Showing 9001 words to 12000 words out of 139076 words

Chapter 4 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

105

nan in ban wanke shi ba sai ta sani mtsww  ta ja tsuki tana dirje waken amma jin ita ma an ja mata tsuki yasa ta zabura tana dube-dube sai dai babu kowa.Watsar da tunanin ta yi ta ci gaba da aikinta wani tsukin ta kuma ji sannan ana magana ?us-?us,gabanta ya faWi jin tamkar ana tafiya cikin falo.Tana shirin fitowa aka Wauke wuta,lalubo ta soma yi cikin duhu ko Allah yasa ta Wauko wayarta ta kuwa yi sa'a ta samu jakarta hannunta har rawa yake ta zuge zip ta ciro wayar sai ta ga saura ?iris batirin ya mutu alhalin a cike ta bar ta.Tana ?o?arin ganin ta kunna fitilar ta ji tamkar saukar huci kusa da ita,ta wani juyo da sauri ta inda take jin abin tare da haska hasken screen babu kowa sai ?afafuwan ?ofato da ta yi arba da su babu kuma gangar jiki.......
*ZAWARCI*


LoVe aNd HoRrOr StOrY &?

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI=ث?
'?)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS&?*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________
26/09/24


9


Babu shiri Sakeenatu ta saki wayar ta arta a guje,sai dai ta nemi ?ofar fita ta rasa saboda mugun duhun da ya mamaye gidan baki Waya.Cikin ?an?anan lokaci duk ta firgice,dakyar ta iya samu ta fito tsakar gida da lalabe zuciyarta sai ?ara tsananta gudu Waige-waige ta fara sai ta ga ashe kaf unguwar ne babu wuta,ba ta gama daidaita numfashinta ba wata ba?ar mage ba?a ?irin ta soma yin kuka miyau!miyau! Kukanta duk ya cika gidan.


Ta Waga kai dakyar ta dubi inda sautin kukan ke fitowa,ido huWu suka yi da magen wacce hasken idonta yake kamar na lantarki sai canza kaza suke.A hankali ta sauko daga katangar ta soma nufo inda Sakeenatu ke tsaye da gajiyayun ?afafunta,Allah ya gani ba ta wani ba wai karatun addini muhimmanci ba dukkan lokacinta da haza?arta ta zuba su ne a harakar boko wannan ya sa ba ta iya wasu addu'o'i ba .A halin yanzu da take tsaye ta yarda kuma ta aminta rayuwarta na cikin haWari,tabbas ta san wannan magen ba normal ba ce muguwa ce cutar da ita za ta yi.


Ta na dab da ta kawo kusa da ita ta samu bakinta na furta  la haula wala ?uwata illa billah!!! ?iiii magen ta wani ci burki tana mai canza salon kuka zuwa na jarirai amma sam Sakeenatu ba ta yi gigin yin shiru da bakinta ba sai ma ?aimi da ta fara wurin maimaita addu'ar.A gaban idonta magen ta soma mayar da idonta kamar na mutane kafin ta ruga a guje ta yi tsalle Waya ta haye katanga,daidai nan kuma aka maido wuta yaran unguwa suka hau ihun murna.Sakeenatu ta ja ajiyar zuciya tana mai yin hamdala ga Ubangiji,bakinta bai gushe ba yana ta furta lahaula wala ?uwata illa billah a haka ta koma can ciki.Gas Win ta kashe saboda muguwar gajiya da ta saukar mata wacce ba ta san dalili ba,wayarta ta Wauka Allah yayi sa'a babu abin da ya same ta abun mamaki kuma yanzu cajin wayar a cike yake saSnin Wazu da aka nuna mata ta kusa mutuwa.


Lambar Nafisa ta kira,tana Wauka babu wani tsaya wa gaisuwa ta ce  Nafi ki turo min karatun nan da kike saurare don Allah duk dare
 Anty Sakeena lafiyar ki kuwa?
 Ki turo min karatun dai don Allah ina son saurare 
 Ok to bari na hauda data yanzu zan turo miki
 Yawwa ina jira ta faWa tare da kashe kiran,ita ma datar ta kunna babu jimawa kuwa karatun ya shigo suratul Ba?ara ce ta turo mata sai Yasin .Tamkar abun tsiya network Win ya Wauke Wif ko Waya babu wanda ya buWe,juyin duniya ta yi amma sun ?i buWewa har wayar ta kashe ta kunna amma network Win ya ?i yi.Cike da damuwa ta sake kiran wayar ?anwarta,tana Wauka sai ta rasa abin da za ta ce mata kawai ta fashe da kuka.Daga can Sangaren Nafisa ta ce  subahanallah! Anty Sakeena don Allah mike faruwa? Mike damun ki?

Cikin muryar kuka take cewa  Nafisa tsoro nake ji! A tsorace nake ji nake kamar ba ni Waya ba ce cikin gidan nan tamkar ina ....inaaa ta kasa ida maganar saboda motsin da ta gani ana yi can cikin labule wanda ta tabbata kuma ba Sera ne ba saboda girman halittar.Ihu ta fasa ganin ?atuwar gafiya ta faWo timmm da ?asa,yayin da kuma wata ta biyu ita ma ta sake fitowa a guje ya kama waccan wacce ta faWo a gaban idonta suka soma faWa suna cizon junansu.Babu shiri Sakeenatu ta haye Waram kan bed ta na kuka,Nafisa na jin haka ta ziri hijabi ta fito ko Mamarsu ba ta sanar ma ba ta fito ta samu Wan sahu.Allah yayi sa'a ba wani nisa ne sosai a tsakaninsu ba,da gudu ta shigo gidan tana ambaton sunan Allah daidai nan gafiyoyin suka yi Satan dabo hatta.



Nafisa ta je ta rungume ?ar uwarta wacce da ace tana da cutar asuma da tuni numfashinta ya fita, yi shiru don Allah ya isa yi min bayanin mike faruwa? Ina shi Abbas Win?


 Yana asibiti wurin Mamuh,na dawo na dafa mata wake da shinkafa ne shi ne ake ta firgita ni nan ta kwashe duk abin da ya faru ta shaida wa ?anwarta.
Nafisa ta ja dogon numfashi bayan ta saurare ta,sannan ta ce  wannan duk sharrin miyagu ne shi yasa a kullum ake son bawa ya keSe wani lokaci don nemawa kansa kariyar ruhi da gangar jiki ba wai gyaran duniyarka ba kawai.Ni wallahi na fara zargin Mamuh Win nan,kina dai ganin yadda Ma'idah ta caka mata cokali da dukkan alamu ta hango abin da idanunmu basu gani.In ba masifa ba cikin daren nan za ki dafa mata wake kamar mayya,ke ?ila ma ita ce.Tashi mu je ki yi alwala ai zama bai gan ki ba tun da kin ji kin gani aure a inda ba a ?aunar ki

Da taimakon Nafisa ta yo alwala dama ita Nafisar kusan kowanne lokaci tana da alwala mace ce mai ri?o da addini ba ta da sake,hasali ma malamar makaranta ce a wata islamiyya.
Karatun Alkur'ani ta soma koya wa Sakeenatu kamar wata ?ar yarinya haka take biyawa inda ta yi kuskure kuma ta gyara mata.
 Ki kasance kullum cikin tsarki bima'ana alwala saboda tana da muhimmanci sosai wurin bada kariya,ko sheWanu suna shakkar mutum mai zama da alwala a koyaushe,ke ko period kike to ki yi abarki sannan ki ri?e azkhar na safe da maraice

 Amma ai kin san ban iya su ba ko?
 Ki koya mana anty Sakeena ,shi ilimi ai bai da ?a'ida shekaru ko tsoho Wan shekara Wari zai iya shiga makaranta ballantana ke da ko talatin ba ki kai ba
 Ni rubutun larabcin ne ke bani wuya 
 Zan nemo miki littafi mai fassarar Hausa ,sai na dinga koya miki yanzu bari na tura miki app Win Alkur'ani sai ki dinga saurare 
Ta karSi wayarta ta tura mata tare da saita mata komai ta kunna sautin ya soma tashi,ta ce  to ni zan tafi gida ko Mama ban sanar ma ba

 Don Allah Nafisa kar ki tafi ki bar ni ki jira har Abbas ya dawo,bari na kira Mamar na shaida mata haka suka yi kuwa,tun suna jiran Abbas har ?arfe sha biyun dare bai zo ba a tare suka fito suka rufe gida da ko ina sannan suka je suka kwanta.


A can asibiti kuwa bayan fitar Sakeenatu,Gwaggo Rahamu ta yi wani kishingiWa ga kujera kamar mai bacci nan kuwa ruhinta ne ta soma fitar wa daga gangar jikinta.Sawun Sakeenatu ta bi,hasali ma ta rige ta zuwa gidan duk abin da take yi akan idonta hanyar farko da ta soma bi shi ne tafiya ta shiga tunanin mai kula da nepa na unguwar ya Wauke wuta ba tare da shi kansa ya san dalili ba a cikin wannan duhun ne ta yi ta yi wa Sakeenatu mugunta.Da ta koro ta da addu'a shine ta biya wurin wasu miyagun ?awayenta ta basu address suka je a siffar gafiya,su ma ba su bar gidan ba sai zuwan Nafisa.

Abbas na daga can gefe Mamuh na yi masa hira tana murmushi saboda duk abin da ke faruwa ita tana gani saSanin shi Abbas Win.Bayyanar esprits biyun yasa yanayin sha?ar iskan Wakin ta sauya saboda tsabar muguntar su, wannan karon hatta Abbas sai da ya ji wani iri.Har yanzu Gwoggo Rahamu ba ta farka daga baccin ?aryar da take ba,cikin hirarsu ta ?an duniyar Soye suke bata labarin yadda suka firgita Sakeenatu tana ta yin kuka.
 Na gode sosai ?awayena,kar ku manta in kun gama yawon Maitar dare ku biyo ta nan mu sake komawa mu uku mu haWa ?arfi mu shayar da ita mamaki ba?in ruhin Gwaggo Rahamu ya faWa ,suka yi dariyar mugunta tare da Waukar mata al?awari kafin su bar wurin.Cikin ?warewa ta dawo da ruhinta a gangar jikinta,ta dubi Abbas tana mai cewa  bacci ya Wauke ni duk yau ban rintsa ba,ina sauran waken ni ma na ci yunwa nake ji


Shi Abbas sam ya manta da wani zancen wake saboda yadda Mamuh ke masa hira,sai yanzu ya tuna Sakeenatu ta je gida dafawa.Da ya duba agogon hannunsa ransa ne yayi mugun Saci, uwar tamu ai ba ta dafo ba tana can tana gantalin da ta saba,ah to dama su likitoci ba su da kamun kai tsakaninsu da abokan aikinsu suke neman juna in aka ce miki tana can asibiti wani ?ato ya taushe kar ki yi gardama Mamuh ta faWa ,yayin da Gwaggo ta karSe  i sosai ita ma wannan shegiyarta ta ai shugabansu ne ya Wirka mata cikin ya bar yaronmu da wahala,wai Abbasi wai ya ?a?aba maka aurenta?
Kasa cewa komai yayi,haushi goma da gomiya tara ya rasa da wane zai ji abin ka kuma da zuciyar namiji sai ya ji zargi ya Warsu a ransa.Da ya nuna zai je gida Mamuh ta hana shi tafiya ta hanyar amfani da tsafinta,haka suka dinga kwaso sharri iri-iri suna yaSa ma Sakeenatu sosai kuma suke samun gurbi a zuciyarsa.Can waje ya koma ya kwanta kan wani banci yana ta tunanin rayuwa baya yadda neman aurensa ya kasance yadda sam Sakeenatu ba ta samu shaidar ?warai ba ga mutanen unguwa amma ya rumtse ido ya ce sai ita .


?arfe biyu da rabi na dare ?awayen Gwaggo Rahamu suka biyo mata,kafin su yi tsinke gidan Sakeenatu.Sai da suka shiga kitchen suka cinye kaf abincin da ta dafa sannan suka dawo falo suka fara shawarar abin da za su yi mata,suna dariyar mugunta suka tura ?ofar falon sai dai da zarar sun yi niyyar Wora ?afarsu a tile Win bedroom sai su ji tamkar cikin garwashin wuta ne suke Wora su.Gwaggo Rahamu ta ?an?ance ido tana kallon gefen Nafisa inda kusan kanta ta Wora wayarta ne sautin karatun Alqur'ani na tashi a hankali wanda ba ma a jinsa sosai,kamar ta san suna nan kuwa sai ta kai hannu ta ?ara volume a tare suka saki wani ihu wanda sai da gidan ya girgiza a firgice Sakeenatu ta farka tana zarar ido



My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank DM +22795045822



My book is only 500 via 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,DM +22795045822
*ZAWARCI*


LoVe aNd HoRrOr StOrY &?

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI=ث?
'?)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS&?*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________
28/09/24


10

A wahalce Gwaggo Hajara ke bin bango don isa Wakinta,fatar nan tata ta tsakaka duk ta yi wani taushi ta fara fitar da wani fanko.A yadda bango ke zuzar fatar cikinta ji take kamar ta yi ta ?urma ihu sai dai ba dama sata lahira! Tana isa Wakinta ta Wauki siffa ta mutum nan ne fa ta yi tozali da yadda duk jikinta ya kumbura yayi ja kamar wacce aka soya,mai ta Wauko ta shafe jikinta da shi tana matsar ?walla tare da jin tsanar Safeenatu na sake feso mata daga can ?asan zuciyarta.
A fili ta furta  sai na wula?anta rayuwarki,sai na saka kin tozarta a duniya,sai na shayar da ke gubar azaba wacce sai kin gwammaci mutuwa akan rayuwarki. Ke kan ki Habibah ba zan bar ki ba zan Wora miki karatu da alamu har yanzu ba ki ji jiki ba shi yasa kike taimaka wa wata wurin ruguje plan Wina shiru ta yi jin an turo ?ofa.Daddy ne ya shigo da sallama a bakinsa,ba ta amsa ba sai ma saurin jawo hijabi da ta yi ta saka duk ta luluSe jikinta.

 Ni kam Hajara lafiya kike? Kin ga yadda fuskarki ta yi suntum sai huci take kamar ?ullun wainar da ya ji yis? Daddy ya faWa yana ?are mata kallo.Wani ?ululun ba?in ciki ne ya ?ara turnu?e Hajara ta ce  uwar waina ce.... ba ta ida kai aya ba ta ji yatsun Daddy biyar kan kuncinta,shaye da mamaki take kallonsa nan ta hango wani ba?in tauraro tsakiyar goshinsa wanda ko shakka babu aikin Habiba ne ta tura masa shi.
Ba ta gama dawowa daga duniyar mamakin da ta je ba Daddy ya soma magana cikin masifa, wato abun naki ya fara zama iskanci,daga tambaya shine za ki zagin uwata saboda kin san yau za ta zo.To tsaya ki ji Hajara duk wata tijararki ki tattara ta ki ajiye wuri guda muddin Hajiya ta koma da ba?in cikinki gida to wallahi akan aurenki.Ki tashi ki Wora girki tsabar lalaci muna da mai jego a gida amma kin zo kin shige Waki kin haye gado tare da saka hijabi kamar matar liman kowacce za ta yi aikin ?warai yana gama faWa ya nufi ?ofa,sai kuma ya juyo ya ce  Murjanatu na kan hanya sai ki fara shirin tarben ta kawai ya fice.


Gwaggo Habibah da ke zaune kan kujera a falo ta saki wani irin murmushin nasara,tun da uwarta ta haife ta yau ce ranar farko da ta juya taurarinta na baiwa ta yi aiki da su.Tun bayan da ta yi wa Twins wanka ta shirya su sannan ta bai wa uwarsu abin da za ta ci kawai ta fito falo ta zauna,Daddy na fitowa ta soma yi masa transfer Win tauraron ta hanyar kallonsa tsakiyar ido da farko har ya tambaye ta lafiya sai kuma yayi shiru jin sabon abu a tattare da shi.
Duk abin da yake faWa wa Gwaggo Hajara sarai ta ji alamun aikinta yayi kyau,ta saki murmushin nasara tana mai cewa  mijinki zai zame miki kumurci,da haka zan raunata muguwar zuciyarki

 Habibah karSi wannan ko kuna da bu?atar wani abu sai a Wauka ciki Daddy ya faWa yana mai katse mata tunanin zuci.Ta karSa tana mai cewa  Yaya ?ayyabu na ce bayan biki sai Safeenatu ta koma can gida wurin Hajiya ko?
 Saboda me? Ba a nan za ki zauna ba?
 Eh to ni ma da haka na ce Win amma sai na ga kamar anty Hajara ba ta son zamana tun da na zo idonta kamar za su faWo tsabar yadda take jifana da mugun kallo


Ran daWi ya Sace, yanayin fuskarsa ya canza tuni tauraron goshinsa ya ?ara yin ba?i ba tare da ya ce komai ba ya ?ara komawa Wakin Gwaggo Hajara ita kuwa Habibah har da wata dariyar mugunta ta yi tare da tashi tana taka rawar murna.

Daddy na shiga Waki ya yi wa Hajara wankin babban bargo,ko ina ana jin muryarsa yadda yake yi mata masifa in ta je yin magana kuma sai ya gwaSe bakin.Da wannan ba?in cikin ya fita ya bar ta,sai da ta sha kuka wiwi sannan ta fito ta Wora girki babu jimawa kuwa sai ga Hajiya ta zo .A ladabce Gwoggo Hajara ta gaishe ta wanda sosai ita hajiyar ta yi mamaki don rabon da ta yi mata irin wannan ladabin tun ranar da ?ayyabu ya kawo mata ita a matsayin matar da zai aura.Cikin sakin fuska ta amsa tare da cewa  to barkarmu Safeena an sauka Allah raya kan sunnah,kin samu mai taya ki aiki da kuma miji Hajiya ta faWa tana murmushi a doli ita ma ta yi murmushin ya?en a can ?asar zuciyarta tana cewa  an haifo mana masifa dai aljanar jaririya muguwa wacce ta yi gadon jaraba 

 Zan shiga daga ciki hajiyar ta faWa tare da nufar Wakin Safeenatu,cike da murna ta zauna tana kallon jariran Gwaggo Habibah ta Wauki namijin ta bai wa Hajiya ta karSa tana mai kai masa sumba haWi da yi masa addu'a sannan ta mi?a shi.Ana Wora mata macen jikin Hajiya ya Wau kyarma kamar mazari,murya na Wan rawa ta ce  wane suna za a saka musu?
 Basheer da Baseerat  Habibah ta bata amsa tana murmushi tana kallon mahaifiyarta wacce kambun muguntar Gwaggo Hajara duk ya dabaibaye ta yanzu kuma ya fara barazanar tarwatsewa.
Hajiya ta ce  karSar ta tana mai mi?o Baseerat don ruhinta ya soma yin rauni, Habibah ta ce  Hajiya don Allah ki ri?e t... ba ta kai ?arshe ba Hajiya ta mi?e ta je ta shimfiWe Baseerat a shimfiWa,sai aka yi rashin sa'a safar da aka saka ma hannunta na hagu ta fita wani mugun haske ya fito ya shiga ?irjin Hajiya saura ?iris ta faWi saboda yadda fitilun idonta suka rufe jiri kuma ya Webe ta.


Safeenatu dai na daga gefe tana kallon abubuwan ban al'ajabi , Gwaggo Habibah ce ta kamo Hajiya ta taimaka mata ta zauna.Kamar mai cutar huka haka numfashinta ke fita,ruwan sanyi ta nema da sauri aka bata ta shanye ?atuwar gora.

 Habibah bani pilow bacci nake ji cewar Hajiya ,da sauri ta Wauko ta mi?a mata ita kuma ta kwanta babu jimawa bacci mai nauyi ya Wauke ta .


Safeenatu ta ce 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login