Showing 84001 words to 87000 words out of 139076 words

Chapter 29 - ZAWARCI COMPLETE HAUSA NOVEL

14 Oct 2025

139

sai me? Haka aka ce ni zan aure ta kuma na zama sarki saboda mahaifinta bai da Magaji 

Na ce  a'a ga shi nan amaryarsa za ta haifa masa shi
Ya ce  kin manta kin kayar da ita ta faWi Wan cikin nata ya mutu?
Gabana ya faWi rasss,kafin na kai ga cewa wani abu sai ga Yaya Khaleed yana cewa  mi kuke tattaunawa haka?

 Babu komai Yayanmu cewar Basheer,tashi na yi na bar su a nan na wuce Wakinmu wanda yanzu nake jinsa yayi min girma saboda babu Mama.Hawaye suka zubo min ina jin maraicina na dawo wa sabo dal,da ace mahaifina nada rai da yanzu Mama ba ta yi nisa da ni ba sam amma babu yadda na iya sai ha?uri.





#COTONOU

Cikin amincin Allah suka isa ,kasancewar suna zuwa Niamey daga nan jirgi suka shiga .Dangin mahaifiyar Safeenatu sosai suka yi murna ganin gidan da suka kawo ta,wanda ba sai an faWa maka ba an gama tara dukiya har an gaji.Yadda dangin likita Mu'az suka tarbe su kuwa abun ba magana,cike da karamci da daraja.Ita kanta Safeenatu sai ta ji ta ?ara samun nutsuwa da kuma ?aunar Mu'az,sun ci sun sha kafin a nuna musu sashen da za ta zauna wanda tuni an zuba masa kaya iri-iri babu wani gyara da yake da bu?ata.Wani Sangare suka kwana yayin da ita kuma Safeenat ta zauna Wakinta tana jiran shigowar mijinta,tsawon lokaci kafin ya shigo da murmushin nan nasa wanda ke ?ara lula ta cikin duniyar sonsa.Hira sosai ya yi mata a wannan daren har ta yi bacci,tun washegari ?an rakiya suka kamo hanyar gida bayan sun samu goma ta arziki.

Safeenatu ta yi wanka ta fito cikin wani rantsatsen less ja sai walwali take,fuskarta Wauke da murmushi ta fito falon inda surukanta ke zauna da kuma ?a?ansu.Cike da girmamawa ta ?ara gishe su,suka amsa cikin sakin fuska kafin Mamy mahaifiyar Mu'az kenan ta ce  yawwa amarya a nan gidan muna da wata al'ada,in an kawo amarya muna shirya mata liyafa ,da farko za a yi mata wanka da ruwa masu tsarki floris sai kuma turaren wuta daga nan sai cin abinci fatan Mu'az ya sanar da ke duk wannan?

Safeenatu ta yi murmushi kawai,yayin da kuma wata daga cikin ?an gidan ta zo ta kama hannunta ta mi?ar da ita zuwa wani sashe duk suka take mata baya.Zuciyar Safeenatu sai da ta kusa tsinkewa sa'ilin da ta ?etara wani jan layi ta ji zuuuu duk wata sutura da ke ga jikinta sai da ta fice da kanta,amma abun mamaki ko kaWan ba ta ji za ta iya yin gardama ba.
Kan wani jan ?yalle aka kwantar da ita can kusan kanta aka Wora wani kasko mai Wauke da wutar kyandir,sai Wakin yayi duhu sai hasken wutar kawai.Ta lumshe ido sa'ilin da aka soma zuba mata ruwan masu masifar sanyi a gangar jiki,ji take tamkar ana sauya mata halitta ne daga ta ?an adam zuwa wata can daban.Wa?e-wa?en da suke yi masu kama da na wa?o?in coci jinsu take tamkar ana zage ranta ne,tsawon lokaci kafin a yi mata sutura da wani jan ?yalle aka naWe ta da shi kamar sahari sai kuma matar nan ta ?ara jawo ta suka fita zuwa wani sashe inda ke da wani ?aton table mai abinci iri-iri.
Matar ta zaunar da ita face da kujerar Mu'az wanda zuwa yanzu sam fuskarsa babu Wigon annuri cikinta, Safeenatu ta Waga kai ta dubi shi sai ta ga wannan ba wanda ta aura ba ne .Idonta taf da ?walla take kallon tsakiyar nasa idon,da sauri ya kawar da kai gefe ita kuwa tuni ta fahimci rayuwarta na tsikin hatsari.

 Lokacin yanka cake yayi a kawo shi wannan karon Papy ne ya yi magana,yayin da matar nan wacce ta ja Safeenatu ta je ta Wauko ?aton cake Win , Mamy ta mi?a wa Safeenatu wu?a ta ce  ki yanka ita kuwa ido ta tsura wa cake Win ganin an yi shi ne da hoton fuskokin mutanen da duk duniya ta fi so,sune duniyarta ba hoton kowa ba ne sai na SEERAT da BASHEER......






Assalamu alaikum,mata da ?an matan garin Agadas.CHAFA'ATU MAKE-UP fitacciya kuma jajirtaciyar mai koyar da kwalliya iri-iri.Ta yi tattaki tun daga ?asar Nigeria ta zo nan Nijar a garin Agadas domin horar da masu bu?atar koyon kwalliya,Waurin kallabi.Wannan horar wa da za a yi za ta kwashi kimanin sati biyu ,kuWin koyo jika ashirin ne (20.000f).Ga masu bu?atar ?arin bayanin za su iya kiranmu kai tsaye ta wannan lambar 88584336 ,ko kuma ku tuntuSe mu lambarmu ta WhatsApp 09041604348 .
```MRS SADAUKI=ث?
'?```


My book is only 500 via
6042551755
Hassana ibrahim
Keystone bank,ko kuma katin MTN na 500? ?an Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 500f sai a turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822,in kin san ba ki biya kuWin karatu ba kar ki karanta min littafi domin mallakina ne .

___________________
BOOK2


19_20

Duk da Safeenatu ba matsafiya ba ce,amma ta san sarai wannan alama ce ta duniyar Ruhaniya.Ta yaya ma za a ce hoton ?a?anta ne kan cake? Ta yi imanin cewa Dr Mu'az bai taSa ganin BASHEER ba sai SEERAT kawai ta dai shaida masa ?a?anta biyu kuma Twins ne.Sai ga shi yanzu ta ci karo da cake mai hoton fuskokinsu,tana tsaka da tunanin wannan wane irin gida ne kuma ta kawo kanta? Sai jin muryar Dr Mu'az ta yi bayanta yana cewa  sweety ki yanka mana

Idonta taf ?walla ta juya tana kallonsa kafin ta ce  ?a?ana ne fa
 Bai komai fa kawai na yi amfani da hotonsu ne don faranta miki rai na nuni miki ni ma ?a?ana ne ,don ina da niyyar kawo su nan Win su ci gaba da yin karatu Mu'az ya faWa cikin taushin murya yana yi mata murmushi.


Safeenatu ta girgiza kai ta ce  Ni dai ba zan iya yanka ?a?ana ba

 Kin ga al'adar gidanmu ce wannan,doli ki yanka shi Mamy ta faWa tana zuwa ta kama hannun Safeenatu mai ri?e da wu?a ta nufi cake Win duk yadda ta so ?in yankawa amma sai da ta yi sakamakon wani mugun ru?o da Mamy Win ta yi mata wanda ta yi imanin ba nata ba ne kawai.


Yanka biyu aka yi da wurin fuskar BASHEER da kuma ta SEERAT,dukkan mutanen gidan suka hau ihu annuri cike da fuskokinsu shi kuwa Dr Mu'az wani murmushi yake yana kallon tsakiyar idon Safeenatu wacce banda kyarma babu abin da jikinta ke yi,hannunta ya kama suka nufi sashensu tana waigo ta ga yadda suke cin cake Win sai kace mayuwanta ko kuma yau ne suka soma ganinsa.



Har tsakiyar gado ya kwantar da ita ya ja zane ya rufe ta tun daga ?afafunta har zuwa ?irjinta ita kuwa banda kallonsa babu abin da take yi.Ya goge hawayen da ke yi mata zuba ya ce  kin fi kyau in kina murmushi Feenat Win Mu'az

Ta buWe baki da niyyar yin magana amma kuka ya kubce mata, yi shiru mana na san kina da tarin tambayoyi a gare ni ,amma ki yi ha?uri da sannu za ki fahimci komai sai y yun?ura zai tashi ta yi saurin kamo hannunsa murya na rawa ta ce  don Allah kar ku cutar min da yarana ina sonsu,su kaWai gare ni waWanda suke maye min gurbin mahaifinsu 

Ya Wan Sata rai ya ce  kenan ni ban maye gurbin ba?
Ta girgiza kai ta ce  Dr Mu'az babu ta yadda za ka maye gurbin mutumin kirki irin Bashir ,halinka da nasa ba iri Waya ba ne ko kaWan ba su yi kamanceceniya ba.Shi ruhinsa tsarkake ne ba irin naka ba,ko kaWan ban yi tunanin rayuwar ?unci ka yi min tanadi ba.Duk mene ne wannan? Wanka da ruwa masu tsarki,yin wa?a kamar ta tsafi ga wata wutar kyandir da aka kunna haka ma kayan jikina suka cire kansu


Bai bata amsa ba sai fuskarsa da ya matsa kusan tata,bai Wauki wani lokaci ba ya soma sumbatar ta.Duk uban tsimin da Safeenatu ta sha na gyaran jiki ya tashi a banza saboda tsaka mai wuyar da take ciki,ko kaWan ba ta jin daWin abin da yake yi mata.Duk yadda ta so katange masa jikinta amma ba ta yi nasara ba sai da ya san ta a Wiya mace,abu guda ya bata mamaki yadda ya kawo addu'ar kasancewa da iyali tare da wasu dogayen addu'o'i na tsari.Ta hasken da ya rage yake kallon ta,wani irin mugun sonta ne ya ratsa masa zuciya a yanzu da ya gama mu'amala da ita.


 Feenat .... bai kai ?arshe ba ta dire daga bed Win ta shiga toilet.Tana wanka tana kuka ,sai da ta fito shi ma ya shiga .Kayan atamfa ta saka tare da Waukar wayarta hannunta na rawa ta turawa Goggo Habibah text kan cewa  Goggona na shiga uku ashe ban auru ba,da matsala gidan matsafa na faWo sa?on ko minti Waya bai yi ba Habibah ta kira ta, ki aje hankalinki ki yi mini bayanin duk abin da ke faruwa

Sai da Safeenatu ta waiga ta ga eh babu dai kowa sannan ta soma yi wa Goggo Habibah bayanin komai daki-daki a ?arshe ta ce  ban taSa tunanin Dr Mu'az zai yi min haka ba,sai yanzu nake mamakin yadda na aminta da shi cikin sati guda kacal har na aure shi ga mamakinta sai ta ji ita Habibah na yin wani murmushi kamar wacce aka yi wa bushara da gidan aljanna ta ce  Safeenatu in ba ki manta ba tun SEERAT na cikin tsumman goye na taSa shaida miki cewa sai kin yi ha?uri za ki dinga ganin abin da hankali bai Wauka,to wannan Win ma yana ciki sai ki yi ha?uri ki samu nutsuwar zuciya ko kaWan kar ki nuna musu wankan ?addamawar da suka yi miki bai game jikinki ba .Sannan in sha Allah tun yau zan shirya kayan Twins suna nan tafe kamar yadda suka aiko musu katin gayyata,in kin fita ki shaida musu yaranki suna nan tafe tana gama faWa ?ittt ta kashe kiran.



Kaso ashirin na fargaba da damuwar Safeenatu sai ta ji sun gushe,ko ba komai ta san Goggonta ba za ta taSa yi mata ?arya ba ballantana ta saka rayuwar yaranta da ita kanta cikin matsala.Ta saki wani murmushi tuna yadda SEERAT ta yi wa Mamuh,kamar wacce aka tsikara haka ta mi?e ta je gaban dressing mirror ta shafa hoda da kwalli da man leSe.Ko da Dr Mu'az ya fito ya tarar da ita tana zaSar kayan da za ta saka,wata doguwar riga ta Wauko blue ta saka ta Wora mayafinta a kai.



Shi ma a gaggauce ya shirya kafin ya zo inda take tsaye ya ce  kina jin yunwa ne? kai ta jinjina masa,da kansa ya zaSo hijabi ya saka mata sannan ya ja hannunta zuwa waje.Ga mamakinta duk ahalin gidan hankalinsu na kan ?ofar fitowa wannan yasa suna ganinsu duk suka mi?e suna kallon Safeenatu.Ita kuma ta dubi Dr Mu'az ,ya ce  ki faWa musu har za ta tambaye shi me? Sai kuma ta tuna da zancen Goggonta sai ta sakar musu murmushi ta ce  suna zuwa nan da kwana biyu fuskokinsu ne suka faWaWa,Mu'az ya ja ta zuwa waje .


Direba ne ya ja su zuwa wani gidan cin abinci,suna baya zaune Dr Mu'az sai wasu abubuwa yake yi mata don nuna ?aunar da yake mata.Tamkar wata yarinya haka ya kama hannunta suka shiga ciki,da kansa ya ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna face da ita yana saka mata murmushi.

Wanda ke kula da ba?i ya zo ya tambaye su abin da suke so,nan suka faWa masa babu jimawa aka kawo musu.Hankali kwance suke cin abincin,ita dai Safeenatu can ?asan zuciyarta sai sa?e-sa?e take bayan sun gama sai ya kaita can wurin Teku Cotonou .Daga inda take tsaye take hango wani haske can tsakiyar ruwan,ta ?an?ance ido tana kallo sai ta ga wani ?aton kifi ya fito tare da sake yin nitso ba ta san lokacin da ta ce  dubi kifi ta nuna masa da hannu.


Dr Mu'az ya ce  da gaske kin ga kifi? ta buWe baki za ta basa amsa kifin ya sake yin sufa ya fito wannan karon SEERAT ta gani zaune daram kansa kafin ya koma cikin ruwan.
Ta waro ido tana jin zuciyarta na Wan bugawa,ganin ba za ta basa amsa ba kawai ya ja ta suka koma mota direba ya ja su zuwa gida.Wannan karon babu kowa tsit yake,part Winsu suka wuce Dr Mu'az sai hira yake yi mata don gusar mata da damuwarta ita kuma tun tana saurarensa har bacci ya Wauke ta.

Ko da ta farka ba ta gansa ba,yunwa take ji sosai sai ta fita falo duk da tana tsoron cin abincinsu har yanzu babu kowa gidan tsit yake tamkar ita Waya ce ma a ciki.Hanyar da take tunanin kitchen ce ta nufa,komai jere yake ras babu datti daga bayanta ta ji motsi ta juyo da sauri sai ta ga ashe Dr Mu'az ne.Ya sakar mata murmushi tare da mi?o mata ledar hannunsa ta karSa tare da fitowa tana cewa  gidan yayi shiru
 Ai ba za su sake fitowa ba sai kuma wani lokaci


Da mamaki ta dube shi ta ce  don me?
 Hum!" Shine kawai abin da ya ce har suka isa sashensu,ledar ta buWe kayan ma?ulashe ne Cocao Win ta soma ci har sai da ta ?oshi ta hauda madara.




#NIJAR

Da kuka da zubar majina aka SanSare ni daga jikin Yaya Khaleed wanda yake tsaye cikin shirin tafiya Yamai.A gaban idona ya shiga mota yana Waga min hannu,shi kansa a fuskarsa ina iya hango rashin jin daWin rabuwar tamu.Haka muka dawo gida ni da Ammy,tamkar wata laSuSuwa haka na koma ina manne a jikinta maraici duk ya dabaibaye ni ta ko ina.Dakyar na iya barin ta shiga kitchen ta yi mana girki,ina nan kwance ina tunani iri-iri sai ji na yi tana cewa  SEERAT za ku je ke da BASHEER ku yi wa Mamarku sati guda sai ku dawo,zan je makarantarku na shaida musu

Wani irin daWi ne na ji ya rufe ni ban san lokacin da na mi?e na je na rungume Ammy ba,a gaban idona ta haWa kayanmu.Basheer na dawowa daga yawonsa na je da murna na faWa jikinsa ina cewa  albishirin ka?

Bai ce komai ba sai murmushi da yayi min yana mai jan tsoron kitsona,na buge hannunsa na ce  kai ai ba ka san abun arziki ba ina cewa albishir shine ka yi wani banza da ni

Ya kamo tsintsiyar hannuna ya ce  SEERAT na fi ki za?uwa da mu je gun Mama fa
 Ya aka yi ka san can za mu je?


 Ke zo ki ga wani abu ya faWa tare da jan hannuna zuwa tsakar gida,irin tsuntsuwar nan ce wacce na taSa ganin Yaya Khaleed na bata abinci.
 Tun Wazu take zagayen gidan nan ko me take nema oho cewar BASHEER.

Ni kuwa tambarin da ke kusan wuyanta kawai nake kallo tabbas na san shi amma na manta . Tsuntsuwa ce fa kawai na furta zan koma ciki amma Basheer ya ri?e min hannu yana mai cewa  mi ya haWa ku faWa da Bafulatanarki?

 Wace Bafulatana ? na tambaye shi,yayi min wani kallo kafin ya ce  kar ki raina min hankali mana kin zata ban sani ba?
 Mi ka sani? na faWa don son tabbatar da shin gaske ya sani Win,hannuna ya jim?e sosai har sai da na yi ?ara cike da azaba na basa amsa  ni ma ban sani ba kawai dai ta bar zuwa
Ya sake min hannu yana dariya tare da yin gaba,na bi shi da kallo ina mamakin yadda Basheer ke da ?arfi har haka.


Da dare sai da Ammy ta kira mana Mama muka yi ?ar hira tare da faWa mata jibi za mu zo ita ma ta nuna murnar ta .Da Daddy ya dawo Ammy ce ta yi masa bayani,da farko har zai hana amma kuma sai ya ha?ura.A cikin kwana biyu aka shirya tafiyarmu,gidan mota Daddy y kai mu bayan ya mi?awa Basheer kuWin da za mu ci abinci a hanya.Daga Zinder motarmu da ta tashi ta Maradi muka fara biyowa,muka tsaya aka ?ara Waukar wasu kafin mu cira zuwa Niamey.Ina kusan window yayin da Basheer ke gefena yana bacci,na juyo tare da tsura wa fuskarsa ido tamkar wani Zaki haka nake ganin fuskar na rikiWa.Cikin magagin bacci yayi kamar zai faWi amma na yi saurin taro shi na kwantar da kansa a kafaWata,ya Wan ware ido kaWan yana kallona kafin ya ci gaba da baccinsa.Sai da motar ta tsaya wani gari ne sannan na tashe shi,a tare muka fito muka yi tsaye muna kallon wurin.Dukkanmu yau ne muka soma yin balaguro, yunwa fa nake ji cewar Basheer,na dube shi abin da na lura tun da aka ce za mu yi tafiyar nan ya soma cin tsiya kamar mai MACIJIN CIKI (MRS SADAUKI).



 Ni dai fitsari zan yi na faWa ina kallon banWakunan da aka rubuta na mata ne, to in kin gama sai kuma cikin mota ni bari na sayo mana abinci a haka muka rabu na je na Wauki buta sai da na jira wata ta fito sannan na shiga ina fitowa kuwa na koma cikin mota.


Ina ta jiran BASHEER amma shiru ga mutane sai shigowa suke tuni kuma direba ya zauna mazauninsa yana tambayar in kowa ya shigo,duk suka amsa kowa na kusa da shi ya dawo amma banda ni da tuni na mi?e ina cewa  ?anena bai dawo ba don Allah ku tsaya na dubo shi na faWa kamar zan yi kuka tare da fita.Duk sai da na bincike gidan motar amma ban ga Basheer ba ina jin direba na min horne amma na yi banza da shi sai raba ido nake.


 Ke ki tawo mu tafi kin wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login