Showing 3001 words to 6000 words out of 139076 words

Chapter 2 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

147

shiga kan ki ne? Yanzu dai na baki minti goma ki tabbatar kin yi mata girkin abin da take so yana gama faWa ya yanke kiran.


Tamkar za ta fashe haka take ji,mai Wan sawu ma dakyar ta faWa masa inda zai kaita.Tana shiga gidan ta tarar da Mamuh zaune kan kujera ta Wora ?afa Waya kan Waya tana wani yamutsa fuska,gaban Sakeenatu ya faWi kamar kullum muddin dai za su haWa inuwa Waya da surukarta ta.

 Barka da yamma Mamuh ta faWa murya na rawa,Mamuhn ta ce  in kin gama yawon tanbaWar sai ki shiga kitchen ki girka min wake da shinkafa


Idonta tab ?walla ta shiga kitchen Win ta Wora tukunya ko kayan ba ta cire ba haka ta tsaya sai da ta tabbatar ta gama sannan ta zuba a plate ta kai wa Mamuh.
Da zafi da komai ta saka hannunta tana ci mai na bin hannunta sai wani lumshe ido take alamun yana yi mata daWi, Sakeenatu wacce ta tsaya don ganin ko yau ma Mamuh za ta yi irin yanayin nan sai kuwa ta ga ta yi.Idon Mamuh sai wani haske-haske suke fitar wa kamar kullum muddin dai wake da shinkafa ta girka mata.


A tsorace ta nufi Wakinta ,kayan jikinta ta rage sannan ta shiga toilet.Shower ta sakar wa kanta,kamar abun almara haka ta soma jin yanayin jikinta na canzawa tana jin feeling wanda kuma abu ne mai wuyar faruwa da ita muddin dai ba Abbas ke a wurin ba.


Abu kamar wasa amma sai yin gaba-gaba yake,kafin Sakeenatu ta farga tuni ta hankalinta ya soma gushewa ta dumulmiya duniyar son kasancewa da mijinta.Tamkar a mafarki ta soma jin kamar ana wasa da sassan jikinta,sai dai idonta sun yi nauyin da ba za ta iya buWe su ba ballantana har ta ga shin zahiri ne ko kuwa? Sama da minti goma tana cikin wannan yanayi kafin ta dawo hayyacinta,a doli ta tsarkake jikinta ta fito tana mamakin al'amarin.Bayan ta shirya tsab cikin riga da zane sai ta fito falo,Mamuh ta gani sai sharar bacci take kamar matatta .Dining ta je ta zauna ta buWe kulolin da ?ar aikinta ta yi girki,shinkafa ce da miyar kaji haka ta zuba ta soma ci tana mamakin yadda aka yi Mamuh ta zaSi cin wake da shinkafa akan lafiyayen abincin nan .Bayan ta gama ta Wauki waya ta kira Safeenat ta shaida mata za ta zo yanzu ,sai kuma ta koma Waki ta saka hijabinta ta Wauko jaka ta fito.Tana fita ba ta wani wuya ba ta samu Wan sawu ya kaita,da sallama ta shiga gidan har ta wuce can Wakin da Safeenatu take wanda ya cika da mutane kusan dangin Bashir ne.
A mutumce take gaishe da kowa amma yanayin jikinta na bata ana kallonta,tana juyawa suka haWa ido da Habibah wacce ta kasa Wauke idonta kan Sakeenatu har sai da ta ji ta tsargu.Ta zauna kusan Safeenat tana mai cewa  waccan wace ce sai kallona take?
 ?anwar Daddy ce fa ba ki gane ta ba? Feenat ta faWa tana mai mi?a mata boy bayan ta shafi kansa sai kuma ta ajiye shi aka mi?a mata girl Win.Wani irin shock ne ya ratsa Sakeenatu har sai da ta zabura,yayin da gabanta yayi mummunar faWuwa ganin Babyn ta buWe idonta tana kallon ta alhalin lokacin da aka mi?o mata ita tana bacci.Sakeenatu ba ta ida shiga tashin hankali ba sai da ta ga tamkar Babyn na yi mata murmushi......
*ZAWARCI*


LoVe aNd HoRrOr StOrY &?

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI=ث?
'?)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS&?*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________
23/09/24


4-5


Wani irin abu ne marar misaltawa ke ratsa Sakeenatu tun daga kan babban yatsan ?afarta har zuwa kwanyarta da ta soma toshe wa .Lamarin da take ji a al'aurarta kuwa kusan girme wa hankalinta ya yi,tamkar wacce ake fitar wa da wani dafi haka take jin ana yi mata motsi gami kuma da samun sassauci a doli ta lumshe ido ba ta shirya ba.Ita kuwa Gwaggo Habibah da ke can gefe sai murmushi take tare da yin zancen zuci don duk tana ankare da abin da ke faruwa. Tabbas a duk inda ke da mugunta da cutar wa Allah sai ya kawo mai ceto mai magani,na zo kenan a gidan nan mutuwa kawai za ta fitar da ni zan saka ido sosai akan jaririyar nan zan raine ta da hannuna ta yadda zan taimaka mata wurin fahimtar baiwar da Allah ya yi mata da yadda za ta sarrafa ta sai kuma ta mi?e tana yin wani murmushin nasara.Babyn ta Wauke daga cinyar Sakeenatu wacce gumi ya ji?a ta har goshinta na Wiga,babu kuma wanda hankalinsa ke wurin hatta ita Safeenat sai hira take da dangin mijinta waWanda suke cewa shi namijin a saka masa suna Bashir a yi madadi.


Sakeenatu ta ware idonta jikinta na Wan rawa kamar wacce ta farka daga mummunan mafarki.Idonsu ya sar?e cikin na juna,Gwaggo Habibah ta ce  sannu! Bari na nemo miki ruwa masu sanyi sai kuma ta shimfiWe babyn wacce tuni ta koma baccinta.


Kitchen ta nufa don samo ruwa masu sanyi,sai suka yi kiciSis da Gwaggo Hajara ?ar kallon-kallon suka yi kowacce na hararen ?ar uwarta.
 In tusa za ta iya hura wuta a yi mu gani mana,sai shegen kinibibi da nuna isa kan an san Soyayyar duniya nan kuma ba asss  Gwaggo Hajara ta faWa don kuwa a goshin Habibah ta fahimci sun karya wata muguntar tsafi.


Ita kuwa Habibar murmushi ta yi don ta fahimci mi take nufi wato in ta isa ta yi wa kanta maganin damuwarta. Nan gishirinki zai ?are a dafuwar ?aho,yadda bacci ya bar ido haka za ki gaji ki bar Habibah saboda kabewar kan kabari nake ba?in cikin masu taushe


 Aikin banza sai aukin cika baki ,a hakan kuma na yi sanadin hana ki baccin kullum cikin kukan kin ?i haihu ba

 Haihuwa ai ta Allah ce,kuma alhamdullah yanzu na samu irina wacce tsoron samun ta yasa kika jefo min mugun nufinki  Habibah ta faWa tana wani murmushi,Gwaggo Hajara ta kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa  ko ba ki gane abin da nake nufi ba? To Safeenatu ta haifi wata Habibar sak irina ce ko na ce ma ta fi ni don ita murucin kan dutse ce ba ta fito ba sai da ta shirya mu?ut! Gwaggo Hajara ta haWiye wasu yawun tsoro don kuwa ta fi kowa sanin babyn Safeenatu ba normal jaririya ce ba tun da ta ga zahiri.


Ta ja wani irin numfashi jin saukar ruwan sanyi kan fuskarta,dakyar ta ware ido tana kallon Habibah wacce tuni ta juya ta yi tafiyarta tamkar ba ita ce ta gama zuba mata ruwan a fuska ba.Cike da ba?in ciki ta koma Wakinta,a yadda take jin jininta ya hau in ba jini ta sha ba ?ila zuciyarta sai ta buga.Tukunyar tsafinta ta Wauko ta yi ?an surkullenta kafin ta Wauki mayafi ta fita waje,yara ta gani suna wasa daga inda take a tsaye ta soma kiran kurwar wani yaro cike da ?warewa wurin maita tsafi.Yaron ya dafe gefen wuyansa inda ya ji kamar an tsikare shi da allura amma bai bar wasar ba haka yake ci gaba da gudun yana son kamo wani,idonsa ne suka soma rufe wa kafin bugun zuciyarsa ya tsaya cak kawai sai ya faWi ga ?asa.Ita kuwa Gwaggo Hajara da wani mugun sauri ta rufe ?ofa,tuni yara sun fara ihu suna faman kiran sunansa.


?akinta ta koma ta ci gaba da tsotse jinin yaron ko jira ba ta yi ba,don ta san sarai in ta jinkirta ajiye kurwarsa Habibah za ta iya fahimtar haka.Tsawon lokaci ta Wauka cikin siffar mugunta kafin ta dawo normal,zuciyarta ta ji fayau babu ?unci.Tana nan zaune sai ga Munira wacce rabon ta da gidan tun lokacin da aka ce ta fita.Kusa da mahaifiyarta ta zauna ta soma bata labarin yadda yaron ma?wabciyarsu ya faWi suna tsaka da wasa, je ki nemo min Munir ya dawo gida  shi ne kawai abin da ta ce tana jin wani daWi a ranta ba don komai ba sai don ta yi mugunta.




Habibah na shiga ta mi?a wa Sakeenatu gorar ruwa mai sanyi haka ta shanye su tasss tana sauke ajiyar zuciya. Ki dinga kula da kan ki mana,ko barin kai a buWe ai yana sa ma?iya su yi galaba kanka

 To in sha Allah  Sakeenatu ta faWa tana mai Wan satar kallon jaririyar ?awarta,ido Waya babyn ta buWe ita ma tana kallonta babu shiri Sakeenatu ta mi?e tsaye tana cewa  Feenat zan tafi sai kuma gobe in sha Allah zan zo da safe tun da babu aiki
 Na gode sosai Keenat wai ina Ma'idah?
 Tana wurin Mama tun wancan satin na kai ta kin san Komandan ta zo


Safeenat ta waro ido ta ce  ki ce dai a takure kuke yanzu,kai tsohuwar nan an yi ?ar masifa mine ne na zuwa hutu ke ba ?ar makaranta ba

Sakeenatu ta tuntsire da dariya ta ce  kar a yi babu ita mana,duk gani take wasu kuWi ne da shi ba ta san rabin hidimar gidan ni ke yi ba a haka kuma za ta dinga tsiro da abubuwa tana saka sharaWin abin da take so


Safeenatu ta ce  ah lalle ta ci sunan Komandan Win nan dai suka yi sallama Sakeenatu ta fito.Kafin ta isa gida sai da ta saya wa Mamuh kifi don ta san tana son shi,da sallama ta shiga amma ta ?i amsa mata sai ma tambaya da ta jefo mata  daga gidan uban wa kike? Wato kin matsu na koma ?auye shi ne kika je gidan malamai da bokaye a yi min asiri na tafi ban shirya ba


Jikin Sakeenatu banda rawa babu abin da yake yi,kanta ?asa ta soma rantse-rantse tare da sanar da ita inda ta je.
 Ita ?awar taki ce ta baki magani kika yi wanka da shi ta yadda zan ji tsoron ki? Sakeena lalacewar taki har takai ki dinga faWawa ?awarki ?arya da gaskiya akan ta baki magani? In maganin za ki nema mi yasa ba ki ce a baki na haihuwa ba sai na korar ma?iyiyarki


 Wallahi Mamuh babu wani magani da aka bani,na faWa miki barka kawai na je Keenat ta faWa cikin muryar kuka.


Mamuh ta tsure ta da ido,sam babu tabon duk muguntar da ta ajiye a jikin Sakeenatun komai ya rushe ta koma normal.Sannan a baccinta aka nuna mata ta yi wanka da ruwan magani duk mugun nufinta ya fita daga jikinta,jin shiru yasa Sakeenatu ta Wago ido da zumar kallon Mamuh mugun ganin da ta yi ne yasa zuciyarta kusan faso allon ?irjinta ta faWo.


Idon Mamuh sak irin na maciji yanayin fuskarta ma ya canza duk ta yi ba?i, in kin gama gulmar sai ki wuce ki Wora min wake da shinkafa Mamuh ta faWa tare da yin gaba,Sakeenatu ta ce  akwai sauran na Wazu bari na zubo miki 
Ba tare da ta juyo ba ta ce  ban so wani nake so ki dafa min

Jakarta ta ajiye ta shiga kitchen ta Wora girkin,wannan karon ko waken ba ta wanke ba kamar yadda tsarin dafa shi ya zo mata daga Mamuh Win ,dama ita shinkafar ba irin wacce ake wankewa ce ba.Cikin plate ta zuba bayan ta tsalala mai dayawa,sai ta fito ta nufi Wakin Mamuh da sallama ta shiga duk da ta san ba za ta amsa ba.


Cike da ladabi ta du?a har ?asa ta mi?awa Mamuh plate Win wake da shinkafar amma ta ?i karSa sai ido da tsura mata.Tuni gaban Sakeenatu ya fara dukan uku-uku, ba zan ci ba!
 Amma ke kika ce na girka miki  ta faWa murya na rawa.
 Tun zuwana gidan nan na faWa miki sai an dirje wake an waken shi da hannu sannan ake girka min mi yasa yanzu ba ki yi ba?


 Na zata kina jin yunwa ne sosai shi yasa na yi haka don na yi sauri

 To sai ki je ki sake dafa wani Mamuh ta faWa tana mai mi?e wa tsaye,cikin dakiyar zuciya Sakeenatu ta ajiye plate Win ta ce  ki yi ha?uri Mamuh akwai aikin da nake son yi yanzu,ki ci wannan Win gobe in Allah ya kai mu sai na yi miki irin wanda kike so Win


Sam ko kaWan Mamuh ba ta yi mamakin furucinta ba ,don dama da tsafi ne ta ci galaba har Sakeenatun ke mugun tsoronta yanzu kuma komai ya karye.Ita kuma tana gama faWar haka ta fice,da ta fito har sai da ta ja ajiyar zuciya tana mamakin yadda yau ta cire tsoron Mamuh.
Tana shiga wanka sai ta ga period Winta ya zo,wanda kuma ba komai ya haifar da haka ba sai gwagwarmayar fitar da sihirin jikinta.Cikin ?ananan kaya ta shirya sannan ta haye bed tare da kiran Abbas,cike da nishaWi suka yi hirar soyayya nan ne kuma ya shaida mata gobe zai zo sannan a karSo Ma'idah don ita yake son fara cin karo.Har ?asan ranta ta ji daWin furucinsa , wannan yasa suna gamawa ta kira can gidansu ta ce a kawo mata Ma'idar.

Washegari
Kuwa tun safe Sakeenatu ta soma gyaran gida ita da ?ar aikinta wacce ba za ta wuce shekara ashirin ba mai suna Fa'iza.Mamuh dai na ta kallonsu ba ta ce komai ba don fushi take da Sakeenatu,da kanta ta yi girki Fa'iza na kama mata.

 Shi kuma waken nawa sai yaushe za a girka? Mamuh ta le?o kitchen Win tana mai faWar haka.
Sakeenatu ta ce  yanzu zan yi ba ta ?ara cewa komai ba ta tafi.

 Fa'iza wanke min waken nan da kyau sai ki girka wa Komandan ban son ta kawo min cikas ina cikin farin ciki

?ar dariya Fa'iza ta yi kafin ta soma wanke waken kamar mai wankin kaya,ita ce ta girka shi kuma.Sakeenatu ta zuba a plate da kanta ta kai wa Mamuh jikinta har rawa yake ta soma ci tana lumshe idonta waWanda tuni suka soma yin hasken nan.Ita dai Sakeenatu Allah na gani tsoron yanayin nan take ,da sauri ta wuce Wakinta ta yi wanka ta shirya cikin wani rantsatsen less tana tsaka da fesa turare Ma'idah ta shigo da gudunta ta na kiran Ammyna.Ita ma sosai ta yi kewar yarinyar sai ta rungume abarta tana cewa  ke da wa ne?
 Anty ta bata amsa.
A Wan firgice Nafisa ta shigo tana cewa  anty Sakeena wace ce waccan a kitchen? Zo ki ga abin da take
 ?ar aikina ce lafiya?
 Zo dai ki gani cewar Nafisar tana mai yin gaba Sakeenatu na take mata baya har suka shiga kitchen Win.
Fa'iza suka tarar duk ta cire suturar jikinta tana fitar da wani nishi idonta a rufe suna tsiyayar da hawaye.......
*ZAWARCI*


LoVe aNd HoRrOr StOrY &?

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI=ث?
'?)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS&?*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________
24/09/24


6-7


Tamkar wacce ke wata mu'amala da namiji haka Fa'iza ke yi ,hankalin Sakeenatu in yayi dubu to ya watse.Ta kalli ?anwarta ta ce  Nafisa ko iskokai ne? Dubi abin da take yi
Nafisa ta ce  anty Sakeena tun da nake ban taSa ganin mai kalar iskokan nan ba,hatta masu aljanin soyayya ai sai in suna bacci ne suke zuwar musu dubi ita wannan fa tamkar idonta biyu fa

 Yanzu dai don Allah ki taimaka mata tun da ke Malama ce kin ga Ma'idah har ta soma kuka cewar Sakeenatu tana mai jan ?arta zuwa waje.Nafisa ta cika kofi da ruwa ta tofa ayatul ?ursiyu da amanar rasulu sannan ta shiga watsa ma Fa'iza ruwan,a sannu a hankali ta soma barin abin da take daga ?arshe ta buWe idonta waWanda suka kaWa suka yi ja.Nafisa ta shiga yi mata sannu kafin ta taimaka mata ta mayar da kayan jikinta, dama kina da aljanu? Sakeenatu ta tambaya wacce ta dawo.

Fa'iza ta girgiza kai, to tashi ki yi wanka sai ki zo ki zuba abinci ki ci
Da  toh ta amsa kafin ta fita zuwa Toilet Win tsakar gida kamar yadda Sakeenatu ta shaida mata da ita za ta dinga amfani.
Wanka ta soma sai da ta saSa jikinta har sau biyu sannan ta fito,wasu kayan Sakeenatu ta bata ta saka abincin ma da ta zuba gidansu ta wuce da shi.
Su kuwa a falo suka zauna suna hira Nafisa na bai wa Ma'idah abinci a baki,Abbas yayi sallama da gudu ta nufe shi tana  Daddyyy ya caSe ta tare da cira ta sama yana yi mata wasa haWi da kai mata sumba.
Cike da farin ciki ya ?arasa ya zauna,Nafisa ta gaishe shi yayin da suke aikawa juna wani kallon so shi da Sakeenatu mai cike da kewa.
 Mu je ka fara yin wanka ko?
 A bani abinci tukuna don Allah  ya faWa yana wani murmushi,Ma'idah ta ce  Daddy ni ma ina ci sai aka zuba musu ya dinga bata a baki ita kuma sai surutu take yi masa.Suna tsaka da nishaWinsu sai ga Mamuh ta fito,fuskar nan kicin-kicin, ita kuma wannan farar tinkiyar? ta yi tambayar tana zunWen Ma'idah wacce ta tsorata da ganin Mamuhn.
 Ina wuni Mamuh? Fatan na same ku lafiya? Abbas ya faWa cike da ladabi.
 Ka bani amsa ta
 Ma'idah ce fa ?ar wurin Keenat ya bata amsa a sanyayye.

 Shegiya za ka ce wacce ba a san ta?amaimai wane ne ubanta ba,kai da ka iya kwashe-kwashe ka rasa wacce za ka auro sai wadda ta gama yawon duniya ta tsiyayar da duk ?waya?wayin haihuwarta a titi.To ban yarda ban lamunce wannan tinkiyar ta zauna a gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login