Showing 147001 words to 150000 words out of 157890 words

Chapter 50 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

156

da baka jin daɗi." Malam ya jinjina kai sannan ya ce, "Da ace da yuwar haka da na haƙura amma Raihan kamar ƴa take a wurina hasalima Mahaifinta ya mallaka min komai na aurenta." A hargitse Al'amin ya furta, "Aure kuma? Tun yanzu za ta yi aure?" Mamaki da dariya suka kama Malam ya ce, "Me ye naka a ciki? Ga abin da na ce maka ƙafa tana yi min ciwo ka zo ka kaini ɗaurin aure." A fusace Al'amin ya yi gaba Malam ya kalle shi yana ƙunshe dariyarsa don dama da biyu ya yi haka don ya harzuƙa masa zuciya, saboda har lokacin idan Malam ya tuna abin da Al'amin ya yi wa Raihan ransa sai ya ɓaci. Wani irin gudu Al'amin yake yi fuska a murtuke babu walwala don haka Malam ya dube shi ya ce, "Aminu ni ko wani abu yana damunka?" Al'amin ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce, "Lafiya ƙalau Daddy me ka gani?" Malam ya furta, "To ka ja ni a hankali don na ga gudu kake kamar za ka tashi sama, kuma yanayinka duk sai a hankali." Da to kawai Al'amin ya amsa baƙinciki ya mamaye zuciyarsa har suka ƙarasa ƙofar gidansu Raihan da ke cike damƙam da mutane, suna zuwa Malam ya ce masa, "Sauko mu je don babu jimawa kai za ka mayar da ni." Kamar Al'amin zai yi kuka ya ce, "Gaskiya ni ba zan je ba Daddy ba na son hayaniyar mutane." Malam ya yi murmushi sannan ya fice daga motar, Malam na fita Al'amin ya juya akalamar motarsa ya bawa gidansu Raihan baya sai dai jin zuciyarsa yake kamar za ta hudo ƙirjinsa, don da ace Malam ba Mahaifinsa ba ne babu yadda za a yi ya iya jiransa a ɗaurawa Raihan aure yana tsaye a wurin. Yana nan zaune ya ji an ɗaura auren Raihan tare da Alhaji Shatima akan sadaki dubu ɗari, maimatawar da maroƙa suke yi shi ya sake dagula lissafinsa har ya gagara haƙuri ya kira wayar Daddy don ya ce masa ya fito su tafi amma har ta katse ba a ɗauka ba. Malam bai fito ba sai da suka gama gaisawa da mutane sanaan ya yi wa Daddy Allah sanya alheri ya shiga mota, a lokacin Al'amin ya haɗa kai da sitiyarin mota yana jin ɗaci a zuciyarsa. Yana tayar da mota ya hango wani babban mutun da wata dakakkiyyar shadda yana tafe maroƙa na biye da shi da alama shi ne Alhaji Shatima, karaf ya ji Malam ya furta, "Al'amin ka ga Angon Raihan nan idan ma baka son hayaniya nan babu mutane ya kamata ka yi masa Allah sanya alheri tun da ga Mahaifinta can shi ma ka ƙarasa ku gaisa." Al'amin bai gama jin maganar Malam ba ya figi motarsa ya kamar zai bi ta kan Alhaji Shatima.

Daga cikin gida mata ne suke gudanar da yini sai dai babu wasu mutane da yawa, yawancinsu ƴan uwa ne da abokan arzƙi. Raihan ta yi kyau sosai an yi mata ɗinkuna gwanin birgewa sai shiga take tana fita, su Inno suma sun fito shar Daddy ya yi musu ɗinkuna kusan duk iri ɗaya ne. Bayan sallar magriba Daddy da kansa ya ɗauki Raihan ya kaita gidanta da ke unguwar Gaida, yana dire Raihan motocin su Mama Hafsa suka yi parking. Bayan shiga gidan Raihan nasiha suka yi mata sosai kowa maganarsa ɗaya ta riƙe mijinta hannu bibbiyu kamar yadda yake ƙaunarta, ba su ɗauki lokaci ba suka yi mata sallama suka tafi. Fitar su ke da wuya Alhaji Shatima ya shigo tare da abokansa biyu, Raihan tana jin su suna zolayarsa wata maganar idan suka yi har kunya take ji. Su ma ba su daɗe ba Alhaji Shatima ya yi musu rakiya sannan ya dawo wurin Raihan, cike da shauƙin so da ƙauna ya zame mata mayafi yana sakar mata murmushi. Ita ma murmushi ta mayar masa sannan sunne kanta ƙasa, sauka ya yi ya baje musu lodojin da ya shigo da su ya fara ƙoƙarin jan Raihan da hira don ya lura kunyarsa take ji ya ɗora da cewa, "Amarya bakya laifi." Murmushi Raihan ta yi ya ruƙo hannunta suka ba je a ƙasa ya fara bata kayan ciye-ciye a baki tana karɓa a kunyace. Don ba ƙaramin mamaki ta yi ganin yadda Alhaji Shatima ya iya soyayya kamar matashin saurayi ba. Bayan sun ci sun ƙoshi Alhaji ya miƙe don ya ɗauro alwala su gabatar da sallah, wayarsa ta fara ringing yana ɗauka wata baƙuwar lamba ya ga ta shigo kamar kar ya ɗauka sai kuma wata zuciyar ta ce ya ɗauka don ya ji wanda yake kiransa a wannan lokacin da yake shirin amarcewa da amaryarsa. Wayar ya kara a kunne tun bai yi magana ba ya ji an ce, "Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa, don haka ka yi hanzarin zuwa gidan gonarka da ke By pass ta yuwu kafin ka je ka sa mu matattun awaki da shanunka idan kuma ka yi jinkira sai dai ka samu tokarsu."



Na ce ba🥵 Auren suger Daddy's fa duniya ne🤭🌚 Na so kammala book ɗin nan a wannan shafin amma sai a na gaba insha Allah, don sai Alhaji Shatima ya hallake mata wancan gayen Huzzy kenan☹️

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

51


A hargitse Alhaji Shatima ya furta, "Kai yaro saurare ni da kyau ka san da wanda kake magana kuwa." Dariya mai sauti ya ji an yi sannan aka ce, "Azarɓaɓin me kake yi haka Dattijo, indai ni ne da sannu za ka fahimci ko wanene ni." Daga haka ya ji ƙit an kashe wayar." Shiru ya yi yana kallon lambar, Raihan da ke gefe ta ɗago ta ce, "Lafiya kuwa Alhaji." Alhaji Shatima ya ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali don tuni hantar cikinsa ta kaɗa ya ce, "Wani sakarai ne ya kira ni yana yi min surutan iska da wofi, amma share kawai irin ƴan iskan gari ne." Sai da ya ajiye wayarsa ya fara naɗe hannun babbar riga ya ce, "Mutane ba su da hankali wallahi, sai kana cikin farinciki su nemi su dagula maka lissafi." Har ya kai bakin toilet wayarsa ta sake yin ƙara ya saki guntun tsaki ya furta, "Ƙyale ƴan wahala sa yi su gama." Banɗaki ya shiga ya ɗauro alwala ya dubi Raihan ya ce, "My baby shiga ki ɗauro alwala." Ajiye mayafinta ta yi har ta gifta ta gefensa ya rungumo ya haɗe ta da jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, sunkuyar da kanta ƙasa ta yi jikinta ya fara rawa. Alhaji Shatima ya sakar mata kiss a kumatu sannan ta shiga banɗaki don ta ɗauro alwala. Yana zaune ya ga lambar Alhaji Tasi'u ta shigo wayarsa, da mamaki ya dubi lambar ya kai hannu ya ɗauka cikin shaƙiyanci ya ce, "Haba mutumina wannan lamarin akwai shiga haƙƙi fa, ka sa ni ko ina nan ina takara da miraja'a za ka kira ni yanzu..." Bai ƙarasa maganar ba Alhaji Tasi'u ya katse shi da cewar, "Wai baka san abin da yake faruwa ba ne Alhaji Shatima?" Gaban Alhaji Shatima ya yanke ya faɗi cikin hanzari ya furta, "Ban gane ba wani abu ne ya faru?" Alhaji Tasi'u ya ce, "Ga ƴan kwana-kwana can a gidan gonarka tana ta ci da wuta nima yanzu Hafuz ya shigo yake gaya min ya wuce ta hanyar ya ga abin da yake faruwa." Wani irin gumi ne ya riƙa tsattsafowa Alhaji Shatima, jiki da karkarwa ya ce, "Don Allah abin da kake faɗa haka ne?" Haushi ya fara kama Alhaji Tasi'u a daƙile ya ce, "Wai ina yi maka irin wannan wasan ne? Ai ko zan yi maka ƙarya ba zan yi maka akan wannan abin mara daɗin faɗa ba." Alhaji Shatima tun bai katse kiran ba ya wurgar da wayar ya fice a guje wurin harabar motarsa, yana shiga motarsa ya riƙa sakin horn har sai da Maigadi ya fito da sauri ya buɗe masa gate ya fice a guje. Yana fita Raihan ta fito da gudu don ta ji fitarsa ta samu mai gadi a tsaye da alama shi ma jimamin yanayin yadda Alhaji Shatima ya fita yake yi. Da sauri ta tambayi Maigadi wurin da Alhaji ya tafi, hannuwa biyu ya rungume sannan ya ce, "Wallahi Hajiya idan na ce ga wurin da Alhaji ya tafi na yi ƙarya, ina cikin ɗaki na ji yana zabga horn sai na fito na buɗe masa ya fice a guje." Jiki a sanyaye Raihan ta amsa sannan ta koma ɗaki ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido, dabara ce ta faɗo mata ta ɗauko wayarta ta kira lambarsa sai jin ringing ɗin wayar ta yi a bayanta. Tagumi ta zuba hannu bibbiyu tana jiran ta ji shigowar mijinta amma har ta fara gyangyaɗi bata ji motsinsa ba. Miƙewa ta yi ta rage kayan jikinta, ta gabatar da shafa'i da wuturi sannan ta koma gado ta zauna tana nan zaune bacci ya yi awon gaba da ita. Sama-sama cikin baccinta ta ji motsin shigowarsa, da sauri ta zabura tana mutssika idanu ta kalle shi ta ce, "Alhaji ina ka je haka? Tun ɗa zu nake jiranka." Kamar wanda aka zare wa laka a jiki haka ya zauna ya haɗa hannuwa biyu ya rafka uban tagumi, tana shirin sake yi masa magana sai gani ta yi hawaye na zuba bibbiyu a fuskarsa. A rikice Raihan ta dube shi ta ce, "Me yake faruwa ne Alhaji?" Zuciyarsa na zafi ya furta, "Gidan gonata gabaɗaya ya babbake da wuta, hatta dabbobi da tsuntsayen da suke ciki babu wanda ya tsira. Wannan wacce irin masifa ce a ce a daren Angwancina wannan bala'in ya faru da ni." Jikin Raihan ne ya yi sanyi a hankali ta furta, "Innalillahi'wainna ilahirraji'un. Addu'a za ka yi Allah ya sa haka ne ya fi alheri..." Tun bata rufe baki ba a zafafe Alhaji Shatima ya furta, "Alheri a gidan uban wa? Asara kamar wannan ta same ni ki ce Allah sa shi ne mafi alheri? Ko shanu kaɗai kin san guda nawa ne a ciki? Ko shanun da suka ƙone sun haure guda tamanin kar a zo ga raguna da ƙananan dabbobi." Shiru Raihan ta yi don ta lura kamar akanta yake shirin sauke zafin da ya ɗauko, a hankali ta bi gefen gado ta zauna tana nan zaune har bacci ya sake yin awon gaba da ita. Kiran asubar farko ne ya tashe ta, tana tashi ta hangi Alhaji Shatima ya ɓingire a jikin gado da alama shi ma a zaune baccin ya yi awon gaba da shi. Sai da ta ɗauro alwala ta yi raka'atanal fijir sannan ta fara tashinsa, a hargitse ya farka yana faɗin, "Ku yi sauri ku kashe shanu da awakin ciki za su ƙone." Murza ido ya yi da ya ji muryar Raihan tana faɗin, "Na ji masallaci sun kusa shiga ka tashi ka yi sallah." Guntun tsaki ya yi ya miƙe don wani irin haushinta yake ji uwa-uba ga ɓacin ran da yake damunsa. Yana dawowa daga masallaci wayoyin mutane suka fara shigo masa, mafi yawa daga cikinsu masu yi masa jajae ne. Daga cikin masu kira har da Daddy don tun cikin dare ya samu labarin faruwa lamarin, sai da ya yi masa jaje sannan ya ce zai tura masa da tallafin wasu ƴan kuɗaɗe don ya rage asara. Ba ƙaramin daɗi Alhaji Shatima ya ji ba haka abokanansa suka riƙa kiransa kowa da irin gudummawar da yake bashi. Wannan ne ya rage masa raɗaɗin zafin abin da ya faru don wunin ranar haka ya yi ta amsa wayar mutane, Nura da Abubakar ƴaƴansa ne biyu rak a duniya. Suna karatu a Sudan suma sun samu labarin abin da ya faru don haka suka kira mahaifinsu suka jajanta masa akan abin da ya faru.

Washegarin ranar haka ƴan uwa da abokan arziki daga ɓangaren Raihan zuwa na Alhaji Shatima suka riƙa zuwa suna yi musu jajaen abin da ya faru, gidan su bai sarara da mutane ba sai bayan la'asar sannan Raihan ta samu ta sake fesa wanka ta shirya cikin doguwar rigar shadda. Ranar da Raihan ta tare Al'amin ji ya yi kamar zai yi hauka saboda tashin hankali, hatta Sumayya ta fahimci abin da yake faruwa da shi don haka ta riƙa baya-baya da shi don ta tabbata idan bata yi da gaske ba sai ya sauke faɗan akanta. Haka daga ɓangaren Kabiru wani abu ya ji ya tsaye masa a rai don har ji ya yi kamar ya fice daga gidan saboda yadda duniyar ta yi masa zafi.

Tallafin da Alhaji Shatima ya samu ne ya bashi damar samun ƙwarin gwiwa har ya rage jin zafin Raihan, saboda ya samu kuɗaɗe masu yawan gaske. Don haka magriba na yi ya fita ya sake yi musu siyayyar kamar yadda Angwaye suke yi idan za su shiga ɗakin amarensu, lokacin da ya dawo Raihan na kwance tana danna wayarta ta yunƙura ta yi masa barka da zuwa sannan ta karɓi ledar hannunsa. Plate ta ɗauko a kitchen ta fara saka musu Alhaji Shatima na tayata, da kansa ya ɗauko musu ƙananan kofuna ya zuba musu lemo suka fara ci yana yi mata hira a hankali. Wannan karon Raihan da kanta take ci sai dai Alhaji Shatima na jikinta tsam kamar wai zai kwaceta. A haka har suka gama ci suka taɓa hira sannan suka ya da zango akan gado, ƙirjin Raihan sai bugawa yake jikinta na rawa don haka Alhaji Shatima ya raɗa mata a kunne, "Karki tsoro haba kamar ba jarumar mata ba." Ajiyar zuciya Raihan ta sauke yana ci gaba da aika mata sakwanni masu zafi, tun tana ɗari-ɗari da shi har ta saki jikinta. Jin yana ƙoƙarin shigarta ya sa ta dube shi duk da tana jin nauyinsa, ta kamo hannunsa ta ɗora akanta sannan ta furta. "Don Allah karka manta da addu'ar da Annabin Rahama ya koyar da mu a wurin kusantar iyali." Saboda ita kaɗai ta san irin abin da ta fara ji a jikinta game da shi, ta tabbata akwai abin da yake shirin faruwa don ko kaɗan bata ji Alhaji Shatima ya ambaci sunan Ubangiji don neman tsari. A kunyace Alhaji Shatima ya furta, "Tabbas ko rannan na ji wani Malami ya karantata amma sam ban iya ba." Raihan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce, "Duk abin da na faɗa ka maimaita, saboda mutane da dama na manta wa da wannan addu'ar kuma tana da muhimmanci domin idan Allah ya ƙaddara za a samu rabo shaiɗan ba zai yi tasiri a rayuwar wannan yaron ba, duk wani sharri da kaidin shaɗan da tawagarsa Ubangiji zai kare ku daga sharrinsu." Gyaɗa mata kai ya yi sannan ta fara karanta masa kamar haka: "Allahumma Jannibnasshaɗan,Wajannibnasshaiɗana Marazaktana." Sannan ya ci gaba da aikata mata da kalaman soyayya har ya cimma burinsa. A hankali Alhaji Shatima yake sauke ajiyar zuciya, ya yunƙura ya faɗa banɗaki don tsarkake jikinsa sannan ya dawo ya taimakawa Raihan ita ma ta gyara jikinta sannan suka yi addu'a suka koma bacci. Asubar Fari Raihan ce ta fara tashi yana jin motsinta shi ma ya tashi, tare suka shiga toilet suka ɗauro alwala Alhaji Shatima sai nannan yake yi da ita, Raihan har mamaki take yi zuciyarta fes don ko babu komai Alhaji Shatima ya nuna mata kulawa da tsantsar soyayya. Doguwar riga ya zura ya wuce masallaci Raihan ta tayar da sallah bayan ta idar ta ɗaga hannu ta godewa Allah da ya bata miji mai ƙaunarta yake bata kulawa.Tana nan zaune ta ji shigowarsa, shigarsa ta yi daidai da kiran wayarsa. Kallon Raihan ya yi ya sakar mata murmushi sannan ya ɗauki wayarsa, ganin baƙuwar lamba ya sa ya yi zaton ko masu yi masa jaje ne don tun da abin ya faru mutane kala-kala suke kiransa. Yana ɗauka ya ji an ƙyaƙyace da wata irin mahaukaciyar dariya, ransa ne ya fara ɓaci a harzuƙe ya ce, "Wa ye haka kamar mara aikin yi?" Daga can ɓangaren aka amsa masa da cewar, "Ni ne kuwa mai aikin yi tun da na fara yi maka ɓarna a daren jiya, bar ganin ka shiga gonar da ba taka ba na rantse da hatsabibancin da kakana ya bar min ba za ka keta haddin Raihan a banza ba, Raihan tawa ce kamar yadda na faɗa ina ƙara nanatawa Idan kuma kana tantama ka buɗe Whatsapp ɗin ka zan turo maka hotunan da muka ɗauka a daren jiya bayan fitarka wurin gidan gonarka da ya babbake. Sai da muka ɓarje amarcinmu sannan kuma muka yi hotuna..." A fusace Alhaji Shatima ya katse shi da cewar, "Kai wai me kake faɗa ne? Wacece matar taka?" Dariya aka sake yi sannan aka ci gaba da cewa, "Saurin me kake yi za ka ga gane ko wanene ai, amma kafin nan ina yi maka albishir da na cinnawa kamfanin shinkafarka da na robobinka wuta sai ka ɗauki duk wani mataki da ka ga damar ɗauka. Amma ka duba Whatsapp ɗin ka za ka gani idan ƙarya na yi maka, kuma wallahi da ni kake zance." Ƙit! Alhaji Shatima ya ji an katse wayar, a rikice hannunsa na rawa ya kunna data saƙonni na fara shigowa ya ga wata lamba an turo masa hotuna rututu, yana shiga ya ga hotunan tsiraici ne na Raihan da wani matashi. Raihan na daga gefe jikinta ban da rawa babu abin da yake yi, hawaye ne ya taru a idonta don duk hirar da suka yi ta ji ta a kunnenta. Fuskarsa ce ta haɗe murtuk ya kalli Raihan suna haɗa ido ta fara matsawa da baya tana faɗin, "Na rantse da Allah ban san komai ba. Wallahi duk sharri ne ya yi min ni ban san akan me yake magana ba." Miƙe wa ya yi yana huci ya ƙarasa kan Raihan ya daƙumota, yana shirin kai mata mari wayarsa ta sake ringing. Ganin lambar ɗazu ya sa shi ɗauka da sauri yana karawa a kunne aka ce, "Idan ka sake ka taɓa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login