Showing 135001 words to 138000 words out of 139076 words

Chapter 46 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

136

nemi maganin jinnu ta wannan hanyar ce kawai aljanun za su barsa,ko kuma in sun nuna masa abin sai ya ?aryata jinnu na jin haushin haka daga wannan ne sai su rage faWa musu.


Na ja ajiyar zuciya na ce  to ai kuwa za mu yi wa Ammy magana ita ma ta nemi magani

Yayi murmushi ya ce  ai ba ta so ta ce abar ta da kayanta, Basheer dai shi yana can ana yi masa magani.In ya samu lafiya zan saka ku makarantar islamiyya ku biyun don fitar da duhun jahilci 

Na soma kukan shagwaSa na ce  ai a addininmu cewa aka yi in mace ba ta da ilimi kar miji ya kusance ta

Fuska ya haWe wannan yasa da sauri na shiga hankalina,?ofar aka bubuga ya je ya buWe Ammy ta shigo ita da Shuraim nan fa aka zauna aka soma yin hira .Likita ya shigo ya bani takardar sallama,Ammy ta ce  ku zo ku duba Ma'idar 

Yaya Khaleed ya ce  don Allah Ammy mu je  harara ta yi masa wannan yasa dole muka shiga Wakin,baiwar Allah tana rakuSe tana shan ayaba duk ta rame.


Shuraim kuwa ido ya ?ura mata yana kallo har sai da kowa ya lura,da muka fito ya kasa ha?uri ya ce  abokina ya kuke da waccan Win? Da na ga ko ranar da aka yi musu shari'a kana ta kula su


 To wannan Win bazawara ce,kuma ma dai kusan za ku kai shekaru guda cewar Yaya Khaleed.
Ammy ta ce  to sai me? Ita bazawara ba mutum ba ce? Ka ga in kana sonta je ka karSo lambarta ni nan zan tsaya ma har komai ya tafi daidai

Shuraim ya sosa ?eya yana murmushi kafin ya ja hannun Khaleed su koma ciki,ba su wani jima ba suka fito suna dariya .Sai bayan mun shiga mota ne Yaya Khaleed ke bamu labarin yadda aka yi kasa fa magana yayi sai ni ne na karSo bayan na yi wa mahaifiyarta bayani

 To tonan min asiri

 To ai gaskiya ce,wai ya zancen mayyar Shareef? sai kuma suka tuntsire da dariya kafin Shuraim ya basa amsa da  tuni an kira danginta ai suna can za ku sallace ta,ai maganin mai ruwan ido da Wan hassada kenan .Kana ganin Oga tuni ya bani umarnin na je na tone abubuwan da ya binne 


 Ai Shareef gadon mugunta ce yayi,Allah dai ya kyauta 


Haka suka ta yin hirarsu,ina saurarensu na yi lamo a jikin Ammy na yi tunanin gida za mu je sai na ga ya Wauki hanyar Say.Har sai da na yi bacci na farka ba a kai ba,haka na zauna na yi ta ?arewa garin kallo har muka isa masarauta.



Da ihun Basheer muka ci karo,da sauri na shige gaba jiki na min rawa.Kwance na tarar da shi dogarai duk sun danne shi yayin da malami sai karatu yake zubawa,aljanin kuwa sai ?ara jadadda maganarsa yake ba zai fita ba.Sai da ya galabaita sosai sannan ya yarda ya fice bayan ya karSi kalmar shahada,tuni shi kuwa BASHEER ya Singire da bacci.


?auke shi suka yi suka mayar da shi Waki,daga nan wurin mai martaba muka je yana zaune yana sauraren sautin ?ira'a a cikin wani MP3 .Duk muka gaishe shi da jiki ya amsa cikin sakin fuska, Khaleed ya je ya rungume mahaifinsa yana murmushi kafin kuma su yi mana sallama shi da Shuraim su koma can Yamai



&Bayan sati biyu da zuwan Ammy aka Waura aurenta da mai martaba ,a kuma wannan rana ce yayi murabus daga kujerar mulki juyin duniya aka da Khaleed amma ya ?i hawa a dole aka baiwa Uwais ri?on ?warya na karagal mulki.


A can Zinder aka yi Waurin aure amma biki kuma a nan aka yi,WaiWaikun danginmu sun zo ciki kuwa har da Mama wacce sai a yau ne na ji ashe aurenta ya mutu.


Ina zaune kusa da ita take ce min  Alhaji fa na can tension ta buge shi ba hannu ba ?afa tun ranar da ya so yi miki fyaWe,ban san mene ne ya gani ba amma sabatu iri-iri haka yake yin su har da cewa ya tsane ni na je ya sake ni dama da ZAWARCI na fi dacewa rabon a yi ne yasa shi aurena 


A yayin da Mama ke maganar fuskarta sai ta canza,na yi ?asa da murya na ce  Mama in sha Allah ai za ki yi aure har ma ki hai... sallamar Uwais ce ta katse min ?arshen zancen,da sauri Mama ta mi?e za ta bar wurin shi kuwa sai wani kallo yake yi mata .


 Sarauniya SEERAT zo kin yi ba?i ya furta.
Na ce  mai girma mai martaba shine kuma da kanka za ka zo kira na? na faWa tare da fice wa na barsa da Mama ban sn me suka tattauna ba.



 Gimbiya Safeena na ce don Allah a bani damar nan na gwada sa'a ta

Safeenatu ta haWe rai ta ce  na faWa ma ban gama idda ba,kuma a ko wane irin lokaci mijina zai iya mayar da ni tun da saki Waya ne

Ya murmusa ya ce  na sani amma ba na fatan hakan ya kasance domin ke Win matar manya ce ba ta tsofi ba wani kallo ta yi masa kafin ta Wauke kai,duk yadda ya so ta yi masa magana mai daWi amma hakan bai samu ba dole ya shafa mata lafiya.




Su Yaya Khaleed ne da Shuraim da Shareef,a mutumce duk muka gaisa na lura har yanzu Shareef na jin kunyata.
Kayan marmarin da aka zube a gabansu na kalla yawuna suka tsinke,na dubi Yaya Khaleed cikin ido tuni kuwa ya fahimci me nake so ya Wauko ya mi?a min na karSa na soma sha.



 Abokina ko mun yi ajiya ne? Shareef ya faWa yana dariya.

Shuraim ya ce  ai kuwa dai little Princess za a haifa mana ka ga sai na yi ta biyu da ita

Shareef yayi masa dukan wasa ya ce  Allah ya sawwa?a na bayar da ?ata ga tsoho can ka iya da Bazawararka

Khaleed ya ce  cewa ake Baz hahaha! ?

 Ko ma dai me za ku ce sai na aure ta,yo ai dama an ce sun fi sanin makashin aure

Gyaran murya na yi kafin na ce  ni dai a bari har na gusa 

Shareef ya ce  ni ma ki samo min ko baz Win ce na angonce don wallahi ba zan zauna a gwabro ba

Shuraim ya ?yal?yace da dariya ya ce  a'a bazawari zaka ce ko ka manta cikin zawarci kake?

Duk muka dara har shi Shareef Win kafin Yaya Khaleed ya ce  wato har maza ma ana cewa suna zawarci?

 I sosai mana ! Ka ga kamar abokina sakin wawuya ce  haka suka dinga tsokanar junansu gwanin sha'awa,ina zaune gefe ina kallonsu da lokacin cin abinci yayi na je na bada umarni bayi suka zo suka kawo.




#SAKEENATU


Tun daga ranar da FA'IZA ta mutu har izuwa yau ba ta taSa kwanciya bacci ba sai ta yi mafarkinta tana ro?on ta don Allah ta kula da ?annenta .Wannan yasa sam ba ta yi ?asa da gwiwa wurin tallafa musu ba,masu karatun har makarantarsu ta je ta bayar da lambar da za a dinga kiranta in ana bu?atar wani abu.

Sauran kuma makarantar koyon Winki ta saka su domin su koya ta yadda za su tsaya da ?afarsu ,don yau da gobe sai Allah duk da ba ta fatan ranar da za ta gajiya .


Bayan Shari'a Ma'idah ta kwanta jinya,ita ta kula da ita yayin da dangin ubanta suka biya kuWin komai.Daga lokacin da Shuraim ya nuna yana son ta kuwa sai dangin Agali suka fara bar masa nauyin kula da ita duk don su ga in zai iya,shi kuwa ya nuna musu cikkaken namiji ne sai Wawainiya yake da ita.

Ba wata hira suke yi sosai ba,ko a waya in ya kira ta iya gaisuwa da kuma tambayar jikinta kawai yake yi.Wani sa'in ne yake haWawa da nasiha,a ?arshe kuma sai ta fashe masa da kuka har yayi mata sunan wasa da mai saurin kuka.


Tun da manyan suka shiga lamarin aka soma yi wa Ma'idah gyaran jiki,sosai ta yi kyau sai dai akwai rama saboda tunanin tsohon mijinta da kuma na mahaifinta wanda a halin yanzu ba su san inda igiyar hauka ta kai shi ba.

Ana gobe walimar bikin Ma'idah Abbas ya zo gidansu Sakeenatu,har cikin falo aka yi masa iso.Shiru ta yi tana sauraren jawabinsa, Keenat wallahi tun bayan rabuwarmu babu sallah ?waya Waya da na taSa yi wacce ban ro?i Allah ya maido min ke cikin rayuwata ba,ina sonki sosai ke shaida ce .Ki Wauka duk abubuwan da suka faru matsayin ?addara ne,ki bani dama don Allah na ?ara zama mijinki


 To sai na yi shawara, sannan ni ma ai ka san ina sonka sai dai a halin yanzu hankalina ba kwance yake ba ga bikin Ma'idah ga kuma abubuwan da suka yi ta faruwa a rayuwata


 Haka ne , Allah shige mana gaba
 Amen
Sai da suka taSa hira kafin su yi sallama.




&YAMAI


Wani irin katafaren gida na gani na faWa mai Martaba ya saya wa Yaya Khaleed,sai da aka ?ara sabunta shi sannan aka zuba mana sabbin kaya.WaWan can tsofin kuma aka sayar aka saya min mota da su,motar da Yaya Khaleed yayi tsalle ya dire kan ba zai bari na hau ba sai dai a nema min direba.


Kamar wata sabuwar amarya sai da Ammy da wasu bayi suka yi min rakiya zuwa sabon gidana wanda babu ce kawai babu.Sosai na yi murna har da taka rawa,a ranar ko agwagwa albarka wurin wasa da ruwa.Haka na dinga shiga bahon wanka ina camSal-camSal a ciki har sai da Yaya Khaleed ya soma yi min faWa .



An zuba min masu yi min hidima har mace huWu,ga mai gadi da direba amma tsabar tsiyar gumi haka yake saka ni shiga kitchen wai ya fi son girkina .

Yanzu ma girkin nake suna taya ni har muka kammala,wanka na je na tsala na caSa kwalliya.Bayan sallar magarib ya shigo yayi wanka ya shirya cikin wasu blue suit har da shace kai tare da soma Sarin turare.

Kasa ha?uri na yi na ce  wai ina za ka je?

 Wurin partyn Shuraim mana  ya bani amsa kai tsaye.

 To amma ai tun shekaran jiya aka yi bikin ko?

 Eh! Jiya aka kawo amarya,yau kuma taron taya murna da police suka shirya

 Amma mu da aka yi bikinmu ba a yi wannan ba

 Eh ni ne nan na hana saboda ina da kishi ba zan bari a kalle min mata ba

 To na ji! Bari na kawo ma abinci

 Ina sauri in na je can zan ci ya faWa yana Waura agogo,da sauri na je na tsaya a gabansa na ce  wallahi babu inda za ka je

Cak ya Wauke ni ya Wora tsakiyar gado,yayi min kiss a goshi ya ce  sai na dawo yana gama faWa ya fice.Na bi shi da kallo ina jin wasu hawaye na zubo min kafin na mi?e da sauri na biyo bayansa.


A gaban idona ya shiga mota na dubi tafin hannuna ina cewa ina ma ace har yanzu ina da power da tabbas sai na tsayar da motar nan na hana ta tashi,haka na koma ciki ina hawaye.Duk kwalliyar da na yi da wahalar girki sun tashi a banza,?awata Maryam na kira don ita ce na ware matsayin ?awar shawara,kamar wata uwata tana Waga wa na fashe mata da kuka wiwi kafin na koro mata bayani ta shiga yin wani murmushi mai sauti kafin ta ce  SEERAT abin da ba ki sani duk yadda namiji ya kai ga son ki to akwai ranar da sai ya ba?anta miki rai,ke ce kike ganin wannan a laifi shi kuwa a wurinsa sam ba wata matsala ba ce don bai tsaya cin abincin da shine ya fitar da kuWinsa aka dafa.Sannan bari na faWa miki wani sirri,ba kowanne lokaci ba ne mace za ta nuna sarautarta ba .Misali kamar yau da take ranar walimar babban abokinsa ta ya ke ma kike tunanin za ki hana shi fita kuma ya biye miki? Inda dai kamar fita ce zuwa majalisa ko kuma wani yawo da suka shirya su da abokansa waWannan duk za ki iya yin gadara a matsayinki na ?a mace ki hana shi fitar


 To na ji tun da kin shigar masa,yanzu yana can yana kallon ?an mata fa na faWa wasu ruwan hawaye na sake zubo min.
Maryam ta tuntsire da dariya ta ce  ke fa duk tsiyar mace ba za ta iya hana mijinta kallon Mata ba,Allah na tuba yo ko matar indiya namiji ya aura wallahi in ya fita sai ya kalli wasun.Kawai dai ki yi addu'a in ma kishiyar ce Allah sa ta gari ce ba irin namu ba da suka asirce mana mazaje

Na ce  wai kishiyarki?
 A'a fa matarsa dai ko ba ki da labarin na bar gidan? 

 Innalillahi saboda me? Inda kin yi zamanki ko ba komai kana Wakinka ya fi gaban iyaye

 Wallahi gwara gidan iyayena da gidan habibi, ke tsabar Wiyan iskanci fa shi da matarsa suka dinga yi min abubuwa iri-iri wai fa sai abin da ta ce ake zartar wa a gidan har da hana ni zuwa makaranta


Na ce  Maryam anya kuwa ba aljanin kanki ba ne ke juya miki kwanya? Ya zancen maganin kina amfani da shi?

 Na bari,ke ni fa ban san daWin aure ba hakan ma ya fiye min kwanciyar hankali Wan cikin da na samu ma Sarewa yayi


 Duk sharrin jinnu ne ki nemi magani,in ba haka ba zai dinga zubar miki da cikin kenan ko wani auren kika yi don da alamu ke naki aljanin mai barin a yi aure ne haihuwa ce bai so


 SEERAT ?ar baiwa! Amma kin ji daWinki fa komai kin sani na Soyayyar duniya ban kai ga bata amsa ba kuWina suka ida ,na ajiye wayar tare da shiga toilet na wanke fuskata.




& A wurin diner kuwa sosai aka ?awata komai ,dangin amarya da na ango da kuma abokai sai hidima ake yi.Komai yana tafiya kan tsari,Shareef ya koma can gefe yana kallon ?an mata amma sam bai jin irin wannan yanayin nan da yake shiga in ya ga mace da wannan tsoron ya zauna wuri guda har aka gama aka mayar da amayar gidanta wanda aka cika tan?am da dukiya .


Khaleed da Shareef har tsakiyar falo suka yi wa Shuraim rakiya kafin kowa ya kama gabansa.Da sallama ya shiga Wakin, Ma'idah bazawara ce amma tamkar wata budurwa haka take wani no?ewa.Dakyar ta yarda suka yi wanka a tare,yau ma sai da ya sake jan su sallah suka yi ?an ciye-ciye kafin ya ja su shimfiWa.Da farko ta soma jin kunya amma da ta Wauki caji dolenta ta soma mayar masa da martani,a nitse suka yi komai cikin kwanciyar hankali .Da asubah haka suka shiga wanka tare Shuraim sai wani manne mata yake ita kuwa Ma'idah duk wata sauran damuwarta duk ta kau,bayan sun yi sallah ya soma koya mata karatu kafin kuma ta shiga kitchen shi kuma ya shige Waki yana shat.





&A Sangaren Basheer kuwa sai da ya sha ayoyin Alkur'ani yayi wanka da su kamar ba gobe sannan hankalinsa ya dawo jikinsa.Haka zai zauna yayi ta tunanin abubuwa wasu yana sane wasu kuma jinsu yake kamar a mafarki don ba cikin kansa ya aikata su ba.Kusan kullum sai sun yi waya da Hawa'u wacce ta mutu cikin sonsa duk da a yanzu shi a Sangaren Baseer Win gani yake ta yi masa girma tun da ta girme masa amma a haka yake biye mata suna amintar mai cakuWe da soyayya.Burin zama sarki kuwa raWam yake a zuciyarsa,kuma haka yake sake jadadda wa Hawa'u shi kusan kullum.




&&&


 Zo mu zauna zo mu saSa waWannan abubuwan biyu na koye su ne tun ranar da Maryam ta yi min nasiha,wannan yasa ko a ranar da Yaya Khaleed ya dawo ban nuna masa Sacin rai ba sai ma kulawa ta musamman da na basa wacce a washegarin ranar ne kuma ya kai ni makaranta domin ci gaban karatuna wanda da farko ya so katse igiyar numfashinsa.Farin ciki da nutsuwa sune suka wanzu a familyna,hankalinmu kusan za mu ce duk a kwance yake ,?ar tangarWa da muke ciki bai wuce yadda Mama ta shafa kwallin rashin mutumci tare da hawan kujerar ZAWARCI ta ?i sauka.Juyin duniya mun haWa baki wurin rarrashinta akan ta amince da auren sarki Uwais amma ta ?i,a cewar ta ba ta da rabo a zaman aure miji guda ne ta aura Wan mutumci wato mahaifinmu bayan shi ta yi aure biyu waWanda gwara babu su,don haka babu wanda zai ci gaba da yi mata ?irgen gidajen da ta yi aure.


Wannan ?o?on barar na Uwais ya kwashe tsawon watanni shidda kenan amma ta ?i karSarsa,sai yau kamar daga sama ta ce ta amince farin cikin da na shiga ya haifar min da na?udar wuri tun kafin lokacin haihuwar yayi .Ban wani ci wuya na haifo ?ata ?ar mitsitsiya da ita,don tsabar ?arantarta sai da aka saka ta cikin kwalba.
Ammy tuni ta kawo girgiza asibitin ita da masu yi mata hidima,wata kula ta musamman ta soma bani ko motsi na yi sai ta tambaye ni me nake so .Shi kuwa Khaleed ya kasa zama kusan kowanne lokaci yana asibitin haka ba kunya zai wani manne min sai in Ammy ta yi masa faWa ,sai da muka yi sati guda currr kafin a sallamo me mu.

Kaka ita ce ?ar tsaron bi?i,ita da Samira ta zo wacce sam auren da ta yi a idona ban ga ya karSe ta ba.A ranar da ?awata Maryam ta zo kowa sai da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login