Showing 21001 words to 24000 words out of 135404 words

Chapter 8 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46377

mu gani, in tusa zata hura wuta).

Ko bayan dawowar Daddy da bai tarar da shi a parlour tare da Mom ɗin shi ba yasa yayi tunanin ko bacci yayi tunda ba wani hutawa yayi ba.

★★★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Wasa wasa sati guda kenan Ƴar Iya bata shiga sabgar kowa ba haka babu mai shiga tata saboda tsoro. Aunty Ajiram kaɗai ke samun magantuwa da ita cikin sauƙi kuma Alhamdulillah su Ƴar Iya cikin satin nan an iya ABCD zuwa Z wanda duk ƙwarin guiwar ta same ta ne daga Aunty Ajiram. Wasu lokutan takan ƙarfafa mata guiwa da rayuwar birni tuni Ƴar Iya an fara dagewa da karatu.

Malaman ma sukan yi mata uzuri duk iya shegen da zata yi basa tanka mata, idan kuma aka samu matsala sai su nemo Aunty Ajiram.

Dawowar su daga classroom kenan zasu je dining, Ƴar Iya babu abinda ke damun ta irin rashin cin abinci isasshe, sai a wani zuba mata abincin da ko baki baya wuce mata bare ya ƙarasa wuya har ya shiga ciki. (A faɗar ta kenan).

Bayan an zuba musu sun cinye taji bata ƙoshi ba ai kuwa ta ɗauki bowl nata ta koma wurin matar da ke serving nasu.
Ba tare da tace komai ba ta miƙa bowl ɗin da nufin a ƙara mata.

Abun ya ɗaurewa mai raba abincin kai don ita a tsawon aikin ta a nan almost 12-13years Bata taɓa zuba abinci wani ya dawo da sunan ƙari ba. Kallon mamaki take bin Ƴaƴan Iya da shi ko ina dalili gashi da gani sabuwar ɗaliba ce don bata san ta ba.

Students da basu bar dining ba tsayawa suka yi suna ganin ikon Allah, don kuwa so suke suga wannan drama ta Mama Jebu da Angel 👼 (Sunan da suka bata kenan don wannan basa mata kallon mutum cikakkiya).

Basu san ya aka yi ba kawai suka jiyo Muryar ta tana faɗin
“Kinga bigi-bigi bombom ki ƙara min bai ishe Ni ba”
Dariya students ɗin suka yi jin sunan da Angel ta ƙira Mama Jebu da shi, ai kuwa sunan ya dace da ita. Mama Jebu irin matan nan ne manya manya masu ƙirar maza, gata da ƙaton ɗuwawu don kuwa da ƙyar take tafiya kawai ƙarfin hali ne da neman halal ya danne ta har take iya wannan aikin na raba abinci wa ƴan makaranta.

Kallon banza Mama Jebu ta aiko mata tana faɗin “Ke amma sabuwar ɗaliba ce naga sai wani karambani kike yi?”
Ƴar Iya bata kula ta ba saboda Aunty Ajiram na gwaɓar ta kan ta koyi haƙuri thatz why ta ƙara miƙa bowl ɗin ta gaban Mama Jebu.
“Jiran ki nake bigi-bigi bombom”
Ai kuwa sai a lokacin Mama Jebu taji sunan da sabuwar ɗalibar ta ƙira ta da shi. A hasale ta zagayo daga gaban tukunyar tayi kan Ƴar Iya. Ƴar Iya da bata yi tsammani ba kawai taji dundu a bayan ta. Babu shiri ta janyo robar yaji da ta gani a gefen tukunyar, bata tsaya ɓata lokaci ba ta ɗiba ta watso wa Mama Jebu a ido.

Ihu Mama Jebu ta saka
“Wayyo Allah na na shiga uku, jama'a ku kawo ɗauki wayyoh wayyoh na shiga uku wayyoh ido na shikenan don Allah jama'a a taimaka min”
Ja da baya Ƴar Iya ta yi ganin Mama Jebu na ihu tana sowa, ga kuma lalume-lalume da take yi ganin ta taɓo wani.

Dariya sauran students suka fara wasu na madallah musamman foodies irin Ƴar Iya yayin da wasu ke jin tausayin ta amma babu damar taimaka mata, su je garin taimako Ƴar Iya ta dawo kan su?, A'a babu ruwan su.

Ana cikin haka wata student ta lallaɓa ta tafi clinic don samowa Mama Jebu ɗauki. Ƴar Iya kuwa kujera ta samu tana babbaka dariyar ta. Bata yi aune ba taji Muryar Aunty Ajiram na doka mata ƙira.
“A'ishatu A'isha”

Bata amsa ba sai ta lallaɓa bayan Mama Jebu da ke rausa ihu jikin ta sharƙaf da gumi da hawaye har da majina. ta ɓuya, ƙara damƙo wani yajin tayi a hannun ta, a hankali ta fara ware zanin Mama Jebu ta watsa mata tare da arta a na kare.

Bayan clinician ɗin yazo da ƙyar aka samu manya manyan students dake senior class suka tallafawa Mama Jebu aka wuce da ita clinic.
Taimakon gaggawa aka bata amma ina ta kasa buɗe idanuwan ta.

Duk wannan tsiya da Ƴar Iya ta tsula babu wanda yayi gigin kai ƙarar ta saboda tsoron abun da zai je ya dawo.

Washegari da yamma dai da ƙyar idon Mama Jebu ya buɗe, duk ta bi ta faɗa har abun tausayi. Bayan ta ji sauƙi clinician ɗin ya tambaye ta meh ya faru da idon nata, garin yaya ta zuba yaji haka a ciki.

Bayanin abinda ya faru tsakanin ta da sabuwar ɗaliba ta bashi tare da roƙon shi don Allah ya taya ta neman fada wurin Principal a samu a koru ɗalibar nan in ba haka ba zata iya kashe mutum wallahi.

A yau ne kuma da yamma aka sallamo uncle Bello daga asibiti, babu laifi jikin sa yayi ƙwari kuma fuzge-fuzge da kuma surutai da yake yi duk ya daina sai dai ma wani tsoron Ƴar Iya da ya ɗarsu a kogon zuciyar shi.

Bayan Ƴar Iya ta koma hostel Bata samu Aunty Ajiram ba hakan yasa tayi murna don ta san idan taji labarin abun da ya faru sai tayi mata faɗa.

(Nace, aaah an fa samu ci gaba, su ƴar iya har da gudun magana...eh..lallai kam).

Ganin bata samu AISHATU ba yasa ta yanke hukuncin dawo hostel. A kwance ta same ta tana sheƙa baccin ta hankali kwance, ƙarar gwartin ta ne kawai ke tashi.

“Aishstu Aishatu”, Aunty Ajiram ta faɗa tana tapping bayan ta “Tashi mana Aishstu”
Miƙa tayi ta tashi nan Aunty Ajiram ta tisa ta gaba akan abun da tayi wa Mama Jebu.
Kuka ta saka ita wallahi sharri akayi mata ita da yau ko dining Bata je ba ma akan bishiyar mangwaro take.
“Kuma tun ɗazu da na sauƙo daga bishiyar nan nan dawo na kwanta bacci, Aradu duk mai min sharri sai na hukunta shi”
“Shikenan ya isa na yadda dake, sharri aka yi miki, is ohk stop crying” ta faɗa tana tapping bayan ta cikin sigar rarrashi.

Sai dare aka ƙira Principal aka sanar da shi abun da ke faruwa, duk irin yadda yake tausayin Ƴar Iya da kuma jarrabawar da take ciki sai da ranshi ya ɓaci yana ayyana wa a ranshi wannan ai har da sakaci ba iya Aljanu ke saka ta yin hakan ba.

Principal yayi alƙawarin zai ɗau mataki a kanta, saboda yana jin tausayin Baban ta shiyasa ya barta da wannan karan babu mai hana shi koran ta a school ɗin.

Washegari da safe sai ga jiniya wiwiwi....wiwiwi.... Tun daga cikin hostel ɗin su ake jin ƙarar jiniyar, lokacin da yawa suke saka uniform don tafiya classroom.

Bayan motar tayi packing dai-dai office na Principal, wasu daga cikin Ƴan sandan suka shiga. Bayan sun gaida Principal suka sanar da shi aiko su da ogan su yayi.

Bai ɓata lokaci ba yace
“Hostel zaku je kuce waye Angel, in ta zo sai kuce tazo zaku kaita wurin Baffin ta da Iya. Kai tsaye ku wuce police station da ita, ku kaita ɗaki mai duhu sannan ku hukunta ta sosai sai taji jiki tukun ku ƙyale ta sai ku dawo min da ita nan”
“Alright ur wish is our command sir”

Daga haka suka fito da Principal's office, Basu tsaya ko ina ba sai hostel, a lokacin Ƴar Iya tare da Aunty Ajiram da ke riƙe da hannun ta suka fito daga hostel ɗin zasu wuce classroom.

Alama police ɗaya yayiwa Aunty Ajiram da tazo Saboda gargaɗin Principal Akan yarinyar na da hatsari gaske. Bayan Aunty Ajiram da Ƴar Iya sun ƙaraso yace
“Please sisters ku shiga hostel ɗin ku kuce Angel ta zo”

Shaye da mamaki suke kallon police ɗin...............


TOH INA TEAM ƳAR IYA, YAU FA ZAKU HAƊU DA GABAN KU!
KO ME ZAI FARU?
ZA'A TAFI DA ƳAR IYA POLICE STATION, KO A CAN NE ZATA YI HANKALI??

DUK AMSOSHIN KU SUNA A TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎.

COMMENT &SHARE PLEASE!


[5/1, 8:11 PM] 💎Diamond Bhatool💎:


🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __



SHAFI NA ‘‘‘‘‘23&24’’’’'

[Ƴan uwa na masu albarka ina muku nasiha da ku yawaita yin sadaƙa.
Ko kun san irin alkhairin da ke tattare da sadaƙa musamman gare mu mata?.

TOH bari kuji wani hadisi.
Daga Abi Sa'eed Alkudriyyu yace:
Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata a gare shi ya fita ranar sallar idi ƙarama ko babba zuwa wurin sallah, sai ya biyo ta wurin wasu mata daga wurin sai ya tsaya yace:
«Ya ku taron mata, ku yawaita sadaƙa, domin mafi yawancin ku kun kasance ƴan wuta»

Bukhari ya rawaito.

Mai buƙatar ƙarin bayani game da wannan hadisi tana iya yi min magana kai tsaye a nan WhatsApp +2347061707238].


Shaye da mamaki suke kallon police ɗin da ya basu wannan saƙo. Shiru suka yi su biyun, ganin sun yi shiru yasa police ɗin faɗin
“Kinga sister ki ƙira mana ita ba komai zai faru ba wurin Baffin ta za'a kai ta”

Jin an ambaci Baffi yasa Ƴar Iya faɗin
“Toh ai gani a gaban ku, Aradu da na fita kilasmum da wuri da bazan ga Baffi na ba, Allah sarki banda Iya zan gani?”
Ta tambaya tare da marairaice fuska.

Murmushi police ɗin yayi yace
“Har da Iya duk suna jiran ki, maza shigo Mu tafi.”
Ya faɗa yana nuna mata wurin da suke ajiye masu laifi in zasu tafi.
Aunty Ajiram haka nan taji babu daɗi daga nan tayi wa Ƴar Iya sallama.
“Ki gaida min Baffi da Iya kinji A'ishah?”
Kai ta gyaɗa tare da zagayawa don shiga wurin da aka nuna mata.

Ganin polisawa da yawa kusan biyar zaune suna pointing mata wani ɗan wuri a tsakiya yasa ta Banka musu harara.
“Kutumelesi, Aradu ni ba Ƴar Iska bace da zan shiga tsakiyar ku, sai dai ku koma can ku cakuɗu in ba haka ba na faɗawa ogan ku”

Ƙasa magana suka yi saboda tsantsar mamaki ganin yarinya ƙarama na tsula musu tsiya son ranta, ko mutuncin uniform ɗin su bata gani.
A harzuƙe ɗaya daga cikin su ya buga mata tsawa
“Oya get in or else I'll shoot u to death”
Ya faɗa yana saita ta da wata pistol ɗin roba. Ba shiri ganin bindiga ta shige ciki. Cikin ranta duk tsoro ya cika ta har ta fara tunanin satar bindiga.
“Wannan fah irin bindigar nan ne da ake kashe mutane da ita a TV, kutt, Aradu don wurin Baffi zasu Kaini amma sai na sace ɗaya saboda ƴan banzan mutane.


★★★★★★★★★


Zaune suke a katafaren dining area na gida, Daddy, Mom, Sarah sai kuma Fauzah. Babu abun da ke tashi sai ƙarar cokali yayin da na jiyo sautin taku daga staircase na gidan.

Sanye yake cikin wata haɗaɗɗiyar Black suit da farin shirt a ciki sai farin necktie. Sumar Kan shi ta sha gyara sai wani ƙyalli take kamar wanda ta fito daga rijiyar mai, Black shoe ne a ƙafan shi sai kuma wani uban ƙamshi da yake yi na turaren _majesté impériale_ wanda tuni ya sanar da mutanen dake dining ɗin isowar shi.

Mom da tunda ta fara jiyo ƙamshin sa ta daina cin abincin sai sakin murmushi take haka Daddy yayin da Fauzah taji kamar ta tashita bar wurin. Idon Sarah ƙyam a kan shi yayin da shi kuma babu abinda yake kallo sai frame ɗin dake kallon shi, fuskar nan a tamke kamar kullum ammah hakan bai hana kyawun shi fitowa ba.

Yana ƙarasawa dining area kusan Mom ya fara zuwa yayi mata side hug tare da peck a cheek nata
“Good morning Mom”
Murmushi tayi tana faɗin
“Morning first love, how's your night?”
“Absolutely fine one”
“Alhamdulillah”
Daga nan ya ƙarasa zuwa wurin Daddy, kamar yadda yayi wa Mom haka suka gaisa da Daddy tukun ya samu kujerar shi ya zauna.

Mom da kanta tayi serving nashi cips and fried egg sai Hot coffee.
A hankali Fauzah tace “Good morning Hamma Zaki”
Ba tare da ya ɗago ba yace
“Morning”
Sarah ma ta gaida shi ya amsa kamar baya so.

Fauzah ce ta fara barin dining ɗin ta ɗauko school bag nata tayi waje, Sarah ma ta miƙe zuwa bedroom ɗin ta. Ya rage saura Mom da Daddy.
Daddy ya kalli Hamma Zaki ɗauke da murmushi a kan fuskar shi
“Daddy's love jiya na dawo da dare, I was thinking of meeting you a parlour sai na tarar kayi bacci ma”
Shima murmushin yayi yace
“I'm sorry Daddy, I'll squeeze and have time with u”
Daga haka ya miƙe yana waving hands
“Bye, Mom and Daddy”

Yana fita Joseph ya zo ya amshi Briefcase nashi zuwa mota, daga nan driver ya ja motar sai Barrack.
Bai dawo ba sai wajen yamma saboda ayyukan da ke gaban shi.

A wahalce ya dawo, yayi wanka sannan ya wuce bedroom ɗin Mom. Saman sallaya ya same ta alamar sallah tayi. Sallama yayi ya shige daga nan ya samu gefen sallayar ya ɗan kwanta yana ɗora kanshi akan cinyar ta.

Murmushi Mom tayi tace
“Welcome back Son”
“Thanks Mom”
“Ya aikin dai, da alamu ka gaji da yawa, muje kaci abinci”
Kan shi ya jijjiga saying
“No Mom, Ina cake ɗin da kika yi baking?, Shi nake so sai Hot coffee”
“Ohk ɗaga Ni na haɗo maka”
Kwaɓe face yayi yace
“Nifah Mom ban gaji da cinyar ba, baki ganin ina jimawa ban hau ba...da na hau kuma sai ki tashe ni”
Murmushi tayi tana jan kumatun shi
“Toh shikenan sai ka zauna da yunwa haka kake so?”
“Auchh..sakar min kunnen mana ko so kike ya cire saboda yafi naki kyau?”
“No yi haƙuri Son Bari na haɗo maka.”

Dining ya wuce ya jira Mom sai gata ɗauke da cakes cikin bowl sai kuma hot coffee a kan tray.
Da kanta tayi feeding sakaltaccen yaron ta daga nan ta kawo mishi batun Sarah coz sun taɓa magana da Mommyn Sarah ɗin wai tana so su haɗa yaran aure. Mom ɗin Sarah cousin ɗin Mom ce.

“Son Kun gaisa da Sarah kuwa?, Ta zo ne saboda kai Please ka ke sakar mata fuska”
Fuskar shi ya ɓata yana tura baki
“Wai Ni Mom meyasa kuke son cusa mutane cikin rayuwa ta, bana buƙatar kowa bayan ku don Allah Mom ku daina zubo mutane rayuwar classic yaron ku”
Dariya Mom tayi coz Bata son duk wani abu da favourite ɗin ta baya so.
“Is ok Son, na daina but ko ba komai Sarah is your sister”
“I know, all I hate from her shine rashin kamun kanta, but if she'll change me too I'll change”

Bayan ya gama ci ya ce ma Mom zai je garden zuwa maghrib.

★★★★★★★★★★★

*POLICE STATION*

Suna isa duk suka dire haka Ƴar Iya ma tayi ganin yadda suka yi. Kallon su tayi tace
“Ina Baffi?”
Banza suka yi mata yayin da biyu daga ciki suka fizgo hannun ta, tana turjewa suna ja har suka isa ciki. Da yake an riga an musu bayanin me zasu yi tuni suka shigar da ita Cell. Fitowa suka yi don su nemo abun da zasu hukunta ta da shi bayan sun sakawa ƙofar kwaɗo da key.

Few minutes suka dawo ɗauke da Koboko (Dorina) irin wacce ake jibgar Dawaki da ita, suka haɗo da bucket cike da ruwan sanyi har wani tururi yake yana fitar da raɓa.

Ƴar Iya da ke cikin Cell hankalin ta baya kan su duk tunanin ta Baffi zasu ƙira mata. Har suka buɗe ƙofar bata sani ba, babu zato babu tsammani police ɗaya ya janye Hijabin check ɗin ta, tuni ta fito daga duniyar tunani ta fuskanci duniyar asali. Tana juyowa kuwa ɗayan ya fizge rigar ta da sauri yayin da ɗayan ya zame wandon.

Tsabar mamaki da ya cika ta rasa me zata yi ma tayi.
“Kutumar Uba, me nayi muku zaku cire min kaya na?, Dama ba gun Baffi zaku Kaini ba ku Ƴan Iska ne?”

Bata aune ba taji ruwan sanyi a jikin ta...tuni ta fara rawar sanyi, yo ita wankan ma yaushe tayi shi ballantana ma da ruwa irin wannan. Har abun tausayi yadda take rawar sanyin ammah su basu ji ba, wani bucket ɗin suka ƙara janyowa suka ƙara tsula mata shi tas.

(Toh fah Ƴar Iya yau kin gamu da gamon ki).

Sai da suka tabbatar sanyin ya ratsa ta suka ciro dorinonin su suka fara sharɓa mata, irin yanayin da take ci ba zata iya ƙwatar kanta ba saboda zazzaɓin da ya rufe ta lokacin ɗaya.

Dukan ta suke yi su biyu da dorinonin su tun tana ihu har Muryar ta ta dishe ta daina fita da kai. Duk da haka maimakon su sarara mata saboda ƙarancin shekaru irin nata sai suka ci gaba da dukan ta har sai da ta daina motsi.

(ALLAH SARKI, ƳAR IYA AN MUTU)

A haka suka fice suka barta. Ta share kusan awa biyu zuwa uku a suke kafin ta farfaɗo, lokacin kuma zazzaɓin da take ji ya sake ta tana buɗe idon ta ya sauƙa a kan baƙin ɗakin da take, nan ta fara tariyo abun da ya faru da ita.

Babu shiri ta fara miƙewa, a hankali ta janyo wandon ta da har ya bushe da kuma rigar ta ta ƙwama, bata ƙara bi takan hijabin ba ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar sai dai ƙyam ƙofa taƙi buɗuwa alamun akwai padlock jiki. Ba tare da ta damu ba ta fara jan ƙofar da iyakar ƙarfin ta.

Kyawawan ja guda uku tayi lock ɗin jikin ƙofar ya ɓalle, wangalewa tayi ta fito. A reception ta fara tarar da wasu polisawa saboda haka tayi kansu ba tare da ɓaga lokaci ba. Wani katako ta gani a gefe ai kuwa ta wawuro shi tayi kan su.

Tsabar mamaki da jin kai irin na polisawa suka ƙame suna jiran ganin ƙarshen iskancin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login