Showing 78001 words to 81000 words out of 139076 words

Chapter 27 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

144

san juna da shi,kamar wacce ke son kama fara haka na ware tafin hannuna a hankali shi kuma ya rage girma ya zo ya shige.Ido na tsura masa ina sauraron jawabin da yake min na shine mai Webe min kewa sannan kuma abokin aikina wurin kawar da magauta.



Can falo na jiyo sautin ihun Murjanatu tare da wata murya na cewa "tun da uwarki ta yi silar mutuwar ?ar uwata wallahi ke ma sai kin mutu"da sauri na nufi falon Rahamu ce tsaye kai ga anty Murjanatu tana zuke kurwata tana Wura ta cikin wata butar shayi,tuni na makara don kuwa babu abin da zan iya yi wa Murjanatun a halin yanzu amma ba zan ?yale Rahamu ba wannan ya saka na jefa mata macijin hannuna shi kuma kamar jira yake ya ciro dukkan idonta biyu ta yi kara tare da sakin butar shayin sai dai ba ta kai ?asa ba sar?ar wuyana ta kara tsayi kifin nan ya hadiye butar .Na nufi Murjanatu ina kiran sunanta amma tuni rai yayi halinsa,daga bayana na ji muryar BASHEER na cewa "ta fa mutu"furicinsa yayi daidai da shigowar Daddy.



 Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un ! shine abin da DADDY ya ce kafin ya zo yana duba anty Murjanatu,muryar Basheer ce ta sake Waukar amo  amaryarka ce ta kashe ta,ka ganta nan kwance ta suma nan hankalin Daddy ya ?ara tashi cike da takaici ya ce  yaushe na auri wannan Win? sai dai ba mu basa amsa ba.Babu jimawa yaransa suka shigo,wasu suka ciciSi Murjanatu wasu kuma Goggo Rahamu  ku wuce da ita can gidan sarki tun da mun yi magana da shi yana maganin tsageru irin ta Daddy na gama faWar haka ni ma na take musu baya zuwa can gidan sarki.


A bakin ?ofa na ji an kira sunana na waiga sai muka haWa ido da matashiyar budurwar nan wacce farkon zuwana Mama Salmu ta umarce ta da ta kawo min abin motsa baki.Murmushi ta sakar min kafin ta ce  tun Wazu nake ta jiran dawowar ki a nan


Na dube ta da Wan mamaki na ce  kamar ya?

Ta ce  eh na san za ki dawo ai
Jin haka yasa na gyara tsayuwa na ce  ya aka yi kika sani?


Ta ce  saboda na ga hakan ne a tattare da ke Wazu da kika zo nan
 Wace ce ke? na jefo mata tambayar ina saka idona cikin nata sai dai sam na kasa ganin allon sirrinta.
 To ni kaina dai ban sani ba,kawai abin da zan iya cewa shine in na kalli mutum ina gane wasu abubuwa dangane da shi


Na jinjina kai ina mai ci gaba da kallonta,ita kuma kamar wacce aka tsikara ta soma bani labari.

 Ina da labarai da yawa a duniya, wata rana ina wanke farantin da na ci abinci kusan pampo, sai na ji wata murya da ta yi magana a kunnena tamkar ta wani matashi da na taSa gani a hanya,muryar umarni ta soma bani kan na je na gidan ma?wabciyar mu da ta haihu na faWa mata kar ta ci naman da wata za ta kawo wurinsu domin idan ta ci wannan za ta rasa gidan aurenta mijin zai kore ta. Amma sai na ?i tafiya saboda tsoro kuma ban Wauka maganar gaskiya ce ba sai washegari da na ji an ce wai mijin ya kore ta


Na ce  to don me ba ki je ba?

 In na je na faWa mata kamar na cakawa kaina wu?a ne don ba lallai ta yarda ba,kuma in ta tambaye ni wa ya faWa min mi zan ce mata?

 Amma bayan nan bai sake zuwar miki ba? Ina nufin muryar?

 Bayan nan ina ganin abubuwa da yawa masu hana ni samun rayuwa ta normal mutane, a duk inda nake ina ji ko tsammanin cewa wani marar ganuwa wanda ido basu iya gani yana kula da ni, kamar dai akwai tashoshi biyu da ke magana da ni a cikin kwanyata haka kawai sai in ji ina karanta tunanin mutane .Hakan sai ya bani sha'awar fara rubuta littafi game da mafarki da duk abin da nake gani


 Zan iya ganin littafin? na tambaye ta,sai ta girgiza na ja tsuki na ce  to uwar mi zan yi miki da kika wani tsaya jira na?

Murya na Wan rawa ta ce  ki yi ha?uri na ga kina kama da matashin saurayin nan ne da muka haWu a hanya kuma wallahi muryarsa ce ke yi min magana a kullum cikin kunne

Kallonta kawai na tsaya yi jin wani zance kafin na ce  siffanta min shi ya yake? ai kuwa ta soma zayyano sifofin BASHEER,na taSe baki na ce  ban san shi ba sai na yi gaba abina.Ko da na isa fadar sarki tuni Goggo Rahamu an farfaWo daga suma sai dai babu idanu sai kuka take tana yi wa sarki bayani  na tuba don Allah kuma ka duba duk jikina babu wata ?wayar maita,dama fansa na zo Wauka da suka kashe min ?ar uwa ban taSa sanin cewa mutuwata ce na zo wurinta ba


Daga bayanta na ce  ya aka yi har kika auri Daddy shi nake son sani wannan dalili yasa ma na zo nan Win

 Baseerat zo ki zauna nan sarki ya furta yana mai nuna min kujera,tsabar iya yi dogarai biyu Win nan da na koyawa hankali wancan lokacin har da yi min kirari.Sai yanzu na gaishe shi tare da zaunawa,sarki ya ce  yau Princess za ta yi shari'a don haka ki yanke mata hukunci

Na saki murmushi na ce  a kaita can a rufe har wani lokaci  ai kuwa suka ja ta ?iiii kamar wasu kayan wanki.Sarki ya ba kowa umarnin fita, ina ta jiran ki amma shiru ba ki dawo ba ya furta cikin wata murya yana kallona.Na sunne kai ina murmushi,daga bakin ?ofa jakadiya ta soma kirari kafin ta ce  uwar Magaji na son ganawa da mai martaba
 Bismillah shine abin da Sarkin ya ce,na Wago kai na sauke idona kan gimbiyar nan sai wani shan ?amshi take tana turo ciki gaba.

 Ina son yin magana da kai ne Daddyn Prince mu biyu kawai ta furta tana wani yi min malalacin kallo,da sauri na mi?e ba don tsoro ba sai don saboda kar ran sarki ya Sace.Bakin ?ofa na tsaya ,tsawon lokaci kafin ta fito tana hurar hanci jakadiya ta take mata baya.Sai da na bari sun yi nisa sosai sannan na ware tafin hannuna na zarge ?afafunta ta faWi timmm da ?asa kuma bisa cikin.Na saki murmushi tare da fita,sai a lokacin kuma na nufi asibiti ganin Yaya Khaleed sai na tarar ma an basu takardar sallama Mama na gangamar kaya.

Tsaye kawai na yi ina kallonsa ina jin sonsa na tsikarar zuciyata,da sauri na sunne kai ganin ya tawo. Daga ina kike? ita ce tambayar da yayi min.
 Gida na basa amsa, na sani! Amma kafin ki zo nan nake nufi 
Na Wago na dube shi,ya zabga min harara kafin ya ci gaba da cewa  wannan kayan ban hana ki saka su ba?
 To ai banda wasu
 Zan Winka miki,sannan wannan sar?ar ta wuyanki ban son ganinta ki cire ta shiru na yi kawai, ko ba ki ji ba?
 Na ji zan cire in sha Allah 

 Ban gane za ki cire ba? Wato ba ma yanzu za ki fitar da ita daga wuyanki ba? ya faWa kamar wani ubana.Na turo baki tare da kai hannu na cire ta daga wuyana,ya buWe tafin hannunsa duk da na fahimci abin da yake nufi amma sai na ?i Wora masa sar?ar.


 Mu je kuka yi tsaye kamar sojoji cewar Ammy Habibah.Yaya Khaleed ya kama hannuna ya murWe tare da ?wace sar?ar,idonsa kamar zai faWo tsabar yadda yake harare na.


Waje muka fita,sai na ga ashe bazawarin Mama ne zai kai mu gida.Yaya Khaleed ya shiga gaba mu kuma a baya ,ko da muka isa har an ha?a rumfa a ?ofar gida  mike faruwa kuma nan? Mama ta tambaya.
Kai tsaye na bata amsa da  anty Murjanatu ce ta rasu
Duk suka fara salati,muka fita muka shiga ciki nan dai Mama ta yi ta kuka kafin wani lokaci mutane sun fara shigowa gefe guda kuma an Wora tukunyar abinci.
Ina nan zaune na ga Basheer ya shigo yana harare na,da mamaki na dube shi ina yi wa kaina tambaya  to laifin mi na yi masa? sai dai banda mai bani amsa.

A ranar aka sallaci gawar Murjanatu an yi zaman makoki kuma da addu'ar uku du a ranar.Da dare ina kwance ina tunanin da ya aure ni na Yaya Khaleed kawai na ji an yi kutufo da ni har sai da na zabura na tashi da sauri,ido huWu muka yi da Basheer sai cika yake yana batsewa .Ban kai ga yi masa tambaya ba ya wani finciko ni ya sha?e min wuya sosai,muryarsa cike da Sacin rai ya soma magana  saboda iskanci da ba?in ciki irin naki kin kasa cika min burina,wato da ta zayyano miki siffofina maimakon ki tabbatar mata cewa ni Win Wan uwanki ne amma kika gwasalar da ita


 Kai sake ta Muryar Yaya Khaleed ta furta,a hassale ya ce  ka san laifin da ta yi min ne kake wani cewa na sake ta?

 Umarni ne ba shawara ba Yaya Khaleed ya sake faWa , Basheer ya ture ni da ?arfi har sai da na faWi kafin ya fice. Ina son sanin sirrin da ke ga wannan sar?ar wuyan naki  ya faWa yana kallon wuyana,da sauri na laluba ina mai cewa  amma ai tana gare... sauran maganar ce ta ma?ale jin sar?a daram a wuyana.

Yadda ya doso ni gadan-gadan yasa na yi saurin tashi da sauri,yana isowa na faWa jikinsa na ?an?ame shi.Duk da ina jin yadda yake kokowa da numfashinsa hakan bai sa na janye jikina daga nasa ba,ban yi hakan da wata manufa ba sai don kar ya dake ni amma sai abun ya haifar masa da matsala.Muryasa na sar?ewa yake cewa  SEE..R..ATH don Allah ki bari ina jin wani iri


 A'a za ka dake ni ne kuma ban so na faWa ina cusa fuskata a ?irjinsa har ina jin yadda gargasarsa ke zuzar fuskata.Numfashi ya soma saukewa akai-akai,da dukkan alamu jikinsa yayi sanyi bai da ?arfin cire ni.Aka turo ?ofa tare da furta  innalillahi na shiga uku ni Habibah


Sai a lokacin na sake shi tare da rugawa da sauri na nufe ta ina cewa  don Allah Ammy ki ce kar ya dake ni amma ashe gudun Gara na yi na faWa gidan zanzaro,wani uban dundu ta yi min tana cewa  in na sake ganin ki da shi sai na karya miki ?afa na fita a guje ina kuka,ina fita tsakar gida kamar dama zaman jirana yake sai na ji ya dam?o ni  don ubanki ko ki koma ku yi magana ke da Hawa'u ko kuma wallahi na yi miki lahanin da ba ki taSa zato ba

 Wace Hawa'u kuma? na tambaya a wahalce.
 ?ar sarki mana
 Ina ka san ta?
 Babu ruwanki ki yi kawai abin da na ce
 To na ji gobe zan je na kawo ta har nan gidan cike da murna Basheer ya sake ni ya fice.Na bi bayansa da kallo cike da mamaki ,ina nan tsaye na ji muryar Khaleed  ki koma ciki

 Ina za ka je? na jefo masa tambaya, gidan Hajiya  ban ?ara ce masa komai ba na wuce.Hankalin Ammy Habibah na kaina da zarar mun haWa ido sai ta harare ni,da na gaji da ganin haka kawai na shige Waki na haye gado.


Washegari ta kama ranar alhamis ba muda cours tun safe wannan yasa da na gama sallah na yi kwancina,sama-sama nake jin Ammy na shaida wa Mama yau za ta je sayen trolly da kuma kayan lefen yaya Khaleed.
 Haba don Allah Goggo yanzu don ya ce aure zai yi sai biye masa? Duka-duka nawa yake?  Mama ke faWa .

 Wata mai kamawa zai shiga shekara ta ashirin da biyu,gwara dai a yi auren hankalina zai fi kwanciya.Kullum cikin yi min ?orafi yake ,sau biyu kuma ina ganinsa da Baseerat sun yi kusanci dayawa 

 To amma ai aikin soja zai shiga

 A'a na hana,na ce dai yayi Wan sanda tuni Yaya ?ayyabu ma ya kai takardunsa
 Allah ya nuna mana
 Amen ya Rabb,gobe za a Waura aurenki bayan sallar juma'a mijinki kuma ya ce ranar Litinin za ku wuce can Cotonou

 Ya faWa min Wazu,amma ina ta tunanin barin BASHEER a nan Win

 To ni mine ne amfanina ? Wurina zai zauna mana kafin Yaya ?ayyabu ya auro wata

 Hum! Allah sa dai ta ukun ba mayya ba ce

 In ma ita ce za ta koma da sharrinta.... ban sake jin hirar tasu ba saboda bacci,?arfe takwas ta gota Mama ta tashe ni na yi wanka na shirya cikin uniform Win makaranta.

Ina fitowa falo na ga yaya Khaleed a zaune yana shan tea,muna haWa ido ya ajiye kofin.A sanyaye na isa wurinsa, babu gaisuwa? ya furta,na Wan turo baki tare da waigawa baya na ga babu kowa sai na du?o na ce  yau Ammy za ta je sayo akwatinan aurenmu

Ya saki murmushi ya ce  wa ya faWa miki? ban basa amsa ba sai Wan madaidaicin gemunsa da na ja tare da ficewa a guje.Ina isa makaranta sai na ga yau Ubaidah ta zo,da murna muka rungume juna ina mai cewa  ya jikin naki?
 Da sau?i alhamdullah! Amma tsoro nake ji kar ?an aji su yi ta min iskanci 

 Ke manta da su mu je

 Malam fa ya mutu
 Yaushe?
 Jiya da dare,duka gangar jikinsa ta zuganye
Na yi murmushi kawai,da muka isa can aji haka ?an gulma ke kallonmu amma na ce Ubaidah ta share su.Haka muka yi cours har muka tashi,ina fito bakin ?ofa na ci karo da Hawa'u tana jirana.Na Wan taSe baki na ce  wannan Win ma kin gansa?
Kai ta jinjina min ta ce  eh za mu je gidanku kanzil ban ?ara ce mata ba har muka isa gida,Basheer na zaune kan kujera a tsakar gida yana ganin mu ya tashi tsaye ita kuma murmushi ta saki.Ban bi ta kansu ba na bar su nan na wuce ciki,na tarar da Mama ta shafa dilka ta gyaran jiki na dubi ?ofar kitchen na ce  Allah sarki anty Murjanatu Allah ya ji?an ki sai kuma na shiga na zuba abinci na ci na ?oshi sannan na wuce Waki na cire uniform na yi wanka.Na haye bed ina tunanin dalilin da yasa sam Bafulatana ba ta kawo min hira ba,bacci ya Wauke ni nan na ci karo da ita kuwa a mafarkina fuskarta kicin-kicin alamun fushi.Ba ta ce min komai ba har na tashi,na yi wanka na yi sallah.


Dab da magrib Ammy Habibah da wasu ?awayenta biyu suka shigo gidan da akwatina ma?il da kaya.Sai da Daddy ya zo da Hajiya sannan aka buWa su,ina daga can gefe ina hange komai masu kyau ne da tsada daidai ?arfinta.

 Yanzu dai har a gama na goben in hankali ya kwanta sai a je can a kai gidan dangin mahaifinta cewar Daddy.
Ammy Habibah ta ce  tun jiya mun yi waya da Kaka duk na shaida mata komai,har da auren Safeenatu ta ci kuka ta kuma yi murna tare da addu'o'in fatan alkhairi 

Hira sosai aka yi akan kan lefen nan,abun mamaki sam yau Yaya Khaleed bai zo da dadare ba.Washegari tun safe aka soma shirin walimar bikin Mama,dangi duk sun zo ni ma sai na ?i tafiya makaranta haka na zauna har da yin lalle da wankin gashi .Bayan sallar juma'a aka Waura auren Mama da likitanta,sosai aka yi walima mun ci mun sha.



Kamar kuma yadda aka tsara ranar Litinin ya zo da mota aka tafi da Mama sai kuma dangin Momah su biyu waWanda za su yi mata gyaran Waki.Sosai na ci kuka saboda Ammy Habibah ta hana a tafi da ni,a kuma wannan ranar ce aka kai lefena can wajen dangin mahaifina wanda ban taSa gani ba sai a hoto.Duk yinin ranar na yi shi ne a Waki a takure,sai yamma lis ?an kai lefe suka shigo suna guWa suna cewa aure ya Wauru.Hawaye suka zubo min masu game da farin ciki lokacin da wata ke cewa  an riga an Waura an tsayar da biki kuma nan da shekara Waya da wata biyu lokacin shi angon ya gama karatun aikin Wan sandar da zai yi

 Allah ya kai mu ai kamar gobe ne wannan karon muryar Ammy Habibah ce,wacce tsantsar farin cikinta har kana jinsa a muryar.
 Amarsu Basheer ya furta yana murmushi,na dube shi sai kuma na yi saurin cire bargon da na rufe na je na rungume shi na fasa kuka.Dariya ya shiga yi har da ?yar?yatawa kafin ya ce  ke duk kukan nan fa ba zai sa na ji tausayin ki ba gwara ma ki bari

Na Wago na dube shi na ce  Mama fa ta tafi

 Za mu je daga baya kar ki damu,ni yanzu yunwa nake ji wallahi
 Bari na samo ma abin da za ka ci
 A'a kar ki fita akwai mutane sosai,bari na je da kaina sai kuma ya fice.Haka na zauna ni Waya na tsawon lokaci kafin Ammy ta shigo hannunta ri?e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login