Showing 90001 words to 93000 words out of 157890 words
wurin Kabiru suna hira, don Kabiru shi ya zame wa Raihan babbar ƙawa duk wasu shawarwari a wurinsa take nema kuma yana bata shawarwari masu kyau. Tun da su Barista suka zo gaban Kabiru yake faɗuwa ya rasa dalili, fargabarsa ɗaya kar ace masa manema aurenta ne, amma da ya ga sun fito da wuri sai ya ɗauka kawai baƙi ne wani uzuri ya kawo su. Suna zaune Raihan ta dube shi ta ce, "Fillo shawara na zo nema!" Ras! Ya ji gabansa ya faɗi sai ya yi ƙarfin hali ya ce, "Ina jin ki fillo me yake faruwa?" Raihan ta ajiye lemon hannunta ta ɗora da cewa, "Ina mutanen da suka zo jiya? Ba ka lura da wani mai baƙar hula ba?" Da sauri Kabiru ya gyaɗa kai gabansa na ci gaba da faɗuwa, Raihan ta taɓe baki ta ce, "Wai sona yake da aure shi ne ya zo ya samu Daddy da maganar kasan abokin Dr da ya yi wa Mommy Cs ne." Nan take Kabiru ya sauya fuska cikin yanayin damuwa, gudun kar Raihan ta harbo jirkinsa ya ce, "Ah kai masha Allah, Allah sanya alheri." Raihan ta ɓata rai ta ce, "Shawara da na zo ka bani ko ka ga ya yi ne." Hararar wasa ya yi mata sannan ya ce, "Malama ki ce kin faɗa sonsa kawai, to da za ki tambaye ni, ni zan zauna miki da shi?" Raihan ta yi murmushi cikin zolaya ta ce, "Ina za ka zauna min da shi na zauna da abina dai, kaima wataƙila kana can da amaryarka." Wannan maganar ba ƙaramin dagula wa Kabiru rai ta yi ba, cikin damuwa ya miƙe yana faɗin, "Fillo kin yi na lokacinki sai gobe." Raihan ta miƙe tana dariya don ita bata kawo komai ba ta ce, "Au yaji za ka min, shi kenan wallahi idan ni ce ina zaune za ka zo nemana." Tana gama maganar ta wuce cikin gida. Kabiru na shiga ɗakinsa ya fara kaiwa da kawo wa don zuciyarsa ba ƙaramin zafi take yi ba, shi kansa ya san Raihan ta yi masa nisa amma babu yanda zai yi don zuciyarsa har kullin azalzalarsa take ƙaunarta na ci gaba da ruruwa a ruhinsa.
A cikin ƙasa da sati guda Daddy ya sa aka binciko masa wanene Barista Huzaifa asalinsa, sana'arsa, mu'amalarsa da waɗanda yake hulɗa da su. Huzaifa ɗan asalin unguwar Kurawa ne wata unguwa da ke cikin garin Kano, su biyar ne a wurin iyayensa yana da yaya Ibrahim shi ne na biyu sai ƙannensa mata guda uku biyu suna ɗakin aure ɗaya budurwa ce tana karatu a FCE Kano. Tare suka taso da Dr Hussain gidajen iyayensu na maƙotaka da juna, daga baya sai iyayen Barista suka tashi daga unguwar kurawa zuwa Fagge, sakamakon gina musu gida da yayan Mustafa ya yi. Barista Huzaifa yana da ilimin addini da na zamani daidai gwargwado, ya karanci ɓangaren shari'a a jami'ar Bayero. Ya samu aiki bai fi da shekara guda ba Mahaifiyar Dr Hussain Allah ya yi mata rasuwa. Fara aikinsa da shekara biyar ya samu canjin aiki zuwa garin Kaduna. Barista Huzaifa yana da kyawawan halaye sai dai abu ɗaya gare shi mummuna wato bin mata, wannan ya samo asali ne tun lokacin da ya fara soyayya da wata yarinaya Sakina, ya so sakina matuƙa daga ƙarshen iyayenta suka ce wani ɗan uwanta za su aura mata. A wannan lokacin ya shiga matsanciyar damuwa, ganin halin da yake ciki ya sa wani abokinsa yi masa tayin fara zuwa Club. Duk da bai taɓa zuwa ba amma ko kaɗan bai musa wa abokinsa Abubakar ba, saboda a lokacin neman duk wani abu da zai ɗebe masa kewa yake yi. Tun a ranar farko ya haɗu da Sima wata riƙaƙƙiyar karuwa, kuma dama tun da ta lura da Barista Huzaifa yawunta ya tsinke a kansa. Babban farincikinta da Abubakar ya sanar da ita sabon yankan rake ne bai saba harkar ba, haka suka jone da Sima suka ci gaba da rayuwa kamar mata da miji. Sannu a hankali Abubakar ya nuna masa ai zama wuri ɗaya tsautsayi ne don haka ya riƙa yi yana cancanza mazauni, wato ya riƙa neman mata kala-kala sun fi ɗebe kewa. A da Barista Huzaifa ya ɗauka ba zai taɓa jin daɗin mace bayan Sima ba, sai da ya tsunduma a harkar sannan ya ji ashe ita ma shafar mai ce. A haka ya ci gaba da rayuwa lokaci-lokaci yana kawo wa iyayensa ziyara, sai dai kullin cikin yi masa faɗan ya fito da mata suke yi, sai dai ya ce musu aure lokaci ne idan lokacin ya zo zai yi. Daga ƙarshe ma sai ya ke ce musu akwai yarinyar da suka daidaita karatu take yi sai ta gama za a yi maganar aure.
Bayan Daddy ya gama bincike da kansa ya samu Raihan da maganar Barista Huzaifa, bata da zaɓi don ita kanta tana sha'awar ace yau ita ce ta yi aure take zaune a gidan mijinta. Musamman da take ganin mafi yawan ƙawayensu duk sun yi aure, don haka ta dubi Daddy ta ce, "Daddy na amince Allah ya tabbatar mana da alheri." Daddy ya yi murmushi ya amsa da Amin. A ranar Daddy ya kira Dr Hussain ya ce masa ya amince ita ma daga ɓangaren Raihan ta amince, Dr Hussain godiya ya yi sannan ya ce zai sanar da Barista Huzaifa duk abin da yake faruwa da yake tuni ya koma wurin aiki. Lambar Raihan Dr Hussain ya roƙa a wurin Daddy a cewarsa zai tura wa Barista kafin ya zo, idan ya so sai su fara gaisawa. Daddy bai musa ba ya turawa Dr Hussain number Raihan, shi ma Daddy na tura masa bayan ya kira Barista ya gama sanar da shi yadda suka yi da Daddy sannan ya tura masa lambar Raihan.
Da daddare bayan sallar Isha'i Raihan na zaune da Laptop a gabanta tana binciko wasu kaya da take son yin order su, wayarta ta fara ringing. Ganin baƙuwar lamba ya sa bata ɗauka ba har sai da aka kira sau biyu. A gajarce ta ɗauki wayar ta furta, "Assalamu alaikum." Sai da ya amsa mata sannan ya ce, "Ashe dai ƴanmatan ta ɗauki nasiha ta, ta koyo sallama." Guntun tsaki Raihan ta yi don a yanayin maganar sa ta fahimci wanene shi. Bata tanka masa ba ta riski muryarsa yana cewa, "Barkanki da dare ina fatan ban takura miki ba." Raihan ta furta, "Kusan haka ne." Siririyar dariya ya yi wacce ya saba saye zuciyar ƴanmata da ita sannan ya fara yi wa Raihan bayanin abin da yake tafe da shi, amsa ta riƙa bashi daki-daki daga ƙarshe ta shaida masa ta taɓa aure da yadda yanayin auren nata ya kasance. Sun ɗan jima suna hira sannan suka yi sallama. Sannu a hankali soyayya ta fara ƙulluwa tsakanin Raihan da Barista Huzaifa, tun Raihan bata sakin jiki da shi har ta fara saki. Sai dai abin da ta lura da shi Barista Huzaifa yana da matuƙar son zolaya, gashi da barkwanci don idan suna hira yana dariya kamar ba shi ba. A haka har manya suka shiga maganar aka tsayar da ranar aure wata biyar, a lokacin kuwa saura wata biyu auren Kabiru da ƴar yayan Mahaifinsa wacce aka yi alƙawarin aurensu tun suna ƙanana. Kasancewar Barista Huzaifa a nesa yake ya sa bai cika zuwa akai-akai ba, don zuwansa biyu aka tsayar musu da ranar aure sai dai waya da chart da suke yawan yi. Su mommy ba ƙaramin farinciki suka yi ba, haka daga ɓangaren ƴan uwan Salim da suka samu labari har gida Farida ta zo ta yi wa Raihan murna. A ranar ne kuma Raihan take gaya mata maganar auren Kabiru, don a lokacin auren Kabiru saura bai fi sati biyu ba. Wannan maganar ba ƙaramin muni ta yi wa Farida ba, don haka ta wuce gida zuciyarta babu daɗi. Lokacin da za ta tafi Raihan ta haɗa mata sha tara ta azziki, har atamfa ta ɗauka daga cikin atamfofin da ta sayawa Kabiru sabida so take ta yi masa bazata ko akwati biyu ta haɗa masa, duk da ta lura ko kaɗan auren baya gabansa. Ita kanta tana damuwa da rashin walwalar Kabiru saboda a baya mutum ne mai matuƙara barkwanci, da son hira.
Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624
34
Raihan ba ƙaramin kaya ta haɗa wa Kabiru ba kusan akwati uku don akwati biyu ta cika taf, wasu kayan masu yawa suka ragu don haka ta ɗora masa da kit. Ba ƙaramin daɗi ya ji ba duk da ko kaɗan baya maraba da auren, daga ɓangaren Daddy kuɗi ya ba wa Kabiru masu tsoka a cewarsa ya sayi duk abin da yake da buƙata wajen hidimar biki. Mommy kayan abinci ta saya masu ɗan dama a lokacin da Kabiru zai tafi ta bashi don a yi hidimar biki kafin su je. Kabiru ba ƙaramin daɗi ya ji ba don dama ya san za su yi masa saboda mutane ne masu karamci da kyauta, ko kaɗan abin hannunsu bai rufe musu ido ba. Saura sati guda biki Kabiru ya tafi garinsu don Mahaifiyarsa kusan kullin sai ta kira shi a waya game da aure.
Kabiru ɗan asalin garin Shanono ne cikin wani ƙauye mai suna Rigar Arɗo, daga dangin mahaifi da Mahaifiya gabaɗayansu haifaffin garin shanono ne. Mahaifinsa sunansa Musa Balarabe amma an fi saninsa da Baffajo, sai mahaifinyarsa mai suna Karime ana kiranta Inna wuro sakamakon ta ci sunan kakarta ta wurin Mahaifi. Kabiru su biyar ne a wurin iyayensa, shi ne babba sai ƙanwarsa mai bin sa Rahane wacce ake kira Rahe. Tana da aure da ƴaƴa shida, sai mai bin ta Fatsim ita ma tana da aure da ƴaƴa uku, daga ita sai Shatu wacce take da ƴaƴa biyu sai ɗan autansu mai suna Bala wanda yake da shekara goma sha biyu. Baffajo manomi ne kuma makiyayi ne ya riƙi sana'ar noma da kiwo tubalin da yake gina iyalinsa ta hanyar ci da sha, ilimi da tufatarwa. Yana da rufin asiri sosai kasancewar Ubangiji ya yalwata su da arziƙin dabbobi musamman shanu da awaki. Baffajo yana tsayawa ƴaƴansa kai da fata wurin ganin sun samu ilimin addini sai dai basa karatun boko kasancewar basu ɗauke shi da muhimmanci ba. Kabiru tun yana da kimanin shekara goma Mahaifinsa Baffajo ya ɗauke ya kashi almajiranci can garin gombe, sai dai bai bar shi kara zube ba yana shirya wa lokaci-lokaci yana kai masa ziyara haɗe da kai masa kayan abinciki ya damƙa wa Malaminsu Malma Iro. Kasancewar Malam Iro mutane da dama sun shede shi akan kula wa da almajiransa, Mutum ne mai amana da kula wa da haƙƙin da aka ba shi don haka ya sa su Kabiru suke matuƙar ƙaunarsa. A makarantar Malam Iro Kabiru ya haɗu da wani almajiri mai suna Babbale, Babbale nutsattse ne ba shi da hayaniya kamar dai Kabiru don haka ta su ta zo ɗaya suka ci gaba da rayuwa da daɗi babu daɗi har Allah ya kai su lokacin da suka yi saukar alƙur'ani kowa ya kama gabansa. Kabiru ya koma garinsu ko shekara bai yi ba watarana shi da Baffajo sun shiga gona wasu ɓata gari da ake zargin ɓarayi ne suka shiga gonaki suka riƙa illata manoman da makiyaya sannan suka kaɗe duka shanun garin suka yi awon gaba da su. A cikin waɗanda suka jikkata har da Mahaifin Kabiru wanda suka harbe shi har a wuri biyu. Harbin farko a gwiwar ƙafarsa harsashi ya ratsa sai tsakiyar bayansa da nan ma suka sakar masa harbi. Kabiru kuma karaya ɗaya ya yi a ƙafa sakamakon saran da suka riƙa kai masa har suka ci galaba akansa. A wannan lokacin mutanen wannan ƙauyen sun shiga firgici da tashin hankali sakamakon ba su taɓa cin karo da irin wannan ta'addancin a cikin garinsu ba. A haka suka ci ga ba rayuwa waɗanda suka rasu aka yi musu sitira waɗanda suka jikkata aka shiga nema musu magani. Mahaifin Kabiru yana ɗaya daga cikin mutanen da aka yi wa mummunan rauni, saboda da farko maganin hausa ake yi masa sai da suka ga ƙafarsa ta tasamma lalace wa sannan aka fara kai shi cikin gari babban asibiti. Tashin farko likitoci suka tabbatar da yanke ƙafar Baffajo za a yi saboda ta riga da ta lalace ba zai sake morarta ba, a wannan lokacin su Inna wuro ba ƙaramin tashin hanakali suka shiga ba. Amma da yake suna da ragowar ƴan kadarorinsu sai suka ganganɗa suka sayar da aka biya kuɗi aka yanke wa Baffajo ƙafa tun daga wurin gwiwarsa har zuwa idon sawunsa. Sai da likitoci suka sake yin gwaje-gwaje da hotuna aka sake gano babbar matsalar da take tattare da Baffajo domin ƙashin bayansa ya samu matsala, don haka sai an yi masa aiki. Tashin farko kuɗin hoton ƙashin bayansa kusan dubu ɗari biyu da hamsin aka caje su sannan da aka gano ciwon aka tabbatar da za a yi masa aiki amma sai sun zube maƙudan kuɗi naira miliyan ashirin da biyar. Wannan magana ta likitoci ba ƙaramin ɗaga hankulansu ta yi ba, Kabiru da kansa ya riƙa bi cikin rugarsu yana neman taimako koda karo-karo ne amma ko dubu ɗari a cikin ƙauyensu bai samu ba. Ganin ba su da damar waɗannan kuɗaɗen suka tattaro suka dawo gida da Baffajo ya ci gaba da jinyar jikinsa ana yi masa maganin hausa. Sai dai tun da ya kwanta wannan jinyar komai sai an yi masa, sai an ɗaga sa an kwantar hatta fitsari sai dai ya yi a wurin idan kuwa aka zo gyara shi ya rinƙa ihu saboda tsananin azabar da yake ji a jikinsa. Ana cikin haka har duk abin da suke da shi ya ƙare har ya kai Inna Wuro ta fara sayar da sitirar da suke saka wa. Ganin haka ya sa Kabiru ya yi tattaki zuwa gidan kansilan garinsu don ya yi masa hanyar zuwa wurin sanatan yankinsu ko zai samu ya taimaka masa. Amma fir Kansilan ya ƙi daga ƙarshe wani abokinsa Na Sa'ade ya kira bayan ya zauna ya nuna Kabiru sannan ya yi masa bayanin halin da Baffajo yake ciki, Na Sa'ade mazaunin garin ne amma yana zuwa kasuwanci cikin garin Kano don haka ya fi su wayewar kai don haka Kansila yake ji da shi a garin. Na Sa'ade yana gama jin bayanin Kansila cikin yanayin tausayi ya ce, "Taimako ɗaya zan yi maka na haɗa ka da wani mutumi a birni amma shi aikinsa zai nema maka gida ka riƙa gadi amma a ƙa'idarsa albashinka na wata ukun farko shi zai karɓa. Amma fa zai kai ka gidajen masu yatsu da yawa, don ba za ka yi zaɓen tumin dare ba. Ina taƙaice maka wataƙila duk wata ka riƙa samun dubu hamsin."
Jin wannan maganar ya sa Kabiru ya ce zai je ya yi shawara da Mahaifiyarsa idan ta amince, saboda suna fuakantar matsanancin talauci. Lokacin da Kabiru ya sanar wa da Inna wuro ƙin amincewa ta yi saboda tana tsoron kar a tafi da Kabiru birni a sayar da shi, amma da Kabiru ya nuna mata mutumin na hannun daman Kansila ne sai ta amince amma da sharaɗin sai sun je gaban Mai gari an yi maganar a gabansa. Lokacin da Na'sade ya ji wannan maganar ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba har ya nuna ya fasa tafiya da Kabiru, amma da Kabiru ya lallaɓa shi kuma ya nuna masa yanayin rikicin tsofaffi ne sai ya amince. A gaban Mai gari aka yi komai bayan wannan zaman da kwana biyu Kabiru da Na Sa'ade suka taho garin kano. A washegarin ranar da suka sauka Na Sa'ade ya kai Kabiru gidan Malam Haru sannan ya gabatar da Kabiru, cikin mutumci ya tarbe shi sai da suka zauna sannan ya sanar wa da Kabiru sharuɗɗansa nan take ya amsa tun da dama Na Sa'ade ya sanar da shi kafin su zo. Satin Kabiru ɗaya a gidan Malam Haru aka zo masa da maganar samun aiki a gidan Daddy, ba ƙaramin daɗi ya ji ba don haka ya fara aikinsa cikin mutumci da mayar da hankali. Haka Kabiru ya ci gaba da aikin gaidinsa sai dai tun zuwansa yake waɗansu irin miyagun mafarkai masu ban tsoro, a ranar da ya fara cin karo da Mama Uwani ranar kwana ya yi kansa na tsananin yi masa ciwo da mafarkin manyan baƙaƙen shanu suna biye da shi za su halaka shi. Haka kawai ya ji ta su bata zo ɗaya ba don haka ko shiga sabgarta baya yi tun da dama ba fito wa harabar wurinsa take yi ba.
Ana gobe ɗaurin auren Kabiru da amaryarsa Dije su Raihan suka dira a garin su Kabiru da kwatance ta waya, duk sai kunya ta kama Kabiru da ya tuna irin katafaren gidan da su Mommy suke rayuwa a ciki ya duba nasu gidan, ya ga ko kwatan na Daddy bai kai ba. Haka su Inna wuro suka riƙa nannan da su Mommy don ɗaki guda suka basu gabaɗaya ita da su Inno. Shi kuma Daddy aka sauke shi a gidan Mahaifin Amarya wato yayan Baffajo. Raihan gabaɗaya ji ta yi kamar tana kewar Kabiru don kusan kullin tun tafiyarsa sai sun yi waya da shi wani lokacin idan Barista Huzaifa ya ji tana yawan ambatar sunan Fillon har haushi yake ji. A daren ranar da suka sauka bayan sun huta Kabiru da Raihan suka fito suna tafiya a cikin garin, don Raihan ta tilasta masa sai ya kaita gidansu amarya ta ganta. Amma a ɓangare ɗaya haka kawai ta riƙa jin ranta yana matuƙar ɓaci, ganin yanayinta ya sa Kabiru ya furta, "Lafiyarki kuwa fillo?" Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Ba komai Fillo, wai don Allah baka yi missing ɗina ba saboda Allah ace amini guda wai ko dai ka samu sabbin abokai ne Fillo?" Kabiru ya yi dariya zuciyarsa wasai don ko