Showing 132001 words to 135000 words out of 157890 words

Chapter 45 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

168

haka har yanzu ba mu zo tashar da za mu shigar motar garinku ba?" Ibrahim ya yi murmushi ya ce, "Kai ragon maza rufe idonka." Babu musu Kabiru ya rufe ido yana faɗin, "Ni da kai a samu ragon don ko makaho ya shafa ƙwanjinmu ya san da bambamci." Jin hayaniya ya sa Kabiru buɗe ido da sauri ya fara bin wurin da kallo tare da mutanen da ke wurin, Ibrahim ne ya riƙo hannun Kabiru ya ce, "Mun ƙaraso waɗannan mutanen garinmu ne ka ga ƙofar gidanmu can." Ya nuna masa wani katafaren gida mai siffa da na sarauta, daga bayansa ya ji wasu magidanta suna faɗin, "Abokin Ibrahim muna yi maka barka da zuwa." Kabiru ka sa amsawa ya yi ya dubi Ibrahim ya ce, "Ibrahim yaushe ka fara aiki da aljanu ban sani ba, wato duk gargaɗin da Malam yake yi mana akan laƙanin rufa ido baka ji ba kenan?" Dariya ce ta kama Ibrahim sai da ya yi mai isarsa sannan ya ce, "Kai don Allah wuce mu je." Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka Kabiru ya bi bayan Ibrahim har suka shiga cikin gidan, cike da girmamawa Mahaifiyar Ibrahim ta sauke su da abinci kala-kala. Har lokacin jikin Kabiru a ɗarare yake don haka Ibrahim da ya lura da yanayinsa ya riƙa jan sa da hira amma gabaɗaya ji yake wani iri. Yayar Ibrahim ce ta shiga gidan hannunta ɗauke da ƙaramin jariri, tana ganin Kabiru ta washe baki tana faɗin, "Ikon Allah, wannan fa shi ne karo na farko da bil'adam ya zo cikinmu gaskiya Ibrahim abotarka da Bil'adam ɗin nan ya matuƙar burge ni." A fusace Mahaifiyarsu Ibrahim ta dubi Yahanasu ta ce, "Wai me ya sa wani lokacin baki da tunani Yahanasu kamar ba ki ji kashedin da Malam ya gama yi ba jiya ko?" Daga bakin ƙofa Kabiru ya hango yadda yara da manya suke leƙensa don haka ya sake shan jinin jikinsa, ya dubi Ibrahim a tsorace ya ce: "Don Allah kar ka cutar da ni Ibrahim domin a zamantakewata da kai ban taɓa zalintarka ba, idan ma na yi sai dai wataƙila lokacin da muna cikin ƙuruciya." Dafe kai Ibrahim ya yi jiki a sanyaye don ya fahimci Kabiru ya gano shi ya ce, "Ba zan taɓa cutar da kai ba Kabiru domin jin ka nake har cikin zuciyata saboda Baffajo bai taɓa bambamta mu ba duk abin da zai kawo maka sai ya kawo min, kuma zaman da muka yi na amana ne babu zalinci a tsakaninmu." Ganin hankalin Kabiru ya tashi ya sa Ibrahim ya saka shi sake runtse ido, muryar malaminsu ce ta farkar da shi yana buɗe ido ya gan shi zaune a shagon Malam. Malam ya kalli Kabiru ya yi murmushi ya ce, "Dama abin da na yi gudu kenan amma gudun kar ku yi min mummunar fahimta ya sa na amince da tafiyarku. Ibrahim ba mutum ba ne kamar yadda ka yi tsammani, tun kafin zuwanka Mahaifinsa ya kawo shi karatu wurina saboda Mahaifinsa abokina ne mun haɗu da shi ne a wani aikin Hajji da na je. Ka kwantar da hankalinka Ibrahim da zuri'arsa ba za su taɓa cutar da kai ba domin su cikakkun musulmai masu kyawawan ɗabi'a ne, sai dai ka yi haƙuri don na tabbata ba lallai ka sake ganin Ibrahim a nan tsagayata ba sai dai wataƙila idan ka koma rugarku." Kabiru cikin damuwa ya furta, "Amma har yanzu tsoro nake ji, zuciyata ta gaza aminta da Ibrahim na jinsina ba ne Malam." Malam ya yi murmushi sannan ya ce, "Ka ji tsoron Allah Kabiru domin shi zai isar maka, babu abin da mutum ko wani jinsi zai yi maka wanda Allah bai ƙaddara ba, ka yarda da maganata Ibrahim da zuri'arsa ba za su cutar da kai ba." Jinjina kai Kabiru ya yi ya miƙe ya ci gaba da harkokinsa sai dai gabaɗaya ji yake babu daɗi kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa, don a daren ranar da ya je kwanciya ya kalli wurin kwanciyar Ibrahim sai kawai ya fashe da kuka, haka ya ci gaba da rayuwa cikin kaɗaici da damuwa har ranar da Baffajo ya zo ɗaukansa a nan Malam yake sanar masa da komai game da Ibrahim, bai gama amincewa da maganarsa ba sai da Malam ya kira Mahaifin Ibrahim da Ibrahim suka bayyana a wurin suka gaisa cikin mutumtawa sannan suka sake ɓace wa. Shi kansa Baffajo ya yi mamaki da wannan lamarin, daga haka ya yi wa Malam alheri da godiya mai yawa sannan ya ɗauki Kabiru suka tafi daga Malam har Kabiru kowannensu yana zubda ƙwallah. Wannan dalilin ne ya saka lokaci zuwa lokaci a duk lokacin da Kabiru ya shiga wani yanayi yake kawo masa ziyara ba tare da ya fahimci shi ba ne, don ko kaɗan baya son ya razana abokinsa don haka a duk lokacin da ya ziyarce shi baya taɓa bari ya ga fuskarsa. Lokacin da lamarim gidansu Raihan ya same shi a lokacin Mahaifiyarsa ce babu lafiya a gaggauce ta tafi birnin ƙudus don ɗebo mata wata ciyawa wacce take tsakiyar tekun Milabi, don yi mata magani. Shi ya sa bai nemi karawa da Huzaifa ba, a ɓangare ɗaya kuma yana ganin duk abin da yake faruwa akan lamuran Raihan sai ya yi kamar ya shiga sai wani uzurin ya faɗo masa.

Shafin Rayuwar ƙunci ne ya buɗe wa Raihan a gidan Al'amin ban da tsangwama kyara da habaici babu abin da take fuskanta, fushin da Al'amin ya ɗauka da ita ya fi komai ɗaga mata hankali don ko gaishe shi ta yi baya kallon ƙurarta balle ta saka ran zai amsa mata. Ita kuwa Sumayya ta samu abin da take so don haka bata da aiki sai yi wa Raihan habaici da baƙaƙen maganganu, saboda ko kofi Raihan ta taɓa sai Sumayya ta saka omo ta wanke a cewarta karta shafa musu dattin zina a jiki. Waɗannan maganganu na su ya sake jefa Raihan cikin ruɗu don ita bata san duk abin da yake faruwa ba, wata rana da safe tana zaune a falo Al'amin ya fito da sauri ta ƙarasa gabansa ta ce, "Don Allah ka taimaka ka gaya min laifin da na yi maka ko na samu sassauci a zuciyata." Wani irin kallo ya bita da shi sai kawai ya saki tsaki ya wuce." Sumayya na fitowa ta bita da kallon ƙyanƙyami tana yarfe hannu ta gegareta ta gefe ta wuce. A wurin Raihan ta durƙushe tana wani irin kuka mai cin zuciya, tana ji tana gani Sumayya ta raka Al'amin ta dawo ta zazzage mata baƙaƙen maganganu ta wuce ɗakinta. A hankali Raihan ta ja ƙafa ta koma ɗaki tana ci gaba da kuka mai tsuma zuciya, tunani goma da ashirin ne ya mamaye zuciyata. Wanda ya zame mata jigo shi ne halin da take ciki tsakaninta da Al'amin, na biyu kuma rashin lafiyar Kabiru da Mommy kira sabon layin da Al'amin ya sauya mata take sanar mata Daddy ya kira waya don ya ji dalilin da ya saka Kabiru ya shafe kwana da kwanaki ba tare da ya dawo bakin aiki ba ake sanar masa. Waɗannan abubuwan ne suka sake dagula lissafin rayuwarta ya sa ko abinci bata iya ci daga ruwa sa ruwan tea. Wata ranar Asabar Mommy ta ce mata za su je duba Kabiru don haka Al'amin na dawowa da dare ta same shi da maganar duk da baya amsa maganarta. Bayan ya gama sauraro ta kallon tsaf ya yi mata ya ce, "Wato jaraba na cinki kin ga babu yadda za ki yi shi ne za ki ɓullo min ta haka, fasiƙar banza fasiƙar wofi tashi ki bani wuri ba Kabiru ba ko waye babu inda za ki." Jin haka ya sa Raihan ta fashe da wani irin matsananci kuka tana shiga ɗaki ta kira Mommy ta gaya mata ba za ta samu damar zuwa ba. Mommy na son fahimtar Raihan game da lamarin zaman aurenta amma babu wata shaida da zata kafa hujja da ita, amma akwai abubuwa da dama da take lura da yanayinta don dai kar ta yi magana ne ta ga kamar ta saka mata ido. Daddy da Mommy ne suka shirya suka tafi gano jikin Kabiru, Mommy har da kayan barkarta rigib masu yawa wanda ta kaiwa Mai jego da jaririn da aka haifa. Sai dai har suka je suka ƙaraci zamansu uffan Kabiru bai tanka masa ba hasalima bai nuna ya san su balle su saka ran zai tanka musu. Jiki a sanyaye su Daddy suka dawo gida lamarin ciwon Kabiru ya matuƙar ba su tsoro, kusan kwana su Mommy suka yi suna jajantawa a junansu daga ƙarshe Daddy ya ci alwashin taimaka wa su Inna wuro da duk abin da Kabiru yake yi musu, har yake ayyana ko ya yi wa Malam maganar ciwon Kabiru don dai kuma yana ganin kamar kar su ga ya yi musu shisshigi a lamarin Ɗansu.

Sumayya ce take fama da matsanancin zazzaɓi da ciwon kai don haka wayewar garin wata talata Al'amin ya ce ta shirya don ya kaita asibiti. Lokacin da suka fita Raihan na ɗaki a kwance don haka bata yi tsammanin da Sumayya suka fita ba, Al'amin da Sumayya suna zuwa asibiti aka yi mata gwaje-gwaje daga ƙarshe aka tabbatar da tana ɗauke da ciki har na tsawon sati bakwai. Murna wurin Al'amin da Sumayya abin ya baya musaltuwa, tun a mota Al'amin ya fara kafawa Sumayya dokokin abubuwan da za ta riƙa yi don ya ce wannan cikin baya fatan wani abu ya same shi. Al'amin na shawo kwanar layinsu ya hango Raihan ta fito daga wata baƙar mota, da sauri ya taka burkin motarsa Sumayya bakinta har rawa yake ta ce, "Hubby waccen ba Raihan aka sauke ba?" Da hannu ya yi mata nuni da ta yi shiru yana ƙare musu kallo, akan idon sa ya ga ta zagaya mazaunin direba ta sumbaci mutumin da ke cikin mota. Abu ya ji ya tsikari kahon zuciyar shi yana gani ta ƙarasa bakin gate ta saka key ta buɗe ta shige hannunta ɗauke da wata farar leda. Yana ganin mutumin ya fara tafiya ya kunna tashi motar ya fige ta da gudu amma yana shan kwanar ya nemi motar sama da ƙasa ya rasa, da gudun gaske ya juyo har sai da suka kusa yin gware da wani maƙocinsa ya ƙarasa bakin gate. Yana kashe motar Sumayya na fitowa ya saka wa motar key, buɗe ƙofar gidan ya yi da ƙarfi jikinsa har rawa yake, da kayan da ya ga ta fita da su ya same ta ta zubo abinci daga kitchen tana zaune a falon. Yana zuwa ya fisgota da ƙarfi ya damƙi gashin kanta cikin wani irin ƙaraji ya furta, "Uban waye ya sauke ki a mota? Gidan uban wa kika je da izinin wa?" Tsoro ne ya kamata bakinta na rawa ta ce, "Wallahi babu in da na je yanzun nan na fito daga wanka na fito cin abinci." Da ƙarfin gaske ya sake fisgota gabansa ya ce, "Ƙarya na yi miki kenan ko? Ki bi ni a sannu wallahi darajar Mahaifina kike ci amma ba don haka ba da tuni na aika ki gidanku don har abada ba zan taɓa hanya da fasiƙi ba." Ya wurgata ƙasa ta faɗa kan abincin da zubo ruwan shayin da ke gefe ya kwaro mata a hannu, a fusace ya nuna ta da ɗan yatsa ya furta. "Wallahi kin ci sa'a ba na daga sahun maza masu duka da yau dai na baki mamaki." Yana gama maganar ya shige ɗaki, Sumayya ta watsa mata harara sannan ta ce, "An dai ji jiki wallahi karuwancin ma ai yana cin darajar aure da sai ki bari idan ya sauwaƙe miki sai ki ci gaba daga inda kika tsaya." Tana gama maganarta wuce ɗakinta ta ci gaba da zuga Al'amin san ranta. Idanunun Raihan bushewa suka yi saboda ɓacin rai, nan take ƙirjinta ya ƙulle wani abu ya turnuƙeta ta fara wani irin kakari jini na fita ta bakinta. A hankali ta rarrafa ta shiga ɗakinta ta wuce banɗaki da rarrafe ta saka ruwa ta wanke sannan ta koma kan carpet ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Wuni ranar haka Al'amin da Raihan suka yi kowa zuciyarsa babu daɗi musamman Raihan da duk abin da yake faruwa bata da masaniya akai. Sumayya babu yadda bata yi da Al'amin akan ya saki Raihan ba amma yaƙi sai magana ɗaya da yake nanata mata na cewar darajar Mahafinsa ta sa ba zai sake ta amma zaman da za ta yi ta gwammace dama sakinta ya yi. Duk da ba haka ta so ba amma abin ya yi mata daɗi don ko babu komai ta san ko kaɗan Raihan bata gabansa, shi ya sa ta ci gaba da shuka tsiyarta san ranta.

Sati biyun da aka ɗebawar Sumayya sun cika don haka Talata da ta zagayowa Al'amin ya shirya zai kai Sumayya asibiti amma da yake yana da uzuri sai ya ce ta bari ya kaita da yamma, kamar yadda ya faɗa mata bayan la'asar ya ƙaraso cikin gidan. Yana gabda wuce sashen Raihan ya ji muryarta da namiji suna faɗin, "Tabbas kai kaɗai kake faranta min zuciya, ko kwanaki haka mahaukacin can ya zo yana ta haukan banza wai sai na faɗi wanda ya zo ya ɗauke ni." Muryar namijin ya ji ya bata amsa da cewar, "Ni dai yanzu duk ba wannan ba, kin san dai yau sau biyu kawai kika faranta min. Yanzu yaushe za mu kuma haɗuwa?" Dariyar Raihan ya ji sannan ta ce, "Ka bari na ji sakaran nan yana gayawa matarsa zai yi tafiya idan ya tafi ba sai mu sha shagalinmu ba. Amma kafin nan bari na ɗauko maka rigarka ka saka..." Da ƙarfi Al'amin ya doka ƙofar Raihan a daidai lokacin Sumayya ta fito wurinsa tana faɗin, "Dear ashe ka shigo tuntuni kana wurin Raihan..." Magarta ce ta maƙale sakamakon wata bangaza da ta ji an yi mata sai da ta ji ta har tsakiyar kanta, cikin zafin nama Al'amin ya rufa masa baya don wannan karon ya ci alwashin sai ya kama koma wane ne yake cin amanarsa da matarsa, tun da lambar da yake zargi duk iya binciken ƴan sanda sun gagara gano mai amfani da ita. Duk yadda Al'amin ya kai ga son ganin ya kama mutumin da yake gudu daga shi sai gajeren wando abin ya ci tura, ihu ya ji Sumayya ta ƙwalla tana faɗin cikinta, wannan ya sa Al'amin ya rabu da shi don dama tuni mutumin ya je bakin gate ya fice. Yana komawa Raihan ta fito a hargitse daga ita sai ɗaurin ƙirji da alama daga wanka ta fito, dafa Sumayya ta yi ta ce: "Lafiya Sumayya me yake faruwa." Azababben marin da Al'amin ya zabga mata ne ya sa ta gani wasu taurari don har sai da kanta ya yi dum! Na wucin gadi ta riski muryarsa yana faɗin, "Ni za ki mayar ɗan tasha saboda kin raina min hankali har gidana za ki riƙa kawo kwaratanki?" Raihan riƙe gunci ta yi tana bin sa da kallo don ta rasa abin da za ta ce masa.

Daga Abar bauta har Hatsabibiya rasa mai bakin magana aka yi, mamaki, tsoro haɗe da tashin hankali ya mamaye zuƙatansu. Huzaifa ya fara takawa a hankali cikin takun isa da ƙasaita har sai da ya zo wurinsu ya fara zagaye su ɗaya bayan ɗaya yana ƙyaƙyata dariya. Sai da ya zagaye su kusan sau uku sannan ya ce, "Waɗanda suka mutu kafin ku ƙaraso ina yi musu murna da farinciki domin duk waɗanda kuka ga irin wulaƙantacciyar mutuwar da suka yi rahama ce akan taku. Ni Huzaifa na tumbatsa ban ga wani Mahaluki da zai ga bayana matuƙar ina numfashi a duniya, ban da toshewar tunani da basira irin taku ta yaya za ku zo neman sa'a a kaina kuma wurin Kakana? Kun san kaf jikokin Jabbul-ƙasi babu wanda ya fi ƙauna sama da ni ta yaya zai taimaka muku ku hallaka ni? Na san kafin ku ƙaraso kun ga mace a ɗaure ban sani ba ko kun gane ta, to idan ma ba ku gane ta ba Mugaza ce. Na gano duk kaidinta da cin amanata da na yi domin dama na jima ina ɗora zargi akanta. Yau kimanin sama da watanni biyar kenan tana ɗaure babu ci babu sha kuma a duk rana ina kawo wasu kifayen aljanu suna tsotsar jininta. Ina raga mata azaba ne saboda ita ɗin uwar ƴaƴana ce ko babu komai mun haɗa zuri'a ɗaya da ita. Amma ba zan yafe irin cutarwar da ta yi matata Raihan ba, ta mayar min da ita matsafiyar ƙarfi da ya ji ta saka ta aikata kisa ba tare da tana cikin hayyacinta ba. Ta saka ta shan jini alhalin ba ɗabi'arta bace ya za a yi na yafe mata waɗannan laifuffukan?" Ilahirin jikin su Hatsabibiya ban da rawa babu abin da yake yi, baki na rawa Abar bauta ta ce, "Wallahi babu laifinmu a ciki ita ta gayyato mana ita cikin mu amma bata gaya mana..." Abar bauta ba ta gama magana ta ji an raɗa mata wani abu a tsakiyar kanta nan take ta faɗi sumammiya. Jabbul-ƙasi na zaune akan kujerar farin dutse ya kalli Huzaifa cikin jin daɗi ya furta, "Dalilai biyu ne suka sa na fi jin ƙaunarka a cikin zuciyata, dalili na farko duk cikin jikoki da ƴaƴana babu wanda ya ɗauko halaye da ɗabi'u irin nawa sai kai. Dalili na biyu ina ƙaunarka saboda taurin zuciya, taurin kai da rashin tsoronka. Tabbas kai namiji ne kuma ka cancanci ka gaji kujerata koda ba na raye, amma ka sani tsugunne bata ƙare maka ba domin zuri'ar gidan Alƙasim Bn Muhammad Mustafa na gabda tunkararka akan jinin ɗan abokinsa da ka ɗauke. A kullin ina yi maka fatan nasara sai dai wanann karon zuciyata rawa take domin Muhammad Mustafa kakan Ibrahim Alƙasim hatsababin Aljani ne fiye da tunanin mai tunani. A shekaru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login