Showing 135001 words to 138000 words out of 157890 words

Chapter 46 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

142

ɗari uku da suka wuce ya taɓa zuwa tsibirin nan har ya ci ni da yaƙi don haka nake jin ɗar a zuciyata domin sun dogara da Alƙur'ani. Na sani kaima ka sani Alƙur'ani zancen gaskiya amma saboda..." A hanzarce Huzaifa ya furta, "Dakata Jabbu. Ba na buƙatar jin yabo da ambaton kowanne addini bayan wanda na buɗi ido nake gani kuma nake wanzarwa." Jabbul-ƙasi bai damu ba don haka ya murza hannun kujerar da yake kai nan take ya koma cikin ƙarƙashin ƙasa. Inkiya Huzaifa ya yi nan take wasu tsuntsayen Aljanu suka ƙaraso suka kwasu su Hatsabibiya kai tsaye aka fara wucewa ɗakin horo da su, ana watsa su ciki kofar wurin ta shafe gabaɗaya.

A fusace Al'amin ya nunawa Raihan ƙofa ya ce, "Fice min daga gida." Idanunta ne suka ciko da ƙwallah tana shirin yin magana ya buga mata tsawa da cewar, "Fice min daga gida na ce." A tsorace Raihan ta juya za ta koma ɗaki ta ji ya fisgota yana faɗin, "Kina hauka ne baki ji me na ce ba?" Jikin Raihan na rawa ta ce, "Kaya zan saka..." Da ƙarfi ya wurga ta jikin ƙofa yana faɗin, "Baƙar munafuka kina kunyar za ki riƙa mu'amala da maza? Ki fice min daga gida na sake ki saki ɗaya, na sake ki saki biyu na sake ki saki uku babu ni babu ke ko a lahira ba na fatan haɗuwa da ke." Wani irin abu Raiha ta ji yaaaam! A tsakar kanta kalaman Al'amin suka fara yi mata amsa-amo adodon kunnenta. Bata ankara ba ta ji ya fisgi hannunta da ƙarfi bai kaita ko'ina ba sai ƙofar gida ya wurgar, da sauri ya dawo kan Sumayya da je kwance cikin jini don tun buguwar da mutumin ɗakin Raihan ya yi mata jini ya fara zuba. Da sauri ya ɗauketa ya saka a cikin mota ya fice daga gidan, Raihan na gefe a zauna ya fito a mota ya saka wa gidan key ya tayar da motar ya bar wurin. Daga ita sai ɗaurin ƙirji haka ta kunce ɗankwalin kanta ta rufe kanta da kafaɗarta ta fara takawa, tafiya take ba tare da tasan inda take jefa ƙafarta ba. Gani take tamkar a mafarki don har a lokacin da take tafiya bata gama gasgata abin da yake faruwa a duniyarta ba. Tana tafe a gefen titi mutane sai kallonta suke, wasu ma kallon mahaukaciya suke mata ya yinda wasu suke yi mata kallon mabaraciya. A bakin titi ta tsaya duk Ɗan sahun da ta tsaida sai dai ya wuce, tana nan tsaye wata mota ruwan toka ta faka a gabanta. Daga mazaunin mai zaman banza aka buɗe tana fitowa ta furta, "Matar Yaya." Kallon wurin Raihan ta yi tana ganin Fatima ta furta, "Na yi rashin masoyi Fatima, na rasa Salim na rasa masoyi na har abada. Na san Salima da yana raye ba zai min haka ba kuma ba za taɓa bari a yi min haka ba." Kallon yanayinta Fatima ta yi ta furta, "Matar yaya daga ina kike haka." Idanun Raihan suka ciko da ƙwalla ta ce, "Daga gidana nake don Allah ki kaini gida." Ba ta musa ba ta buɗe mata baya sannan ta ce, "Tare muke da Abban Salim (Mijinta) bari mu sauke ki." Raihan bata amsa mata ba ta shiga motar sai kawai ta kifa kai a cikin cinyoyi ta ta fashe da matsanancin kuka.


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624


48


Kukan da Raihan take yi har cikin zuciyar Fatima don haka ita ma ta ji duk babu daɗi ga shi bata son ta tambayeta don ta fahimci tana cikin wani irin yanayi. Nuna wa mijinta hanya ta riƙa yi har ya nufi unguwarsu Raihan, a daidai ƙofar gidansu Raihan ya yi parking ɗin motar jin haka ya tabbatarwa mata da an ƙaraso gidansu. Ɗagowa ta yi fuskarta jawur ta furta, "Na gode Fatima." Daga haka bata sake furta komai ba ta fice daga motar, kai tsaye gate ɗin gidansu ta fara bugawa tana nan tsaye ta ji motar su Fatima ta bar wurin. Daga cikin gidan ta ji ana faɗin, "Waye?" Murya na rawa Raihan ta furta, "Ni ce." Daga cikin gidan ta ji an sake cewa, "Alhaji bai daɗe da shigowa ba, ku yi haƙuri zuwa safiya." A tunaninsa irin matan da suke zuwa maula ne, saboda duhun magriba ya fara yi. Da ƙarfi Raihan ta sake buga ƙofar tana faɗin, "Ni ce Raihan ka buɗe min." Da sauri ya zare sakatar ƙofar ta tura ta shiga ba tare da ta bi ta kansa ba. Da idanu Auwalu ya bita don ba ƙaramin mamakin ganinta ya yi a wannan ɗokacin ba, tafe take ƙafa babu takalmi zani a tsangale babu kykkyawan mayafi a jiki, tana cikin tafiya hango Daddy akan baranda da alamu waya yake don ta riske shi yana faɗin, "To shi ke nan Malam haka za a yi, don lamarin yaron akwai rikitarwa. Zan kira su a waya na sa su kawo shi don a san abin yi..." Maganarsa ce ta maƙale sakamakon hango Raihan na tunkaro shi ƙafa ko takalmi babu. A hanzarce ya furta, "Zan kiraka Malam." Katse wayar ya yi da sauri ya ƙarasa wurin Raihan yana faɗin, "Raihan! Ke ce a daren nan? Daga ina kike?" A madadin ta bashi amsa sai kawai ta faɗa jikinsa ta rushe da matsanancin kuka. Jikin Daddy har rawa yake ya fara hangen bakin gate sai ya ɗago ta yana faɗin, "Wai me ya faru ina Al'amin ɗin?" Cikin matsanancin kuka Raihan ta furta, "Ya sake ni Daddy. Al'amin ya sake ni ban san me na yi masa ba." Sak Daddy ya yi yana jin maganar Raihan na zaga ƙwaƙwalwarsa, rungumota jikinsa ya yi ya ja ta cikin gida. Lokacin da suka shiga Inno da Goggo na falo a zaune suna cin Abinci Inno ta furta, "Saboda Allah me ake da sirika irin Zainabu, yarinyar nan na riƙe ta tsakani da Allah kamar yadda na ɗauki Audullahi amma kulli ta riƙa dafa mana shinkafa kayan basir, yanzu don Allah Zinaru idan ciwon suga ya samu matsuguni a jikinmu wa gari ya waya?" Goggo ta taɓe baki tana tura kwanon gabanta gefe ta ce, "Wallahi ko mutuwa na yi a gidan nan kina da kamasho saboda kullin sai na yi niyyar komawa Albasu ki ba ni haƙuri, ina dalili Audullahi yana da kuɗi daidai misali yau ko gonar masara ba zai iya siya don ya kawo a riƙa dafa mana ba? Ita kuma Abu son namiji ya rufe mata ido sai abin da yake so za ta girki mu ko oho." Inno ta wara hannuwa sannan ta ce, "Bar ta Namiji ƙarin kunama ne balle Audullahi da ya yi rayuwar turawa ina jin tsoron kar wataran ya auro mata Elizabet..." Maganar Inno ce ta maƙale ganin Daddy rungume da Raihan tana kuka, kusan tare suka tashi Goggo na salallami. Inno ta gyara ɗaurin ɗankwalinta tana cewa, "Audullahi wa nake gani da tsohon daren nan?" Zaunar da Raihan ya yi a kujera ya furta, "Raihan ce." A tsorace suka dubi Daddy, Goggo ta dafe ƙirji ta ce, "Raihan kuma a daren nan meye haka na ganta kamar korarriya. Ni wallahi ko a Albasu ban taɓa ganin ziyara irin wannan ba." Mommy ce ta ƙarasa cikin falon hannunta ɗauke da Muhammad ta cewa, "MD wallahi ka fiye rigima ka zauna a wurin su Inno amma fir ka..." Maganarta ce ta maƙake ganin su Inno carko-carko suna tsaye akan Raihan da take sharɓar kuka. Jikinta har rawa yake ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Daddyn Raihan lafiya me yake faruwa?" Daddy ya kalleta fuska babu walwala ya ce, "Je ki da ita cikin ɗaki ki taimaka mata ta yi wanka da saka kaya." Cike da damuwa Mommy ta dubi Raihan tun daga ƙasa har sama ta ce, "A ina ka tsinto ta Daddyn Raihan ko a hanyar Office ɗinka? Ya na ganta kamar ko takalmi babu kamar wata korarriya..." Daddy ya katse ta da cewar, "Ki wuce da ita ciki na ce." Hannun Raihan Mommy ta kamo suka wuce ɗaki suna shiga Mommy ta zaunar da Raihan akan gado tana tattaɓa jikinta ta furta, "Daga ina kike haka Raihan ko kaya babu a jikinki?" Raihan ta kwantar da kanta a jikin mommy tana ƙwalla ta furta, "Mommy ya sake ni." Zaro ido Mommy ta yi tana ja da baya ta furta, "Wa kenan waye ya sake ki me kika yi masa?" Kuka ne ya sake ƙwacewa Raihan ta ce, "Ban sani ba Mommy, ban san me na yi masa ba." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke sannan ta ce, "Shi kenan shiga ki watsa ruwa ki same ni a falo." A hankali Raihan ta shiga toilet sannan mommy ta dawo falo ta samu su Inno ban da faɗa babu abin da suke yi, Daddy ne ya dubi su Inno ya ce, "Inno ba a yanke hukunci ta bakin mutum ɗaya, ya kamata mu tsaya mu ji ta bakin yaron nan kafin mu yanke masa hukunci ta yiwu akwai abin da ya haɗa su wanda ba mu sani ba." Mommy da ranta ya kai ƙololuwar ɓaci ta karɓe zancen da cewar, "Amma ko me ta yi masa bai kamata ya koro mana yarinya a wannan lokacin ba, ka lura da jikinta ko riga babu daga ita sai ɗaurin ƙirjin wannan wanne irin wulaƙanci ne?" Duk da zuciyar Daddy na raɗaɗi bisa abin da ya faru sai ya danne ɓacin ransa ya furta, "Duk ba wannan za mu duba, kamata ya yi mu duba mu ji ta bakin Raihan idan muka ji ta bakinta sai na nemi Malam na ji abin da yake faruwa, saboda da alama bai san abin da yake faruwa ba tun da muna tsaka da waya da shi ta shigo." Mommy bata tanka ba sai jinjina kai da take yi, su Inno kuwa ba su yi shiru ba ban da ɗebewa Al'amin albarka babu abin da suke yi ba.

Al'amin na zuwa asibiti aka karɓi Sumayya aka shiga bata kukawar da ta dace, ban da zarya babu abin da yake yi lokaci-lokaci yake kaiwa iska naushi. Lambar Mahaifiyar Sumayya ya kira nan take yake sanar musu halin da ake ciki, yana gama waya da ita babu jimawa ya kira lambar Ammi ita ma ya sanar mata. Mahaifinsa ne ya faɗo masa a rai don haka ya ji gabansa ya yi wani mummunar faɗuwa. A ɗarare ya kira Malam tana fara shiga ya ji an ɗauka, sai dai yanayin yadda ya ji muryar mahaifinsa ya tabbatar masa da bai san abin da yake faruwa ba. Har lokacin jikinsa a sanyaye yake ya sanar masa abin da yake faruwa da Sumayya da asibitin da suke, a gaggauce suka yi sallama Malam ya ce zai ƙaraso. Abin duniya goma da ashirin ne ya dagula lissafin Al'amin, wani irin fargaba da tashin hankali ya riski kansa a ciki, amma da ya tuna irin cin kashin da Raihan take yi masa sai ya ji ƙwarin gwiwa ta lulluɓe shi. Ammi ce ta fara shiryawa ta tafi asibitin tana sauka daga Adaidaita sahu mahaifiyar Sumayya da ƙannenta suka ƙaraso, fuskokinsu ɗauke da damuwa suka gaisa haɗe da jajantawa juna abin da ya faru. A harabar asibitin suka samu Al'amin da ke kai-kawo, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Ganin Ammi ya sake tsinka hanjin cikinsa, suna ƙarasowa wurinsa ya tattaro jarumta ya gaishe su. Mahaifiyar Sumayya ta dube shi sheƙeƙe tana faɗin, "Al'amin garin yaya haka ta faru ko wannan karon ma kunamar aka sake turo mata?" Sosa kai Al'amin ya yi ya ce, "Amm dama dai...dama..." Ammi ta yi masa kallon tsaf cikin tausayawa don ba ƙaramar damuwa ta gani kwance a fuskarsa ba. Waigawa ta yi ta ce, "Ina Raihan ne ko bata ƙaraso ba?" Da sauri Al'amin ya furta, "Na'am Raihan...Ehto...Dama..." Wata Nurse ta katse Al'amin da cewar, "Ina mijin Sumayya ko ƴan uwanta suke?" Da sauri Al'amin ya isa gabanta ya ce, "Gani." Juyawa ta yi ta ce, "Dr yana son ganinka yanzu." Tun bata rufe baki ba ya bi bayanta suka ƙarasa Office ɗin Dr Mu'azzam. Su Ammi na tsaye jigum-jigum da ka dubi fuskokinsu za ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa.

Bayan Raihan ta fito daga wanka doguwar rigar Mommy ta zaman gida ta saka, har lokacin fuskarta a kumbure take ta ƙarasa falon. A inda ta bar su a nan ta koma ta same su, tana zuwa Daddy ya nuna mata kujera yana faɗin, "Zauna nan." Ta lura da Fuskar Daddy babu alamun wasa don haka jikinta ya yi sanyi, a takure ta zauna Daddy ya dube ta yana cewa, "Laifin me kika yi Al'amin ya sake ki don na san haka kawai ba zai sake ki ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba." Hawaye ne ya zubo mata ta kalli Daddy za ta yi magana kuka ya ci ƙarfinta. Murtuke fuska ya yi cikin tsawa ya ce, "Ba kuka na ce ki raira min ba amsa za ki ba ni idan ba haka ba, ranki ya yi mummunan ɓaci." Tun da take da Mahaifnta wannan ne karo na farko da ta gan shi a wannan yanayin ba, bakinta na rawa hawaye na zuba ta ce, "Wallahi ban san me na yi masa ba ina fitowa daga wanka na ji ihun Sumayya, zuwana wurinta ke da wuya sai kawai ya wanke ni da mari daga ƙarshe ya ce ya sake ni." Kafe ta da Ido Daddy ya yi tana rufe baki ya furta, "Kin tabbata abin da kike faɗa haka ne?" Raihan ta gyaɗa masa kai. Inno ta yi kicin-kicin ta haɗe fuska Daddy na miƙe wa ta ciro wayarta daga cikin ɗan tofinta ta miƙe masa tana faɗin, "Audullahi ungo kira min Faruku." Da mamaki Daddy ya ce, "Inno wane Faruku kuma." Inno ta sake ɗaure fuska ta ce, "Faruku barista ɗan uwana za ka kira min wallahi mai hana ni ɗaure wannan fitsararren yaron Aminu sai Allah, saboda Allah baiwa aka kai masa zai rufe ta da duka ya korota kamar mara gata?" Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "To kawo akira shi." Daddy karɓa ya danna lamabar Inno ya kira don ya san idan ba haka ya yi mata ba, tun da ta hau sama ba za ta yadda da duk lallashin da zai yi mata ba. A kunnenta ta ji ƴar baturiya na magana, don haka ta ja dogon tsaki ta miƙa hannu ta karɓi wayar tana cewa, "Allah wadaran naka ya lalace shi dai Faruku a haka zai ƙare kullin waya a kashe." Daddy fita ya yi ya bar su Inno suna ta sababi. Ita kuwa Mommy baƙinciki goma da ashirin ne ya mamaye zuciyarta, don haka uffan bata tanka musu ba tana ayyana abubuwa da yawa a cikin zuciyarta. Da farko Daddy ya yi niyyar ya taka har gidan Malam ya same shi amma sai ya yanke shawarar kiransa a waya, ɗakin da yake saukar baƙi ya shiga ya zauna ya danna wayar Malam bugu biyu Malam ya ɗauka da sallama sannan ya ce, "Alhaji ɗazu muna magana ba mu ƙarasa ba." Muryar Daddy babu walwala ya furta, "Malam akwai ƴar matsala." Da sauri Malam ya furta, "Ta me fa?" Nan take Daddy ya zayyane masa duk abin da yake faruwa, salati Malam ya ɗauka ransa a matuƙar ɓace ya furta, "Yanzu haka Al'amin zai watsa min ƙasa a ido ban sani ba, ni Al'amin zai wulaƙanta ya nuna ban isa ba kenan?" Daddy ya ce, "A'a Malam abi lamarin a sannu kasan sha'anin yaran nan ka fara jin ta bakinsa ka ga sai a ji komai." Malam cikin huci ya furta, "Ina zuwa Alhaji." Malam ya kira wayar Al'amin ya fi a irga amma ba a ɗauka ba da yake ya saka ta a silient. A fusace ya shi ga motarsa kai tsaye ya nufi asibitin, saboda tsabar sauri gani yake hanyar na ƙara yi masa tsayi. Wurin da aka tanada saboda ajiye motoci (Parking space.) Ya ƙarasa ya ajiye motarsa, a gaggauce ya fito ya ƙarasa cikin asibitin tun daga nesa ya hango Al'amin a bakin wani ɗaki a tsaye. Al'amin na hango Malam hantar cikinsa ta kaɗa gabansa ya yi mummunar faɗuwa, Malam na ƙarasawa Ammi ta furta, "Malam har ka ƙaraso?" Bai tanka mata ba ya ƙarasa wurin Al'amin ya ɗauke shi da wani azababban mari, yana ɗago wa ya sake ɗauke shi da wani marin. Takaici, baƙinciki haɗe da baƙin rai suka sake mamaye zuciyar Malam. Ya dubi Al'amin a fusace yana faɗin, "Na gode Al'amin, na gode ka ji. Yanzu ka nuna min na haife ka ne amma ban isa da kai ba. Wallahi ka ji na rantse idan har ni na haife ka, ka je maza ka ɗauki ƴar mutane ka wuce gidanka da ita." Ammi da bata fahimci komai ba ta shiga tskiyar su Malam tana faɗin, "Me yake faruwa Malam?" Da hannu ya nuna mata Al'amin sannan ya furta, "Ki tambayi ɗanki zai gaya miki irin rashin mutumcin da ya aikata." Malam ya juya a fusace zai bar wurin har ya fara takawa ya juya ya ce, "Idan ka ga dama ka same ni a gida." Daga haka bai sake furta komai ba ya wuce ya shiga motarsa ya fice daga asibitin. Da tsananin mamaki Ammi ta dubi Al'amin ta ce, "Me yake faruwa Al'amin." Al'amin da hankalinsa ya fi na koyaushe tashi ya ce, "Ammi laifi ne don na saki Raihan alhalin cin amanata take yi, Ammi har fa maza take kawo min cikin gida amma kina jin abin da Daddy ya faɗa." Idanu ta zaro waje ta ce, "Innalillahi'wa'inna'ilahirraji'un. Yanzu dai kar ka ɓata lokaci ka ga a yadda mahaifinka ya fita maza ka je kiran da ya yi maka." Amsa mata ya yi jiki babu ƙwari ya wuce wurin da motarsa take, Mahaifiyar Sumayya ce ta cika fam don ba ƙaramin haushi ta ji ba ganin irin abin da Malam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login