Showing 63001 words to 66000 words out of 157890 words

Chapter 22 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

172

fara ɗari-ɗari da ita, akwai ranar da ciwon ta ya tashi ranar mommy ta je shopping wani store a lokacin daga Goggo sai Inno a gidan, Inno na tafe ta hango Raihan a tsaye ta ƙurawa kusurwar bango ido tana murmushi Inno ta ja guntun tsaki ta ce, "Ƙarfi da yaji Audullahi ya koma bayahude, yanzu saboda Allah yarinyar nan ko makaho ya shafata ai ya san ba ita kaɗai ba ce." Goggo da ƙarasowarta kenan wurin ta karɓe zancen da cewar, "Wallahi don kar na faɗa Abu ta ji haushi na shi ya sa na yi shiru, ki dubi yarinyar kamar jikar ifiritu yau da lafiya gobe ta hau cije-cije ni tun da na yi rayuwa a Albasu ko mai kwantankwacin wannan ciwon ban gani ba." Mama Uwani ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da mopper ta ce, "Gafaranku dai." Cikin haɗin baki suka amsa mata, jin yadda suke yi wa Raihan ya sa ta ce, "Yanzu dai Inno tun da ba wani abu kuka ga ta yi ba don Allah ku sararawa Uwar ɗakina haka." Rufe bakin Mama Uwani ya sa Raihan ɗagowa ta kalle su da jajayen idonta, Inno na ganin haka fara salati tana ƙoƙarin jan ƙafarta zuwa ɗaki. Kamar tsuntauwa haka Raihan ta dira a gaban Mama Uwani ta fisgi mofar hannunta ta fara bin su Inno tama raɗa musu sandar mofar a baya. Ganin Raihan ta tasamma nakasa su ya sa ba shiri suka neman tsira da rarrafe suka fita gate, a lokacin Marigayi Ado mai gadi yana nan, yana zaune yana jin rediyo ya hango su Inno sun tunkaro shi da rarrafe. Da sauri ya nufi wurin yana son kora Raihan gida ta yo kansa gadan-gadan, tana faɗawa Ado su Inno suka samu nasarar bankawa ɗakinsa. Sufa Raihan ta yi ta fisgo ƙafar Goggo ɗaya ta Inno ɗaya ta fara saka baki tana gantsara musu cizo, Mama Uwani ce ta zo ta janye Raiham daga wurin su Inno ban da kuka babu abin da suke yi, Goggo kuwa saboda ruɗewa ta yi fitsari ya kai uku a wurin.

Kafin Mommy ta dawo tuni Raihan ta dawo hayyacinta, sai Mama Uwani ce take sanarwa da Mommy abin da ya faru. Ba ƙaramin tausayi su Inno suka bata ba, tun daga ranar idan za ta fita unguwa ta daina barinta da su a cikin gida dukda dai akwai Mama Uwani. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau ciwon Rihan ya tashi anjima ya lafa, har ta fara girma ta fara nisa a makaranta. Tana gama firamare sai kuma ciwonta ya fara yin sanyi wani lokacin sai ta shafe wata shida wani abu bai faru da ita ba, sai kuma ya zamana idan ciwon nata zai zo ma sai dai ta yanke jiki ta faɗi kamar mai farfaɗiya sai ta kusa wuni guda bata farko ba. Ita ba mai bacci ba ita ba ido biyu ba. Tun da mommy ta duba yanayin ciwon Raihan babu yadda bata yi a nemar mata magani ba amma abin ya ci tura, daga ƙarshe ma ɗaukanta ya yi da Mommy suka sakamakon harkar ƙaro da ya fara yin safararsa daga nan gida najeriya. Ba ƙaramin samu yake yi ba don haka ya ce zamansu a can yafi don a can ne za a newa wa Raihan lafiya yadda ya kamata. Ko kaɗan Mommy bata so ba amma babu yadda ta iya haka suka tafi suka bar su Inno da Mama Uwani a gidan, lokaci bayan lokaci Daddy na turowa ɗaya daga cikin yaran kawunsa kuɗi yana yi wa su Inno duk siyayyar da ta dace.

Daddy da iyalansa ba su suka dawo Nigeria ba sai da Raihan ta gama secondry school a lokacin tana da shekara goma sha shida, sai dai an samu sauki sosai don ciwon nata yana jimawa har fin shekara bai tashi ba, musamman da su Mommy suke kiyaye abubuwan da yake tayar mata da ciwon, amma sukan zo gida lokaci zuwa lokaci a lokacin ƙanwar Mommy wurin haihuwarta biyar. Duk wannan tsahon shekarun da aka ɗauka Mama Uwani tana tare da su Inno suna zaune gwanin birgewa, dawowarsu Nijeriya samari da dama ƴaƴan abokan Daddy sun nuna soyayayrsu ga Raihan, sai dai gabaɗaya babu wanda ta taɓa aminta da shi. Hasalima daga ranar da ka ce kana sonta shi kenan ta yanke duk wata alaƙa da kai, ko kaɗan abin bai damu Daddy ba da yake dama bai yi niyyar aurar da ita a lokacin ba. Ya ci burin sai ta yi karatu mai zurfi ta karanci harkar lafiya, amma ita Raihan sam karatun likitanci ba shi ne a gabanta ba tafi sha'awar lecturing. Mommy tun tana ɗaukan abin wasa da shirmen ƙuruciya har abin ya fara damunta a zuciya, don har Raihan ta kai shekara goma sha takwas babu wanda ya taɓa fitowa ya ce yana sonta ta amshi tayinsa. Hasalima daga ƙarshe samarin ma daina zuwa suka yi, idan mommy ta yi wa Daddy magana sai dai ya rufe ta da faɗa ya ce Raihan nawa take da don bata yi saurayi ba har za a damu. Daga ƙarshe Mommy daina bin ta kansa ta yi, ita ma Raihan ɗin idan mommy ta yi mata magana sai dai ta ce mata ita fa tana da mijin aure. Kusan kullin sai Mommy ta yi nafilar dare ta kaiwa Allah kukanta akan ya bayyana musu abin da yake daminta dan kuma jinkirin aure ne ya sa jinkirin ya zama alƙairi.

MU DAWO LABARI.

Jin Huzaifa ya datse maganar da ya fara yi ya sa Malam Usman ya ce, "Idan baka da abin faɗa Huzaifa kar ka ɓata min lokaci." Huzaifa ya sake numfasawa sannan ya ce, "Wata rana ina shawagi a sararin samaniya ranar ina cikin farinciki, kawai ta raya min na bi gidajen Bil'adam ko na kashe ƙwarƙwatar idona, a wani gida na ci karo da Raihan a lokacin bata fi shekara huɗu a duniya ba. Cikin dare ne don dare ya tsala sosai, tana kwance a ɗakinta wanda ya ƙayatu fa ƴar tsanoni kala-kala, daga gefen gadonta Mahaifinta ne a zaune yana ɗan danne-danne a laptop. Sai wayarsa da take fitar da sautin sasaanyar waƙa turawa, har na yi hiyyar giftawa na hangi surara yarinyar gwanin birgewa kanta ba ɗankwali gashi tana rungume da wani teddy. Shafata na yi nan take naji wani sabon yanayi da ban taɓa ji a jikina ba, dukda na yi mu'amala da matan bil'adam babu adadi amma yanayin da na ji game da ita na musamman ne. Ina cikin wannan yanayin Mahaifiyarta ta shigo ɗakin tana yi wa mahaifinta magana, "Haba Daddyn Raihan. Dare fa mahutar bawa ne ka rinƙa hutawa ranka mana, ga shi ka kunna waƙa biyu saura fa. Ni ma daga yin shafa'i da wuturi shikenan bacci ya yi gaba da ni, yarinyar nan ban san lokacin da ka kwnatar da ita ba." Ina kallo mahaifinta ya miƙe yace, "Ai na gama mu wuce kawai." Mahaifiyarta ce ta ƙaraso wurin da nake rungume da Raihan ta fara yi mata addu'a ba shiri na tashi daga wurin daga ƙarshe ma karatun kur'ani ta kunna mata a waya akan dole na haƙura da gidan gabaɗaya."

Wash🤭 yau na sha typin.



Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ki min mgna 0706 206 2624


23


Na yi tsammanin barina daga gidan zai sa na manta da duniyar Raihan, amma sai dai wani abin mamaki har zuwa wayewar gari haka na yi ta fama da dakon tunaninta. A ranar matata har sai da ta fahimci sauyin da na tsinci kaina a ciki, don sai da ta tambaye ni na ce mata babu komai. A ƴan kwanakin nan haka na yi ta ƙoƙarin ganin na sake shiga gidan amma da na zura kaina zan ji wani tururi, sakamakon a ƴan kwanakin na yi tsammanin mahaifiyarta na yawaita saka karatun alƙur'ani. Duk yanda na yi na sake samun damar ganin Raihan sai abin ya ta'azzara, a gefe ɗaya ni kuma ina ta fama da dakon soyayyarta. Ana cikin haka kwatsam wata rana sun fita unguwa idan ban mata ba gidan wasan yara aka kaita, kawai sai na ga wannan wata dama ce a gare ni domin ranar har Mahaifiyarta sun manta ba su yi addu'ar fita daga gida ba. Dama ba a zancen mahaifinta don shi waɗannan abubuwan ba su dame shi ba, dabbara ce ta faɗo min akan na tunkari wurin da suke cikin siffar ƙadangare don na san mafi yawan mata sun fi tsoronsa. Na yi haka ne don na samu damar da zan kori mahaifiyarta, don yanda na lura ita ce za ta fi bani matsala. Ina zuwa kuwa kamar yadda na yi tsammani haka ce ta faru, ba ita kaɗai ba hatta tsirarin matan da suke wurin duka dare wa suka yi. A madadin na wuce sai na tsaya a wurin na fara tsintar abubuwan da suka ci suka zubar a wurin ina ci, Raihan na ganin haka ta fara watsa min ruwan lemon da ke hannunta. Amma a madadim na ji haushin abin da ta min sai ma ƙara kwanciya na yi a wurin, Mahaifiyarta na daga nesa ta zabura tana kwaɓarta akan ta daina amma nan take Mahaifinta ya rufeta da faɗa wai wata ƙila burgeta na yi. Daga wurin da Mommy take na fahimci irin kallon da take yi min na zargi, don haka ta ƙaraso wurina tana karanta addu'o'i da sauri na matsa daga wurin suka ci gaba da harkokinsu. Tun a wurin na fara tunanin yanda zan shagaltal da Mahaifiyarta don ta rage saka karatu a cikin gida, saboda na samu damar kawo wa Raihan ziyara. Ana cikin haka sai suka shiga shagalin wani bikin ƴan uwansu, tun ranar da mommy ta dawo a gajiye ta kwanta ko addu'ar kwanciya bata yi ba na fara saka mata nauyin bacci haɗe da kasala. A ranar kwana na yi a jikin Raihan tun ina ƙare wa hallitarta kallo har sha'awarta ta fara fisgata na fara kai hannuwa a sassan jikinta. Ranar kwana na yi a jikinta na yi bacci mai daɗin da ban taɓa irinsa ba, daga haka kusan kullin na samu wurin kwana tun Mugaza bata fara zargin wani abu ba har ta fara bibiyar sahuna. A nan ta gano wurin wacce nake yada zango don haka ta kafa mata ƙahon zuƙa, saboda na juya mata baya komai nata baya birgeni, sai da na yi da gaske sannan Raihan ta tsira daga kaidin Mugaza. Tafiya da ta miƙa daga ƙarshe sai na yanke shawarar fara neman aiki a cikin gidansu Raihan, ni da kaina nine na kashe Laraba mai wanke-wanke." Jin wannan furuci na Huzaifa ya sa Mommy da Daddy da ke kan kujeru a zaune suka ɗauki salati cike da mamaki, don ba ƙaramin sabo suka yi ba Laraba ba mace ce mai kirki a lokacin da tana raye. Sun shafe sama da shekara goma tare da ita, kwatsam suka yi wayi gari ta fara wata irin rashin lafiya. Tun tana yi a gidan su Mommy har lamarin ya yi tsamari suka mayar da ita garinsu, suka bata kuɗi masu yawa. Lokaci-lokaci suke zuwa duba ta bayan doguwar jinyarta sai waya aka yi musu Allah ya yi mata rasuwa. Su mommy na tsaka da tunani suka riski Huzaifa ya ci gaba da cewa, "Na kashe ta ne don na san matuƙar na zo neman aiki ba za su ɗauke ni ba tun da Laraba babu abin da ta gaza musu, tun bata bar gidan ba lokacin tana jinya wata rana da safe na zo a siffar tsohuwa na roƙe su akan su ɗauke ni wanke-wanke da aikin gida. Ban samu matsala ba suka amince min na fara rayuwa a cikin gidan, tun zama na a gidan na fahimci sam Mommy bata saki jiki da ni ba, don ba na manta akwai ranar da na ji tana gaya wa Daddy wai duk lokacin da ta zo kusa da ni gabanta yana faɗuwa, tsigar jikinta na tashi. A ranar Daddy ya so aminta da zancenta, ina jin haka a washegari na fara yin duk wani abu da na san zan shiga zuciyar Raihan. Na zama bawa duk don na zamu gurbin zama a gidan, kuma buƙata ta biya domin Daddy na ganin irin kulawar da nake bawa Raihan na kawar da zancen tafiyata. Ita kanta mommy aka ce mai Ɗa wawa tana ganin irin kulawar da nake bawa Raiha ta bar abin a ranta ba tare da ta sake furta wata kalma a kaina ba.

Wannan shaƙuwa tamu ba ƙaramin daɗi ta yi min ba, kuma dama duk dare a wurin Raihan nake kwana. Na fara kusantar Raihan tun tana shekara biyar a duniya, kafin na fara kusantarta har sai da na biya sadaki ba haka kawai na fara haike mata ba. Wata rana Daddy ya ɗauke ta sun fita suna hanyar dawowa motarsa ta ɗan samu matsala, Yana tsaye a gefen titi ita ma Raihan ta fito tana jingine da shi a lokacin Daddy na jiran bakanikensa. Ina ganinsu na ɓullo ta hanyar cikin siffar Tsoho kuma almajiri, Ina ƙaraso wa wurinsu na yi masa bara nan take ya ciro dubu biyu ya miƙa wa Raihan ya ce ta kawo min. Da murmushi na karɓa na ce, "Amaryata ya makaranta." Nan take Raihan ta yi dariya ta ce, "Lafiya ƙalau." Ganin muna wasa da Raihan ya faranta ran Daddy ya ce, "Baba Wannan amaryar taka za ta cika ka da surutu." Na ji daɗin maganar Daddy ƙwarai don haka na ce, "Alhaji ban yi wa amaryar tawa tsufa ba kuwa." Daddy ya ɗauka maganar a wasa ce don haka kai tsaye ya kalli Raihan ya ce, "My Love wai baba ya miki tsufa?" Abinka da yaro Raihan bata san me ake nufi ba don haka ta girgiza kai, Daddy ya yi dariya ya ce, "Ka ji ko ai tun da Raihan na sonka na baka ita." Nan take na ciro dubu ɗaya a cikin kuɗin da aka bani na miƙa mata na ce, "Ga sadaki Amaryata." Kallona ta tsaya tana yi Daddy ya karɓa ya miƙa mata sannan ya sake ƙara min kuɗi, a daidai lokacin bakanikensa ya ƙaraso ganin haka ya sa na yi musu sallama na bar wurin. Tun daga ranar na fara kusantar Raihan, kuma sai na ji matata ta fice min a ka don haka ta fara kawo wa Raihan farmaki. Ana cikin haka ta haifa min yaro namiji, Mugaza na ganin haka ta ɗauke shi ta kashe shi, a lokacin da Raihan za ta haihu na ɗauketa zuwa duniyarmu kuma ta ga abin da ta haifa mai siffar kifi da ƙarninsa, ita kuma Mugaza tana zuwar mata da siffar wasu dabbobin a duk lokacin da za ta ɗauke mata Ɗa. Raihan sai da ta haifar min ƴaƴa masu yawa amma Mugaza tana kashe su sai wannan na ƙarshen ne ba ta samu wannan damar ba, na sha ɗaukan Raihan na kaita duniyarmu na ajiye musu jabinta amma babu wanda ya taɓa lura da haka. Kuma tun zamana a gidan nan basu taɓa fahimtar ni ba jinsunsu bace sakamkon takatsantsan da nake yi. Bala mai gadi ne ya taɓa ankara shi ma a ranar da ya tabbatar da ni wacece a ranar na kashe shi." Wannan karon ma Mommy da Daddy jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, don sun gama tsorata da lamarin Huzaifa. Suka riski muryarsa yana ci gana da cewa.

"Na kashe masu gadi kusan uku sai wannan yaron Kabiru ne ya gagare ni kasancewar ba haka kawai yake zaune ba, yana da riƙo da addini kuma jikina yana bani akwai wani ɓoyayyan al'amari a tattare da shi. Na kashe samari kusan Biyu a kan Raihan saboda na lura suna yunƙurin bani matsala, kuma har gobe ba zan taɓa bari Raihan ta ƙaunaci wani namiji bayan ni ba. Lokacin da na tafi nemar mana mafita gabannin bayyanar hallitata ta ainihi, na ji labarin ta faɗa soyayyar wani yaro tabbas sai na hallaka shi. Kuma abin farimcikin ma kisa zan yi masa mai matuƙar wahalarwa." Huzaifa na gama maganar Malam Usman ya ce, "Idan har na barka a raye ko?" Malam bai saurari abin da Huzaifa zai faɗa ba ya buɗe masa wuta da ayar Allah, duk irin roƙo da magiyar da Huzaifa ya yi Malam bai saurara masa ba sai da ya yi lugub da ƙyar yake iya magana ya ce, "Malam wallahi zan fita." Malam Usman ya ce, "Ta ina za ka fita?" Huzaifa a galabaice ya ce, "Ta ido zan fita." Da sauri Malam ya ce, "Ba za ka fita ta ido ba ka sauya wuri." Huzaifa ya ce, "Zan fita ta hannu ko ƙafa." Wannan karon Malam ya ce, "Ka fita ta hanci kuma umarni ne nake baka." Huzaifa ya yi shiru bai sake magana ba, ganin haka ya sa Malam ya ci gaba da karatu. Sai da Huzaifa ya ji Malam ya tasamma halaka shi ya ce, "Wallahi zan fita ta hancin." Malam Usman ya ce, "Maza ka fice kuma babu kai babu ita har abada ka ji mai nace?" Huzaifa ya amsawa Malam. Yana gama magana Raihan ta fara jero atishawa ba adadi.

Ajiyar zuciya Malam Usman ya yi yana furta, "Alhamdullah." Kayan aikinsa Yaransa mata suka shigo suka fara kwashe wa jin hamdalar da Malam ya yi ya sa su Mommy suka fahimci an yi nasara. Fitowa ya yi ya ce Malama Rahama da Mommy su shiga su taimaka mata don jikinta gabaɗaya babu ƙwari, a hankali Raihan ta fara kallon wurin tana ganin Mommy ta miƙa mata hannu. Mommy ɓoye ƙwallar idonta ta yi don kar Raihan ta fahimci abin da yake faruwa, ɗakin da Raihan take har da toilet a ciki don haka mommy ta taimaka wa Raihan suka shiga ta sauya kaya, kafin su fito Malama Rahama ta kunna garin habbatussauda. Da mamaki Raihan ta dubi Mommy ta ce, "Mommy ina ne nan?" Mommy ya ce, "Raihan baki ji daɗi ba ne muka kawo ki nan amma insha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login