Showing 120001 words to 123000 words out of 139076 words

Chapter 41 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

118

hana ki yin darasin? Ina ce ma jiya kin yi bacci sosai

 Eh rabi da rabi ba,ka manta ka hana mu sa?at motsi kaWan ka manne min,ni fa har sai da ka bani tsoro na yi tunanin ko Bafulatanata ce ta hura ma wutar sha'awa 


 Wace Bafulatana ? 

Shiru na yi na Wan wani lokaci kafin na ce  sai da safe Yayana 

 A'a sai dai in na tashe ki domin kula da ni

 A'a wallahi ban so

 Ni ina so

 To ai yanzu mun yi

 In an jima ba yanzu ba ce

 Don Allah ka bari Yaya,kar ka tashe ni bai ?ara cewa komai ba har na yi bacci,nan Win ma mafarkin masarautar na soma.Fitinar Yaya Khaleed ce ta katse min baccin,sam ban yi tsammanin cewa zai tashe ni ba duk yadda na so bijire masa amma haka nane mini kamar mayen ?arfe.Ina kuka ya sukuce ni zuwa toilet,ina shirin komawa bacci na ji ana kiran sallah dole na tsaya sai da na gabatar sannan na kwanta.


Cikin bacci nake jin muryarsa wai na tashi na yi shirin makaranta, Ni fa ba zan je ba

 Tashi za ki yi Malama  ya faWa tare da zaunar da ni zaune,wani haushi ne ya rufe ni na soma kuka wiwi sam gani nake Yaya Khaleed bai tausayina ai kuwa sai ya tabbatar da zargina ya soma yi min faWan da yasa dole na je na yi wanka na zo na shirya.

Muna fita waje sai na ga yau Shareef ne ya zo Waukar mu,shi ya buWe min gidan baya kafin ya shiga gaba.Ta madubi muka haWa ido Shareef,ban gaishe shi ba haka shi ma bai ce min komai ba sai labari da ya soma yi .

 Zuwa gobe zan tafi Say ka fara shirin haWa mini gift Win tarben amarya Shareef ya faWa yana murmushi.

Khaleed ya ce  ma sha Allah ka ce ?ar fillo za ka auro? Amma dama ka san mutane a can ?

 Eh Daddyna a can ne asalinsu nan aiki ne ya kawo shi

 Abokina kana iya zama da Bafulatana ?auye kuwa?

 Wa ya faWa ma ?auye ce? Duk Nijar akwai inda ya fi can kyau da tsaruwa? Ka kuwa san irin yadda Allah ya azurta su da dukiya da kuma kayan more rayuwa

 A'a in auren naka ya tashi za mu je ai 

 Ai kuwa nan kusa ne yayi furicin yana kallon madubi muka haWa ido ,na zabga masa uwar harara kafin na kawar da kai.A daidai ?ofar makarantarmu yayi parking,na ?i fita sai da Yaya Khaleed ya buWe min ?ofar,duk da ban ganin Shareef amma na tabbata idonsa na kanmu hakan yasa na ri?e hannunsa na soma zuba masa rigima tare da ?orafin ?ila ma yau in na je baccin zan ta yi.Mun kusa minti goma kafin ya bani kuWi na karSa shi kuma ya shige mota,yau dai da Wan dama ban yi bacci a aji ba sai dai jefi-jefi ina yin tunani akan labarin Yaya Khaleed a yanzu na sani ba Ammy ce mahaifiyarsa ba amma ban san ta yaya aka yi ya zo nan Win ba.Yau ma muna sauka daga makaranta na shiga taxi zuwa gida,ko da na zo ?ofar gidan na tarar duk an shimfiWa tabarmi da alamu zaman makoki ake yi.Ina shiga ciki na fiddo key don buWe ?ofar kewayena sai ga Shafa'atu ta fito tana cewa  dama tun Wazu ke nake jira

 Ga ni lafiya? na faWa don yanzu ina kiyaye saka kaina a matsala.
 Hajiya ta rasu mai gidan nan,tashi za mu yi ?arshen satin nan za mu koma gida kafin nan za a yi wa Isma'il karatu dangane da abin da ya faru

Na taSe baki na ce  yanzu a hakan za ki ci gaba da zama da shi?

Ba ta kai ga bani amsa ba ya fito yana kiranta,da sauri na shige kewayena na ja ?ofa na rufe.Ina buWe daki na cillar da jakar makaranta sannan na shiga wanka ,bayan na fito ne na Wora girki na ci na ?oshi.



Sai bayan sallar isha'i Yaya Khaleed ya shigo a cikin wani yanayi na haWe rai wanda ya wanzar min da tsoronsa.Da na gaishe shi ma dakyar ya iya amsawa,abinci ma da kansa ya zuba ya saka TV a gaba yana kallo duk sai na ji babu daWi na je bedroom na canza yanayin shiga ta na saka kayan da ya fi so.Ina fitowa na je na zauna kan cinyarsa a shagwaSe na tambaye shi  wai don Allah laifin me na yi? kamar jira yake yi ya soma yi min ihu cikin kai  abin da kike yi kin kyauta kenan? Abokina ma ba za ki iya gaishe shi ba? Sannan yau ina lura da ke a cikin mota sai hararen shi kike laifin mi yayi miki? In yanzu yayi aure ya kawo matarsa ta yi min abin da kike masa za ki ji daWi ne? Amma ba laifinki ba nawa Shareef yayi gaskiya saboda ina sake miki fuska ne yana gama faWa ya ture ni ya fice ya bar gidan.

Tun ina jiran dawowarsa har na gaji na ja Waki na rufe,kan kujera na kwanta dakyar bacci ya Wauke ni.Kiran sallah ya tashe ni,shaf na manta da abin da ya faru na wuce toilet na yi wanka sai da na fito ne na lura Yaya Khaleed bai kan gado wato ba gida ya kwana ba.


Da na buWe ?ofa sai na ga babu ma alamunsa,sai na ji duk zuciyata ta ?iya na koma ciki ina ta kuka.Ashe ban ma soma ba har biyun rana babu ko mai kama da shi ne,haka na wuni sukuku kamar kazar da ?wai ya fashewa a ciki.Dakyar na iya yin girkin dare,na zauna jungum ina zaman jiransa,sai dai yau Win ma bai kwana ba wayarsa kuma a kashe.Washegari bugun ?ofarsa ya tashe ni,na buWe masa ya shigo a yanayinsa kawai na lura daga daji yake na ja ajiyar zuciya tare da cewa  Barka da zuwa

 Yawwa ya amsa tare da nufar bedroom,na take masa baya tare da taimaka masa ya cire kayan jikinsa duk da kuwa sai hurar hanci yake ban damu ba har toilet na yi masa rakiya na taya shi wanka bayan ya fito kuma na basa abinci,yana ci yana kallona har ya ida.


Kamar wasu ba?in juna haka duk muka yi shiru,a dole ni ma na soma kallon TV daga bisani kuma na shige bedroom.Wayata na Wauka na soma tunanin lambar ?awata Maryam cikin ikon Allah na samo ta daidai,tana jin muryata ta gane hira sosai muke inda take sanar da ni cewa tana ta ganin canji da ta soma amfani da man zaitun da sauran.

 ?awata ya amarci? ta tambaye ni tana dariya.
Na saki murmushi mai sauti na ce  to ga shi nan da dama dai ba daWi ba wuya 

 Har yanzu ba ki saba ba kenan?

Ban bata amsa ba don ban ga amfani yin hirar sirrin shimfiWar aurena ba sai na canza zancen????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
 ya makaranta kuna ta zuwa duk na yi kewar Zinder 
 In na haihu ai za ki zo
 Ciki gare ki ?
 Eh ina ta laulayi 
Na ce  ?ila dama can aljanin jikinki ne ya hana haihuwar,to Allah ?ara lafiya kin ji ko kuma ki ci gaba da amfani da maganin

 In sha Allah kuwa ,wai.... da sauri na yanke kiran ba tare da na jira jin abin da za ta ce ba sakamakon Yaya Khaleed da ya zo yayi a tsaye a gabana yana faman cire kayan jikinsa.


Gadon ya hauro ba ummm ba a'a ya soma shafa ta,takaici ya rufe ni sai kawai na fizge zan sauka amma ya cabko ni tare da saka ?arfi ya karSi ha?insa,kwana biyun da bai yi a gida ba sai da yayi nasu su ma.Washegari ma da zai tafi aiki sai da ya maimaita ya kuma fice ya bar ni ina kuka, kwata-kwata sai na ji na tsani auren.


Tun daga wannan lokaci rayuwarmu ta koma wata iri,ba mu yin hira ni da Yaya Khaleed tsakaninmu na yi abinci na basa ya ci ya ?oshi sai kuma ya hau turmusa ta.?angaren Shareef kuwa ya Wauke ?afarsa a gidanmu,sai dai kamar wani saurayi da budurwa kullum cikin kiran Yaya Khaleed yake a waya suna hira da dariya.Wani sa'in ma muna kwance kan bed yake kiran nasa haka shi kuma zai Wauka, ni kuma sai dai na maida fuska ga bango na yi ta kuka.


Tsawon sati guda currr kenan ban je makaranta ba kuma Yaya Khaleed bai matsa min ba sai na ga kamar ma ya ji daWin haka.Ina zaune ina kallonsa yana shiryawa muna haWa ido yayi saurin kawar da kai,kafin ya ce  Shareef zai kawo budurwarsa zan kawo kaji ki yi musu girki irin na ranar farkon zuwan ki yayi daWi sosai,sannan ki nutsu ita Win ba wata babba ba ce ?ila ma kin girme ta ki kula da kyau ban son a samu matsala har su koma



Idona na ji sun ciko da hawaye na ce  Yaya Khaleed yanzu hakan da kake yi min ka kyauta? Dube mu kamar wasu ba?i babu hira ,babu komai da muke yi na romantic komai kamar na dabbobi in kana da bu?ata ne kawai kake neman sulh... mugun kallon da yake jifa na da shi yasa na haWiye sauran maganar.



 Kenan faWa muka yi ban sani ba? Wato so kike na dinga sake miki fuska kina raina ni ? Dama Shareef ya faWa saboda ina biye wa shiriritarki ne yasa kika raina ni kike min iskanci iri-iri 


 Kenan shi ya baka shawarar ka canza min? Shawarar mugun aboki kake bi? na tambaye shi hawaye na zubo min shaaa a kumatu,irin kallon da na jima ban gani ba Yaya Khaleed ke aiko min mai cike da tausayina da kuma ?aunata.Sai ya fice ba tare da ya amsa min ba,sai da na ci kuka na gaji kafin na yi aikin gida.

Kamar yadda ya faWa Win ya kawo kajin na gyara na yi komai,wuraren ?arfe biyar na maraice suka iso.Wata kyakkyawar Bafulatanata ce mai shegen kyau kana ganinta ka san iyayenta Naira ta gama ji?a su,dukkan jikinta kuWi ke magana agogon hannunta kawai a bar kallo ce.


Ta ci uban ado kamar ?ar tsanar zinare,bayan sun zauna na gaishe su cike da ladabi Shareef kawai ya amsa ita kuwa tun da muka haWa ido take haWe rai tana wani cin magani .


Na je na kawo musu ruwa na zuba musu,da Shareef zai karSar kofin har da wani shafar hannuna yayi yana sauke ajiyar zuciya.Na yi saurin ja da baya ina hararensa,kafin na zauna kusa da Yaya Khaleed ai kuwa sai budurwar ta sunne kai.



 Aboki ka fa san amarya akwai ta da kunya da dai kun Wan matsa da junanku  cewar Shareef .
Khaleed yayi murmushi tare da tashi ya canza wuri,muka haWa ido da Shareef ya sakar min murmushin gefen baki ya tsure ni da ido yana min tambayoyi irin  ya kika ga wasar? Yanzu kin yarda da ina iya juya mijinki? Kin fahimci cewa ina da matu?ar tasiri ? cikin muna kallon juna ne na soma jin kukan kyankyaso a cikin kunnuwana hannuna na kawai na soma sarrafawa ina nemo kyankyason cike da son Waukar fansa na so cilla shi a rigar Shareef sai na mayar da su da yawa ta yadda zai yi ihu amma sai na ji an tare hanyar faruwar haka.Sai a lokacin na janye idona muka kuwa haWa ido da budurwarsa wacce a yanzu ta bayyanar da Soyayyar siffarta ta matsafiya.


Na janye idona tare da fasa abin da nake shirin yi Win, abincin ma ba za a kawo mana ba sai mun ro?a? SHAREEF ya faWa ,da sauri na mi?e na je na kawo,sai kuma na shige bedroom ina ta tunanin ina kuma ya kwaso waccan budurwar mai shegen hatsari amma banda amsar tambayar.


Sai da za su tafi ne na fita don yi musu sallama, ba za ki yi wa amaryata kyautar komai ba?

Cikin gajiya da salon raininsa na ce  eh ba zan bayar ba Win,ba dai amaryarka ba uwar amarya....


 Keeee!  Khaleed ya min tsawa,sai kuma ya dubi Shareef  abokina mu je haka suka fice ni kuma na zauna zuciyata na suya.Da ya dawo haka ya tisa ni gaba yana faman yin faWan banda ha?uri kuma banda kunya har da bada misali da ita budurwar Shareef Win wai tsabar kunya kasa cin abinci ta yi,daren nan dai ba mu yi shi cikin daWi ba.



Washegari da ihun Yaya Khaleed na tashi,akan kaf kayansa na zuwa aiki sun yi dauWa ban wanke ba.Ni kuwa cike da mamaki nake dubansa don kuwa dukkansu sai da na wanke na goge.

 Allah Yaya Khaleed na wanke su... hannu yasa ya buge min baki har sai da ya fasa abin da na kasa jura kenan na Waga masa murya tare da nuna shi da yarsa ina cewa  wannan shine na farko kuma na ?arshe da za ka sa hannu ka dake ni,ba a haifo ni ba don wani ?aton banza ya dinga jibga ta ba.Kaya ne na wanke su kuma ai niyyata ce yasa nake wankewa to daga yau ban sake yi ka wanke da kanka


 Eh lalle wuyanki ya isa yanka Baseerat ni Khaleed yau Ni kike nuna wa da yatsa?

 Eh Win ubana ne kai?

Ya wato ido ya ce  rashin kunyar taki har ya kai haka? Kin kuwa san matsayina a wurin ki?

 Ina ce dai miji ne,kuma miji ba uba ba ne ballantana nace ban iya rabuwa da kai

 Alamu sun nuna kin gaji da aurena 

 Eh in kuma ka ji haushi sai ka sake ni

 Ai na ga alamun haka ,kuma in ba ki bini sannu ba wallahi kin kusa kama layin zawarawa 

 To sai me? ZAWARCI ai ba gare ni farau ba ga iyayenmu muka gani

Zuwa wannan lokacin na san na ?ure Yaya Khaleed kawai ya Wauke ni da mari har biyu yana cewa  wato da Ammyna kike ? Ita bazawara ? Ki na ji na SEERAT ki haWa kayanki ki bar min gidana tun da iskancin naki ya wuce ni ya kai har ga uwar da ta kawo ni duniya


Sai ya watso min kuWi  ki je ki shiga mota ta ?arfe tara in kuma kin isa sai ki wuce gidan matar aure ba wurin bazawara ba yana gama faWa ya fice.


Wani irin tsoro ne ya dirar min,sai yanzu nake ganin laifina da na biye masa.Ina kuka ina ?ari na kwashi kuWin,tsinke ban Wauka ba iya wayar hannuna kawai na fita da ita.Sai da na rufe ko ina kafin na je na shiga taxi zuwa gidan Bus .Na ciri takardar ?an balaguro,sai da na yi wajen awa Waya kafin motarmu ta tashi .Kuka na soma yi ina tuna ranar da za a kawo ni nan,aure duka wata Waya amma ga shi miji ya kore ni silar mugun aboki .

Dakyar na iya samun abin da na sakawa cikina,sai bayan sallar magarib motarmu ta kai Zinder.Kalaman Yaya Khaleed suka dawo min sai da na auna su da kyau sannan na fahimci mi yake nufi,wato kar na je gun Ammynsa na tafi gun Mama.


Sai da na saka kati sannan na kira Mama,ko gaishe ta ban yi ba na ce  Mama wace unguwa kike?
 Ban gane wace unguwa nake ba?

 Ina Zinder ne yanzu na shigo

 Lafiya?  ban bata amsa ba sai kuka da na fashe mata da shi, kina gidan wacce Bus ? dakyar na sanar da ita,an Wauki lokaci kafin ta zo ta Wauke ni.


Kanzil ba ta ce min ba har muka isa gida,nan na ga gidanta mai shegen kyawu.Wanka ta umarce ni na je na yi,bayan na gama ne kuma na soma neman kayan da zan saka banda.Zanenta na Waura na saka hijabinta,abinci ta zuba min na ci na ?oshi sannan ta nemi ba'asi kamar pampo haka na soma zuba babu abin da na Soye mata har baccin da nake yi a makaranta da kuma barin zuwa da na yi .


A gabana ta Wauki waya ta kira Ammy ta sanar da ita ,amma da alamu ma kamar tun tuni ita Ammyn ta sani duba da yanayin da take bata amsar a da?ile.

Mama ta aje wayar tana cewa  SEERAT ki faWa min gaskiya da gaske ya dake ki? A yanayin yadda na ji Goggo da alamu Khaleed ya sanar da ita kuma ina ga ke ce mai laifin

Hawaye kawai na soma gogewa,muna a haka sai ga mijinta ya shigo.Na gaishe shi cike da ladabi ya amsa cikin kamala,Mama ta yi masa bayanin cewa ni ce ?arta amma ba ta sanar da shi matsalar da ta kawo ni nan ba.


Wani Waki Mama ta kai ni,bayan na yi sallah na haye katifar sai baccin gajiya.Tsakar dare yunwa ta tashe ni ,haka na fita domin samawa kaina abinci amma ashe rabon na yi mugun ji ne.A yanayin sautin da ke fitowa a Wakin Mama na fahimci komai,sai mamaki nake yadda mijin nata ke faWar abubuwa masu cike da abun kunya.Jikina har rawa yake na shiga kitchen na zuba abincin,cikin sauri na ci na ?oshi na sha ruwa na koma yanzu ma da na ratsa ta falo haka na yi ta jin sautinsu.

Da na koma Waki sai bacci ya ?aurace wa idona,wata irin kewar Yaya Khaleed ce nake ji babu abin da nake bu?ata irin na samu kaina a tare da shi.Na haye katifa tare da curewa wuri guda,da na duba waya ?arfe ukun dare moments Winmu da shi duk ya dawo min da yanzu ina gida muna second round ne saboda mijina jarumi ne.Haka na yi ta tunani har bacci ya Wauke ni mai cike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login