Showing 156001 words to 157890 words out of 157890 words

Chapter 53 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

143

sake kare mu ya tsare mu daga kaidinsu bakiɗaya. Daddy ya amsa da Amin.

Al'amin da Raihan buɗe shafin soyayya sabuwa dal suka yi suna gurzar amarci, Al'amin idan ya shiga ɓangaren Raihan sai sallah ce take fito da shi, Sumayya na daga ɗaki take jiyo hayaniyar wasanninsu da iface-ifacen wasannin soyayya, sai dai idan abin ya yi mata ciwo ta yi kuka ta share hawayenta. Ga shi har lokacin Al'amim ya ƙi sakin jiki da ita ya yarda da ita, komai ta bashi gani yake kamar ta saka asiri a ciki don wani lokacin ma sai ya sakata ta ɗanɗana yake cin abincin ko abin sha. A hankali har Raihan ta fara fahimtar yanayin zaman nasu don haka ta samu Al'amin da maganar da farko ya ƙi sauraronta, sai daga baya ya fahimceta sannan ya ci gaba da bawa kowacce kwana bibbiyunta a lokacin da kwananta na amarci ya ƙare. Sumayya ta sauko sosai ta kama Raihan hannu bibbiyu suna zamansu cikin kwanciyar hankali. Raihan watanta uku laulayin ya takura mata, wata rana da safe Al'amin na shiryawa bayan ya fesa turare da gudu Raihan ta tafi banɗaki tana kwara amai, sai da ta fito a galabaice Al'amin zai ruƙota ta sa hannu ta toshe hanci tana faɗin, "Love don Allah mu je asibiti aman nan ya takura min ga warin turarenka babu daɗi." Ƙarasawa ya yi wurinta ya shafa saman cikinta ya ce, "Ajiya ce na yi anan ki bar damun kanki amma dole dama za mu je asibiti sai na dawo daga wurin aiki ko mu bari sai gobe." Gyaɗa masa kai kawai ta yi don yadda take jin ta tana buɗe baki za ta iya yin wani aman saboda yadda warin turaren yake yamutsa hanjin cikinta.


Kabiru ya warware garau, Maryama ta yi wani irin haske da yake laulayin ciki ya karɓeta. A cikin wannan ƴan kwanakin Kabiru ya sayi fili a unguwar Maidile ya fara ginawa, Daddy ne ya wuce masa kan gaba aka yi cinikin filin sannan ya mayar da hankalinsa wurin ginin gidan. Laulayi ya saka Raihan a gaba sosai ta rame ta yi wani irin haske, wata ranar Litinin bayan Al'amin ya kaita asibiti ya sauketa a gida idan ya dawo da daddare zai ɗauketa su wuce gida. Raihan ba haka ta so ba ta so ace ya barta a gida ta kwana biyu saboda ta sake warwarewa don ko abincin kirki bata ci. Bata da abinci ban da kwaɗon rama da zogale, don haka kusan kullin sai Al'amin ya saya ya kai mata. Shi ma tana cin na kwana biyu ya fita daga kanta, tana zaune Mommy ta ƙaraso cikin falon. Da gudu Raihan ta maƙale Mommy tana faɗin, "Mommy wai Ina MD ban ji motsinsa ba?" Mommy ta zauna tana faɗin, "Daddynku ya fita da shi, kin san Allah Raihan kar ki karya ni ina zaune ƙalau ki cuci mijina ki gudu gidanki ki bar ni." Inno da ke gefe ta saki murmushi tana faɗin, "Raihane ni kam wai gidanku akwai safayar ɗaki ko?" Raihan kanta tsaye ta ce, "Eh akwai me za a yi Inno." Inno ta ɗaga hannuwa sama ta ce, "Alhamdulillahi. Allah ya sani haɗa kayana zan yi na koma gidanki da zama, ina dalili ciki ya saka ki a gaba wai Aminu yana baki abinci kina ƙoshi kuwa?" Raihan ta tura baki ta ce, "Wai ke Inno ce miki na yi ciki gare ni?" Goggo ta yi dariya tana ɓallo mata goro ta ce, "Shakiyyar yarinya ga idanunki da hannuwanki nan sun nuna, amshi goro ko kyaji daɗin bakinki kin ji. Ai zuwa Albasu ya kama ni don na ci alwashin babu wanda ba zai zo ba idan kin sauka, Daddawa ma zan sa a yi mini ta kwano guda." Kunyar duniya ta kama Raihan don su Inno babu ruwansu ban da sako zance babu abin da suke yi. Suna nan zaune suna hira Daddy ya dawo, bayan sun gaisa Daddy ya kira Mommy ɗaki. Cikin damuwa ya dube ta yana faɗin, "Zainabu an ya yarinyar nan tana jin daɗin zaman gidan yaron nan kuwa?" Mommy ta yi murmushi ta ce, "To me ƴa me kuma ka gani?" Daddy ya sauya fuska cikin damuwa ya ce, "Na ga fa ta rame ta lalace gaskiya..." Dariyar Mommy ce ta katse shi sannan ta ce, "To ramar Raihan dai ba komai ba ce Jika za ka samu don yanzu haka daga asibiti suka dawo mijinta ya sauketa, kuma na tabbata ciki gare ni don su Inno tuni sun harbo jikinta." Farinciki ne ya mamaye fuskar Daddy, kamar almara haka yake ganin abin wai shi ne zai ga ɗan da Raihan za ta haifa. Bayan sallar Isha'i Al'amin ya zo har gida ya tafi da ita, sun jima suna hira da Kabiru a ƙofar gida. Lokacin da Al'amin ya zo Raihan na sashen su Inno wuro suna hira, lokacin da za ta tafi har ƙulle-ƙulle Inno wuro ta yi mata dangin su Daddawa da kuka. Raihan ta ɗauki Inno wuro kamar kakarta haka Maryama ta ɗauki Raihan tamkar yayarta don ita take koya mata abubuwan kula da miji da haɗin magungunan da zata gyara kanta. Don haka ta sake zama dass a zuciyar Kabiru, har idan ta yi wani abun ba ƙaramin mamaki take bashi ba. Su Raihan suna komawa gida suka samu Sumayya a falo, tana ganinsu ta ɗauke kai gefe tana tura baki da alamun fushin wasa. Raihan tun daga bakin ƙofa ta nuna Al'amin tana wara hannu haɗe da faɗin, "Wallahi ban da laifi ko ɗaya mijinki ne." Hannuwa biyu Al'amin ya sa ya riƙe kunne ya ce, "Kaina bisa wuya ranki ya daɗe." Sumayya ta miƙe sai da ta je gabansu sannan ta ce, "Wallahi kin ci daraja babyna ke ba zan baki punishment ba amma kai dai Hubby sai ka ɗana tsallan kwaɗo." Raihan ta dubi Al'amin tana yi masa gwalo ta fara tafiya ɗaiɗai sannan ta ce, "Dama ai na ce maka ka zo ka ɗauke ni da wuri kar mu barta ita kaɗai a gida ka ƙi." Al'amin ya marairaice murya yana ƙoƙarin tsugunnawa ya furta, "Ni ma fa aiki ne ya yi min yawa amma ya na iya guda nawa zan yi?" Sumayya da Raihan suka saka dariya don yadda Al'amin ya yi maganar sai ka rantse da Allah kuka zai yi. A falo suka zube Sumayya ta kawo musu abinci, kaɗan Raihan ta fara ci ta ji ya fita daga ranta sai furar da Al'amin ya siyo musu ta iya sha sannan suka ci gaba da hira. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya zaman Raihan da Sumayya lafiya ƙalau babu wata matsala, a haka har cikinta ya tsufa ya shiga watan haihuwarta. Gabanin za ta haihu Sumayya ta samu ciki don ma ita bata cika laulayi mai wahala ba sai dai yawan baccin da take yi. Ranar wata juma'a da asuba Raihan ta tashi da naƙuda ba shiri suka tafi asibiti anan ma wuni ta yi cir tana naƙuda sai ƙarfe ɗayan dare Allah ya sauketa lafiya ta haifo Jaririyarta mace gwanin sha'awa. Kamarta ɗaya sak da Al'amin sai hasken fatar Raihan da ta ɗauko, Sumayya ita ta kula da ita a asibiti har a washegari aka sallameta suka wuce gida. Farinciki wurin Al'amin da su Mommy abin baya musaltuwa, Al'amin ya so a wuce da Raihan gidansa amma su Mommy suka buƙaci da a kaita gida. Kusan kullin sai sumayya ta je har sai da aka yi suna, ranar suna Jaririya ta ci sunan Zainab ake kiranta da Nihla. A lokacin da Raihan ta haihu tuni Kabiru ya kammala gidansa sun koma can har su Inno wuro da zama, Maryama ta sake haihuwar Jaririnta namiji kyakkyawa mai kama da ita, sha tara ta arziƙi su Kabiru suka haɗowa Raihan Daddy ba ƙaramin daɗi ya ji ba. A haka har Raihan ta shafe kwana Arba'in da haihuwa, ranar da ta yi kwana Arba'in da ɗaya Al'amin ne ya je gidansu yana fitowa daga mota Kabiru na parker Lifan ɗinsa Maryama ta sauko, sai da suka gaisa ta wuce ciki ta bar Kabiru da Al'amin suna gaisawa Kabiru na zolayarsa sannan suka shiga cikin gidan. A falon baƙinsu Raihan take saukar Al'amin yana zaune ta shigo sanye da doguwar rigar Abaya, sai baza ƙamshi take ga wata ƙiba da ta yi jego ya karɓeta. Nihlanta ta ƙara girma tana shiga ya rungumo su ya haɗe goshinsu wuri ɗaya, a ɗan kunyace Raihan ta fara ƙoƙarin ƙwacewa tana faɗin, "Kalbee kar fa wani ya shigo." Al'amin ya sake matseta yana faɗin, "Wai don Allah yaushe za a mayar min da matata, i always miss you, yau fa kina Fourty one days." Cikin zolaya Raihan ta ce, "Ka san mu sai an yi Arba'in uku ake mayar da mace gidanta idan ta haihu..." Tun bata ƙarasa ba Al'amin ya katseta da cewar, "What? Ashe kuwa su Mommy za su neme ki su rasa don wallahi guduwa zan da matata." Raihan ta saka dariya ta ce, "Amma wallahi da an yi mara kunyar siriki, amma ina ƙanwata ya jikinta." Al'amin ya karɓi Nihla sannan ya ce, "Wallahi tana nan jikinta da sauƙi kullin sai ta yi min maganar yaushe za ki dawo." Daga bakin ƙofa suka ji muryar Kabiru yana faɗin, "Za mu iya shigowa ko mu koma?" Cikin Shakiyanci Al'amin ya ce, "Gaskiya ka koma don ina tare da iyalina kar ka shigo a samu matsala." Kabiru ya ɗaga labulen ɗakin cikin dariya ya ce, "Wallahi sai dai ka yi wa Gwauro wannan gorin daɗin abin na riga shiga daga ciki, nima kuma tare da matata nake." Al'amin ya yi dariya sannan ya furta, "Oho dai amma baka ji me haushe ya ce ba Mai mace ɗaya aminin gwauro." Kabiru ya rungumo Maryama ya ce, "In dai haka ne ni da kai ai ɗaya muke yanzu, tun da sai dai ka zo ka rage zafi ka yi gaba yanzu ma zan shiga na ce su Mommy su bari sai ta ƙara Arba'in huɗu nan gaba." Raihan ta dubi Kabiru tana faɗin, "Fillo ban san lokacin da ka ƙuna ba wallahi yanzu baka kunyar faɗar magana sam." Har ya juya za su tafi ya juyo ya ce, "Gashi nan ki hukunta mijinki shi ya lalata ni da surutu don wallahi idonsa a soye yake." Gabaɗaya suka saka dariya lokaci ɗaya.




TAMMATA BIHAMDULILLAH🥰

Anan littafin nan ya zo ƙarshe ta yiwu akwai kura-kurai da wasu abubuwa da kuka karanta da bai yi muku daɗi ba, ni ƴar Adam ce tara nake ban cika goma ba kuskuren da na yi a labarin Allah ya yafe mana gabaɗaya. Faɗarkawar da na yi Ubangiji ya ba mu ikon ɗauka ya tsare mu daga sharrin dukkan wani shaiɗani. Na gode sosai da yadda kuka juri karanta labarin nan ba dare ba rana yau na yi posting gobe ban yi ba, na ji daɗi ƙwarai da yadda kuka saka kuɗinku kuka sayi abin da na rubuta wannan ma ƙauna ce kuma ina alfahari da haka. Allah ya bar zumunci ya saka da alheri ya bar zaman tare.🌚 Mu haɗe nan gaba cikin wani littafin, shima salonsa daban yake lbrn na musamman ne, za ku ji tsantsar zalinci😰 ban tausayi da Al'ajabi.

Don Allah a taya ninda addu'ar samun nasara Monday zan fara exams👏🏼

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki yi min mgn 0706 206 2624







Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login