Showing 120001 words to 123000 words out of 157890 words

Chapter 41 - ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

03 Nov 2025

130

Al'amin tare suka taho, tun a mota Summaya ta zame mayafinta tana watsawa Raihan wulaƙantaccen kallo. Sai da Malam ya biya ya yi musu siyayya irin wacce ake yi wa amare a daren amarcinsu sannan ya kai su gidansu da ke Kuntau. Kowacce ɓangarenta daban don haka kowacce sai da ya kai ta ɓarinta, kafin tafiyarsa sai da ya haɗa su ya yi musu nasiha mai ratsa zuciya sannan ya yi musu sallama ya fita daga gidan.



Littafin kuɗi ne 300 idan kina mgn ki min mgn 0706 206 2624


44


Raihan na zaune shiru akan gado a hankali ta zame mayafin kanta tana ƙare wa ɗakin kallo, lokaci ɗaya gidan Huzaifa ya faɗo mata da lokacin da take zaune ya dawo wurinta. Gabanta ne ya faɗi a hankali ta matsa ta jingina da fuskar gado, wayarta ta zaro ta kunna karatun Alƙur'ani kamar yadda Malam ya gaya mata, lumshe ido ta yi tana jin wata nutsuwa na shigarta. Hannuwa biyu ta haɗa ta yi tagumi tana tunanin sabuwar rayuwar da za ta fara, a hankali ta ji an turo ƙofa ƙamshin turarensa ya dokin hancinta. Numfashinta ne ya kusa ɗaukewa gabanta na ci gaba da faɗuwa, ɗago kanta ta yi karaf suka haɗa ido. Ɗauke kanta ta yi ta sunkuyar da kai gefe tare da amsa masa sallamar da ya yi, a gefen gadonta ya ajiye ledojin hannunta sannan ya harɗe hannuwansa a ƙirji ya ce, "Ki fito Falo ina jiranki." Jiki a sanyaye ta amsa masa daga haka ya fice daga ɗakin, yana fita ta miƙe ta gyara tsayuwar mayafinta sannan ta bi bayansa. A falo ta same shi zaune shi da Sumayya akan kujera, kujerar da take kallon tasu ta zaune kanta a ƙasa. Tun da ta shigo Sumayya take bin ta da harara, ganin ta zauna ya sa Sumayya ta sake kwantar da kanta a jikin Al'amin, ta gefen ido take kallon duk abin da yake faruwa don haka ta ji wani abu ya caki gefen zuciyarta. Cikin zuciyarta ta fara ambatar sunan Allah don jin sanyi a zuciyarta, tana cikin wannan yanayin ta riski muryarsa yana faɗin, "Dukkan godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, Alhamdullah muna sake nuna godiyar mu da Allah ya nuna mana wannan rana mai albarka. Dalilin da ya sa na tara ku a nan domin na sanar da ku dukkanku matana ne, babu wacce take zaman wata duk zamana kuke yi, kuma kowacce ɓarinta daban don haka bana buƙatar tashin hankali ko rashin girmama juna, ku haɗa kanku ku zauna lafiya saboda Allah ne ya haɗa mu don haka sai mu haɗu mu gina rayuwarmu bisa tubar addinin musulunci." Yana gama maganar Sumayya ta ɗago ta dubi Raihan sannan ta ja dogon tsaki ta ce, "Ya kamata ka ce dukkanmu matanka ne amma kowacce da matsayinta a zuciyarka, don ka sakan akwai bambamci mai tazara tsakakin matar na gani ina so da matar shige, tun da ko hausawa sun ce matar shige bata dara..." Kallon da Al'amin ya wurga wa Sumayya ne ya katse ragowar maganar bakinta, ganin haka ya sake ƙona mata rai ƙwalla ta ciko idonta cikin kuka ta ce, "Wallahi dama na san kana sonta kawai ka yi haka ne don ka tarwatsa farincikina, tun da haka ne ka je gata nan na bar mata kai." Tana gama maganar ta miƙe cikin kuka ta wuce ɗakinta. Dafe kai Al'amin ya yi rai a ɓace don ko kaɗan ba haka ya so daren amarcinsa da Sumayya ya kasance ba, ajiyar zuciya ya sauke ya dubi Raihan cikin jin haushi ya furta, "Shi kenan hankalinki ya kwanta!" Ɗago wa Raihan ta yi ta kalle shi nan take idonta ya ciko da ƙwalla, Al'amin ya ƙarasa gaban Raihan da ƙarfi ya fisgi hannunta ya wuce ɗakinta yana shiga ya zaunar da ita akan gado fuska a haɗe ya furta, "Ba dai ni kike so ba? To ga ni." Hawayen da Raihan take dannewa ne ya suɓuce mata, ta fara ƙwalla haɗe da shassheƙar kuka. Kaiwa da kawo wa ya fara yi cikin takaici ya kalleta sannan ya ce, "Me kike buƙata yanzu." Shiru Raihan ta yi ba tare da ta furta komai ba sai kuka da take rairawa gwanin ban tausayi, a ɗan tsawace ya furta: "Ba magana nake yi miki ba?" A zabure Raihan ta ce, "Ba na buƙatar komai." Da sauri Al'amin ya nufi ƙofa yana faɗin, "Ban da shiga haƙƙi haka kawai a haɗa ni da mata biyu ina ji ina gani ƙanƙanin yaro da ni." Waɗannan kalamai ba ƙaramin taɓa zuciyar Raihan suka yi ba, wani irin ɗaci ta ji a zuciyarta musamman da ta tuna wurin wata zai tafi, kifa kanta ta yi akan gado ta ci gaba da raira kuka mai ban tausayi.

Al'amin na shiga ɗakin Sumayya ya same ta kwance akan fado tana gursheƙen kuka, ta baya ya ɗagota ya zauna akan gadon yana jinginata da jikinsa. Ajiyar zuciya take sauke wa sai kuma ta fara mutsu-mutsu tana son ƙwace jikinta, riƙe ta ya yi gam a jikinsa ya kwantar da kansa jikin wuyanta yana cewa, "Kina son Allah ya ƙona ni ne Sumayya?" Shiru ta yi bata tanka masa ba ya ci gaba da cewa, "Ke da ita duka matana ne don haka babu wacce zan fifita saboda sai Allah ya hukunta ni da yin haka..." Wani abu ne ya soke ta a zuciya ya fisge hannunta ta furta, "Dama na jima zuciyata na gaya min kana ƙaunar yarinyar nan idan ba haka ba babu yadda za a yi ka fara wulaƙanta ni a gabanta." Janyota jikinsa ya sake yi yana murmushi don ya fahimci zallar kishi ne ya lulluɓe idon Sumayya, wannan karon bata yi yunƙurin ƙwace wa ba. A daidai kunnenta ya fara lallashinta da cewar, "My Summee kin san dai ina ƙaunarki don Allah kar kishi ya hana ki yi min adalci, na gaya miki ke kaɗai ce a birnin zuciyata ta yaya wata za ta zo ta samu gurbi a wurinki? Ko kina shakku akan soyayyar da nake yi miki?Yarinyar nan na gaya miki Daddy ne ya tilasta ni aurenta amma babu ko ɗishin ƙaunarta a zuciyata." Al'amin ya jima yana lallashin Sumayya sai da ƙyar ta sauko sannan suka gabatar da sallar nafila, da kansa ya riƙa ciyar da Sumayya sai da suka ci suka ƙat sannan ya riƙe hannunta suka fita ya riƙa nuna mata sauran ɗakunan, tsarin gidan ba ƙaramin birgeta ya yi ba takaicinta ɗaya da ta tuna ba ita kaɗai ba ce a wurin Al'amin. Amma da ta tuna irin kalaman da yake yi mata sai ta ji komai ya ɓace daga ranta, ta ci alwashin sai Raihan ta bar gidan da ƙafarta don ko da wuta take yawo sai ta bar mata Al'amin ɗin ta. Raihan na ɗaki sai da ta ci kukanta ta godewa Allah sannan ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara gabatar da sallah tana kai wa Allah kukanta, ta jima akan dadduma don har sai da bacci ya fara awon gaba da ita sannan ta miƙe ta sauya kayan bacci ta hau kan gado. Sai dai a madadin baccin ya ɗauke ta sai tunani ya hana ta, babban abin da ya tsaya mata a rai da take ayyana irin soyayyar da Al'amin yake yi wa Sumayya, bata yi aune ba sai ji ta yi hawaye na zuba. Gefen hannunta ta sa ta goge ta janyo blanket ta rufa sakamakon zazzaɓin da ta fara ji a jikinta, ledar da Al'amin ya ajiye mata ta ƙurawa ido tana ayyana wai yau daren amarcinta ne amma take kwance haka miji yana wurin wata. Mutuwar Salim ce ta dawo mata sabuwa take tuna irin kulawar da yake bata da alƙawarurrukan da ya yi mata har zuwa ranar Dinner su, da irin abubuwan da ya shiga tsakaninta da shi a ranar. Kuka take sosai kamar ranta zai fita, sai da dare ya tsala sannan bacci ya yi awon gaba da ita.

Washegari

Al'amin shi ya taimakawa Sumayya ta gyara kanta ban da raki babu abin da take yi, duk ta cika ɗakin da ihu don ma Al'amin yana nuna mata ta yi shiru kar maƙota su ji abin da yake faruwa, ita kuwa Sumayya da biyu take ihun don Raihan ta ji ta tabbatar da wani abu ya faru a tsakaninsu. Ya rakata toilet suka gyara jikinsu sannan ya ɗauro alwala yana fito wa ya zura jallabiyarsa ya ɗauko dadduba ya fita, ɗakin Raihan ya wuce ya tura ƙofa har a lokacin bacci take yi. Amma kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci baccin da take yi ba na daɗi ba ne, a takure ya ganta wuri ɗaya ya sa hannu ya fara buga ƙafarta. Buɗe ido ta yi yana ganin haka ya furta, "Ki tashi ki yi sallah." Jiki ba ƙwari Raihan ta miƙe ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah. Tana zaune tana lazumi bacci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta sani ba, don bacci ne sosai akanta tun da bata samu yin bacci da wuri ba. Cikin baccinta ta ji ana kiran sunanta, tashi ta yi tana murtsika ido sai a lokacin ta fahimci a wurin da take kwance. Ganinsa ta yi cikin ƙananan kaya ba ƙaramin kyau ya yi mata ba har bata san lokacin da ta shagala da kallonsa ba, iska ta ji ya hura mata a fuska sannan ya ce, "Ki zo ki taimakawa Sumayya ta gyara jikinta daga nan sai ki girka mana breakfast, saboda gari ya waye almost nine thirty yanzu." Raihan ji ta yi kamar an kwaɗa mata guduma akanta don ta fahimci abin da Al'amin yake nufi, haɗiyar yawu mai ɗaci ta yi ta miƙe jiki ba ƙwari ta furta: "Ok bari na yi wanka na zo." Guntun tsaki Al'amin ya yi ya ce, "Na saka ki abu yanzu jira zan yi sa kin yi wanka, jiranki za ta yi tana fama da kanta har sai kin shirya." Ajiye daddumar hannunta ta yi ta wuce sum sum sum ba tare da ta iya furta masa komai ba saboda yadda zuciyarta take zafi. Tana tafe gabanta na faɗuwa har ta tura ƙofar ɗakin sumayya ta shiga, daga falo ta riƙa sallama sai da ta yi kusan sau uku sannan ta ji Sumayya ta amsa ta kuma ce mata ta shiga. Raihan na shiga ƙirjinta ya buga ganin yadda Sumayya ta yi ɗaiɗai daga ita sai ɗaurin ƙirji, ga kayanan kayanta na ciki duk a warwatse a ƙasa. Daga bakin ƙofa Raihan ta tsaya ta ce, "Ina kwana?" Sumayya ta taɓe baki da kamar ba za ta amsa ba sai kuma ta amsa sannan ta ɗora da cewa, "Na tura Hayati don ya kira ki, ki zo ki taya ni gyara jikina saboda da asuba shi ya gyara ni so kuma na ga ya gaji da yawa. Amma na ga ke bazawara ce kin san komai wannan ba baƙonki ba ne, sai kuma na ga kin yi min ƙerere aka." Zuciyar Raihan ce ta fara tafasa wani irin abu ya tokare maƙoshinta, bata furta mata komai ba ta ƙarasa bakin gadon ta ce, "Ai da asubar ma da kin turo shi sai na zo na gyara ki, ai duk yi wa kaine." Sumayya ta fahimci baƙar magana Raihan ta caka mata don haka ta yi murmushi tana faɗin, "Na so tura shi amma yadda ya liƙe min ya sa dole na haƙura saboda kin san irin wannan daren sai ana yi wa Angwaye uzuri." Maganar Sumayya ba ƙaramin ɓata ran Raihan ta yi ba, takaici da baƙin ciki suka lulluɓe zuciyarta. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla da ƙyar ta samu damar mayar da su ba tare da Sumayya ta gani ba. Amma yanayinta kaɗai zai nuna alamar bata ji daɗin maganar ba, miƙa mata hannu Sumayya ta yi ta ce: "Riƙe ni mu shiga toilet ki sirka min ruwa." Babu yanda ta iya don ta ji takun Al'amin ya nufo ɗakin, Raihan na ruƙo sumayya ta zuba wata uwar ƙara tana yarfe hannu. Da sauri Al'amin ya ƙaraso yana cewa, "Baby lafiya? Jikin ne?" Girgiza kai ta fara yi tana cije baki, tsaye ya yi a gabanta ya dubi Raihan yana faɗin: "Kamata ya yi ki yi mata a hankali bata da lafiya fa, bakya ganin yanayinta.." Da ido Raihan ta bishi don ranta ba ƙaramun ɓaci ya yi ba, bayan cin kashi da cin fuskar da aka yi mata amma ya zo ƙoƙarin rufeta da faɗa yake akan abin da bata da hurumi da shi. Sumayya ce ta riƙo hannunsa tana cewa, "Hubby ka ɗaga ni ba zan iya tashi ba." Jiki na rawa Al'amin ya ƙarasa bakin gadon yana shirin ɗaukan Sumayya da gayya ta saki zanin jikinta tana faɗin, "Hubby ba haka ba wallahi ciwo nake ji kamar yadda ka ɗauke ni da Asuba." Jin zuciyar Raihan na neman tarwatse wa ya sa ta fice daga ɗakin idonta na zubda hawaye, tana shiga ɗakinta ta faɗa kan gado haɗe da fashewa da matsanancin kuka. A baya ta ɗauka idan ta samu Al'amin ta gama maraicin soyayyarsa, tana yi masa soyayyar da take jin ba za ta iya sharing ɗinsa da wata ba amma sai ga shi akan idonta yana rungume da wata, ta ɗauka zama da shi a inuwa ɗaya shi ne gushewar baƙincikinta amma alamu sun nuna sabon babi ta buɗe na ƙunci da matsin rayuwa. Kuka take sosai kamar ranta zai fita, sai da ta yi mai isarta ta faɗa toilet ta yi wanka bayan ta shirya ta fita kitchen don girka musu abinci kamar yadda Al'amin ya ce.

Tana shiga kitchen ɗinta babu abin da babu don haka kai tsaye ruwan tea ta fara dafa musu ta zuba a flask, sannan ta fere dankali ta soya musu sai kuma ta soya ƙwai daban don ta so soya kayan miya ko miyar jajjage ta yi musu, bayan ta haɗa komai tunani ta fara yi a wurin da za ta ajiye musu abinci. Nata ta haɗa daban sannan ta haɗa musu na su a tire ta saka komai ta ɗauka ta nufi ɗakin Sumayya. Da sallama ta shiga a lokacin tuni Sumayya ta shirya cikin ƙananan kaya riga da wando, kanta a ƙasa ta shiga da shi ta jiye musu sannan ta koma ta ɗauki nata ta wuce Main falonsu ta zauna tana karyawa. Ƙarar turo ƙafa ta ji tana kai idonta ta ga Al'amin ɗauke da tiren ya fito da shi ya kawo falon da take zaune, da ido ta bishi har ya koma ya riƙo hannun Sumayya suka dawo cikin falon. Tana zaune ta ci gaba da cin abincinta kamar ma bata gansu ba haka ta ɗauke kanta sai dai gabaɗaya ta daina jin daɗin abincin, turawa kawai take yi don kar su fahimci halin da take ciki. Akan idonta suka riƙa ciyar da juna cikin shauƙin so da ƙauna, suna gamawa Al'amin ya kwashe kayan ya kai su kitchen. Dawo wa ya yi ya zauna Sumayya ta kwantar da kanta a jikinsa cikin shagwaɓa ta furta, "Darling don Allah ka roƙi alfarmar Aunty Raihan ta taimaka t gyara mana ɗaki wallahi zan ji kunya idan baƙin gidanmu suka zo, ka ga a gabanka Mami ta kira ni wai baƙi za su zo ganin ɗaki." Jim Al'amin ya yi yana ganin kamar saka Raihan gyran ɗakin baccinsu bai dace ba, kamar ta san abin da yake nazari ta tashi zaune tana marairaice murya ta ce, "Wallahi ko yatsana da ƙyar nake iya ɗagawa, ka ga ita ma lokacin da za ka koma ɗakinta duk abin da ya dace na gida ai ni zan yi. Amma ka yi haƙuri idan baka so haka ba." Ta ƙarasa maganar tana kwanciya a jikin kujera. Miƙe wa ya yi cike da jin daɗi don gani yake kamar Sumayya ta sauko don su haɗa kansu da Raihan ne ya nufi ɗakin Raihan yana faɗin, "Menene amfanin zaman tare My baby? Bari na yi mata magana." Tura ƙofar ɗakin ya yi a lokacij Raihan na waya da Inno don ta yi kewarsu, tsaye ya yi yana kallonta babu laifi tana da kyau daidai gwargwado gata da gashi irin na fulani har baya. Yana son mace mai tsayin gashi duk da Raihan ba fara ba ce kuma bata da wani jiki amma bata da muni a fuska, tana gama waya ta juyo tana kallonsa. Ɗauke kai ya yi kamar bai ganta ba sannan ya ce, "Am dama cewa na yi ki ɗan gyarawa Sumayya ɗaki ba za ta iya ba." Ɓata fuska ta yi har bata san lokacin da ra furta, "Gyaran ɗaki?" Gyaɗa mata kai ya yi ya ce, "Eh saboda baƙi za su zo ita kuma kin ga yadda jikin nata yake." Raihan bata tanka masa ba zuciyarta na suya ta wuce ta nufi ɗakin Sumayya don ta manta ko ɗankwalinta bata saka balle hijabi. Daga iya sai doguwar rigar leshi, kayan ba ƙaramin kyau suka yi mata ba. Sumayya na ganin Raihan sai da gabanta ya faɗi, saboda koda ta san Raihan bata fita kyau ba amma babu wanda zai kalli Raihan bai ce ta yi masa kyau ba. Kai tsaye ɗakin ta shiga ta fara kaɗe gadon cikin takaici, kayan Raihan duk a warwatse har da ƙananan kayanta na ciki. Sai da ta kwashe su da cusa mata a drower sannan ta gyara gadon ta mayar da komai yadda yake ta wuce ɗakinta. Hankalin Sumayya bai kwanta ba sai da ta ga Raihan ta shiga ɗaki, amma abin da ya ɓata ranta yadda ta lura da irin satar kallon da Al'amin yake yi wa kan Raihan. Idan ka kalli Sumayya tashin farko za ka fahimci ta fi Raihan kyau sai dai Raihan ta nuna mata dirin jiki da tsayin gashi domin Sumayya fara ce kyakkyawa, ita ma doguwa ce amma tafi faɗi daga sama. Shigar Raihan ɗaki babu wuya suka ji bugun gida, ta window Raihan take kallon hanya Al'amin na buɗe wa ta hango su Mama Hafsa da sauran baƙin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login