Showing 144001 words to 147000 words out of 157890 words

Chapter 49 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

161

"Eh." Amsa masa ya yi sannan ya wuce cikin gida, a lokacin Raihan ita kaɗai ce a zaune a falo tana shan ruwan tea Auwalu na leƙawa ya ce, "Hajiya yanzu wani ya ce a yi sallama da ke." Da mamaki Raihan ta ce, "Ni kuma?" Aulwalu ya amsa sannan ta ce, "Ka je ka ce bata nan." Kamar yadda ta faɗa haka Auwalu ya koma ya faɗa sam Al'amin bai ji daɗi ba, don haka ya buɗe motarsa ya cito Memo ya yi rubutu ya miƙawa Auwalu ya ce ya bata. Ba musu Auwalu ya karɓa sannan Al'amin ya wuce gidan su Sumayya, yana zuwa kamar yadda ƙannenta suka saba tarbarsa a falonsu haka suka yi masa. Yana nan zaune ya ga wata baƙuwar lamba ta shigo masa har sai da ya ji gabansa ya faɗi, don ya ɗauka Raihan ce ta kira saboda a rubutun da ya yi har da lambar wayarsa a jiki. Da sauri ya fita ya zagaya ta bayan ɗakin su Sumayya ya ɗauka, yana ɗaga wa ya ji an yi sallama da muryar namiji. Guntun tsaki ya yi cikin girmamawa aka gaishe shi bayan sun kasa ya ji an ce, "Malam wallahi dama maganar Assignment ɗin da ka karɓa ranar ban zo ba shi ne..." Cikin takaici Al'amin ya furta, "Ban gaya muku a cikin rules and regulations ɗina ban da kira a min complain ba? Ba na son sakarcin banza da wofi." Bai jira cewarsa ba ya katse wayar. Yana zagayowa ta daidai windon ɗakin Mahaifiyar Sunayya ya ji muryar Mahaifiyar Sumayya na faɗin, "Ki tabbata kin ya sha lemon nan domin maganin da na karɓo a wurin Malam ya tabbatar min matuƙar ya sha lemon nan wallahi ba Raihan ba ko bebyn roba ba zai kalleta da sunan so ba." Sumayya ta shagwaɓe murya ta ce, "Mommy ina gidansa ma fa haka kika ce, wallahi hatta layar da kika ba ni na saka a cikin filonsa da wacce na binne duk babu wanda ya yi aiki. Ita kanta Raihan duk asirin da muke yi mata da banga yana wani tasiri a jikinta ba, har gwara lokacin da aka haɗa mata da jinin Kasa shi ne ta riƙa baccin nan. Ni kuma so nake yanzu na gama da Al'amin ko tsohon nan da yake shiga lamuranmu kar ya ce masa ya bi gabas ya bi." Jikin Al'amin ba ƙaramin sanyi ya yi ba, yana nan tsaye har ya gama jin duk irin hirar da suke yi. Yana jin alamun tahowar Sumayya da sauri ya wuce cikin falon, tana ganinsa ta yi farrr da ido tana faɗin, "Hubby ina ta jiranka ina ka je ko ka je yin waya da Raihan?" Murmushin ƙarfin hali ya ƙirƙiro ya ce, "Haba dai wani ɗalibina ne ya kira ni." Lemo ta tsiyayo masa tana fari ta miƙa masa sai da ya karɓa har ya kai bakinsa sannan ya cire ya ɗago yana kallonta ya ce, "Sumayya ada na ɗauke kina daga cikin sahun mata masu tunani ashe sam ba haka ba ne." Ras gabanta ya faɗi abinka da mara gaskiya a rikice ta furta, "Ni kuma me na yi?" Haɗe fuska ya yi sannan ya ce, "Yau da safe na tsinci layu a ɗakinki, ɗaya a cikin fulo ɗaya kuma a cikin kayana har da wacce aka binne a ɗakin Raihan. Sannan har wani wuri na ga an haƙa rami an binne abu a ɗakinki..." Shiru ya yi sai kuma ya kalli kofin hannunsa ya ce, "Sai kuma wannan lemon da na ji ana ce miki na mallaka ne, ashe dama soyayyar da kike min bata tsakani da Allah ba ce?" Hawaye ne ya fara zuba daga idonta ta furta, "Ka dubi girman Allah ka rufa min asiri Al'amin wallahi ba halina ba ne soyayyarka ce ta sa na kasa haƙuri har nake ganin ba zan iya haɗa ka da wata..." A fusace Al'amin ya furta, "Kin ci amanata kin cuci kanki, na so ki tsakani da Allah amma kike neman shan gaba tsakanina da iyayena, tir da halinki kin ba ni mamaki." Al'amin na gama maganr ya dire mata kofin ya fice a zafafe, don akwai ciwo wanda ka yarda da shi ka aminta da shi kake yi masa so na tsakani da Allah ya nemi cin amanarka har ta kai ga yana son ganin ya raba ka da mahaifanka. Hankali a tashe Sumayya ta bazama cikin ɗakin Mami tana ihu, kamar wacce ake kwarawa ruwan dalma.

Auwalu na kaiwa Raihan takardar hannunsa mamaki ne ya kamata, a sanyaye ta karɓa don bata yi tsammanin ga daga wurin wanda takardar ta fito ba. Tana karɓa ta fara karantawa kamar haka: "Amincin Allah ya tabbata a gare ki, na zo ne domin na baki haƙuri a bisa zamantakewarmu domin har yanzu zuciyata ta gagara nutsuwa akan abin da na aikata miki. Na zo neman yafiyarki don Allah ki yafe min duk abin da na yi miki a zamantakewarmu ta baya. Saƙo daga Al'amin." Tana gama karantawa daga ƙasa ta hangi lambar wayarsa, hawaye ne ya ciko idonta tana jin wata irin kewa da ƙaunarsa ta mamaye mata zuciya. Rungume takardar ta yi a hankali ta furta, "Na yafe maka duniya da lahira Al'amin saboda kai na musamman ne a birnih zuciyata, na yafe maka saboda Allah, Allah ya yafe mana gabaɗaya." Ƙwallar idonta ta goge ta tashi ta shiga ɗakinta ta ajiye takardar acikin takardunta masu muhimmanci. A ranar kusan kwana ta yi tana tunane-tunane don soyayyar Al'amin sabuwar fil ta dawo mata a zuciya. Al'amin na fita daga gidansu Sumayya kai tsaye gidansa ya nufa, a hargitse ya fara birkice ɗakin Sumayya yana zazzage filonta sai ga layu sun faɗo, ɗaya bayan ɗaya ya riƙa bi yana buɗe su yana karantawa shi abin ma zame masa ya yi tamkar a mafarki. Nan take wata nadama da kewar Raihan ta kama shi yana jin sam bai kyauta ba, don tun da yake a duniya zai iya cewa wannan shi ne abu mafi muni da ya taɓa aikatawa wato cin zarafi da wulaƙanta Raihan. Ranar Lahadi da dare Daddy ya kira shi bayan ya zauna Daddy ya fara yi masa magana, "Aminullah na kira ka ne domin na sanar da kai Kaza na taka ƴaƴanta ne ba don bata son su ba sai don ta koya musu zaman duniya ne, na yi maka hukuncin baya ne don na nusar da kai laifin da ka aikata sam baka kyauta ba, abin da ya faru tsakaninka da yarinyar nan Raihan ban ji daɗinsa ba sai dai ba ni da yadda za mu yi Allah ya rubuta ba za ku yi zama mai tsayi ba, a kullin a kodayaushe ka zama adali ko ba akan Raihan ba kai namiji ne ta yuwu za ka iya ƙara aure nan gaba don haka idan ka ce za ka fifita soyayyar matarka za ka kai kanka halaka. Ka shirya gobe idan Allah ya kaimu ka ɗauki matarka ku wuce gida don..." Da hanzari Al'amin ya furta, "Haka ne Daddy amma wani hanzari ba gudu ba gaskiya ba zan iya mayar da Sumayya gidana yanzu ba. Ita kuma Raihan wallahi na yi nadama Daddy Allah da dama sai na mayar da ita..." Dariyar Daddy ta katse shi sannan ya ce, "Dama ta riga ta wuce maka Aminu. Ita kuma matarka meye dalilin ƙin mayar da ita?" Al'amin ya furta, "Ba komai amma a ɗan bari sai bayan kwana biyu." Jim Daddy ya yi yana nazartarsa sannan ya ce, "Ban lamunce ba, maza umarni na baka gobe ka ɗauki yarinyar mutane ka mayar da ita tun da dama ni na bada umarnin ta wuce gidansu." Fitar Al'amin ke da wuya Daddy ya yi jim yana nazartar lamarin su Al'amin don ya san ruwa baya tsami banza. Kamar yadda Malam ya gaya masa washegari Al'amin ya je ya ɗauki Sumayya ita kanta ba ƙaramin mamaki ta yi ba, don ta fara fidda rai da sake komawa gidansa saboda tsananin fushin da ya ɗauka da ita, sai dai kallo ɗaya ta yi masa wani irin tsoronsa ya ɗarsu a zuciyarta don fuskarsa a tamke take babu alamar wasa. Suna zuwa gida ta shiga ɗakinta a sanyaye shi kuma ya faɗa ɗakin Raihan don tuni ya saka ƙaramar katifa a ɗakin yake kwana a ciki. Zaman Al'amin da Sumayya sai ya koma tamkar zaman doya da manja, saboda daga gaisuwa babu wani abu da yake shiga tsakaninsu. Ko girki ta yi sai ya ga dama yake ci, idan abincin bai yi masa ba ya fita ya siyo takeaway tana kallo ya cinye.

BAYAN WANI LOKACI.


Abubuwa da dama sun faru Raihan ta cire komai a zuciyarta don haka ta kama kasuwancinta hannu bibbiyu, wannan ya sa ta mayar da jikinta ta yi kyau don babu wani abu da yake damunta domin ta fahimci idan so cuta ne haƙuri magani ne. Kabiru gagara haƙuri ya yi da soyayyar Raihan yana son ya tunkareta da maganar yana shakkun abin da kaje ya zo, domin a kullin yana duba matsayinsa da matsayinta don haka watarana ya samu Inno wuro don jin shawararta game da gabatar da soyayyarsa ga Raihan, sai da ta gama saurarsa cikin tashin hankali, tsoro da firgici ta furta, "Hai lallai Kabiru na yarda baka da hankali, yanzu saboda ka samu wuri har bawan Allahn nan ya taimake mu ya jawo mu jikinsa har za ka ce za ka auri ɗiyarsa? Kana cikin hayyacinka kuwa an ya Kabiru baka haukashe ba? Ka dubi ƴar mai arziƙi kamar wannan ka ce ita za ka aura? Aradun Allah ka na aikata wanna ɗanyen aikin ka san shan ruwanmu a gidan nan ya zo ƙarshe, a kull ka rufa mana asiri mu ci arziƙi mu bar arziƙi a mazauninsa." Cikin Damuwa Kabiru ya furta, "Inno wuro wallahi ba tun yau nake son yarinyar nan ba..." A harzuƙe Inno wuro ta katse Kabiru haɗe da yi masa daƙuwa tana faɗin, "Soyayyar gidanku Kabiru, wai yaushe mutanen birni suka lalataka har kake fitsara a gabana. Kwarankwatsa dubu idan Alhaji ya ji maganar nan sai ya kaika wurin Gunduman garin nan, idan baka yi sa'a ba ya sa a ɗaureka har igiya ta yi saura." Zuciyar Kabiru a dagule ya dubi Inno wuro jiki a sanyaye ya ce, "Yanzu shi kenan Inno haka zan haƙura da Raihan?" Inno Wuro ta wara hannuwa tana faɗin, "Eh ka haƙura da ita tun da dai aurenta ba farillah ba ne, muna hannun Allah muna hannun Alhaji shi yake yi mana komai a rayuwa. Idan kuma bijirewa maganata za ka yi ga ka ga hanya nan je ka Kabiru." A sanyaye Kabiru ya amsawa Inno wuro sannan ya fice daga ɗakin, can ɗakinsu ya wuce ganin yanayinsa ya sa Maryama ta fara tambayarsa amma fir ya ƙi sanar mata abin da yake damunsa, sai dai ta lura ransa a matuƙar ɓace yake.

Jim Daddy ya yi bayan gama jin jawabin Alhaji Shatima, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Alhaji ka san dai matsalar yarinyar ba sai na gaya maka ba, amma Alhamdulillah jikinta yanzu ya yi sauƙi babu wani abin da yake faruwa da ita. Kuma ban san daga ɓangaren ita Raihan ba ko yaya za ta amshi wannan maganar." Farinciki ya mamaye zuciyar Alhaji Shatima, ya dubi Daddy ya ce. "A yi mata a hankali ka san yara wani lokacin ba a tikasta su, kuma ba da faɗa ake yi musu magaba ba, maganar lalurarta wannan ai mai sauƙi ne Alhaji tun da ansan ciwon neman magani ai ba zai gagara ba." Daddy ya yi murmushi sannan ya ce, "Shi kenan Allah ya tabbatar mana da alheri." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Daddy ne ya raka Alhaji Shatima bakin mota suka yi sallama, yana komawa gida ya samu Mommy tana zaune a dianning da alama jiransa take. Bayan ya zauna ta fara zuba musu abinci tana cewa, "Daddyn Raihan tun ɗazu cikina yake kiran ciroma, har na yanke shawarar zuba abinci na ci don na san hirarku da su Alhaji Shatima bata ƙarewa." Daddy ya yi murmushi ya ce, "Neman auren ƴarki ne ya kawo shi." Mommy ta yi murmushi don ta ɗauka zolayarta yake ta ce, "Alhaji Shatima da ba ƴaƴa maza ba wa zai nemarwa aure, ai gara ku nemi wata dattijuwar ku ba shi tun yau kusan shekarar Hajiya Asabe uku da rasuwa." Daddy ya ɗauki cokali ya fara cin abin ci sannan ya ce, "Allah da gaske Raihan yake so da aure." A hargitse Mommy ta ce, "Raihan kuma?" Daddy ya gyaɗa mata kai. Mommy ta ajiye cokalin hannunta cikin sanyin jiki tana ci gaba da cewa, "Amma kana ganin Raihan za ta amince da shi, duk da bai kaika a shekaru ba amma fa ya bawa Arba'in baya sai na ga kamar ya yi mata tsufa." Daddy ya saka dariya cikin zolaya ya furta, "Ni ma na yi tsammanin haka amma idan ta ga ya yi mata ai shi kenan, ba Alhaji Shatima ba ko yanzu ai zan iya ɗaukan budurwa don hango wata fillo a rugar su Kabiru." Mommy ta wurga masa hararar wasa sannan ta ce, "To zan yi mata magana na ji Allah ya tabbatar da alheri. Ai ba wani abu ba ne Daddyn Raihan ni da kaina zan haɗa maka laife ka ga MD ya samu mai raino." Dariya Daddy yake sosai don ya san halin Mommy macece mai kishi amma duk zafin kishinta ba za ta bari ka gane lagonta ba.

Washegari da safe Mommy ta samu Raihan da maganar Alhaji Shatima, Wani iri Raihan ta ji maganar sai dai a wannan lokacin duniya ta koya mata ladabi ba komai take zafafawa ba, domin ta lura ko ka zafafa matuƙar abun ba mai alkhairi a wurinka ba ne sai dai ya wahalar da kai a banza. Jiki a sanyaye Raihan ta furta, "Mommy tsoron aure nake ji don gani nake kamar ba ni da rabo a ɓangarensa. A yanzu ba ni da zaɓi sai neman zaɓin Ubangiji domin a baya na ɗauka son raina shi ne alheri ashe ba haka ba ne, don haka matuƙar kun amince da ɗabi'unsa na amince zan aure shi." Ba ƙaramin tausayi Raihan ta bawa Mommy ba, ta riƙo hannunta cikin kulawa ta ce, "Allah ya yi miki albarka Raihan, insha Allah zan sanar da Daddynki duk yadda ake ciki za ki ji." Raihan ta sakar wa Mommy murmushi don ta lura mahaifiyarta na cikin damuwa da halin da take tsintar kanta a ciki. Daddy na dawowa Mommy ta sanar masa duk yadda suka yi da Raihan, sai da ya sake tambayar Raihan ya ji daga gare ta sannan ya ce zai sanar da Alhaji Shatima domin ba baƙo ba ne a wurinsa tun da abokin kasuwancinsa ne. Alhaji Shatima na shiga motarsa ya daki sitiyarin motarsa haɗe da sakin wata ƙaramar ƙara a hankali ya furta, "Burina ya kusa cika domin na tabbata matuƙar na auri Raihan sai na san yadda na yi na mallaki Kamfanin maganin sauronsa da ke unguwar Tudun murtala, ba zan yi ƙasa a gwiwa ba sai na mallako har katafaren kamfanin takalmansa na unguwar sharaɗa. Domin babu yadda za a yi na nuna masa yadda ake kamun kifi sannan ya fini iya kamawa. Idan na mallaketa sannu a hankali zan nemi hanyar da zan bi domin na halaka shi, daga nan Raihan za ta samu kaso mafi tsoka don haka idan ta samu kamar na samu ne." Alhaji Shatima ya yi ajiyar zuciya ya ci gaba da cewa, "Ina baƙin cikin na ga na buɗi ido na ga bawan Allahn nan domin arziƙinsa kullin gaba yake baya yin baya. Alhalin wasu shawarwarin dangane da kasuwanci ma ni na ke bashi, amma ni kullin ji-iyau ba na yin gaba." Yana gama surutansa ya figi motarsa da gudu ya fice daga layin. Sati ɗaya da zuwan Alhaji Shatima Daddy ya kira shi tare da sanar masa Raihan ta amince da batun aurensa, murnarsa har sai da ta ƙi rufuwa a gaban Daddy. Shi kuma Daddy a tsamminsa tsananin soyayyar Raihan ce ta saka shi yin haka don haka ya sake jin wata irin ƙaunar Alhaji Shatima a cikin ransa. Nan take ya yi masa kyautar wata gonarsa da ke garin Kura, farinciki ya sake lulluɓe Alhaji Shatima ya riƙa zuba masa godiya da fatan alheri don wannan ne ya tabbatar masa da Raihan ita ce daidai macen da yake so mai ƙashin arziƙi tun da ga ƙofofin arziƙi nan sun fara buɗe masa. A ranar sai da suka gaisa da Raihan yanayinta babu yabo babu fallasa, ya gabatar mata da kansa da adadin yaransa da wasu al'amuransa na yau da kullin. A cikin ƙasa da wata guda Alhaji Shatima suka daidaita da Raihan don har kuɗin gaisuwa ya kawo an tsayar musu da ranar aure wata biyu, su Inno baki har kunne don kusan duk zuwan da Alhaji Shatima zai yi ƙullin ledar su na musamman ne, don wata rana da ya ciko musu ƙatuwar leda da kaza suna ci faɗa ya kacame a tsakaninsu har sun fara lissafin idan Raihan ta haihu su za su je zaman daɓaro. Sai da Mommy ta shiga faɗan ta sasanta su da cewar wuyarta dai a yi auren a samu cikin tana haihuwa duka za su je gidan su zauna har sai ta yi kwana arba'in. Raihan ba wata soyayyarsa take ji a zuciya ba don dai kawai ta faranta ran mahaifanta ne ya sa ta lamunce za ta aure shi, don haka bata wani zafafa ba saboda wannan karonma ta ce babu abin da za ta yi, tun da aure ba na ɗaya ba ba na biyu ba. Hasalima wasu ƴan uwan na nesa ma ba a gaya musu ba don gudun surutu. Ranar ɗaurin auren Raihan da gayya Malam ya kira Al'amin bayan ya gaida shi ya ce, "Al'amin ina son ka zo ka kaini wurin ɗaurin aure don yau da ƙafar hagun nan na tashi tana yi min ciwo." Al'amin ya kalli ƙafar Malam ya ce, "Subhanalla Daddy ka haƙura da zuwa tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login