa daji, a daidai lokacin da ya ji passingers ɗin motarsu za su kamo shi da ƙarfi su mayar da shi motar da ta gama yin hayaƙi. (LITTAFIN YAWON SALLAR HAJIYA IYA.) Haushi ne ya kama Sumayya ta fice daga ɗakin, Al'amin kuwa na dawowa ta shirya masa ƙarya da gaskiya ta gaya masa nan take ya rufe Raihan da faɗa ba tare da ya bi ba'asi ba. A hana ya ƙare kwanakinsa bakwai cif na ɗakin Sumayya a ranar da zai koma ɗakin Raihan Sumayya har da kukanta, har sai da ta saka shi a gaba ya yi mata alƙawari akan babu wani abu da zai shiga tsakaninsa da Raihan. Alƙawari ya ɗaukar mata don shi kansa gani yake babu wani abu da zai nema a wurin Raihan bayan wanda ya samu a wurin Sumayyansa. Tun bayan magriba Raihan take zuba idon ganin Al'amin amma har bayan tara na dare ba ta ji motsinsa ba, akan dole ta haƙura ta yi kwanciyarta. Cikin bacci ta ji shigowarsa amma sai ta yi kamar bata ji shi ba, a gefenta ta ji ya kwanta ya juya bayansa nan take ƙirjinta ya buga ta sake naɗe wa wuri ɗaya. Da shigarsa ko minti goma bai yi ba suka ji bugun ƙofar Sumayya tana bugu tana kuka wai tsoro take ji ta ga gilmawar wani abu ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, a zabure Al'amin ya miƙe ya nufi ɗakin nata. Ya duba ko'ina amma babu wani abu da ya gani, don haka ya zauna yana gadin sumyya da niyyar idan ta yi bacci sai ya koma ɗakin Raihan don ya fita haƙƙinta saboda ko da baya santa ya san tana da haƙƙi akansa, ada bai yi niyyar haɗa komai da ita amma da ya tuna Ubangiji da haƙƙoƙinta sai yake ƙoƙarin saukewa. Haka Summaya ta riƙa yi yau ta tsiro wannan gobe ta tsiro wannan har kwana ta taɓa yi a ɗakin Raihan don kar ta bari wani abu ya shiga tsakaninsu. Saboda a yanda ta san Al'amin zai yi wuya ya shafe kwanaki bakwai ba tare da wani abu ya shiga tsakaninsu ba, saboda mutum ne mai taƙatsantsan da rashin son shiga haƙƙin na ƙasa da shi. A haka har su Raihan suka shafe wata guda ba tare da ya wani abu ya shiga tsakaninsu ba, ana cikin haka Sumayya ta fara wani irin laulayi mai saka bacci don a daddafe take iya yin sallar Isha'i. A ranar wata juma'a Al'amin ya yi niyyar sauke nauyin Raihan da ke kansa, siyayya ya yi musu kamar yadda ya saba duk dare kowacce ya miƙa mata. Ganin yanayinsa ba ƙaramin faranta mata rai ya yi ba, alwala ya sata ta ɗauro bayan sun gama cin abinci don yanzu idan yana ɗakinta har yana yadda ta zuba masa abinci ya ci a ɗakin, bayan sun gabatar da sallar Nafila Al'amin ya jima yana yi musu addu'o'i sannan ya shafa. Jikin Raihan ba ƙaramin sanyi ya yi ba gabanta na faɗuwa, hannunta ya kama suka wuce kan gado sannu a hankali ya fara sarrafata cikin ƙarfin hali don ko kaɗan babu ɗigon soyayyar Raihan a zuciyarsa. Sai dai yanayin surarta ba ƙaramin hargitsa tunaninsa ta yi ba har ya gagara bambamce Sumayya da Raihan wacce ta fi wata. Hannunsa ya saka yana yawo da shi cikin jikinta, jikin Raihan ban da rawa babu abin da yake yi ana cikin haka ta ji Al'amin na ƙoƙarin...

Allah ya sani ina taya Kabiru kishi ba zan ƙarasawa ba sai Allah ya kaimu😰


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn +234 706 206 2624.



45



Gabanta ne ya ci gaba da faɗuwa jin Al'amin na ƙoƙarin shigarta, ƙwace kanta ta shiga ƙoƙarin yi don yadda fargaba ta mamaye zuciyarta gani take kamar yadda Huzaifa ya yaudareta da siffar bil'adam haka Al'amin zai yi mata, cikin fitar hayyaci ya sake janyota jikinta a hankali ya furta, "Shiiiii." Shiru Raihan ta yi ta saka hannu tana shafa fuskarsa sannan ta ce, "Don Allah Al'amin kai ne dai?" Idonsa a lumshe ya gyaɗa mata kai Raihan na shirin sake magana suka ji an fara buga ƙofa da ƙarfi, muryar Sumayya ce take ihu haɗe ta ƙwala masa kira tana cewa, "Habibi ka taho maciji da kunama za su kashe ni." Hankali a tashi Al'amin ya miƙe ya janyo jallabiyyarsa ya saka. Raihan na daga kwance ta ɗauko zaninta ta ɗaura sannan ta saka hijabinta. Al'amin na buɗe ƙofa Sumayya ta maƙale shi jikinta ban da karkarwa babu abin da yake yi, ƙofar ɗakinta take nuna masa bakinta na rawa ta ce. "Wallahi suna ciki." Janyeta bayansa ya yi ya mayar da ita wurin ƙofar ɗakin Raihan, a hankali ya fara takawa har ya ƙarasa ƙofar ɗakin yana maimaita addu'a a bakinsa. Yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin ya shiga ga mamakinsa wata irin tafkekiyar kunama ya gani kwance a tsakiyar gadon Sumayya, tun da ya zo duniya ko a labari bai taɓa ji labarin makamanciyar wannan kunamar ba. Haka kawai ya ji tsigar jikinsa ta tashi yaarrr! Idanu ya lumshe ya buɗe yana sake ƙurawa kunamar ido, motsi ya ji daga gefen madubi yana kai idonsa ya hango wani baƙin maciji jikinsa baƙi siɗik har sheƙi yake. Tsalle macijin ya yi ya haye kusa da kunawar yana zagayeta tuni ta maƙale jikinsa tana wani irin zagaye a doron bayansa, tsoro ne ya fara kama Al'amin don haka ya ci gaba da karanto ayayon kariya yana tunkarar macijin, yana kusantarsu suka fara nufar hanyar windon Sumayya da yake a buɗe. Da sauri suka ɗare suka fice daga ɗakin, Al'amin sai da ya lalleƙe ko ina sannan ya zuge windon ya rufe shi ruf. Ƙofar ya rufe ya zagaya ta bayan gidan don ganin wurin da macijin ya yi amma babu shi babu alamarsa, duk iya dube-dubensa babu abin da ya gani don haka ya janyo ƙofar ya rufeta ruf sannan ya dawo wurin su Raihan, a daidai lokacin Sumayya ta dafe mara tana ihu haɗe da faɗin, "Wash marata Al'amin." Da sauri ya kamata yana faɗin, "Lafiya Sumayya?" Bai rufe baki ba ya ga jini na bin ƙafarta, ƙirjinsa ne ya buga hankali a tashe ya furta, "Me ye wannan sumayya?" Ganin jini ya sake hartsiga Sumayya ta sake ruɗewa, Raihan ya kalla yana faɗin, "Ɗauko mata hijabi mu tafi asibiti." Jiki na rawa Raihan ta koma ɗakinta ta sako doguwar rigar bacci ta saka hijabi ta ɗauko wa Sumayya hijabinta ta fita, a gaggauce Al'amin ya saka mata ya ɗauke ta cak saboda yadda ciwon mara ya murɗeta suka wuce asibiti, asibitin ba shi da nisa da gidansu don haka ba su jima ba suka ƙarasa. Cikin gaggauwa likitoci suka karɓeta suka shiga bata agajin gaggawa, duk yadda suka so ceto abin cikin sumayya sai da ta yi ɓarinsa. Ta sha wahala sosai don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci ta ji jiki, Raihan ta yi jigum don ita kanta hankalinta ba a kwance yake ba. Kimanin ƙarfe ɗaya na dare aka samu jikin Sumayya ya yi sauki saboda fitar cikin jikinta, allurar bacci suka yi mata sannan Al'amin ta ɗauki Raihan suka wuce gida don ɗauko duk abin da ya kamata su buƙata. Daga Raihan har Al'amin babu wanda ya tankawa ɗan'uwansa sai dai kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci kowannensu yana cikin tashin hankali. A gaggauce suka ɗauki abin da za su ɗauka suka koma asibitin sai dai har lokacin bacci Sumayya take yi, daga Al'amin har Raiban a zaune suka kwana kowane na yin gyangyaɗi. Tun asuba Sumayya ta farka Raihan ce ta taimaka mata ta gyara jikinta, duk kayan jinin da ya ɓaci Raihan ce ta wanke su tas ta gyara wurin sannan ta haɗa wa Sumayya ruwan tea, tun da sumayya ta farka take aika mata da harara tun Raihan bata lura da irin kallon da Sumayya take yi mata ba har ta ankara ta sha jinin jikinta.Tun da suka tashi Raihan take yi mata sannu amma ko sau ɗaya bata amsa mata, ban da yauƙi da shagwaɓa babu abin da take yi wa Al'amin. Kimanin ƙarfe takwas na safe Mahaifiyar Sumayya da ƙannenta suka shiga cikin asibitin, Mami na shiga Sumayya ta fashe da kuka tamkar a lokacin ne ta yi ɓarin cikin.A wulaƙance suka riƙa kallon Raihan suna yamutsa fuska, Al'amin na gaida su ya fice daga wurin. Cikin girmamawa Raihan ta gaida ita tana yunƙurin tashi Mami ta ce, "Yo dama tun da na ji an ce wai kin ga maciji a ɗakinki ai nasan ture ne aka yi miki, ana baƙinciki kin samu ciki ba gara a ɓarar da shi ba. Ai duk makircin mutum ya ƙare akansa don ba a taɓa canjawa tuwo suna kece dai Uwargida wacce kike zaune ɗaram a zuciyar Al'amin amma su shigege sai dai a yi ta cusa kai babu kwarjini to laƙadija'akum tsakaninta da ke, dama ba ance aljani ya aureta har ya taɓa tserewa da ita ba, ni babban tashin hankalina ma kar haukan jikinta ya tashi watarana ta shaƙe min ke a gida ta kashe ki, ta cuce ni tun da ba a shari'a da mahaukaci." Ƙwalla Raihan ta ji na niyyar zubo mata a hankali ta nufi ƙofa ta fice don idan ta ci gaba da jin kalamanta za ta iya gaya mata mara daɗi. Tana fita ta kira Mommy ta sanar da ita abin da ya faru da Sumayya daga ƙarshe Mommy ta ce tana nan tafe da yamma, suna gama waya Ammi da ƙannen Al'amin suka ƙaraso cikin asibitin. Da gimamawa Raihan ta gaida Mami suma ƙannen Al'amin suka gaishe ta ba yabo babu fallasa, sannan suka wuce cikin ɗakin da Raihan take, da yake Malam baya gari sai a waya ya duba Sumayya. Bayan fitar Raihan daga ɗakin Mami ce ta yi ƙasa da murya ta ce, "Wallahi sai mun yi da gaske akan yarinyar nan idan ba haka ba na lura haramta miki zaman cikin gidan za ta yi, a yau ba sai gobe ba zan tafi na amso miki alƙwarin da muka yi da ke. Da zazzaɓi nake fama da shi amma ko ma meye dole na shirya na je don wallahi yarinyar nan dole ta bar miki gidan nan." Daɗi ne ya kama Sumayya ta sake rungume Mami tana faɗin, "Shi ya sa nake ji da ke Mommcy." Shigar su Ammi ya daidaita nutsuwar Sumayya ta sake narkewa tamkar wani azababben ciwo na damunta. Ammi na zama bayan sun gaisa ta fara tambayar Sumayya yadda lamarin ya kasance, Sumayya ta sauya fuska cikin damuwa tana cewa, "Wallahi mommy ina cikin bacci na ji kamar an kira sunana, ina tashi na ga babu kowa sai na koma na kwanta. Ban yi aune ba sai ji na yi abu mai ƙayoyi yana bin jikinta, ina buɗe ido na ga wata irin murtukekiyar kunawa ga maciji a gefen cikina a kwance shi ne na tafi ina ƙwalawa Al'amin kira. Daga haka kawai jini ya ɓalle min, wallahi ni dai Ammi na san lafiyata ƙalau ko ciwon kai ba na yi sai da abin nan ya faru gashi yanzu Likitoci sun ce cikin ya zube." Sumayya ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, lallashinta mutanen ɗakin suka riƙa yi sai daga ƙarshe ta yi shiru, su Ammi sun jima a asibitin sannan suka yi wa su Mami sallama suka tafi. Da yammacin Ranar Mommy ta zo hannunta ɗauke da kayan dubiya niƙi-niƙi, da murna Raihan ta tare ta don wannan ne gani na biyu da ta yi wa Mommy bayan aurenta. A lokacin da Mommy ta zo su Mami sun tafi daga Sumayya sai Raihan da Al'amin, sai da ya gaida Mommy sannan ta ce masa Daddy yana bakin gate, a hanzarce Al'amin ya je ya shiga da shi. Daddy bai zauna ba atsaitsaye ya duba Sumayya ya dire mata kuɗi masu yawa sannan ya tafi, Mommy ta lura da irin ramar da Raihan ta yi, ta rame sosai sai dai ta yi haske, amma sai Mommy bata kawo komai ba don a zatonta ita ma ko Raihan ɗin cikine da ita. Ganin yadda zamansu yake ita da kishiyarta sai ta ji daɗi sosai, don ko kaɗan babu wani abu da Sumayya take nunawa Raihan a idon mutane, har a gaban Al'amin ta rage nunawa Raihan komai sai dai ta yi ta kissa da kisisina tana jan hankalinsa ta yadda sai ya yi mata abin da zai baƙanta ran Raihan. Mommy ba ita ta tafi ba sai da dare ya fara yi sannan Daddy ya kirata yana bakin gate don shi ma wata unguwar ya je ya dawo zai ɗauke ta su tafi. Raihan da Al'amin har bakin mota suka rakata suna yi mata ta gaida gida, duk wanda ya ga su Raihan ba zai ɗauka babu wata rashin jituwa a tare da su ba. Kafin su koma ɗaki tuni Sumayya ta kwashe kuɗin da Daddy da Mommy suka ajiye mata ta ɓoye su don a tunaninta Raihan za ta gaya wa Al'amin wanda sam Raihan bata damu da abin da aka bata ba. Sannu a hankali Sumayya ta warware jikinta ya yi sauƙi kafin a sallameta sai da ta samu Likitar ta zana mata irin dokokin da ya kamata ta gayawa mijinta dangane da lalurarta, lokacin da Dr Halima ta ji bayanin Sumayya bata kawo komai ba ta ɗauka tana son a gayawa Al'amin ne don ta samu kulawar da bata samu, don ko kaɗan bata kawo Raihan kishiyarta ba ce saboda irin kulawar da Raihan take yi da ita. Sai da suka gama komai Dr Halima ta kira Al'amin office ɗinta sannan ta ce, "Malam Aminu yau dai mun sallami Sumayya saboda jiki ya yi kyau, amma fa ba yana nufin shi kenan ta ci gaba da aikin gida ba. Ya kamata ta haƙura da mai gida na tsawon wata guda nan gaba, sannan idan da hali a bari sai bayan wata shida ta sake samun wani cikin saboda mahaifarta ta yi ƙwari. Sannan ta daina aikin wahala da duk wani abu da aka san zai jigatata..." Dr Halima ta jima ta gayawa Al'amin hanyoyin da ya kamata su bi don kaucewa sake samuwar wannan matsalar saboda su a ɓangaren asibiti ba su yadda da asiri ko turen iska.


Tun da aka sallami Sumayya Al'amin ya koma ɗakinta da kwana, Raihan ce take komai a gidan ta girka musu abinci ta kai musu wani lokacin ma sai su kusan azahar bata ji motsinsu ba. Ga cin fuska kala-kala da take gani idan ta je kai musu abinci, wannan lamari ba ƙaramin sakata a damuwa ya yi ba ita da Al'amin sai kallo daga nesa, don haka ta ci alwashin samunsa su yi magana don ta gaji da irin zaman gadin da take yi, a ɓangare ɗaya ga wata irin kyara da ta lura yana yi mata abu kaɗan idan ta yi sai faɗa. A ranar wata Juma'a da safe yana shirin fita tana zaune a falo tana jiransa ta ji ƙamshin turarensa ya doki hancinta, muryar Sumayya ta ji cikin shagwaɓa tana faɗin, "Allah sai ka goya ni ka kaini gate haka kawai ka gama gajiyar da ni kuma ban fanshe gajiyata ba."Ji ta yi an buɗe ƙofar tana kallon wurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login