Showing 87001 words to 90000 words out of 157890 words

Chapter 30 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

147

cikin asibitin.

Raihan tun da ta shiga motarta lokaci-lokaci take zabga tsaki don mutumin ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba, tana zuwa gida ta shiga zabga horn kamar mai shirin tashi sama. A hargitse Kabiru ya leƙa don ganin mai wannan horn ɗin don a iya saninsa mutanen gidan ba sa irin haka. Ganin Raihan ce ya sa shi faɗaɗa fara'arsa, tsayuwarsa a wurin ya dulmiya shi cikin kogin tunani don zuciyarsa ta jima tana yaudararsa akanta. Shi kansa ya san ko a cikin mafarki Raihan ta yi masa nisa kwatankwacin yadda sararin samaniya ta yi hannun riga da ƙasa. Bai yi aune ba ya sake jin ta danna wani horn ɗin da ƙarfi, jiki babu kuzari ya fara jan gate ɗin a hankali ya buɗe yana tsaye wuri ɗaya yana bin ta da wani irin sassanyan kallo. Tana shigo wa tun bata ƙarasa wurin parking ba ta faka motarta a wurin ta sauko, wurin Kabiru ta sake koma wa ta riƙe ƙugu tana kallonsa. Ganin har lokacin bai san tana yi ba ya sa ta ƙarasa wa wurinsa tana tafa hannuwa ta ce, "Filloooo!" A firgice ya ɗago yana sauke ajiyar zuciya suna haɗe ido ya sakar mata wani ni'imtaccen murmushi. Ba ƙaramin kyau ta yi masa ba kasancewar tana sanke da doguwar rigar leshi kafaɗarta maƙale da ƙaramin mayafi. Da ido ta kafe shi tana karantar yanayinsa tamkar wata uwarsa ta haɗe fuska tana faɗin, "Kwana biyu na ga kana cikin damuwa me yake damun ka?" Ba ƙaramin dariya ta bashi ba don yadda ta yi maganar kamar wata uwarsa ko yayarsa, dariya ya yi mai sauti sannan ya ce, "Hai kai yanzu sai na gaya maka abin da yake damuna?" Raihan ta sake haɗe fuska ta ce, "Ban isa ba ne wai me ya sa fillo ka raina ni da yawa?" Kabiru ya jingine sandar hannunsa ya ce, "Don Allah shekara nawa na baki? A ƙalla na baki kusan shekara bakwai." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wallahi na ɗauka ka fi haka don wannan manyancen naka sai kace ka haife ni." Dariya Kabiru ya yi Raihan ta ce, "Da gaske kana cikin damuwa me yake damunka ko jikin Baba?" Raihan ta faɗa a sanyaye da yake daga baya da zama ya yi zama Kabiru ya sanarwa da Raihan rashin lafiyar da Mahaifinsa yake yi, kuma Daddy ba ƙaramin taimaka masa yake yi ba. Wannan kalma ta Raihan na ɗaya daga cikin abin da ya sa ta sace zuciyarsa saboda tana matuƙar ambatar iyayensa da nuna muhimmancinta akansu. Jin ya yi shiru ya sa ta ce, "Idan jikin nasa ne ya yi tsanani ya kamata ka sanarwa da Daddy a yi wani abu, idan kuma zuwa kake son yi sai ka saka rana ka tafi." Murmushi ya sakar mata ya ce, "Duk ba wannan ba ne wata yarinya nake so amma na san zuciyata yaudarata take yi, don na san ko a mafarki ta min nisa." Tsaki Raihan ta yi haɗe da yin wata irin dariya ta ce, "Don Allah da akan tunanin wata yarinyar har ka shanya ni a ƙofar gida?" Kabiru ya marairaice murya ya ce, "Kin san tasirin soyayya kuwa? Kin sa yadda zuciyata take lugude a kanta? Don Allah kar ki ce haka don na yi nisa a soyayyarta." Jikin Raihan ba ƙaramin sanyi ya yi ba musamman da ta tuna tata tsohuwar soyayyar, don haka ta ɗago ta ce masa. "Lallai su fillo a faɗa ruwa tsamo-tsamo, kasan dai ni ce babar aminiyarka yanzu dai ka bari na je na dawo sai mu yi magana ko ƴar gidan waye zan je nema maka soyayyarta." Kabiru ya yi murmushi don ba ƙaramin jin daɗin bayanin Raihan ya yi ba. Cikin gida ta wuce tana kwaɗa sallama, a hakimce ta samu su Inno sun zabga kwalliya kowacce ta saka sabuwar atamfa hannu ɗauke da hijabi, Raihan na ganinsu tun daga bakin ƙofa ta ce, "Inno ina za ku ne haka?" Inno ta kalli ƙofar da Raihan ta shigo ta ce, "Ke ina Audullahi?" Raihan ta ƙarasa tana ajiye mayafinta ta ce, "Yana wurin matarsa." Goggo ta ce, "Mu fa shirya wa muka yi ya kai mu." Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Ya kai ku ina? Don Allah ina ruwan zafin da zan tafi da shi don sauri nake ina koma wa Daddy zai tafi uzurin gabansa." Ta yi maganar a gaggauce don ta fahimci su Inno asibiti za su ce za su je. Inno ta miƙe tsaye ta ce, "Ai sai dai mu tafi tare amma Allah ya sani yau sai na je na gano jikana duk baƙincikin ki." Raihan ta wara hannu alamun rashin damuwa ta ce, "Na hana ku tafiya ne? Amma gaskiya babu wacce za ta shigar min mota ta riƙa yi min ihu. Na ga jiya ma kun je asibitin nan ya ilahi wurin nan fa ba biki ake yi ba, ina jin ma da yamma Dr zai iya sallamarta." Goggo ta miƙe tsaye a fusace ta ce, "Ki gode wa Allah ba a Albasu nake da zama ba wallahi da kullin sai an yo mota guda daga can an zo duba ta, a farke cikin mai rai sannan ace ba za ka je ka yi masa sannu ba. Ƴar nan kina cikin hayyacinki kuwa." Raihan ta nufi hanyar kitchen tana faɗin, "Ku faɗi duk abin da za ku faɗa amma babu wacce za ta shigar min mota." Flask ɗin shayi ta ɗauko har ta nufi hanyar fita wani tunani ya faɗo mata don ta san sarai idan ta fita su Inno suna iya cewa za su fita su tafi da kansu, juyo wa ta yi ta: "Ku taso mu tafi. Amma wallahi kuka nemi tara min mutane Allah a titi zan zube ku." Ba musu su Inno suka taso suka biyo bayan Raihan suna zuwa Raihan ta buɗe musu suka shiga baya. Kabiru na ganin fitowarsu ya ce, "Su Hajiya Inno yau ma fita za a yi?" Inno ta ce, "Bari Kabiru za mu koma dubo jikin Zainabu kaima ba don tsaron gida ba ai da mun je tare." Kabiru ya ce, "Sai kun dawo a yi mata sannu." Ya ƙarasa maganar yana buɗe musu ƙofa sannan suka fice.

Su Inno suna tafe sai kalle-kalle suke babu damar a zo wurin danja sai su hau mitar an tsayar da su, a haka suka ƙarasa asibitin har lokacin Daddy yana zaune. Shigar su Inno ya sa Daddy ya miƙe har zai fita Inno ta ce, "Audullahi dawo magana nake son yi da kai." Daddy ya koma ya zauna Inno ta ci gaba da cewa, "Audullahi saboda Allah me muka tsare wa ƴarka ta ɗauki karan tsana ta ɗora mana, ko don muna zaune a gidan iyayenta." Inno na gama magana Mommy ta waiga ta kalli Raihan saboda dama tun da ta gansu tare ta san za a rina. Daddy ya dubi Raihan rai a ɓace ya ce, "Raihan me kika yi wa su Inno?" Raihan ta tura baki gaba ta ce, "Saboda Allah Daddy me zan yi musu kasan dai halin tsofaffin nan fa." Goggo ta yamutsa fuska ta ce, "To idan saboda zaman mu ai sai mu kama gabanmu ina dalili, daga mun ce za mu zo asibiti yarinya ta saka mu a gaba da jaraba." Daddy ya kalli Raihan ya ce, "Bata kyauta ba amma Inno ku yi haƙuri, ke kuma..." Daddy ya katse zance shi yana nunata da yatsa sannan ya ci gaba da cewa, "Idan kika sake kika ƙara sai ranki ya ɓaci." Inno ta gyaɗa kai sannan ta ɗora da cewa, "Audullahi duk ba wannan ba gaskiya mota za ka saya mana kowa ɗaiɗai, mu riƙa tuƙa abar mu muna zuwa inda ranmu yake so. Haka kawai kullin za ka fita a riƙa ja maka rai, shi kuma direban yaron can ba shi da saiti. Kullin ya zo a ɗame wando kamar zai tsage sai kace jikan Elinzabet, a'a raba ni da wannan lamarin don wallahi sumar kansa tsoro take ba ni ga wari kamar an buɗe shadda."Daddy sai da ya gama jin jawabin Inno ya ce, "Inno mota fa? Duk motocin cikin gidan ba su yi muku ba? Idan Abbati ne bai yi muku ba ai sai na sauya wani." Goggo ta ɓata fusta tana cewa, "A'a ka bar Abbati kar mu zama silar barin cin abincinsa, amma dai mota za ka saya mana ka koya mana. Don idan ka saka Raihanu ta koya mana alƙur'an wataran murje mu za ta yi kamar ƴaƴan boris."

Gabaɗaya mutanen ɗakin sai da suka saka dariya har Daddy don yadda Goggo ta yi maganar ne zai baka dariya, Daddy ya dubi Goggo ya ce, "Goggo yanzu dai don Allah ku ɗan tsahirta da siyan motar nan a bari Zainab ta samu lafiya jikinta ya yi ƙwari kun ga duk abin da zai zo daga baya mai sauƙi ne." Su Inno suka jinjina kai cike da gamsuwa sannan Daddy ya tashi ya fice. A ranar da yammma aka sallami Mommy saboda dama a ƙa'idarsu kwanan mace huɗu da yin Cs suke sallamarta idan har ita da Babynta suna lafiya. Komawar Mommy gida ƴan dubiya da barka suka riƙa zarya, suna zuwa sake ganin Mommy sai dai bata yi taron suna ba don ta ce ta wuce wannan lokacin, taron suna sai Raihan ta haihu. Mommy ta yi shar da ita gwanin birgewa ita da jaririnta suna cikin ƙoshin lafiya, Daddy ya so saka sunan Mahaifinsa amma gudun rigima tsakanin Inno da Goggo ya sa ya saka masa suna Muhammad. Kusan rainon Muhammad a wurin su Inno da Raihan ake yi don Mommy aikinta bayar da mama kawai. Wata ranar talata suna zaune da yamma suna hira; Muhammad a lokacin kwanansa arba'in cif, Raihan na rungume da shi sai kawai ta ji ina ma ita ma ace Muhammad Ɗanta ne. Ta ɗago ta dubi mommy ta ce, "Wallahi mommy Allah ya taimake ki ina gida da ban san ya za ki yi da rainon Muhammad ba, yanda yaron nan yake da rigima ba ƙaramin wuya za ki sha ba." Mommy ta kalli su Inno ta ce, "Yanzun ma ai bake kike min ba ga iyayena su suke min raino, dan gidanku da za ki ce haka da wa ya yi min naki rainon?" Raihan ta miƙe tsaye ta miƙa wa Goggo Muhammad ta ce, "Ai kuwa shi kenan daga yau kuwa na daina taya su." Tana gama maganar ta wuce bakin gate, sanye take da doguwar rigar abaya kanta yane da mayafi. Kujera ta janyo tana ƙawala wa Kabiru kira, yana fitowa ya hangota sannan ya janyo kujera yana fuskantarta ya ce." Don Allah fillo ki daina min kiran mafarauta." Raihan ta yi dariya sannan ta ce, "Ango! Ango!!" Tsaki Kabiru ya yi ya ɗauke kai gefe zai yi magana Raihan ta ce, "Wai ya shgalin bikin zai kasance? Sai wani basarwa kake ka zo mu yi shawara ko garinku ba a komai lokacin biki?" Cikin yanayin damuwa Kabiru ya ce, "Tun farko na gaya miki ba na son auren nan saboda akwai wacce na mallaka wa zuciyata. Amma me ya sa za ki riƙa tambayata akan shirin biki bayan kin san ba son auren nan nake yi ba, biyayya ce kawai zan wa su Baffajo." Ba ƙaramin tausayi ya bawa Raihan ba don haka ta ce, "Ba tun yau ba na tambaye ka, wacece ita a ina take? Idan ka na ganin ni na yi yarinta sai na sa mommy a maganar amma wannan kamar ka daɓa wa kanka ne." Kabiru na shirin yin magana ya ji an fara horn a bakin gate, da sauri ya miƙe ya buɗe ganin motar Daddy ce, sai wata motar da take biye da shi. A jere suka shigo har wurin parking space, Daddy ne ya fara fito wa sai Dr Hussain da ya fita daga tashi motar. Daga ɓangaren mai zaman banza Barista Huzaifa ne ya buɗe ya fito cikin farar dakakkiyar shadda, sai baƙar hula, baƙin takalmi da baƙin agogo ɗaure a hannunsa. Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cikakken bafulatani ne, kayan jikinsa ba ƙaramin amsarsa suka yi ba don shi dama ma'abocin son ado da kwalliya ne.


Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624


33



Da ido Raihan ta bi su don ba ƙaramin mamaki ne ya kamata ba, musamman ganin Barista da ta yi don sarai ta gane fuskarsa. Miƙe wa ta yi ta nufi wurin Daddy ta karɓi jakar hannunsa ta furta, "Daddy barka da zuwa." Tana amsar jakar Daddy ta kalli Dr Hussain ta furta, "Dr yau kai ne a gari?" Dr Hussain ya yi murmushi ya ce, "Ba zuwana ba ne ni ma taso ni aka yi." Ya yi maganar yana kallon Barista haɗe da yin dariya. Raihan ta taɓe baki ba tare da ta kalle shi ba, tana niyyar wuce wa cikin gida Daddy ya ce, "Raihan ki kawo wa su Dr abin sha muna falon baƙi." Ɓata fuska Raihan ta yi don ko kaɗan ba ta so ba, murya can ciki ta amsa sannan ta wuce cikin gida. Daddy ne ya yi musu jagora suka wuce falon da Daddy yake saukar baƙi, bayan sun shiga Dr da Barista suka zube ƙasa cikin ladabi suka gaida Daddy. Daddy ya yi mamakin wannan gaisuwa ta Dr Hussain don sun daɗe da shi kuma bai taɓa yi masa irin haka ba, kujera ya nuna musu ya ce, "Ga kujera ku zauna man kwa zauna a ƙasa." Dr ne ya fara miƙe wa sannan Barista ya miƙe suka hau kan kujera. Da sallama Raihan ta shiga ta dire tiren hannunta wanda yake ɗauke da ruwa da kayan lemuka, bayan ta ajiye ta sake fita ta shigo da wani farantin mai ɗauke da kayan marmari ta ajiye, sannan ta fice daga ɗakin. Daddy ya zuzzuba ya miƙa musu sannan ya ɗora da cewa, "Ai lokacin da ka kira ni Dr na fito daga office babu jima wa don haka ba ce kawai mu haɗu a gida, sai ga shi mun zo kusan lokaci ɗaya." Dr Hussain ya yi murmushi sannan ya ce, "Alhaji dama wata magana ce tafe da mu don haka na ce ya dace mu fara samun ka da maganar hakan ya fi dace wa, wannan dai abokina ne tare muka taso tun muna ƙanana shi ma ɗan Kano ne daga baya da kowa ya samu aikin sai kowa ya kama gabansa. Sunansa Barista Huzaifa kuma haifaffan unguwar Kurawa ne, lauya ne a babbar kotun shari'ar musulunci da ke jihar Kaduna." Daddy ya sake kallon Barista Huzaifa yana jinjina kai sannan Dr ya ɗora da cewa, "Tun kwanaki lokacin da aka yi wa Hajiya aiki ya ga Raihan ya ji yana sonta da aure, don haka da ya same ni da maganar ya ce ya fi son ya fara samun mahaifinta ya sanar da shi kamar yadda ya fi cancanta. Cikakken sunansa Huzaifa Rufa'i Mustafa, amma ana kiransa da Barista Huzaifa." A firgice Daddy ya ɗago yana kallon Barista tare da furta, "Huzaifa!" Da mamaki duka suka kalle shi jin yanda ya ambaci sunan. Dr ya ɗan sosa kai sannan ya ce, "Alhaji shi ne muka ce bari mu zo ba mu sani ba ko an yi mata miji." Daddy ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta, "Raihan ba a yi mata miji ba amma gaskiya ina buƙatar yin nazari sannan kuma sai na ji daga bakin yarinya." Barista Huzaifa ya jinjina kai sannan ya ce, "Babu damuwa Daddy Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alheri." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Lemo kawai suka sha don sauyin da suka gani a tattare da Daddy ba ƙaramin sanyaya gwiwarsu ya yi ba, ba su jima ba suka yi wa Daddy sallama suka wuce don shi Barista tun a lokacin ya fidda rai da samun Raihan saboda yanayin Daddy kaɗai shi zai tabbatar maka da yana cikin ɓacin rai. Suna fita Daddy ya yi cikin gida a lokacin har an fara kiran sallar Magriba, sai da ya yi alwala ya yi sallah ɗsannan ya samu Mommy da maganar. Duk abin da Dr ya gaya masa game da Barista haka ya ba wa Mommy labari sannan ya ɗora da cewa, "Maganar gaskiya ba zan bawa yaron nan Raihan ba, ba don komai ba sai don yana ɗauke da sunan wanda na fi tsana a duniya. Kin san komai game da Huzaifa yanzu kina ga wani zai zo mu bashi aurenta ne?" Mommy ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce, "Don yana ɗauke da suna Huzaifa ba zai zama aibu ba Daddyn Raihan matuƙar mutumin kirki ne, yanzu don Huzaifa aljani ya cutar da Raihan sai mu ce duka masu Suna Huzaifa ba su da Hali kenan? Ka yi tunani sosai Daddyn Raihan kuma ka yi bincike tun da gidan iyayen Dr Hussain ba ɓoyayyun ba ne ka ga kuwa shi ma gidansu Barista Huzaifa ba zai yi wuyar sani ba. Amma batun ka hana shi auren Raihan bai ta so ba, tun da shekarun yarinyar nan ƙara gaba suke yi yanzu a ƙalla Raihan fa ta tafi shekara ashirin da huɗu." Daddy ba ƙaramin gamsuwa ya yi da maganar Mommy ba don haka ya numfasa ya ce, "Shi kenan Allah ya zaɓa mana abin da ya fi zama alheri." Mommy ta amsa masa, "Amin ya rabbi. Addu'a ita ce mafita." Daddy ya karɓi Muhammad yana yi masa wasa sannan ya ce, " Zan sanar da Raihan idan ta amince sai na bincika wanene yaron, asalinsa da tarbiyyarsa." Mommy ta faɗaɗa murmushi sannan ta ce, "Allah ya sa mu ji alheri." Daddy ya amsa da amin.

A daren ranar Daddy ya sanar wa da Raihan abin da yake tafe da Barista, Raihan mamaki abin ya bata. Don haka ta cewa Daddy sai ta yi shawara tukunna, su Inno na jin wannan zance suka riƙa murna da farinciki Goggo har da guɗa yadda kasan an ce mata ɗaura auren Raihan aka yi. Washegari da yamma tana zaune a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login