Showing 93001 words to 96000 words out of 139076 words

Chapter 32 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

140

kamarsu Waya da mahaifinsa.Bai da ?iba sai uban tsayi,yana da gemu da kuma saje haka ma jikinsa irin mai gashi ne sosai.


Ya tako zuwa bed Win ya zauna,zanen da ta rufe jikinta da shi ya yaye tare da nufo ta ya yi mata rumfa.Tsoro ne ya kama Ma'idah,ita da ta yi tunanin ba zai kula ta ba sai sun saba sai ta ga abun mamaki.Sumba ya soma aika mata ta ko ina ,jikinta da nasa duk rawa suke abu guda ta lura da shi shine ya cimma burinsa na tarayya da ita .Kuka ta soma ta ce  don Allah ka bari ban so na gaji kanzil bai ce mata ba ya raba ta da kayan jikinta shi ma ya cire nasa,tsoronta ne ya Wan ragu ganin ?an?antar halittarsa sai dai ?an magana na ce ba a rena allura ita ma ?arfe ce .Razananen ihu ta ?urma ta soma kuka kenan ya mirgina gefe yayi baya,ta yi tunanin ko tausayinta ne ya ji ya bar ta sai da aka Wauki sama da minti talatin kuma ya sake lalubo ta wannan karon ma ko minti biyu ba a yi ba ya samu gamsuwa ya fice ya bar ta nan.Sai da ta gaji da kuka sannan ta mi?e ta shiga toilet ta yi ,ta cika baho da ruwan Wumi ta shige.......

*ZAWARCI*
BOOK 3

LoVe aNd HoRrOr StOrY &?

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI=ث?
'?)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS&?*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________

1_2


Tamkar wata sabuwar halitta haka nake jin kaina,mutanen da ke bi suna wuce wa nake kallo ina duban abubuwan ban al'ajabin da ke tattare da dayawan su.Wata mace na gani tana tafe yayin da wata ba?ar inuwa ke take mata baya,wanda kuma na yi imanin cewa ita kanta ba ta san da akwai wani abun cutarwar da ke bibiyar rayuwarta ba.Na shagala sosai da kallonta na ji muryar wani Wan yaro na cewa  a'a ban ka yi tafiyar ka ,ni ban son kuWin aljani yaron duka-duka ba zai wuce shekara uku zuwa huWu ba,inda yake kallo na duba sai na ga irin inuwar nan dai ce ta matar nan.Daga nan ne na fahimci wato aljani ya fitowa yaron ne Saro-Saro suna ganin juna alhanin ni kuma inuwarsa ko kuma nace sawunsa kawai zan iya gani a matsayina na babba.


 SEERAT wai mene ne duk wannan kin tsaya cak wuri guda,dubi yadda mutane ke kallonmu na ji muryar Yaya Khaleed ta daki kunnena,ni tuni na manta ma a tare muke.Na ja ajiyar zuciya kafin na je na hau babur,sai da muka Wan yi nisa sannan na ce  Wazu lokacin da na faWi kamar na ji muryar Basheer

 Eh shi ne,yayi tafiyarsa ne tun da ya ga kin mi?e Yaya Khaleed ya bani amsa.Ban ?ara cewa komai ba na soma tunanin sabon al'amarin da ya riske ni yau,kwatsam kamar an ce in duba na kai kallona a madubin da ke manne ga babur.Ban san lokacin da na fasa ihu ba tare da ?an?ame shi ina kyarma,saura ?iris ya juye da mu amma Allah ya gyara Yaya Khaleed ya ci nasarar cin burki sai dai tuni madubin babur Win ya tarwatse da kansa.



 Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un ! Wai SEERAT don Allah meke damun ki ne?

 Yaya tsoro nake ji na furta kamar wata doluwa.

 Yaushe SEERAT ta soma jin tsoro? Ke Win ce ke jin tsoro? 

 To ai ni ma mutum ce na basa amsa .

 Mai neman abin da ya fi ?arfinta ba,ina ce nan har rijiyar Mayu kika taSa zuwa tsakar dare Yaya Khaleed ya waigo yana kallona,?irjina ya buga saboda muninsa da na hango,da kuma wani abu mai kamar ?iyayya.


 Hum! yayi tare da ci gaba da tu?a mu,muna daf da shiga makaranta ya ce  mine ne kika gani cikin madubin?

Ban basa amsa ba har ya tsaya na sauka daga babur,tsintsiyar hannuna ya ri?e ya ce  ina sauraren ki

 Ni ban ga komai ba na faWa ina jin tsoronsa ganin ya canza fuska alamun halinsa na rashin mutumci ya hau kansa.

 Ke kar ki raina min hankali faWa min abin da kika gani ya faWa cikin tsawa.

 Allah Yaya Khaleed ban ga komai ba ka yarda da ni  na faWa don haka kawai nake son Soye masa.

 Shi kuma madubin uwar mece ta saka shi tarwatsewa? SEERAT ki sani duk duniyar nan babu wanda zai fi ni sanin ki ciki da baya,bari ganin kanku haWe ke da Ammy to naku wasa ne ni na fi kusa da ke fiye da ita.Duk wani abu da zai faru da ke ina ji a jikina,kai kuma da kake bayanta in ma a tunaninka za ka iya raba hanta da jini to ka makaro aurena da SEERAT mutu ka raba ne takalmin kaza  yana gama faWar haka ya wani Wingiza ni na yi baya shi kuma ya buga babu ya tafi ya bar ni sake da baki.
Har waigawa na yi a bayana don ganin ko akwai da wanda Yaya Khaleed ke magana amma wayam,ciki na shige ina tafe ina kallon ?asa har na isa aji.


Yau haka-haka nake ji na,duk lissafina ya dame.?awata Maryam ta zo ta zauna kusa da ni ta ce  ?an mata na Wago na dube ta sai kuma na Wan zabura ina kallon inuwar da ta yi tsaye ?i?am kusa da ita.


 Na ji daWi sosai da muka haWu yau wajen sati Waya kenan ba mu ga juna ba,ga shi ke kuma ba ki da waya ballantana na kira ki.Shikenan kuma yanzu da mun yi awa Waya sai mu rabu zuwa asibiti,na yi kewarki sosai Maryam ta faWa ,wacce ta kasance abokiyar karatuna ce kullum muna tare yanzu ne da muka tafi aikin gwaji a asibitoci aka raba mu.

 Wai mi kike kallo? ta tambaye ni tana mai waigawa,na girgiza kai na ce  babu komai fa,ya aikin ?
 Alhamdullah ! Akwai gajiya kam,jiya sai dab da magrib na koma gida Habibi na ta masifa kamar zai cinye ni 


Na taSe baki don in da sabo na saba da ?orafin Maryam akan mijinta,sam bai son karatun da take.Muna nan zaune a sannu duk Walibai suka cika ajin,nan na ?ara fahimtar wani abu sannan na samo amsar tambayata  wannan inuwar mece ce? ba komai ba ne face jinnu waWanda ba su samu damar shiga gangar jikin mutum ba sai dai dama kaWan suke jira suke shige.




Malamin da zai koyar da mu dabarun kula da majiyancin da ke Wauke da wata cuta wacce mutane ke ?ama,amma kasantuwarmu malaman jinya bai kamata mu ma mu nuna ?yama ba sai dai tausayi da kuma taka tsantsan.Har ya gama jawabinsa ban fahimci komai ba saboda duniyar tunani da na lula,bayan mun fito ne nake cewa Maryam  wai don Allah mine ne ke yawan gama ku faWa da Habibinki?

 Karatuna mana,sannan na faWa miki ban Soye miki ba ni sam-sam banda wani desir shi kuma hakan na Sata masa rai Maryam ta bani amsa,na ce  yanzu dai sai an in mun sake haWuwa zan yi miki bayanin yadda za ki kawo ?arshen matsalarki  ta wani rungume ni tana godiya kafin mu rabu kowa ya kama gabansa.


Asibitin da aka kai ni na tafi,Wakin da ake ajiye kaya na shiga na ajiye jakata na kuma Wora farar rigar likitoci sannan na nufi sashen maras lafiya.Da ni da sauran Waliban da suka zo koyo duk muka dinga duba maras lafiya,in kuma abin ya fi ?arfinmu sai manyanmu su duba.




 To yau za mu shiga Sangaren masu fama da ciwon asuma wato huka,da farko za ku yi musu tambayoyin abin da suke ji kafin ku fara basu magani cewar likitar da ke koyar da mu,duk muka jinjina kai kafin mu take mata baya.Da na shiga Wakin sai da na ji tsikar jikina ta yi wani tsammm,cak na yi tsaye ina ?arewa majinyatan kallo,dayawa daga cikinsu babu wata cutar asuma da suke fama da ita face jinnu ne ke haifar musu da Waukewar numfashi tare da danne musu ?irji.A haka dai muka duduba su muka fito,yanzu damuwata guda ta ya zan taimaki mutane ban sani ba.



Sai da muka yi aiki tu?uru kafin mu tsaya mu ci abinci,yau Win ma ?arfe biyu muka tashi.Na fito kenan ina neman abin hawa sai na tsinkayi Yaya Khaleed,fuskar nan tasa kicin-kicin tamkar bai taSa dariya.Mugun tsoronsa da shakkarsa ce na ji suna yi wa zuciyata Waurin goro,a sanyayye na ?arasa kusa da shi sallama Wauke da bakina.Ya amsa ciki-ciki,sai kawai na soma wasa da yatsun hannuna.


 Sai na ce ki hau sannan za ki hawa ko? ya tambaye ni yana min wani kallon mai saman ruwa,da sauri na je zan hawa jiki na yi min rawa amma ya daka wata uwar tsawar da ta kusa sa na faWi don tsoro.

 Kar ka saki ka hau min babur ni sa'an ka ne? Yaya Khaleed ya faWa yana hararena,wani shuuu ! Na ji kamar fitar iska ya gusa daga jikina har sai da na ja ajiyar zuciya.

Babur Win na hau ,ya daidaita sabbin madubin babur Win da ya canza yana kallona ta ciki.Kamar wacce aka shuka haka ni ma na tsayar da ?wayar idona cikin nasa muna kallon juna,wani irin azababen so nake hangowa cikin idon Yaya Khaleed da zurfafiyar ?auna.

 Hummm! na ja wani dogon numfashi ba tare da na shirya ba ina mai kai dukkan hannuwana na zagaye cikinsa,a hankali na kwanta a gadon bayansa ina mai lumshe ido.


Na saki wani guntun murmushi jin Yaya Khaleed ma ya sauke ajiyar zuciya,a hankali ya soma tu?a mu kamar bai son gudu.Mun yi nisa sosai kafin na tsinci muryarsa  ina son ki SEERAT 

 SEERAT na son Yayanta na basa amsa ina mai fitar da zallar yarintata.Wani murmushin na kuma saki lokacin da na ji hannunsa kan nawa da ke manne ga cikinsa, zan kula da ke,zan kuma nuna miki ?auna sannan duk rintsi ba zan bari a raba mu ba

 Na gode Yayana na furta ina jin wata irin nutsuwa,a hanya ya tsaya ya saya min kayan marmari muna isa gida ya mi?a min ledar.Wanka na soma yi kafin na wanke su na yayanka,a tare duka ?an gidanmu muka ci Yaya Khaleed sai kallona yake kamar yadda na lura kuma yau hakan na yi wa Ammy Habibah daWi .


Bayan nan Mama ta mi?o min ji?e-ji?en da ta yi na kuwa shanye su tasss,bayan sallar la'asar kuwa wata dun?ulalar kaza ta bani na ci na ?oshi hatta romon sai da na sha.


Da dare kuwa ina zaune a Waki ina duba littattafaina Ammy Habibah ta shigo ta zauna gefena.Na rufe littafin ina mai kallon ta,na saki murmushi na ce  Ammy yau kamar kina cikin damuwa

 A'a ko Waya,kawai ina tunanin wani sati mai zuwa kina can Yamai a Wakinki ta faWa tana wani murmushi wanda na fahimci ?ir?irar shi ne ta yi amma ba daga ?asan zuciyarta ya fito ba.
Na Wan rufe fuskata da tafin hannu ina ?ar dariya,ta ce  ja'ira! BuWe fuskar faWa min abubuwan da suka faru da ke a yau

 Dama na san akwai abin da ya kawo ki  na faWa a zuci kafin na Wan yamutsa fuska na ce  babu komai kawai aiki ne kamar kullum

Hannuna ta kamo ta ce  kina ji na SEERAT kar ki Soye min komai,ki sanar da ni kar ki ji tsoro ko shakka .Ammynki na tare da ke a kowane irin yanayi,Wazu yayanki ya sanar da ni kin ga wani abu har madubi ya fashe , please ina son ki siffanta min abin da kika gani Win

Jikina ne ya Wan soma rawa kafin na soma bata labari, wasu halittu ne biyu Waya ba?i ?irin,Wayan kuma fari tasss 
 Wane ya fi girma daga cikinsu? ta yi saurin jefo min tambayar kamar da alamu ta san da zaman halittun.


 Ba?in ya fi girma na bata amsa,sai ta Sata rai tana cewa  da saura dai har yanzu
 Mi? na tambaya.

 Babu komai yi karatunki tana gama faWa ta fice,na bi bayanta da kallo kawai ina jin a zuciyata tabbas akwai abin da take Soye mini.






#?ASAR KANADA


A nutse Ma'idah ke shirya wa cikin riga da wando jeans,bayan ta gama ta Wora After dress ba?a .Tana tsaka da naWa kallabin a kanta Heesham ya shigo yana yi mata kallon nan da ya saba yi mata tun lokacin da aka kawo ta.Wani takaici ne ya rufe ta ganin ya nufo ta,don tuni ta san sauran ba ta da ikon yin kwalliya ta yi tsaf sai ya neme ta kuma kayan takaici ba gamsar da ita zai yi ba.

Ta rumtse ido hawaye na silalo mata sa'ilin da ta ji yana cire duk uban kayan da ta yi ado da su.Heesham bai magana,ya zama kurma ne na ?arfi da ya ji ko kuma ma za a iya cewa ya mayar da kansa kurma ta sanadin shaye-shayen kayan maye.Wannan ya saka babu wata fahimtar juna tsakaninsa da matarsa Ma'idah,ba su yin hira kawai dai yana sauke bu?atarsa ne a kanta.

Ko kaWan ba ta ?i basa ha?insa ba,sai dai shi yayi kiWinsa da rawarsa.Ko cikakken minti uku ba a yi ba ya koma gefe yana mayar da numfashi,ita kuma cike da takaici ta tashi ta shiga Toilet ta tsarkake jikinta.A gaggauce wannan karon ta shirya cikin doguwar riga fara sol mai mayafi,ji?a?en gashin kanta ta gyara kafin ta Wauki jakar makarantarta ta fice .


Direbanta na ganinta ya taso da sauri ya buWe mata mota,har aka kai ta makarantar tana tunanin mafita sai dai ta rasa wa za ta tunkara da maganar.Sosai take jin kunyar Mamarta Sakeenatu, dama-dama anty Nafisa kuma ba lallai in ta shaida mata za ta bata shawarar rabuwa da Heesham ba duba da Wan uwanta ne na ji.Sannan rabuwar aurensu tamkar saka igiyar auren mahaifiyarta ne a haWari,don ta lura an aura mata Heesham ne don ya zame mata ?arfen ?afa.Har suka gama duk darasinsu na yau takaicin mijinta bai gushe mata ba,ko da ta fito tuni direba ya zo Waukarta.Kalle-kalle ta soma yi tana yaba kyawun garin,har za ta Wauke idonta daga window sai kuma suka sauka kan wani allon sanarwar kan hanya. ?an dakata! ta cewa direba ya kuwa taka burki ta ce  yi baya kaWan  sai yayi yadda ta ce Win rubutun da ke kan allon sanarwar ta karanta,kafin ta ciro wayarta a jaka ta Wauki wani abu. Mu tafi ta faWa tana sakin murmushi,direba na sauke ta direct ciki ta shige a falo ta tarar da shi yana aiki da system.Ta taSe baki ta ce  kamar da gaske ya Wago ya dube ta kawai,ita kuma ta Wauke kai kafin ta shige bedroom Winta.Wanka ta soma sannan ta zo ta haye gado,Mamarta ta kira suka gaisa kafin ta Wauko abin nan da ta gani kan allon sanarwa ta shiga facebook.Searching/recherche ta yi babu jimawa kuwa s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ai ga group Win ya bayyana babu wani tunani ta shiga,a hankali ta soma bibiyar duk abubuwan da aka taSa posting da kuma comments Win mutane.Posting na ?arshe ne ya Wauki hankalinta sai ta ga ma tamkar tana son shiga,zance ne akan mutum ya tura hotonsa za a faWa masa duk matsalolin da ke jikinsa da kuma maganinsu.Kamar wacce aka tsikara haka ta mi?e ta je ta Wauko hoton Heesham ta tura a group Win da yau ne kawai ta shige shi ba ta san komai a kansa ba.Bayan Ma'idah akwai waWanda suka turo nasu hotunan,kamar ?yaftawar ido haka kuma kowa ya samu amsashoshin duban da aka yi masa.Ma'idah ta wani yi zumbur ta tashi zaune tana waro ido ganin an bata tarihin Heesham tun daga ranar da larurar ta same shi har aurensu da shi,da kuma matsalar da yake fuskanta.Gabanta na faWuwa ta danna wani jan layi inda aka rubuta in mutum na son kawo ?arshen damuwarsa ya danna nan,ta kuwa danna babu jimawa aka aiko mata da amsar da ta girgiza tunaninta. Dukkannin illahirin jikinta rawa yake, wannan ai tsafi ne  ta furta tare da son yi left daga group Win sai dai abu ya cuttura don da zarar ta goge sai ta ?ara ganinta ciki,da ta matsa kuwa sai ga kira ya shigo wayar mai Wauke da sunan group Win Ruhaniya......
*ZAWARCI*
BOOK 3

LoVe aNd HoRrOr StOrY &?

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI=ث?
'?)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS&?*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________


3_4


Wayar hannunta ce ta suSuce mata jin wata muryar marar daWin amo na ce mata  Barka da shigowa duniyar Ruhaniya,gidan wanke zuciya da biyan bu?ata.Hajiya Ma'idah ha?i?a kin yi jajirtacen aiki na ceta mijinki da kika,zai samu lafiyar dukkan matsalolinsa mun taya ki murna aikinki yayi kyau mun cika miki muradinkk saura ke ma ki ji namu,ohhhh sai mun sake zuwar miki a karo na biyu tsit muryar ta tsaya.

Ita kuwa Ma'idah ?uri ta yi wa wayar tana kallo cike da tsoro,tana cikin wannan yanayin sai ga Heesham ya shigo da sallama Wauke da bakinsa ,fuskarsa kuwa cike da annuri.

 Maaa...'idaaah! ya kira sunanta kamar mai koyon magana kafin ya ?araso ya rungume ta, kin ga na soma magana ,bakina ya buWe ya sake furta cike da tsantsar farin ciki.


 Mine ne? Ya na ga ba ki murna? Kuka kuma? Kukan mene ne? ya furta yana Wora ta kan cinyarsa ya soma share mata hawayen.Cike da tattali ya soma rarrashinta tare da furta mata kalmar so, tun ranar da na fara ganin ki na soma son ki ,na san ke ma kina sona ko?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login