Showing 99001 words to 102000 words out of 139076 words

Chapter 34 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

141

ne a jikinki! Kuma shi ne ke Wauke ni'imarki,don haka dole ki tashi tsaye.Ki nemi Musk tahara,da jan Musk ,da kuma musk A'isha sai ki haWe su da man habbatu sauda ki yi musu karatu a ciki na ayatul ?ursiyu,da amanar rasulu ke da duk wani abu da kika sani a cikin Alkur'ani tunda dukkansa waraka ne .In kin gama sai ki dinga dangwala auduga ciki kina shafawa a ?asanki


 Na gode sosai amma ya aka yi kika san da wannan?

Shiru na yi don ni kaina ban sani ba kawai dai na samu bakina da furta hakan,na basar na ce  ke dai magani kika ja kuma ga shi nan na baki ta ce  in sha Allah kuwa zan neme su daga nan ta dinga bani shawarwari da kuma wayar mini da kai dangane da daren farko na kuwa ci Wamara in sha Allah zan cire tsoron na bai wa Yaya Khaleed haWin kai mu yi komai cikin soyayya.


Abinci aka shigo da shi na kuwa zauna na ci don Allah na gani duk wata fargaba da nake ji ta gushe.A haka aka gudanar da walima har kowa ya watse,da ruwan Wumi na yi wanka na kwanta tun da wuri saboda gobe motarmu za ta cira zuwa Yamai.


?arfe biyu na dare aka tashe ni na ?ara yin wani wankan na kimtsa,dukkan kayana dama tuni an tafi da su.A falo na fito na samu mata biyun da za su yi min rakiya,Waya daga dangin Mama Wayar kuma ta wurin mahaifi.Cikin motar Daddy muka isa gida gidan Bus Win,sai kuka nake wanda tun a gida na soma shi.Har muka shiga ciki ban daina ba,sai a lokacin na ga Yaya Khaleed bai ce mini komai ba har motar ta soma gudu da mu.Babu jimawa kuwa bacci ya Wauke ni,ban farka ba sai da muka iso Maradi a nan duk muka yi sallar asubah kafin mu cira kuma.

Duk garin da aka tsaya sai Yaya Khaleed ya saya mana wani abu,a haka har muka isa .Wani abokinsa ne ya zo ya Wauke mu da mota,gidan da ya kama mana haya mu uku ne a ciki kowacce da lungunta an kewaye shi da katanga an saka murfi kuma.


?akin muka shiga ciki Waya ne da falo sai toilet,na Sata rai ina mai cewa  wannan Wan ?aramin Wakin Yaya Khaleed yayi min wani kallon ?asa-?asa kafin ya fice,duk wanka muka yi muka canza kaya kafin mu ci abinci da ya samo mana.Daga nan kuma suka hau gyaran Wakina wanda dama tun kafin mu iso motar katakaina da kujeru ta rige mu isa.
Har cikin dare ba su ida haWa komai ba,an dai saka kujeru da kuma gado inda abokan yaya Khaleed biyu suke taimaka musu.A gajiye duk muka yi bacci,sam bai kwana gidan ba tun da safe dai ya zo ya kawo mana waina da miya da kuma dukunu.Bayan mun ci ne suka hau aikinsu,cikin ikon Allah komai ya tafi daidai Waki sai ?amshi yake.Daga nan kuma suka wuce kasuwa,suka bar ni a nan ina raba ido ina kallon kayan.


Ina nan zaune ya shigo,na dube shi ina turo baki.Ticket biyu ya mi?o min ya ce  ga shi ki ajiye musu

 Wai kana nufin gobe za su tafi?
 Eh zaman mi za su yi
 Amma Yaya wannan kamar kora da hali ne fa

 Tun kafin mu tawo suka ce kwana biyu za su yi

 To ai kwanansu Waya

 Zan kawo gas sai ki Wora girki ya faWa yana mai ajiye tickets Win kan kujera ya fice.Ina nan cike da tsoron da tun a gida na yi ?o?arin binne shi ,amma yanzu ya dawo daram.A haka ya zo shi da wani abokinsa suka ha?a min tukunyar gas Win,ga kuma uban cefane duk sai na ruWe don ban taSa girki mai yawa irin wannan ba.

Abokin nasa ya fita daga cikin luguna,a shagwaSe na ce  saboda Allah ya za a yi na yi girki ni Waya?
Jawo ni yayi jikinsa ya ce  don Allah ki cire sakalcin nan ki yi girki mai daWi zuwa an jima abokaina za su zo

Ai kuwa na saka masa kuka jin wani zance har da bubuga ?afa,rarrashina ya soma yana ?ara min ?argin gwiwa tare da faWa min abin da zan fara yi.Muna a haka rungume da juna aka buWe murfin kewayena,har ta yi baya sai kuma Yaya Khaleed ya ce  ah shigo mana sai ya janye jikinsa daga gare ya fice bayan ya amsa gaisuwar matar ba za ta wuce shekara ashirin da bakwai ba.


Da murmushi kan fuskarta ta ce  ma?wabciyarki ce,kewayena ne na can ?arshe sannu da zuwa ya ba?unta?

 Alhamdullah shigo mana na faWa .
Ta ce  a'a dama dai na le?o ne na yi miki sannu da zuwa,na ji daWi sosai da na ji kuna Hausa halan ?ar maraWi ce ke?

Na girgiza kai na ce  a'a Zinder

 Allah sarki ni kuma maraWi,Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a Wayyiba

Na sunne kai tare da amsa wa da  Amen 

Har za ta fice sai kuma na ce  don Allah in babu damuwa ki taya ni girkin nan ban taSa yi ba
 Babu komai bari na canza kaya to


Ba ta wani jima ba ta dawo,a tare muka wanke kajin tasss sannan ta saka a tukunya ta zuba ruwa ta kunna gas ta Wora.Ta yanka albasa mai yawa ta saka kayan yaji,yayin da ni kuma na Sare tafarnuwa na wanke atarugu na saSa.?ar ?aramar cokali ta sa ta Wiba ta zuba a tukunyar,sannan muka hau gyaran karas,dankalin turawa da kuma albasar da za a yi miyar.

Tukunyar kajin ta sauke tana mai cewa  ina mai?
 Ai kuwa babu,kuma banda waya ballantana na kira shi.Yanzu ne suka tafi sayen Garar 

 Ok bari na Wauko ina da shi ta faWa tare da fita ta Wauko nata,haka ta soye kajin muna ta hira abin mu.
Can sai ga ?an sayen Gara sun dawo,sai a lokacin muka Wora tukunyar shinkafa.


 Oh muna ta aiki ban tambayi sunanki ba? na faWa ina dariya.
 Shafa'atu  ta bani amsa.
 Ni kuma Baseerat  ni ma na sanar da ita sunana,kafin mu Wora hira daga inda muka tsaya labarin Yamai ne take bani da irin yadda ta ci wuya farkon zuwanta don ba ta iya yarensu ba.


Sai bayan sallar la'asar muka ida girki ,na zuba mata nata miya daban ,shinkafa ma haka.Na zuba muka ci sauran kuma na juye cikin manyan kuloli,sai na je na yi wanka.


Bayan sallar magarib suka tattara komai nasu wai za su wuce gidan mota ,ina kuka ina ?ari wannan abokin Yaya Khaleed Win ya Wauke su da mota.Can uwar Waka na shige na kwanta,kaina ma ke yi mini ciwo.Ina jin shi ya shigo amma na yi banza da shi,samana ya zo ya kwanta yana min raWa a kunne kafin ya mi?ar da ni  mu je ki yi wanka ki shirya yanzu za su iso duk yadda na so turjewa amma sai da ya tilasta min yin wani wankan,mai kawai na shafa na saka wata shadda irin ta jikinsa.Hijabi na Wora a kai na Wauki turare zan fesa ya shigo ya karSe , ga su nan za su shigo ki fito falo sannan ki nutsu ban son shagwaSar nan

 To ka bani na fesa
 Tun da mahaukaci ne ni ko? Kin ga mu je ya ja ni zuwa falo tuni kuma abokan nasa sun gaji da sallama sun shigo.

Nan suka soma tsokanarsa suna cewa  hankali ya kwanta SEERAT ta zo Yamai  ya Wan dube ni,da sauri na shiga gaishe su suka amsa.Sai na rikice ganin duk kusan ni suke kallo,na yi saurin ri?o hannun Yaya Khaleed ganin shi ma zai bi ayari ya zauna cikinsu.Murya can ?asa-?asa na ce  don Allah ka mayar da ni can ?urya Waki
 Ki nutsu mana ,ki je ki kawo musu ruwa kamar na fasa ihu haka na ji,dakyar na iya sakin hannunsa na nufi table inda na ajiye ruwan da kofofi tun tuni .



 Matsalar auren ?waila kenan,Khaleed ka rasa wacce za ka auro sai baby? Wannan ai ba ta wuce raino ba muryar wani abokinsa ta daki kunnena.


 Kai Shereef haka kake komai Khaleed zai yi sai ka kushe shi muddin dai bai nemi shawararka ba

 Ai kuwa kusan duk manyan abokai haka suke fa

 Ni kuwa ina cewa in akwai ?anwarta na yi kame irin mai bi mata Win nan,ka ga nan da shekaru biyu sai a kawo min abata 

 Kai ma rainon kake son yi kenan ? da sauri na juyo jin muryar abokin nasa tun na farko da ya soma magana,wanda ake cewa shine babban abokin mijina mai suna Shareef.Ai kuwa muka haWa ido sai na ga yana yi min wani kallon mai saman ruwa,da sauri na ci gaba da aikina na zuba ruwan a kowanne kofi.Sai na yi tsaye ina tunanin yadda zan bi na bai wa kowa,sam banda wannan juriyar a shagwaSe kuwa na ce  Yaya tamkar Waukewar ruwa haka falon yayi shiru duk suka maido hankalinsu gare ni,yayin da fuskar SHAREEF ta yi ba?i ?irin muna haWa ido na sa ransa ya Sace.



Yaya Khaleed ya taso ya zo kusa da ni, mene ne SEERAT?
Idona suka ciko da ?walla na ce  kaina ke yi min ciwo sai nake jin kamar wani kusa da ni yana zuga ni akan na kunyatar da kai
Ya wani jawo ni ya manna a ?irji yana duban bayana kafin ya ce  Shuraim don Allah zo ka Wauki tray Win nan ka basu ruwa

Wanda ya kira da Shuraim Win ne ya zo ya Wauki ruwan,ina kallon ya bai wa kowa ya sha amma banda SHAREEF don bai karSi kofin ba.Da sauri na Soye fuskata a ?irjinsa ina tambayar kaina  shin mi na yi wa bawan Allahn can yake jin haushina? banda amsa.

Yaya Khaleed ya ja ni muka koma tsakiyar falo ya Wan saki murmushi ya ce  ku yi ha?uri Madam ba ta jin daWin jikinta ne har yau da gajiyar biki ga kuma ta mota ,sannan ga dadaWan girkin da ta yi muku sai suka hau shewa suna baban love.Daga nan ya ja ni zuwa Waki,kan bed ya shimfiWar da ni ya tofe ni da addu'o'i sannan ya fice ,na lumshe ido ina tunani iri-iri.



A can falo kuwa Khaleed na fita abokansa suka ci gaba da tsokanarsa,Shuraim ne ya zuba musu abincin dakyar Shareef ya ci shi ma don kar ace yana yi wa aminin nasa hassada ne.Bayan an ci an sha sai suka buge da yin hira,kaf cikinsu babu mai aure Khaleed ne ya soma.

?aya daga cikinsu ne ya ce  to mun ci abincin gidan Khaleed saura na gidan wa?

Shuraim yayi murmushi ya ce  ?ila Shareef don a yadda suke gasar juna ina jin ba zai iya ha?uri ba shi ma zai Wauko tasa amaryar duk sai kowa ya maida dubansa ga Shareef Win wanda ya kasa cewa komai,saboda tunani birjit da suke masa yawo a kai.Khaleed ya Wan murmursa ya ce  in sha Allah muna hanya za mu baku mamaki,kun san halin abokina komai nasa special ne kamar dai shi

Duk suka tuntsire da dariya ,don duk kowa ya san halinsa da tseko in abu ya burge mutane to shi in ya zo kushe shi zai yi.Sannan ra'ayinsa tamkar na Aljanu ne ya sha banban da na kowa,da za su tafi suka soma tsokanar Khaleed suna cewa  daga yau dai wani zai cire samartar shi

 Wa ya sani ma tun tuni ya cire Win

 Kai yadda amarya take garas Win nan ban ga alama ba,sai dai ko yau hahaha

 To me za a yi wa wannan Win saboda Allah? In mutum yayi ma mi zai ji? Ai sai dai raino Shareef ya faWa yana dariya,Khaleed dai bai ce komai ba don tun ranar da ya nuna masa hoton SEERAT har izuwa yau bai taSa jin ya yabe ta ba.

Shuraim ya ce  ?an shilla ai su ake yayi,amma ko da yake ban yi mamaki ba ra'ayinka daban da na mutane.Khaleed a kirawo Madam mu yi sallama ko?

 Ta yi bacci ku bar ta haka nan ta huta cewar Khaleed nan Win ma sai da aka samu masu yi masa iskanci,duk suka ajiye abin da suka fi ?arfi na kyautar amarya amma banda Shareef a haka yayi musu rakiya duk suka fita ?ofar gida.


 Wai yau ba za ka zo majalisa ba ne? cewar Shareef ganin Khaleed bai da niyyar bin su don tuni wasu har sun Wauki abin hawansu.
Shuraim ya ce  kai ma ta ya zai tafi ya bar ?ar mutane ita Waya? 
 Don na ga jiya a tare muka cika dare cewar Shareef yana son basar da damuwarsa.
Shuraim ya ce  jiya ai akwai waWanda suka rako ta,Wazu kuma na mayar da su can gidan Bus ka ga zo mu tafi mu ida sauke ha?in da ke kanmu
 Wane ha?i kuma? Shareef ya tambaya .
 Mu sayo kaza da fruits mana Shuraim ya faWa .


Khaleed dai bai ce komai ba,su uku Win abokan juna ne amma ya fi kusa shi da Shareef haka kuma sun fi saurin samun saSani , Shuraim Win ne ke shirya su .Mota suka shiga suka tafi,yayin da shi kuma ya koma ciki.Yana shiga kuwa ya tarar SEERAT na bacci,wurin da suka Sata ya share ya goge ya fesa turare sai ya zauna yayi shiru yana tunani.Tsawon lokaci kafin su dawo, TV ce Shareef ya sayo sabuwa dal wurin da aka tanada don Wora ta ya ajiye ta yana cewa  ga nawa tukuicin na amarya Shuraim ya ajiye ledojin hannunsa tare da cewa  zuwa gobe in sha Allah sai a kunna mu gani

 Wace gobe kuma bari dai na haWa na kunna yanzu haka Shareef ya kunna tv ta kuwa kawo daram, Khaleed ya soma yaba kyawunta da yadda take fitar da hoto kafin kace wani abu Shareef ya san yadda ya ja su da hira har suka zube kan kujeru ana kallo ana dariya har ?arfen biyun dare ta buga,Shuraim ne ya farga da sauri ya mi?e yana cewa  subahanallah ashe dare yayi sosai,Shareef tashi mu tafi kamar ya caka masa wu?a haka ya ji don takaici saboda shi bai ?i su kwana a falon ba,zama ya gyara ya ce  kai na ?i na tafin Win sai sauri kake sai ka ce kai ne angon

Khaleed dai murmushi yake duk da ?asan zuciyarsa ya so kasancewa da SEERAT amma ya bai wa kansa ha?uri da rareashin muradinsa da cewa akwai gobe.........



Nan free page na book 3 ya ida mai so za ta biya 500 ta wannan account Win 6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
```MRS SADAUKI=ث?
'?```


My book is only 500 via
6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,ko kuma katin MTN na 500? ?an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuWin karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne .

___________________
BOOK3

7_8


ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun dadi
*Zuzeam ventures* takawo muku babbar gara basa
Duka akan 6500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa =????=????=????=??<؁?=؃? ?

Wa.me/+2348144015291 For more information say hi =?K? Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku=؃?=؃?=؃? muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu

*DAHUWAR KAZA*

Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya*
Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta <؁? mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya*

*INA MASU JEGO DA AMARE*
Karku bari wannan dama ta wuceku
*08144015291*
Zuzeam ventures

ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1500kacal =?L?
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd
Maganin karin kiba
Maganin nono da hips
Rage tunbi da kiba
Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar g1da set
Mai jego set
Dadai sauransu.......


Cike da takaici da Sakin ciki Shareef ya bi bayan Shuraim suka bar gidan.Sai a lokacin Khaleed ya ja wata sanyayyar ajiyar zuciya.Da Wan saurinsa ya wuce bedroom ya zauna kusa da ita,cikin bacci na ji ana shafa ta na buWe ido da kyar na yi tozali da yaya Khaleed,ya sakar mini murmushi tare da cewa  tashi ki ci abinci kamar ya san yunwar nake ji kuwa,don tunanin kaWaici bai bari na ci abincin ba.Na tashi zaune ina kallonsa, je ki kuskure baki bari na Wauko sai ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ya fita ni kuma na sauka daga gado

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login