Showing 6001 words to 9000 words out of 139076 words

Chapter 3 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

106

nan ba Mamuh ke faWa cikin masifa ita kuwa Ma'idah tuni ta soma kuka musamman irin abin ban tsoron da take hangowa a fuskar Mamuh.

Abbas ya sunne kai ya ce  a dai yi ha?uri Mamuh dukkan bawa bai wuce jarabawa,Ma'idah ita yarinya ce ba ta san komai ba

 Wallahi sai ta bar gidan nan Mamuh ta faWa cikin ?araji, Sakeenatu kuwa banda kuka babu abin da take yi .
Hannun Ma'idah ta kama da niyyar jawo ta,ita kuwa baiwar Allah cike da tsoro ta Wauki cokali mai yatsu ta ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????caka ma Mamuh ita a ido da zumar ceton kanta ga dodo.
Wani uban ihu Mamuh ta yi tana cewa  wayyo idona! ?ar daba ta kashe ni jikin Abbas na rawa ya je ya kamo Mamuh wacce tuni idon ya soma fitar da jini,hankali tashe ya soma goge jinin wani na zubowa a doli ya kama ta zuwa asibiti.
Bayan tafiyarsu ne Nafisa ta soma tofa ma Ma'idah addu'o'i saboda yadda take wani irin kuka tana firgita,cikin kuka Sakeenatu ta ce  Nafisa ki Wauke ta ku wuce gida don Allah
 Ke kuma a nan za ki zauna? 
 To ina zan je Nafisa? Ha?uri zan yi dama aure ya gaji haka sanin kan ki ne a can gidan ba wani jituwa muke ba ni da Mama ta Wauki ?iyayyar Wan farin ta Wora min
 To amma dai ki kula da kan ki,in kin ga abin ya yi yawa kawai ki tawo gida
KuWi ta basu sannan suka bar gidan,ita kuma ta Wauki waya ta kira Abbas don jin asibitin da suke shi da Mamuh yana shaida mata ita ma ta fita ta je.Tuni Mamuhn ma ta yi bacci an naWe idon nata da bandeji ga kuma ?arin ruwa an saka mata.
Jikinta a sanyayye ta ce  ka yi ha?uri Abbas ya kamo hannunta ya ce  dama haka Allah ya tsara,ina Ma'idah?
 Nafisa ta koma da ita can gida
 Don me? Zan rarrashi Mamuh na san za ta amince ta zauna da mu

Ta sakar masa murmushi ta ce  na gode sosai da kawaicinka gare ni wani kallo yake aika mata yana mirza tafin hannunta,da ido Wayan mai lafiya Mamuh ke kallonsu tana jin wani irin haushi da takaici.


 Mine ne haka? A asibiti fa muke ka bari har mu koma gida Sakeenatu ta faWa tana janye jikinta daga nasa ganin abin zai wuce gona da iri.
 Mu je gidan to tun da kin ga Mamuh ta samu bacci ,sai mu dawo daga baya Abbas ya faWa yana langwaSar da kai saboda ba ?aramar kewar ta yayi ba.


 To ai na farka cewar Mamuh tana mai tashi zaune haWi da hararen Sakeenatu,da Wan sauri ya mi?e yana tabayarta jiki. Ka kira likita ya cire min ?arin ruwan nan sai mu wuce gidan tun da uwarka ba za ta barin ka cikin salama ba cewar Mamuh a zafafe,Abbas ya fita don kiran likita.


 Duk tsiyarki dai ba za ki iya canza ma tuwo suna ba,Abbasi Wana ne ba naki ba don haka ni ke da iko da shi ba ke ba.Kuma wannan shegiyar taki sai ta san ni ta caka da cokali sai na shayar da ke mamaki


Da wani mugun sauri Sakeenatu ta je gaban Mamuh ta tsuguna ta ce  don girman Allah Mamuh ki yi ha?uri , Ma'idah yarinya ce ba ta da wayo ko me za ki yi to ki yi min amma kar ki taSa ?ata ta ?arashe maganar hawaye na zubo mata saboda zuwa yanzu ta yarda Mamuh muguwa ce.


Kafin ta kai ga bata amsa Abbas ya shigo shi da likita,ya ce  sai kin yi kwana uku sannan za mu sallamar ki
 To ka sanar da uwarmu wacce ta matsa mu je gida Mamuh ta faWa a zuciye tana hararen Sakeenatu.
Likitan yayi murmushi ya ce  yanzu yadda za a yi sai ka nemo wacce za ta zauna da Mama,amma gaskiya ba za mu sallame ta ba yau sai yayi wa Mamuh allurar bacci,duk yadda masifa ke cin ta haka ta ha?ura saboda ?arfin allurar.


Shi kuwa Abbas Gwaggonsa ya kira wacce ke nan Damagaram ita ke bi ma Mamuh,babu jimawa kuwa ta zo .Ya ja matarsa zuwa gida,cike da zallar soyayya suka gamsar da junansu.





SAFEENATU


Tun bayan da kowa ya watse aka bar su ita da Gwaggo Habibah sai ta nutsu sosai kafin ta ce  Gwoggo ni kam Wazu wani abin ban mamaki ya faru,maciji na gani ya naWe Baby girl Win nan ina yin ihu ya Sace kamar aljani 

Gwaggo Habibah ta yi murmushi ta ce  kar ki wani ji tsoro,sannan ina so ki kwantar da hankalinki duk wani abu da za ki gani ki yi shiru da bakinki.Duk kusan ?an biyu suna da wannan baiwar,to ke macen ce ke da shi don haka ki shirya ganin abubuwa iri-iri wasu na tsoro wasu kuma na almara

Safeenat ta ja wani numfashi kafin ta ce  to Allah cire min tsoron ba ta ida rufe bakinta ba hasken Wakin ya Wauke duhu ya turnu?e shi kai ka ce dare ya tsala.Duk tsit suka yi babu wanda ya ce wani abu,sai kukan jaririyar da ya soma tashi sannu a hankali tsawon minti biyu kafin ta yi shiru.Hasken Wakin na dawowa Safeenatu da Gwoggo Habibah suka yi ?ar rige-rigen Waukar babyn duk suka yi tsaye suna kallon yadda goshinta ke fitar da wani haske yana ?yalli a gaban idonsu ya Wauke sai ga shatun ha?oran maciji ya bayyana raWau .Safeenat ta kai hannu ta shafi wurin sai kuma ya Sace,ta ja ajiyar zuciya tana mai Waukar jaririyar ta soma shayar da ita.

Daddy ya yi sallama ya shigo,duk suka gaishe shi kafin a basa babys Win ya gani.Sosai yayi musu addu'a sannan ya fita,haka suka ci gaba da yin hirarsu har dare ya tsala.Duk sun yi shirin bacci za su kwanta amma ita Baby kamar Wiyar aljanu ta ?i baccin sai ma wani kuka-kuka da take yi.

 Safeenat ki bata abincinta mana Gwaggo Habibah ta faWa tana shirin tashi ta kunna wuta.
 Ina ta ?o?arin bata ta ?i karSa cewar Safeenar.
Kusa da ita ta zauna tana shirin Waukar babyn sai ta lura da yadda hannunta na hagu ke fitar da wani zane mai hasken wuta kamar ta murhu.Wani irin murmushi ne ya suSuce wa Gwaggo Habibah ba tare da ta shirya ba cike da murna ta jawo hannun jaririyar ta ri?e sannu a hankali har zanen ya fito raWam letter M ta fito sai a lokacin kuma jaririyar ta yi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa.
A Wan ruWe Safeenatu ta ce  Gwaggo mine ne kuma wannan?

Sam Gwoggo Habibah ba ta bata amsa ba sai safar hannu da ta je ta binciko cikin kayansu ta saka wa hannun mai zane. Daga yau kar ki ?ara barin hannunta a buWe ki dinga saka mata safar hannu 

 Gwaggo ina tambayar ki mine ne ba ki bani amsa ba

 Alama ce ta proph?tie/prophecy,da yawan ?an baiwa tana soma aiki ne in sun kai shekara sha takwas amma ke yarinyarki tun farkon dirowar ta duniya tata baiwar ta fara aiki.Ta ceci Wan uwan tawaicinta sannan kuma ta ceci ?awarki Sakeenatu 

Ba don ta fahimci zancen da kyau ba ta ce mi ya samu Keenat Win?
 An yi mata ajiya cikin ruhinta ta yadda esprit zai samu damar yin yanda ya so da gangar jikinta har ya cutar da ita
 Ya aka yi kika sani to?
 Safeenatu yi bacci in lokacin fahimtarki yayi babu bu?atar ki yi tambaya

Da wannan duk suka yi bacci, Safeenatu na tsaka da yin mafarki akan goben ?arta Gwaggo Habibah ta tashe ta daga bacci. Ruwan wankan ki na can toilet ta tsakar gida,ki je yi wankan sabulu kafin na zo na gasa miki jikinki da towel
Ta yi mi?a ta tashi a gajiye saboda kwana dare ta yi tana shayarwa,sai da ta Wauki wani zane da hijabi sannan ta fita ta bar Gwaggo Habibah za ta yi wa Twins wanka.


Sakeenatu na fitowa suka yi kiciSis da Gwoggo Hajara ta gaishe ta sannan ta wuce toilet.Ita kuwa tsabar mugunta yasa ta koma Wakinta ta yo shirin mugunta yau ma siffar tsakaka ta Wauka ta yi tsinke can toilet inda Safeenatu ke wanka tun tuni.Da ga can saman katanga Gwaggo Hajara ke ?arewa surar Safeenat kallo,cikin salon mugunta ta mayar da harshenta dogo sannan ta zuro shi tun daga can sama har ?asa yana taSa tile.
Safeenatu ta yi wani ihu wanda bai sauka ko ina ba sai cikin kunnen ?arta jaririya,kwacaaaa Gwaggo Hajara ta faWo cikin ?atuwar robar tafasasshin ruwan zafi.......




Ga masu son fara yin payment su yi min magana ta lambata na basu detail na sabon account number da za a tura kuWin ba waccan na Ecobank ba.DM +22795045822
*ZAWARCI*


LoVe aNd HoRrOr StOrY &?

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI=ث?
'?)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS&?*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.

*Sadaukar wa:* Rahama Sabo Usman


_____________________
25/09/24

8

Da wani mugun sauri Safeenatu ta yi tsalle ta koma jikin ?ofa tana kyarma ,idonta ?ur cikin robar wacce tsakakar ke ta ?o?arin fitowa daga ruwan .Ganin ta soma yin girma sosai yasa Safeenatu ta buWe sakatar toilet Win zane a hannu ta fito Allah yayi sa'a babu kowa a tsakar gidan,dakyar ta yi Waurin ?irji kafin ta nufi can ciki da gudu.

 Ke lafiyar ki? Gwaggo Habibah ta yi tambayar .

Feenat ta dafe gefen zuciyarta da yake mugun bugawa ta ce  tsaka...ka ce ta faWa cikin ruwan da nake wanka

 Shi ne kike wannan ha?in? Kai Allah ya shirya min ke ban san lokacin da za ki girma ba

 Gwaggo ba normal tsakaka da kika sani ba ce, wannan ?atuwa ce inda kin ga yadda halshenta ke da tsayi ya fi pampo fa


Shiru Gwaggo Habibah ta yi tana kallon Baby girl don kuwa a gaban idonta da tana yi mata wanka wani mugun haske ya fita goshinta tamkar an jefa kibiya.

 Allah ni dai ba zan sake shiga toilet Win waje ba ?ila ma aljani ne muryar Safeenatu ta katse mata Wan guntun tunaninta.
 Bari na je na gani  cewar Gwoggo Habibah kafin ta mi?e ta fita zuwa Toilet Win tsakar gida,tun kafin ta ?arasa ciki take jin nishin wahala .
Ido huWu suka yi da Gwaggo Hajara wacce zuwa yanzu tuni ta galabaita ta yi wani tsamo-tsamo cikin ruwan zafin ta kasa fita . Gwaggo Habibah ta yi wani murmushi tana kallon yadda ruwan suka yi ba?i tsabar yadda muguntar da ta shiryo ma Safeenatu ba ?arama ba ce.


 ?arshen alawa ?asa! Yanzu wa gari ya waya? Shi dama ramen mugunta an ce ka gina gajere in kuma ka gina dogo kai za ka faWa .Ai wallahi ba zan taimaka miki ba sai dai ki dawwama a ruwan zafin nan,in kuma kin ga na taSa robar nan to wallahi cikin masai ne zan zubar da ku ke da ruwan Gwaggo Habibah ta faWa tana wani murmushin jin daWi.

Kamar daga sama tsakaka ta soma magana wacce ta kasance Gwaggo Hajara , ki taimaka min Habibah na yi miki al?awarin daga yau na zubar da makaman ya?i
 Kar ma ki zubar ki yi ta ri?on su har sai Mahadi ya bayyana,ba dai maita ita ce jarinki ba? Ki ci gaba da yi wata rana mutuwarki za ki ci tana gama faWar haka ta fito daga toilet Win,sai kuma ta tuna duk wanda ya mutu a ruwa yayi shahada da sauri ta koma ba tare da ta ce komai ba ta Wauko robar ta fito da ita tsakar gida tare da juye ruwan ga ?asa.
Tamkar acid haka turSayar ta soma yin bori tana fitar da kumfa tsabar bala'in da ke tattare da ruwan,a kunyace Gwoggo Hajara tsakaka ta soma jan ciki ta nufi hanyar Waki.


Ita kuwa Gwaggo Habibah ji ta yi kamar ta sa ?afa ta laSe shegiya kowa ya huta.Tana komawa ciki ta cewa Safeenatu  Ki shiga toilet to kafin na juye ruwan yi miki wankan sai kuma ta fita ta ciko ?aton bokiti da ruwan zafi,da Wan ?aramin towel ta soma yi wa Safeenatu wankan jego ita kuma tana ihu kamar wata ?aramar yarinya.



Macijin jiya ne ya sake bayyana a jikin macen yana wani naWe jikinta,ita kuma ta buWe ido taram tana kallonsa kamar mai wayo.Tsawon lokaci ya Wauka tare da ita yana yi mata wasa kafin Sace jin motsin su Safeenatu za su fito.Gefen gado ta zauna ta soma shayar da yaran kafin ta kimtsa cikin riga da zane,sai da Gwaggo Habibah ta gama wanka ita ma ta fito ta shirya sannan ta je ta kawo masu abinci suka ci daga nan suka wuce asibiti bayan sun karSi kuWi wurin Daddy.Lafiyarta da ta babys aka duba kafin su dawo gida,tuni kuma ?an Barka suka fara zuwa in waWannan sun fita wasu sai su shigo.






SAKEENATU


Tana rungume jikin Abbas ta ce  Yau tana Waya daga cikin ranakun ovulation Wina,yau na gama period  cikin tsokana ya ce  period Win Waya rana  ta ja hancinsa ta ce  eh na dai ji,inda ina jimawa kafin ta Wauke ai da yanzu ba ka kasance da ni ba don jiya ne na gan ta
Ya gyara mata kwanciya kan ?irjin nasa yana mai cewa  Keent don Allah ki dinga bin Mamuh a hankali kin san ta tsufa,ban so kina yin abin da zai Sata ranta ki guji Sata mata don farincikina.Ina yi miki wani mugun so ne wanda na san ke ko rabin shi ba ki yi min

 To in sha Allah na yi ma al?awari zan kiyaye,ai Ma'idar ma an tafi da ita

 A'a za ta dawo,sanin kan ki ne yadda nake mugun sonta ba zan iya yin nesa da ita ba

Wani daWi ne ya luluSe zuciyar Sakeenatu,ita ce shaida kan son da yake yi wa ?arta duk da ta fito ba ta hanyar aure ba.Za ta iya cewa halarcin bai nuna mata ?yama ba ne ya Wunguza ta ga aurensa,soyayyarsa ma ba ta jima da samun gurbi a zuciyarta ba.


 Ina son ki Keenat! furucinsa ya katse mata tunani,ta yi murmushi mai Wan sauti ta ce  na gode
 Ke ba za ki faWa kina sona ba? Keenat sai yaushe zan ji furicin so daga bakinki?
Ta la?ace masa hanci ta ce  sai ranar da na haifo ma kyakkyawan Prince mai kama da kai sai kuma ta mi?e ta je ta shiga toilet,shower ta sakarwa kanta tana tunanin saurayinta mahaifin Ma'idah.Ruwan hawayenta haWi da na pampo suka haWu wuri Waya suna zuba.Daga bayanta ta ji an rungume ta,da sauri ta juyo suna fuskantar juna kallo guda yayi mata ya hango damuwa a shimfiWe a ?wayar idonta.Zuciyarsa kuma ta basa ta yi kuka,bai tsaya tambayar ta ba ya Wora bakinsa kan nata a wannan rana a kuma daidai lokacin nan Abbas ya shayar da ita zumar ?auna mai haWe da yayafin kalaman soyayya masu nuni da sadaukarwa.Ba tare da ta shirya ba ta ce  I love You Abbas! numfashinsa ne ya kusan tsaya wa tsabar murna da farin ciki,kamar wani ?aramin yaro ya soma yi mata kuka saboda kawai ta ce tana sonsa.


Shi yayi musu wanka ya shirya su,a ranar a gida ya ja su sallah har ta isha'i .Bayan sun salamce sun yi dogayen addu'o'i ya dube ta da kyau ya ce  Keenat fatan bayan tafiyata duk salloli kin yi su kan lokaci kuma kin tsare su?
Da sauri ta sunne kai ba tare da ta basa amsa ba,yatsun ?afarta ya soma ja mata tare da soma yi mata nasihar da ya saba game da mai wasa da sallah a ?arshe yake cewa  in kuma na ga kin ?i yi zan kawo miki ?anwa ustaziya a shagwaSe ta faWa jikinsa ta ce  to ai ina yi ko
 Kina yi ko za ki dinga yi?
 Duka biyun! Ba za ka koma asibiti ba?
 Tare za mu koma tashi ki shirya da  to ta amsa kafin ta canza kaya suka fito,sai da ya tsaya ya saya musu fruits sannan suka isa asibitin.Da sallama suka shiga Wakin Gwaggo Rahamu ce ta amsa yayin da Mamuh ta juya musu baya tana jin wani irin ba?in ciki ya turnu?e ta saboda a yadda ta gansu cikin farin ciki suna nishaWi ta san sun keSe da junansu.Abbas ya ?arasa yana mai cewa  Mamuh ya jikin naki?
 Ka damu da ni ne ka sa ?afa ka yi tafiyar ka? Wato Abbasi matarka ta fi ni ko? ta faWa cike da masifa tana juyowa.
 Ki yi ha?uri Mamuh Allah dai ya baki lafiya  ya faWa kansa ?asa.


Tsabar fitina ta Mamuh sai cewa ta yi  ina wakena? Abbas ya Wago da sauri yana kallon ta yana mai cewa  wane irin wake kuma Mamuh yanzu da daren nan? Ga ayaba nan da lemu da apple na sayo 

 Na yi da kai na ce ka sayo? Ita waccar abar ai ta san wake nake ci mi yasa ba ta dafo ba?

 Yi ha?uri Mamuh gobe sai a daf.... bai rufe baki ba Mamuh ta saka kuka yana cewa  shinenan tun da mata ta fi uwa

Da mugun sauri Sakeenatu ta ce  bari na koma gida sai na dafo mata
Abbas ya ce  to ki yi sauri ta yi tunanin shi zai kai ta amma sai kuWin Wan sawu ya bata,tana zaune tana hawaye har suka iso gida ta biya shi kuWin kafin ta wuce ciki.
A gaggauce ta soma aikin tana mita  an yi tsohuwa kamar mayya kullum wake yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login