Showing 45001 words to 48000 words out of 157890 words

Chapter 16 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

179

ɗan makarantar ku ne Raihan?" Raihan ta gyaɗa fuskarta ɗauke da murmushi don har ayyanawa take sun tsunduma cikin soyayya. Kwanan Raihan ɗaya aka sallameta saboda babu wani abu da yake damunta, a ranar ne Daddy ya fara binciken Al'amin sai dai ko mai kama da shi babu wanda ya ce ya sani. Wannan maganar ba ƙaramin ɗaga hankalin Raihan ta yi ba, hatta abinci sai mommy ta yi da gaske take samu ta ci. Ga binciken duniya da likitoci suka yi sun ce bata da wani ciwo sai matsalar damuwa (Depression) ce ta yi mata yawa, don haka za ta riƙa abubuwa kamar mara hankali ko shafar iska. Daddy na jin wannan bayanin ya hau kai ya ɗare har yana yi wa mommy ƙarin bayani dangane da ciwon, ita dai Mommy ta ji shi ne amma har zuciyarta bata aminta da maganar ba, daɗin da ta ji da likitan ya ce zai ɗorata a kan allurai wanda za a riƙa bata a kai akai, wanda za su taimka mata wurin rage halin da take shiga. Daddy na fitowa daga asibitin suka haɗu da Dr Muhsin sai dai duk lokacin da Daddy ya ɗago masa da zancen ciwon Raihan zuwa tafiyarsu India sai ya ji ya manta komai, sai dai ya yi ta yi wa Daddy kame-kame. Ganin haka ya sa Daddy ya haƙura ya daina yi masa maganar har ya yi tunanin sake mata wani likitan. Suna haɗuwa suka gaisa faram-faram Dr Muhsin ya tambayi jikin Raihan daga haka suka yi sallama, Daddy na shiga mota saƙo ya same shi daga hukumar makarantar su Raihan, daga harabar asibitin kai tsaye makarantar su Raihan ya wuce. Takarda suka aka bawa Daddy na dakatar da Raihan da aka yi daga makatantar har sai ta samu lafiya, wannan labarin ba ƙaramin ɗaga hankalin Daddy ya yi ba. Lokacin da ya shiga mota har sai da ƙwalla ta zubo masa, zuciyarsa a dagule ya wuce gida yana zuwa ya sanarwa da Mommy abin da yake faruwa. Ita kanta bata ji daɗi ba amma sai ta fauwalawa Allaha lamuranta, tare da addu'ar Allah ya bayyana ainihin ciwon da ke daminta da hanyar warakarsa. A wannan lokacin Mommy ta dage sosai da sallar dare kuma tun abin da ya faru da ita a baya bai sake faruwa da ita ba, wani lokacin idan tana sallar dare har kuka take tana gayawa Allah buƙatunta don komai ya dagule mata, ga mitar da su Inno suke yi mata a kan yarinya ta girma babu tsayayyan miji, abu goma da ashirin ne ya haɗe mata.

Tun bayan dawowar Mama Uwani daga dubiyar mahaifiyarta duk ta sauya musu, hatta fara'a walawala da sauran abubuwan da take yi duk ya ragu, idan ba aiki za ta yi ko wani abin ba kodayaushe tana cikin ɗakinta. Da farko su Inno sun ɗauka jimamin rashin lafiyar mahaifiyarta amma daga baya sai suka lura da mu'amarce ta cikin jama'a bata so don haka suma suka ja baya da ita don tun suna tambayarta ko wani abu yana daminta ta ce a'a har suka zuba mata ido. Har bayan dawowar su Mommy ita kanta ta lura da haka amma sai ta yi mata uzuri kasancewar ɗan'adam ajizi ne yau da daɗi gobe babu. Amma abin na Mama Uwani ƙara gaba yake don yanzu ko aikin gida bata yi, wani lokacin Mommy ta yi ta ƙwalla mata kira amma fir ta ƙi zuwa. Wannan sabon yanayin da aka samu ya sa mommy ta fara tunanin ko gajiya Mama Uwani ta yi da aikin gidan, wata ranar laraba yamma liƙis Mommy ta ƙwallawa Mama Uwani kira tana zaune a falo yana kallo, sai bayan wani lokaci sannan Mama Uwani ta fito fuska babu walawa. Dama kuma Mommy ta kirata ne don ta tambayeta ko ta gaji da aikin a yi mata ihisani a sallameta a ɗauko wata. Ganin surar da Mama Uwani take ciki ba ƙaramin ɗaga hankalin Mommy ya yi ba, tun fitowara daga ɗaki ta fara ƙarewa ƙafarta kallo ƙirjinta na ci gaba da matsanancin bugu. Ilahirin jikinta rawa yake tun Mama Uwani bata lura da halin da Mommy take ciki ba har ta fara shan jinin jikinta, kallon idon mommy ta yi ta lura da wurin da take kallo nan take ta sauke kanta ƙasa tana kallon ƙafafuwanta, ganin Mommy ta gama ganin manyan kofatan dawakai ya sa Mama Uwani ta bushe da wata mahaukaciyar dariya, Mommy na daga kan kujera ta fara ja da baya don bata taɓa tunanin haka daga wurin Mama Uwani ba. Ɗago kofatonta ɗaya ta yi tana nunawa Mommy ta ce, "Gane-ganenki ya kaiki ganin abin da zai hana ki bacci. Tun da kin gano da idonki zan fayyace miki komai, ni ba mutum bace kamar yadda kuka yi tsammani tsawon shekaru. Hasalima ni zaman maye gurin nake yi domin ba ni ce ainihin Uwanin da kuka sani ba, ni sunana Mar'usa ƙanwace a wurin Huzaifa wato mijin ƴarki Raihan. Ya ajiye ni ne don na maye gurbinsa saboda wata doguwar tafiya da ya yi, idan ku ba daƙiƙai ba ne baku lura ɗabi'armu da tashi ta sha bamabam ba? Shi ya zauna da ku shekara da shekaru yana yi muku bauta saboda matarsa a gidan nan take, ni kuwa da babu uwar da zan ƙaru da ita kina ganin zan zage na yi muku bauta. Shi ma aikin da kika ga yana yi ya fansar da aikin wahalar ne a matsayin sadakinta, tun da yanzu kin san komai ni zan yi tafiyata sai ki jirayi dawowarsa don ba zai barki haka ba." Tana rufe baki Inno na ƙaraso wa wurin tana shirin yin magana turus ta tsaya baki a sake murya na rawa ta ce, "Na shiga aljanna na kasa fitowa, Uwani kofato nake gani a ƙafarki ko idona ne?" Mar'usu ta turawa Inno kofaton tana faɗin, "Ni ba Uwani bace ita kanta uwanin da kuke tsammani ba mutum ba ce." Tana rufe baki ta ratsa ta jikin bango ta wuce, Mommy na zaune bata yi aune ba sai ji ta yi kijiffff Inno ta faɗi ƙasa tana faɗin, "Lahamakasabat Wa'alaina makasabat, hasbunallahu La'ilaha'illahu. Wa'innahumin Sulaimanu..." Da sauri Mommy ta yi kanta tana tarota Daddy da shigowarsa kenan ya ƙarasa wurin yana salati, hankalina tashe ya ce, "Lafiya kuwa Inno garin yaya." Inno da ta fita hayyaccinta ta ce, "Idan mafarki nake yi Allah ka farkar da ni, Ina Zinaru take ta riƙe ni mu shiga ƙofar aljanna, Kalidina fiha'abadan cikin aminci."


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624


16


Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya sake yi ba ganin irin yadda Inno ta fara fita hayyacinta, a hargitse ya dubi mommy yana faɗin, "Zainabu me yake faruwa da Inno ne ko faɗuwa ta yi?" Mommy da ita ma ta fara fita hayyacinta ta nuna hanyar da Mar'usa ta bi tana faɗin, "Wallahi ba mutum bace." A daidai lokacin Goggo ta taho ta hanyar tana tafe tana faɗin, "Haka kawai kai ba arne ba kai ba baka haɗa iri da mai jan kunne ba ace gida kullin abu ɗaya, ina dalili ace koyaushe sai dai mu kalli ƙasashen turawa. Wallahi da sake, wannan tsohuwar ta bar ganin ita ta haifi Audullahi ni ma ina da iko da gidan tun da ai Ƴata yake aure, haka kawai wa ya sani ko zaginmu suke da yarensu ba mu sani ba. A'a raba ni da wannan lamarin ko a riƙa kunna min sangaya ko kuma na ɗauki ƙullin kayana na wuce Albasu, yoooo me gare su da babu a Albasu? Allah na tuba waccen tukunyar sanyin ce kaɗai ba ni da ita, tun kafin marigayi ya rasu ya ajiye mini talabijin na kalli sangaya na kalli Jan kunne. Ita ma tukunyar sanyaya ɗaki zan shiga adashin So dangi na haɗa da ƴan samiruna na bawa Zainbu ta cika ta saya min, zaman gidan siriki ko tashin hankali. Allah ya sani daga nan babu in da zan tsaya sai Albasu, abu ɗaya zan tsaya jira Audullahi ya haɗa min tsaraba na kaiwa su Rahila idan ba haka ba kullin suna liƙe da ni, su cika min ɗaki da tsamin kai da na hammata..." Bata kai ƙarshen maganarta ba ta ga Mommy na nuno wurin da take tana faɗin, "Da gaske ba mutum bace yaudararmu take yi aljana." Daddy na ɗaga kai ya yi tozali da Goggo, karaf maganganun mommy suka sauka a kunnen Goggo. Baki a sake ta ƙarasa wurin tana tafa hannuwa, Daddy ya dubi Mommy ya ce, "Ni kam Zainabu kanki bai fara taɓuwa ba kuwa? Taimaka min mu kai Inno asibiti." Inno da take jin maganganun Daddy sama-sama nan take ta tuno irin jijjigawar da Huzaifa ya yi musu cikin siffar Likita nan take ta sake ruɗewa ta ce, "Ina Alhaji Babba?" Da mamaki Daddy ya ce, "Alhaji Babba kuma Inno." Alhaji Babba Mahaifin Daddy ne ya rasu kusan sama da shekara talatin baya. Inno bata san ma Daddy yana yi ba balle ta fahimci tambayarsa, ta sake wawuro hannun Mommy tana cewa, "Alhaji Babba ka riƙe hannuna ka shafa min ƙofar aljannah. Idan mun shiga karka bi da ni ta hanyar masu kofato a ƙafa." Daddy ya sake duban Mommy ya ce, "Wai me yake faruwa?" Mommy na shirin yin magana Goggo ta yi caraf ta karɓe maganar da cewa, "Yooo ka nemi ba'asi Audullah bayan matarka ta gama kwayewa uwarta baya, yanzu Zainabu ni kika maida sheɗaniya wacce ta fito daga jinsin aljanu?" Goggo na faɗin haka ta rushe da matsanancin kuka, ta sa gefen rigarta ta share hawaye sannan ta ɗora da cewa, "Don Allah Audullahi idan Allah ya tsine min za ta bi ni ko ba za ta bini ba?" Daddy da kansa ya ɗaure ya dafa kansa da hannuwa biyu ya ce, "Goggo me ya yi zafi haka?" Goggo ta nuna Mommy ta ce, "Ba ka ji irin tozarcin da matarka ta yi min ba? Na rantse da Allah idan wani ya taɓa maida ni jinsin Aljanu Allah ya watsa min albarka, amma tun da haka ne zan bar muku gidanku na ƙare rayuwata a Albasu ko mutuwa na yi idan ba a kai gawata can ba ban yafe ba." Mommy ta zauna zaman dirshan ta ce, "Goggo ni fa ba manufa ta kenan ba, wallahi uwani ba mutum bace aljana ce yanzu haka abin da muka gani kenan muka firgita ni da Inno..." Gabaɗaya Mommy ta zayyana musu abin da yake faruwa, daga wurin da Goggo take ta yi tsalle ta dira a gadon bayan Daddy cikin kiɗima ƙwaƙumeshi tana faɗin, "Wattaba'u matattulisshayaɗina Alamulki Sulaiman, don Allah Audullahi ka dubi girman Allah ka mayar da ni Albasu ko mayu bamu da su balle Aljanu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Zainabu!" Ɗagowa ta yi tana kallonsa, bai bi ta kanta ba ya ci gaba da cewa: "Yanzu saboda Allah haka kawai za ki riƙa razana kanki, ki dubi tsofaffin nan suma kin razana su." Mommy takaicin duniya da ashirin ya kamata, babban baƙin cikinta da komai ta faɗa Daddy baya amincewa da ita sai dai yace ta cika tsoro. A zafafe ta dube shi don wannan karon zuciyarta ta bushe ta ce, "Na ga ji da yadda idanunka suke rufe wa akan abubuwa da dama, ba tun yau ba nake zargin jinnu sun samu gurbin zama a jikin Raihan amma kullin cikin ƙaryata ni kake yi, me kake ɗauke ne? Kana tunanin duk duniya akwai wanda zai zo Raihan kamar irin soyayyar.da nake mata. Karka manta cikinta na ɗauka wata tara tun tana ƙwayar hallita har zama cikakkiyar mutum, ka san yadda laulayi yake kuwa? Ka san yadda nake son cin wannan ba na son wanna? Idan na ci na yi amai da ƙyar zan samu wani ya zauna. Lokacin da cikina ya tsufa ka san irin nauyin da Ɗa yake da shi a cikin mahaifa? Tun da cikina ya fara girma na daina kwanciyar rigingine sai gefe da gefe kasan irin wahalar da nake sha idan na zauna zan tashi. Tun lokacin da na fara naƙuda ka san irin raɗaɗi da zafin ciwon naƙuda kuwa? Ban raina abubuwan da kake yi min ba na kulawa duk macen da ta samu kamarka ta yi dace amma duk kulawar da kake ba ni; ni kaɗai na san irin abin da nake ji a jikina, shin ka san yadda ratsowar kan ɗa yake daga jikin Mahaifiya kuwa? Na shafe tsawon wata tara ina rainon cikinta, duk wani yanayi da nake ciki tana fuskata na farinciki ko baƙinciki, hatta sautin muryata ta tantance kalarta shin tana samun waɗannan abubuwan daga gare ka? Ka gaya min akwai shaƙuwar da za ta wuce tsakanin ta Ɗa da mahaifiya? Ka ga ya min akwai wanda zai nuna mata soyayya fiye da wacce zan nuna mata? Kana tunanih za ka fini ƙaunarta?"

Mommy ta ƙarasa yi wa Daddy tambaya tana tsare shi da ido babu alamar tsoro a tattare da ita. Shiru ya yi yana nazarin maganganunta, Mommy bata damu da haka ba ta ci gaba da cewa, "Duk wannan gatan da kake nuna mata sam ba soyayya ba ce, kuma ba zan taɓa alaƙanta Raihan da ciwon jinnu ba kawai don son raina ba. Uwani da muka shafe tsawon shekaru da ita ba mutum ba ce ƙaton aljani ne da ya shiga jikin Ƴarka Raihan, ɗazun nan muka fahimci haka ni da Inno idan kuma kana musu wataƙila idan ta gaya maka za ka ɗauki abin da muhimmanci, idan kana tantama ka duba cikin gidan nan kaf idan za ka sake ganinta." A wannan karon hankalin Daddy ya fi na koyaushe tashi, jikinsa har rawa yake ya dubi Inno da hargagin Mommy ya dawo da ita cikin nutsuwarta yana shirin yin magana Inno ta ce, "Audullahi!" Daddy ya amsa mata murya a sanyaye Inno ta ci gaba da cewa, "Idan baka haɗa ni da Zinaru ta kaini albasu ba Alhaji Babba ya dawo duniya. Ganin idona na ga Uwani da Kofato har tana gaya mana ita ba mutum ba ce yau mai hanani tafiya Albasu sai Allah." Goggo na maƙale a bayan Daddy ba tare da ta fahimci a wurin wa take ba, tana miƙa hannu ta shafo gemun Daddy a zabure ta leƙa fuskarsa tana faɗin, "Yau na shiga aljanna na kasa fitowa yau ni ce maƙale a bayan Audullahi, astagafirullah Allah ka yafe min me ya kaini bayan siriki ana zaune ƙalau?" Goggo ta ƙarasa maganar tana zazzage ɗankwali sai da ta ɗaura shi akanta ta ce, "Me zan zauna na ci gaba da yi a gidan nan ban da abin kunya, wannan Idan ƴan Albasu suka ji kashina ya bushe gara na tafi sawuna a likafa tun Audullahi bai yanke hukunci ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyi ya ce, "Zainabu meye mafita?" Mommy kamar dama jira take ta ce, "Mafita dole ka nemo malaman Islamic chemist ɗin da baka son a kira su zo su yi mata ruƙiyya." Inno ta hangame baki tana tafa hannuwa ta ce, "Kai ni dai wallahi Ƙasimu ya nakasa min rayuwa da ya ɗoraka a turbar rayuwar masu jajayen kunne. Kai dai Audullahi da kasan taimakon da malamai suka yi maka kana ƙarami da baka guje su ba, wallahi ko labarin ƙarzuwarka na baka ya isheka ishara, a bar batun fitsarin kwance da sannu Allah sannu Ma'aiki da yaya muka samu ka daina, ka san irin tashin hankalin da na shiga lokacin da na ji za ka yi aure, na ce na ga ta kaina yaro ya zo yana fitsarin kwance mace ta raina shi. A'a wannan lamarin ba na aikin likitoci ba ne, ko rashin haihuwar matarka Allah ya sani ina zargin sheɗanu sun murƙushe maka ƙwayoyin hallita, don kar na yi shisshigi shi ya sa na saka muku ido amma da tuni na kira Ɗan wanzam har gidan nan zai zo shi da Kawunsa Malam mai farin allo sun baku magani." Daddy tuni ya gama ƙosawa da maganar Inno, tun bai ƙarasa jin abin da take faɗa ba ya miƙe yana faɗin, "Yanzu bari na kira Alhaji Munniru na ji a ina zan samu wurin da za a karɓo mata magani..."

"Ba sai ka kira kowa ba, ga mu ga Waraka Islamic chemist a titin sharaɗa, kai tsaye ɗaukan yarinyar nan za mu yi mu wuce da ita, da zafi-zafi kan daki ƙarfe." Mommy ta yi maganar tana miƙewa tsaye. Inno ta yi fiƙi-fiƙi da ido cike da firgice ta ce, "Billahillazi idan kun ga ba mu biku wurin nan ba Allah ya watsa mana albarka, haka kawai ku fice ku bar mu aljanu su dawo su casa hatsi a kanmu?" Mommy da yake neman mafita take bata jira cewarsu ba ta ce, "Shi kenan duk yadda kuka ce haka za a yi." Daddy da kansa ya tunkari ƙofar ɗakin Raihan sai dai lokaci ɗaya ya ji wani irin tsoro ya ɗarsu a zuciyarsa, yana daga tsaye ya fara jin wani irin gurnani kamar gurnanin zaki. Da sauri ya yi baya yana kallonsu Mommy a tsorace, Mommy na shirin yin magana ya ce, "Wallahi ji nake kamar ciwonta ya tashi gurnanin wani abin nake ji." Inno tuni cikinta ya kaɗa, ta maƙale a bayan Goggo tana leƙe. Mommy ita kanta hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, a hankali ta yi ta maza bakinta ɗauke da addu'a ta kalli Daddy ta ce, "Babu abin da ya gagari ubangiji, mu yi addua mu shiga ɗakin." Da sauri Daddy ya fara motsa baki yana biya ayatulkursiyyu yana tura ƙofar Raihan ta yi kuka kura ta faɗo kansu cikin wani irin gurnani mai tafe haushi kamar haushin kare. Idanunta a kakkafe suke kanta ya hargitse ga faratanta tuni suka fara sauya launi. Kafin su farga tuni ta fisgi hannun Daddy ta shige da shi ɗaki, ganin haka ya sa Daddy razana ya manta da addu'ar da yake yi ya fara ihu yana neman taimako. Yagarsa ta fara yi ta ko'ina da faratanta tana ƙoƙarin kai bakinta jikinsa Allah ya bashi sa'a ya hamɓareta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login