Showing 54001 words to 57000 words out of 139076 words

Chapter 19 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

108

madarkina,eh tabbas duk abin da ya faru yanzu na gansa sai ga shi kuma ya faru a gaske .Daga inda nake a kwance na ji tsayuwar mutum kusan kaina,ban Wago ba na dai kai dubana a wurin sai na ga ?afafuwan mace sun sha jan lalle ga kuma zanenta fari ?al.A hankali na soma Waga kaina har na sauke idona kan kyakkyawar fuskarta ta Fulani ta sha ado irin yadda suke zane da kwalli,tufafinta ma irin na Fulani ne.Kan gwiwanta ta zube tare da buWe bakina,gyanWamar hannunta ta buWe ta soma shayar da ni nonon shanu haWi da shafar gashina a haka bacci ya Wauke ni mai daWi.Muryar Kaka ce ta tashe ni da asubah na mi?e na yi sallah,bayan mun gama na zata bacci za a koma a'a sai na ga Samira ta Wauko allonta na jiya ta mi?awa Kaka ta ri?e yayin da ita kuma ta soma koro hadda abin da ke rubuce.Cike da burge wa nake kallonsu yadda da zarar ta faWi ba daidai ba ko ta cije sai Kaka ta gyara mata,na shagala sosai a kallonsu na ji muryarsa kamar daga sama . Irin haka nake son gani kin zama,ki yi ta aman ayoyin Alkur'ani ba wai shigar maza ba na Wago kai na dube shi,sai ya zabga min harara da sauri na sunne kai ina tunanin zuci  wato so yake na zama mahardaciyar Alkur'ani? Tabbb yo ina zan iya wannan.... tunanina ya yanke sakamakon gidanmu da aka shiga bubugawa ana jijiga ?ofar tamkar za a karya ta a shigo,sai muryoyin mutane ke tashi tsabar yawansu ba a ma jin abin da suke cewa.



Jikin Kaka na rawa ta tashi tsaye tana kallonmu ni da Khaleed kafin ta ce  fatan dai cikin ku babu wanda ya je wurin rijiyar Mayu ? a tare muka kalli juna,na yi tunanin zai rufa mana asiri amma kai tsaye ya ce  eh jiya ne da dare... ko kafin ya ida Kaka ta yi zaman ?an bori tashin hankali ?iri-?iri a fuskarta,Samira kuwa dafe ?irji ta yi ta ce  mun shiga uku


Kaka ta mi?e da sauri tana cewa  ko da an tambaye ku kun je kuce a'a ban son rigima da tashin hankali  sai kuma ta nufi ?ofar ta buWe tana mai aro jarumta da kawar da tsoron da ke ranta .Tana buWewa duk suka kutso kai cikin gidan,abin mamaki yawancinsu duk tsoffi ne babu matashi ko Waya haka kuma jinsi biyu ne maza da mata.



 Ina ce dai lafiya duk kuka yi ayari gidana? Kaka ta tambaya cikin Waga murya,wacce ta fi su kauWin baki ce ta amsa da cewa  yaushe kika yi ba?i ? Ba ma dai wannan ba sammaci muka kawo miki don haka mu haWe gidan mai gari sai ki tawo da tawagarki tana maganar ne tana kallon mu.


 To babu damuwa ku je muna zuwa Kaka ta faWa ,bayan sun gama ?an dube-dubensu suka fice,Khaleed ya ce  to wai laifin mine ne don mun je? 
 Ku shirya mu je gidan mai gari,ko an tambaye ku kuce ba ku je ba kun dai ji na faWa muku Kaka ta faWa ranta a Sace.Haka muka shirya muka nufi gidan mai garin,duk fadar tasa ta cika ma?il da mutane.Duk hankalinsu ya dawo kanmu musamman ma ni da hatta mai garin kafe ni yayi da ido kamar mai son tantance wani abu,Kaka ce kawai ta gaishe shi tare da zubewa ?asa yayi gyaran murya ya ce  ashe ba?i muka yi a garin?
 Eh wallahi jikokina ne jiya suka zo cewar Kaka.
Shi kuma ya ci gaba da cewa  to madallah Allah ?ara tsarewa,amma ki ja musu kunne a nan ?auyen ba ko ina ba ne mutum yake sa ?afa ba in ka je wani wuri ka fito wani wurin gawarka ce za ta fito,kai wani wajen ma ko ?asusuwanka ba za a samu ba.Kuna iya tafiya amma a kula sosai mai garin ya ida faWa yana kallona tsakiyar ido,sai na fahimci duk sa?on nan ni ce yake son isar wa da shi.Na saki murmushi na ce  ya mai girma mai gari in babu damuwa ina son zagaya garin nan sa?o da lungu don ganin Soyayyen sirrikansa da kuma.... mitsikar da Yaya Khaleed yayi min ce a gefen ciki ya saka ni yin shiru.



Mai gari ya ce  babu damuwa in kin shirya ko yanzu sai a haWa ki da dogari 
Kaka ta ce  a'a wasa take fa,ita da jibi ma za ta koma a dai yi ha?uri mun gode a huta lafiya sai kuma ta mi?e ta wani kama hannuna muka baro wurin,a kan hanya ita da Khaleed kamar za su cinye ni tsabar yadda suke yi min masifa shi don mugunta har kaina yake dungure wa.


Muna isa gida muka tarar Samira ta ci kuka har ta gaji,amma da ganinmu sai ta taso a guje ta rungume ni cike da murna tana tambayar abin da ya faru bayan mun je can.


Kaka ta faWa mata a ?arshe tana mai cewa  Khaleed ku haWa kayanku gobe tun carar zakara ta farko zan kai ku tashar mota
Ya harare ni kafin ya ce  to Kaka sai kuma ya nufi Wakin da aka sauke shi.


Wunin ranar haka na yi shi sukuku musamman yadda duk suka canza min,?arin takaicina kuma guda yadda na ga hankalin Khaleed duk ya koma kan Samira duk in ta mi?e idonsa na kanta,tsabar iya yi har da koya mata karatu yayi.Tun kiran sallar magrib na rakuSe can jikin bishiyar kurna da ke tsakar gidan,duk tsohon ?uncina,tu?u?i ba?in cikin da ya zamar min abokin hira a ko yaushe su suka taru suka yi min jagora na isa zuwa Soyyyen sirrina ko nace Soyayyar siffata wacce mahaifiyata da Gwaggo Hajara da Ammy Habibah suka yi ?o?arin binne wa don wanzuwar zaman lafiyar al'ummar gidanmu.Kururuwa haWi da hargagin dabbobi ta sa na mi?e a zabure na nufi hanyar fita daga gidan,malam buWa takarda ya ja ragamar ruhina na nushi dajin da aka yi ma la?abi da kogon mutuwa,tafiya ?asa tasa tafukan ?afata fashewa amma ko kaWan ban ji wata aba ba wai gajiya haka na ci gaba da kutsawa ciki har na isa ga wani kogo mai Wauke da wasu ?warin Wajin.Tamkar yadda in Wa ya ga uwarsa yake zuwa yayi mata oyoyo haka duk suka yaSe ni suna min kukansu na ?wari,kafin daga bisani su kama bandejin hannuna su soma jansa suna warware shi.Sama da minti talatin ana warware dogon bandejin wanda a ido za ka Wauke Wan guntu ne amma a baWini zai iya yi wa yaro riga da wando.Cire bandejin yayi daidai da ?ara tsananta bugun zuciyata wanda ba komai ya haifar da haka ba sai wankin ido da aka yi min nake ganin duk abubuwan da hankali ba zai Wauka ba.


Abubuwan da na nema a wurin mai gari sai ga su Soyayyar siffata na kawo min su daki-daki,duk wani lungun muguntar ?auyen taram nake ganinsa.Kamar tsuntsuwa haka na tashi na tashi sama, ban dira ko ina ba sai rijiyar Mayu wacce nan ne cibiyar muguntarsu.A inda nake tsaye ina hango duk abin da ke ?ar?ashin rijiyar,ba komai ba ne ciki illa tarin al'umma birjit suna cin ba?ar azaba.Tafin hannuna na hagu na haska duk sai mutnen suka yo sama suka fara fitowa daga ciki suna guduwa tare da nusar cikin gari a haka har kowa ya fito sai a lokacin kuma rijiyar ta kama da wuta duk wata powers su ta ?one.




 Laha'ilah! Ashe kun ganta fa nan zaune tana bacci muryar Kaka ta tashe ni ko kuma ta fitar da ni daga halin da ban san ta?amaimai mine ne ba.
 Wato duk ihun neman ki da muke kina ji? cewar Khaleed tare da finciko ni,na saki ?ara ina cewa  ?afafuna Kaka ta haska fitilar hannunta a tare duk suka Wauki salati kafin Khaleed ya saSe ni zuwa Waki.


Yadda Kaka ta rakuSe wuri guda sai ta baka tausayi,idona na zubar da ?walla Yaya Khaleed ke cire min ?ayoyi a tafukan ?afafuna da suka yi wata irin dauWa.Samira ta kawo ruwan zafi,haka ya dinga tsoma towel a ruwan yana gasa min ?afa,sai kuka nake ina faman kiran sunansa haWi da ri?e shi.




 Wai duk wannan mine ne Kaka? Na ga lokacin da muka neme ta muka rasa kin fita hayyacinki sosai tare da wasu lafuza da ban gane ba Khaleed ya faWa .
Ita kuwa ni ta duba tsakiyar ido ta ce  ina kuka je Baseerat ? Wane wuri suka kai ki? shiru na yi ban bata amsa ba ina tunanin duk abin da ya faru kafin na Wago hannuna na hagu wanda tun da aka haife ni yau ce ranar farko da na yi tozali da shi a haka babu bandeji.



 Wa ya cire miki? Khaleed ya tambaya yana kamo hannun,wani girrrr duk muka ji yayin da shi kuma yayi saurin dafe zuciyarsa yana mai kallona tsakiyar ido.

Yadda gari ya Wauki harama ne yasa duk suka fice tsakar gida,ina jin Samira na cewa  wuta ce ta tashi dubi yadda take fitowa daga bayan gari,ai wallahi sai na je na gani


An Wauki lokaci kafin su shigo,Samira wacce ta je ganin ?wam da ta dawo take cewa  Kaka duk yaran garin nan da suka Sata sune suka dawo,hatta ?an buWa ido ma suma ga su can duk sun dawo har da Kulu mai waina ma ta dawo,sai dai fa mai gari ya mutu haka ma Talle,da Saude da kande.... nan ta soma zanen mutanen ?auyen waWanda dukkansu Mayu ne babu na kirki a ciki.


A gabana Kaka ta ce Khaleed ya kira mata Ammy Habibah ,abu na farko da ta ce shi ne  alhamdullah! kafin kuma ta fita waje ban san mi suka tattauna ba.
Abinci Yaya Khaleed ya Wauko ya soma bani a baki yana kallona har sai da na ?oshi ya bani ruwa na sha,sai ya fice.Ni kuwa salloli nake son yi amma ban iya tashi,a nan na Singire na soma bacci.Bai yi wani nisa ba,na ga Bafulatanar nan kusan ?afafuna tana shafa min magani haWi da yi min murmushi, washegari ko da na tashi ?afar duk sun dawo normal na yi wanka da alwala na yi salloli muna gama cin abinci muka nufi tashar mota bayan Kaka ta bamu tsaraba mai yawa.Muna tsaka da gudu a hanya direba ya tsaya ya Wauki wani dattijo,tun shigowarsa na ji tafin hannuna na yi min ?ai?ayi.Gefen da yake na duba,sai na ga kusa da wata mace ce mai goyo yaronta na ta yin kuka sai ya fiddo ruwa gora ya ce  basa ya sha  ta karSa tana godiya sai dai yaron ya ?i sha,tana murmushi tace  dama tun Wazu nake jin ?ishi sai ta shiga sha shi kuma yana kallonta yana murmushi.Zama na gyara ina son ganin gudun ruwansa,ko minti Waya ba a yi ba matar ta cewa direba ya tsaya za ta yi fitsari.Bakin titi ya samu ya parker ta fita zane a hannu kamar fitsarin na son kubce mata,sama da minti goma ana jiranta har direba ya kai ga cewa  wai ina matar nan ne wata ta fita ta kirawo ta na so mi?ewa amma Khaleed ya zaunar da ni,wata ce ta fita sai ga ta kuma ta dawo hankali tashe tana cewa  matar nan fa tun da ta fita fitsari ne kawai ke shatata ya ?i tsayawa,kuma ...kuma ina ganin ruwan wannan mutumen ne da ta sha sai ta harare shi,tsoho yayi dariya ya ce  eh sosai kin yi gaskiya,muddin tana so ya tsaya doli sai ta zo ta saka hannunta ga al'aurata  .......
```MRS SADAUKI=ث?
'?```


My book is only 500 via
6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,ko kuma katin MTN na 500? ?an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuWin karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne .

___________________
BOOK2


8

Dukkan mutanen da ke cikin motar suka cika da mamaki jin wai fitsarin ba zai tsaya ba sai in har matar ta yarda ta taSa al'aurarsa.Tuni wasu sun fara zagin tsohon,wanda ya fi za?ewa shi ne direban motar cike da masifa yake cewa  yau na Wauko wa kaina masifa,kai daga taimako shine za ka jawo mana bala'i don ka cika tsohon Wan iska wanda bai tsoron Allah to wallahi haWuwa za mu yi mu maka shegen duka ko bakinsa bai rufe ba tsohon ya ?yal?yace da dariya tare da tofa yawunsa kan fuskar direban,sai ga direba ya koma mimi-mimi da baki amma muryarsa ba ta fita,ganin haka yasa duk mutane suka sha jinin jikinsu.Raina ne ya ?ara Sacewa,na yun?ura a karo na biyu amma Khaleed ya ri?e ni can ?asan ma?oshi ya ce  wai uwar mi za ki yi? So kike ki saka mu a matsala ne uhum? uffan ban ce masa ba sai kallon matar da na yi wacce har zuwa yanzu fitsarin sai zuba yake mata duk zanenta ya ji?e sharkaf,yayin da idonta ke ta tsiyayar da hawaye tana gwanjin kuka ?arta na kama mata.Zuwa wannan lokacin duk mun sauka daga motar,mun yi cirko-cirko kamar kaji.Da rairafe matar ta zo har gaban tsohon,a wannan karon cikin Waga murya na ce  Yaya Khaleed kana ganin fa matar nan taSa wa za ta yi kamar yadda ya bu?ata,ba zan bari hakan ta faru ba

Duk sai kallo ya dawo kaina,sai kubce-kubce nake amma Ya Khaleed ya ri?e ni gam a ?irjinsa,ina ji ina gani a gaban kowa tsohon nan ya since azargagin wandonsa matar ta kai hannunta za ta saka kenan na ture Yaya Khaleed ina mai furta  dakata! haWi da yin alama da hannuna na hagu wanda tuni kalmar M Win ciki ta fito raWau tana fitar da haske.Wannnan abin da na yi shi ya fitar da al'aurar tsohon ta dawo tsakiyar goshinsa,duk mutane suka ja baya suna  wayyyo! Tashin hankali! yayin da shi kuma tsohon ya shiga mummunan tashin hankali.A nan take kuma fitsarin matar ya Wauke Wif,hatta zanenta da ya ji?e sai ga shi ya koma ?amas babu lema.


 Mi kike yi haka SEERAT? Mi yasa za ki shiga abin da bai shafe ki ba? Kin san yin haka mi zai jawo miki ne? Mutane za su soma zargin ki ne Yaya Khaleed ya faWa yana mai ?ara finciko ni,na saki murmushi na ce  kowa ya shiga mota kamar masu jiran umarnina kuwa duk suka shiga suna waige na,matar kuma har da yi min godiya yayin da Baba tsoho ya zube a gabana yana bani ha?uri bayan ya cire rigarsa ya Waura a kai.



 Jikata ki yi min rai,ki tausaya min ashe sara na yi da mutum sama.Da ace na san kina cikin motar nan ko kusa da ita ba zan je ba,ki gafarta min don Allah  tsohon ke faWa yana kuka wiwi,na kalli Yaya Khaleed kafin na janye jikina daga nasa na shige mota shi ma ya take min baya ya zo ya zauna kusa da ni,haka shi ma Baba tsoho ya shigo motar yana kuka,don bai san kunya ba sai ya soma yi wa mutane magiya  ku taimaka ku saka baki ta mayar min abina wurin da yake,don Allah ku tausaya ki taimaki dattijo wanda ke kan gargadar mutuwa to kwana nawa ne ma ya rage min a duniyar


Lafuzansa sun fi komai ba?anta min a rai wannan yasa na ?ara tunzura na ce  ka san shekarunka sun ja shi ne kake mugunta? Wato kai ga matsafi za ka yi amfani da siddabarunka wurin sa mata su dinga biya ma bu?ata? FaWa min ma dai mine ne yasa ba ka yi aure ba in bu?atar mace kake? Wannan halinka ne da dukkan alamu ba yau ka saba yinsa ba don haka ka girbi abin da ka shuka na faWa tare da mayar da dubana kan windown mota,can na Wan Waga murya na ce  direba don Allah tu?a mu sauri muke da akwai abin da za mu yi motar ya soma ja,har zuwa yanzu an kasa samun mai jarumtar yin magana tsit kake ji kamar an yi ruwa an Wauke in ka fidda Baba tsoho da ke ta rantse-rantse haWi da alkawarin ya daina ba zai sake yi ba.Kanzil ban sake ce masa ba har muka isa tashar motar Zinder inda a nan kowa zai sauka,na Wan yi gyaran murya na ce  direba gidan sarki za ka kai mu, ke ma ki tsaya kar ki fita za ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a yi mana shari'a ne


Bayan kowa ya fice direba ya kai mu gidan sarki,zuwa wannan lokacin sai da tsoho yayi zawo a wando.Kowa ya san yadda Sarkin garin ke da tsatsauran hukunci akan azzalumai musamman ga Mayu ko kuma masu muguntar ire-iren haka.Khaleed ?in fita yayi sai mu uku kawai muka je,matar ce ta yi wa wani dogari bayani kafin ya yi mana iso har can fadar sarki.Nan Win ma sake jaddada ma sarki duk abin da ya faru ta yi cikin kuka,abu na farko da sarki ya ce  mayar masa da maganarsa ?iri-?iri babu kunya tsoho ya ce  to sai ya tofa wa direba yawu a fuska raWam muryarsa ta dawo ya soma yi wa sarki godiya.Sai a lokacin kuma sarki ya maido dubansa gare ni ,na yi saurin sunne kaina amma tambayar da ya jefo min ta saka na Wago a razane muna kallon juna ido cikin ido .


 Ke mayya ce? Sarkin ya sake tambaya ta yana turni?e fuska,zuciyata na ji tana tafasa sosai dakyar na buWe baki na ce  in ita ce mi za ka yi min? daga bayana na ji saukar dorinar dogari har sau biyu ya tsala min ita yana cewa  ki gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login