Showing 90001 words to 93000 words out of 139076 words

Chapter 31 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

121

ba sai da na ga a ranar ana kwashe kayanmu wai za mu koma sabon gida,duk yadda nake son yin tunani kuma na kasa a doli na biye musu muka dawo nan gidan yana kawowa nan sai yayi shiru yana kallon matar da ta yi min tsawa Wazu,ya nuna ta da yatsa ya ce  Ga Naylar nan,tun bayan zuwanmu nan gidan take tunzura ni auren zawarawa,auren kuma duk yayi tsayi bai wuce wata uku sai matar ta mutu kun ga duk mutanen nan da kuke tunanin ahalin gidanmu ne? To duk ni nan na aure su dukkansu zawarawa ne babu wacce ta taSa haihuwa,sannan mazajensu mutuwa suka yi ba wai saki ne ya shiga tsakaninsu ba.Da na fahimci Naylah muguwa ce na so fasa aure-auren nan ne fa ta shaida min da cewa ba zan sake ganin iyayena ba muddin na daina,ina sonsu sosai shi yasa na ci alwashin zan yi komai muddin dai zan dinga ganinsu


Cikin ?araji Naylah ta ce  yadda na ci alwashi dole na cika burina,ba zan taSa barin wata bazawara a doron duniya ba tana kukan mutuwar mijinta.Dole ne ta shigo duniyarmu don haka Safeenatu ke ma sai kin mutuuuu  ta yi furicin tare da yin wani tsalle ta dira gaban Mama ta Waga wu?a za ta caka mata , Bafulatanata ta bayyana ta ri?e wu?ar tare da Wauke ta da wani gigitacen mari har sai da ta zube ?asa  Naylah don mijinki ya mutu kin shiga ba?in ciki da damuwa,kika kasa ha?uri kika kashe kan ki kin yi tunanin dukkan mutanen duniya haka suke ? To duk wannan iskancin naki zai tsaya a yau za ki koma makwancinki ke da duk waWannan fatalen da kika cika a gida sannan Dr Mu'az zai fita ya koma rayuwa cikin mutane Bafulatanata ta faWa ,daga ni sai BASHEER kawai ke iya ganinta sai kuma fatalen Mama da Dr Mu'az kuwa iya muryarta kawai suke ji.


 Ba zan koma cikin kabari ba,ko na shiga sai na fito Naylah ta faWa cikin ?araji.Bafulatana ta yi murmushi tare da kiran sunana  SEERAT vash shiru na yi ina tunanin  mi ma kalmar VASH ke nufi?  can na samo tana nufin Walasiman esprit Win cikin ruwa,na same su ne lokacin da na nitse a ruwa.Bakina har rawa yake wurin soma karanto su,nan ruwa suka soma SulSulowa ta ?asa Bafulatana ta ce  Basheer gare ka ko baki ba ta rufe ba ya buWe bakinsa yana hura iska duk wani rufin Wakin da kuma bangunan suka soma rushewa suna nitsewa cikin ruwa kafin ?yaftawar ido komai ya shafe kamar ba a taSa ?awata gidan ba.Kabaruruka ne suka fito ta ko ina,Mamy da Papy da sauran duk fatalen wurin masu siffar mutane duk suka koma makwancinsu sai Naylah uwar taurin kai saboda ita tana da power sosai.Bafulatana ta dube ni,na sakar mata murmushi tare da ciro sar?ar wuyana na cilla jikin Naylah,kifin nan ya haWiye Naylah na du?a na Wauki sar?ata na mayar.


Bafulatana ta Sace, Basheer ya dawo normal,Mama da Dr Mu'az suka fara ?ar kallon-kallon kafin Mama ta yi luuu ta za ta faWi yayi saurin taro ta.
 Mi muke tsakiyar ma?abarta? Basheer ya tambaya yana wani karya wuya,ban basa amsa ba sai wurin Mama na nufa ina kiran sunanta.

Basheer ya matso ya ci gaba da tambayata  Wai mine ne ke faruwa? Ni na kasa tuna komai,wai ba .... cike da masifa na katse shi  don Allah ka rufewa mutane baki kana yin wani abu tamkar ba ka san kai Win wane ne ba,da wannan banzan surutun da amfani ka yi da powerka ka hura mu can cikin gari nan dai ai ka ga a dokar daji muke

Murmushi yayi ya ce  wato yanzu kin fahimta na buge masa hannun da yake jan hancina.Ina shirin sake yin magana Basheer ya hura mu kamar ?yaftawar ido sai ga mu a cikin wata harabar asibiti,Dr Mu'az ya saSi Mama da sauri ya shiga ciki ni kuma dube-dube na soma ta inda BASHEER zai Sullo.Kamar minti biyu sai ga shi ya tawo ?afafunsa duk sun yi datti,na dube shi na taSe baki kafin na wuce gaba ta take min baya.Tuni an karSi Mama an soma yi mata aikin,kan kujeru muka zauna Basheer ya rage sautin muryarsa ya ce  SEERAT dubi wata budurwa can wallahi duk ciko ne ta yi ba hips Winta ba ne ko na nuna miki ki gani?

Na girgiza kai ina murmushi ba tare da na basa amsa ba,ai kuwa ya hura mata iska rigarta ta yi sama ta saki ihu tana tattare rigar ta mayar daidai.Basheer ya ?yal?yace da dariya ya ce  kin gani ko? na jinjina masa kai, to kar dai ki yi koyi da ita babu kyau,maza ba su so a cuce su sai an yi aure suka ba haka ba a ta yi wa matan wula?anci.Amma ko da yake ke duk Yaya Khaleed ya gama gane miki jiki

Na haWe rai na ce  wai Basheer mine ne haka? Duk ya ake yi kake sanin haka? Kenan bibiyata kake? kai ya girgiza ya matso kusa da ni sannan ya ce  ?ar Bafulatanarki dai ce matar Alhajin cikin kwanyata kin ga duk abin da kuka yi zan sani,ke ma nan fa in na yi wani abun sai kin sani

Shiru na yi ina nazari,amma ya ?i bani damar yin tunanin ya ce  ke wasa fa nake,babu abin da za mu sani kawai dai saboda Bafulatanata na mitar cewa kullum Khaleed na manne da ke ba ta samun damar zuwa wurin ki haushi yake bata shi yasa ni ma na sani.Kullum ai suna yin hira da mijinta,kin san mi yasa take fushi da ke? na girgiza kai,ya ci gaba da cewa  kin bar bin umarninta in ta saka ki abu wanda kika ga dama kike yi,ko matar sarki da kika kayar Wan cikinta ya mutu ta ce ba da yawunta kika yi ba kuma ba haka ta tsara ba


Dr Mu'az ya fito ya kira mu sai muka bar zancen tare da nufar shi,Wakin da Mama take tana bacci ne ya kai mu.Na koma gefe Waya na zauna shi ma Basheer haka sai muka saka ta tsakiya kowanen mu kuma ya ri?e hannunta.



 Don Allah ko za ku yi min fashin ba?i dangane da abin da ya faru? Dr Mu'az ya faWa , Basheer ya ce  wane bayani kuma za a yi ma bayan a gaban idonka komai ya faru? Ka fara tunanin rubuta takardar sakin Mamarmu shi ya fi kan wannan banzar tambayar

 Iyayenka sun daWe da rasuwa tun shekaru goma sha biyu, waWanda kake tare da su MUTUM NE DA RIGAR ALJAN (MRS SADAUKI) su Win fatale ne jinin da kake basu na matan da ka aura tamkar ban ruwa ne kake yi musu,yanzu kuma sun koma makwancinsu sai ka yi ha?uri na furta cikin taushin murya ina kallon Basheer da ke harare na. Sai wani lalaSa shi kike kamar ubanki,ke ko irin Wan kishin nan uwarki ta auri wani namiji ba ki ji? To wallahi sai ya sake ta shiru na yi masa ban ce komai ba haka ma Dr Mu'az sai kuka yake kamar wani ?aramin yaro.


Sai da Mama ta kwashe wajen awa Waya kafin ta buWe ido,da mu ta soma yin tozali ta jawo mu ta rungume tana hamdala ga Ubangiji.Hawayen da suke yi mata zuba muka shiga goge mata kafin mu tayar da ita zaune,Dr Mu'az da ke can gefe ya taso ya ce  Safeena ya jikin naki?
Ta kawar da kai gefe ba tare da ta amsa ba,a ?arshe ma toilet ta shiga bayan ta fito ne ta bamu umarnin mu tashi mu tafi.
Duk muka fito waje ina mai tambayar  yanzu ina za mu je Mama?
 Wace irin tambaya ce wannan? Gida za mu je mana can Nijar  cewar Basheer.



 Kafin ku tafi don Allah ku yi min alfarma ku zo mu je can gidana Dr Mu'az ya furta.
Cike da iya shege Basheer ya ce  gidan fatale?
 A'a gidana dai
Duk yadda suka so ?iyawa amma sai da na ci galaba kansu muka bi Dr Mu'az,wani gidan ne daban ya kai mu shi ma babu laifi yana da kyau.KuWi masu yawa ya fiddo ya ce  ga wannan ku tafi da su don ba za su yi min amfanin komai ba
 Ka bani takardar sakina to cewar Mama.
 Na daWe da rabuwa da ke Safeenat Allah ya baki miji na gari
 A'a ka rubuta dai don Allah  cewar Basheer,haka Dr Mu'az Win ya rubuta mata takardar sakin kafin mu fito.


Gidan mota muka nufa bayan mun sayi abubuwan da za mu ci , Basheer sai murna yake. Wai yanzu daWi kake ji don auren Mama ya mutu?

 Seerat wai mi yasa kwanyar kifi ce da ke? Kina tunanin Dr Mu'az haka zai zauna daram da hankalinsa alhalin ya kwashe shekaru masu yawa yana rayuwa da matattu? To wallahi mahaukaci zai zama shi yasa na ce sai ya saki Mama,ko so kike ya dinga dukanta? ban ?ara ce masa komai ba.

Nan muka zauna har dare don sai gobe da asubah motarmu za ta tashi tuni kuma mun sayi ticket Winmu.Kafin motarmu ta tashi mutanen da Basheer ya tsokana Allah kawai ya san iyakar su ,daga waWanda yake Wagewa hijabi ko zane sai waWanda yake cilla abin da suka sayo sama haka mutum zai ta gudu don kamo abinsa shi kuma yana gefe yana dariya.

A cikin mota kujera mai zaman mutum uku muka Wauka,ni kusan window, Mama a tsakiya shi kuma Basheer daga farko. Sosai balaguron ya bada citta musamman yadda Basheer ke nishaWantar da mu yana saka Mama dariya,kwana biyu muka yi a hanya kafin mu iso gida .Kayan jikinmu ashe sun rige mu zuwa hatta na Mama sai da muka taras,na rage murya na cewa Basheer  wannan dai aikin aljanunka ne ya tuntsire da dariya ya ce  aljanunmu dai


Ammy Habibah ta ce  za ku zo ku ci abinci ko kuwa shirmen za ku yi? da sauri muka ?arasa muka zauna ta zuba mana shinkafa tare da miyar kifi, Basheer ya soma ci ni kuwa na kasa sai kifin nake kallo.


 Mine ne kuma? Ammy Habibah ta tambaya ,sar?ar wuyana na nuna mata mai hoton kifi.Ta saki murmushi ta ce  ai kuwa akwai tuwon tu?e da na yi Safeenatu bari na zubo miki  haka ta zuba min tuwo da miyar kuSewa Wanya na ci na ?oshi.

Na mi?e zan shiga Waki na ga yanar gizo-gizo ta ko ina,na yi tsaye ina cewa  Ammy tun yaushe gidan nan ya koma haka?
Daga can ta ce  ya ya koma? Ni ma yau fa na zo tun jiya na tafi can ?auye wurin Kaka lefen Samira aka kawo

 Da matsala fa! Ina Daddy yake? na furta da ?arfi ina juyowa muka haWa ido da Ammy wacce fuskarta ta bayyana da tsoro.Basheer ya mi?e tsaye ya tako izuwa inda nake ya dubi yanar gizo-gizon sannan ya ce  wannan faWana ne ba naku ba,Goggo Hajara ta ziyarci gidan nan a karo na biyu kuma ta ?ara dam?e ruhin Daddy tana can cikin jeji a tunaninta mafaka ce ta samu ba tare da sanin mutuwarta ce ta kaita har daulata ba ............
```MRS SADAUKI=ث?
'?```
BONUS

My book is only 500 via
6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,ko kuma katin MTN na 500? ?an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuWin karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne .

___________________
BOOK2

23

Assalamu alaikum,mata da ?an matan garin Agadas.CHAFA'ATU MAKE-UP fitacciya kuma jajirtaciyar mai koyar da kwalliya iri-iri.Ta yi tattaki tun daga ?asar Nigeria ta zo nan Nijar a garin Agadas domin horar da masu bu?atar koyon kwalliya,Waurin kallabi.Wannan horar wa da za a yi za ta kwashi kimanin sati biyu ,kuWin koyo jika ashirin ne (20.000f).Ga masu bu?atar ?arin bayanin za su iya kiranmu kai tsaye ta wannan lambar 88584336 ,ko kuma ku tuntuSe mu lambarmu ta WhatsApp 09041604348 .


 SEERAT samo min ruwa a kwano ki biyo da cokali cewar BASHEER,ban tambaye shi mi zai yi da su na je na kawo masa ya karSa yana cewa  saura madubi ni da Ammy Habibah muka je muka ciciSo na Wakinmu.Shi ya nuna mana daidai inda za mu tsaya da kuma yadda za yi,madubin ya haska yanar gizo-gizo ta fito Saro-Saro a ciki.Basheer ya tofa yawunsa a kwanon ruwan kafin ya Webo Waya da cokalin ya watsawa yanar gizo-gizon a nan take Goggo Hajara ta bayyana cikin madubin da muke ri?e da shi mu biyu.


Hankalinta a tashe take kallonmu tana son yin magana amma ta kasa,a hankali BASHEER ya soma rikiWa yana zama tamkar mai siffa biyu kafin ya matso ya shiga madubin shuuut ya wuce kamar wanda ya shiga Waki tsabar firgici ya saka na saki madubin tuni kuma ya yi wa Goggo Habibah girman da ba za ta iya ri?e shi ita Waya ba sai ya suSuce mata ya faWi ?asa tare da tarwatsewa. Hakan yayi daidai da shigowar Daddy dafe da saitin zuciya ya zube kan kujera yana wani ha?i kamar mai cutar huka,muka kalli juna ni da Ammy.


 Mine ne na ji ya fashe? Mama ta tambaya wacce fitowarta kenan,da sauri ta nufi Daddy tana kiran sunansa.Mu ma muka je muna jijiga shi saboda idonsa da suka fara kafewa,muna cikin wannan tashin hankalin ne madubin da ya tarwatse a ?asa ya soma yin motsi ji kake  kacauuu! Kacauuu duk suna motsa kansu tamkar ana ya?i.


 SEERAT ki yi amfani da powerki ki haWa madubin nan na ji muryar BASHEER ta fito a cikin tattakar madubi.Jikina na rawa na soma juya hannuna na hagu ,a hankali suka soma haWewa har ana jin ?arar gamewar tsaf madubin ya koma daidai tamkar bai taSa fashewa ba.Na yi baya kamar zan faWi saboda Basheer da ya cillo Goggo Hajara daga cikin madubin,ya haye kan ruwan cikinta ya sha?e mata wuya idonta suka fito luhu-luhu. Tun ina jariri kika yi ?o?arin kashe ni amma ba ki ci nasara ba,to yau ni nan zan aika ki lahira kafin nan.... sai kuma ya Wago ya dube ni,da sauri na ?araso na Wora hannuna kan goshinta ta saki razananen ihu har sai da ?wan lantarki ya tarwatse.Ta bakin Goggo Hajara wani abu ya soma fita yana dosar hancin Daddy,kamar tsawon minti biyu kafin Daddy yayi atishawa tare da kelaya amai.
Basheer ya fizgo sar?ar wuyana ya Wora wa Goggo Habibah,kifin ya kuwa haWiye ta.Yayi baya a wahalce ya zauna yayin da ni kuma na Wauki sar?ata na mayar.



 Alhamdullah! Burina ya cika,sai ki je can ki ?arasa rayuwarki a Soyayyar duniya cewar Ammy Habibah tana zuwa ta rungume ni da BASHEER.Kafin kuma mu je mu yi wa Daddy sannu,daga nan muka gyara gidanmu yayi fesss ?yallin rahama ya shigo a yanzu babu wata fargaba duk ma?iyanmu mun kawar da su.





#GIDAN SAKEENATU



A sannu a hankali ta soma koyawa kanta rayuwa a tare da Agali,kulawa ta musamman yake bata sannan ya buWe mata wata ?ar ?aramar asibiti inda take kula da majiyanta.?angare guda sai shirye-shiryen auren Ma'idah ake da mijin da ita kanta ba ta san shi ba,ko kaWan ba za ta ce tana farin ciki da auren ba haka ma ba ta ba?in ciki.Abu guda ta sani za ta auri cousin Winta ne,yadda kuma Daddynta ke kula da ita yana yi mata duk abin da take so kawai sai ta yi amanna ba zai taSa cutar da ita ba.A haka har aka yi bikin auren,an yi mata kitso da lalle tuni kuma an gama gyaran takardunta.

Idonta tab da hawaye take kallon mahaifiyarta wacce a kullum suna tare duk tsanani duk wuya sai dai ga shi yau za su rabu.Sakeenatu ta shafi gefen kumatunta ta ce  za mu dinga yin waya ai,sannan Daddynki zai dinga kai miki ziyara akai-akai. Ma'idah ta faWa jikinta ta fashe da kuka ta ce  zan yi kewar ki Mama ita ma ta rungume ta,tsawon lokaci suna a haka kafin Agali ya ja hannun Ma'idar yayi mata rakiya har cikin jirgi,da kansa ya Waura mata belt yayi kissing nata a goshi tare da yi mata sallama.



Tun da jirgin ya lula da su sama ta soma tunani iri-iri ,a haka bacci ya Wauke ta.Sanarwar jirgi zai sauka ne ya tashe ta,a sannu duk mutane suka soma fita ita ma ta bi ayari tana saSe da jakarta a kafaWa sai waige-waige take can ta hango wani farin mutum ri?e da wata balon Win leda an rubuta sunanta.Da sauri ta ?arasa tana ce masa  barka kai ya jinjina mata tare da yin gaba ta kuwa take masa baya,gidan gaba ya buWe mata ta shiga ta zauna sannan ya je ya nemo kayanta ya saka a Booth .Da ya dawo kawai tu?i ya fara ba tare da ya ce mata komai ba ,a haka har suka isa wani tanfatsetsen gida wanda tsabar haWuwarsa sai da Ma'idah ta saki baki tana kallon ko ina. Har ciki yayi mata iso,Wakin da ya buWe ya jera mata trollynta sai ta fahimci nan ne masaukin da ya bata kenan.Toilet ta shiga ta yi wanka,ko da ta fito ta tarar ya kawo mata abinci sai da ta ci ta ?oshi sannan ta shirya cikin doguwar riga marar nauyi ta yi sallolin da suka hau kanta.Bed ta haye don hutawa kawai sai ta ga an turo ?ofa,shi dai ne ya shigo idonsa ?yam a kanta.Ita ma sai ta zuba masa na mujiyar tana ?are masa kallo,fari ne sosai ?al za ta iya cewa ma Albino ne yana da kyau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login