Showing 126001 words to 129000 words out of 135404 words

Chapter 43 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46368

ma ƙamshin da take fitarwa ne ta kowanne saƙo, he can't control himself to the act. Lumshe idanunsa ya ƙara yi yana ƙara tuna roƙonta na ya barta but baya ji, don duk tsawon rayuwarsa da pretty he's not satisfied fully even once, he's only managing Amma for only today yadda yake jin kasa emotionally and physically happy and active yasa ya ƙara gode ma Allahn da halicci khairy.

Iƙama da yaji an tayar yasa ya zaro idanuwa yana kai dubansa ga khairy wacce ke baccin wahala, a hankali ya sauƙa ya nufi toilet, ya ko jam'i bai fita ba a nan yayi kayarsa sannan ya fara tunanin ta yaya zai tashi Nour ɗinnasa.
A hankali ya ranƙwafo dai-dai kuncinta ya ajiye mata peck sannan ya hura mata iska cikin kunnenta, kamar a mafarki ta fara buɗe idanuwanta da suka yi nauyi kamar an ɗaura abu a kansu. Mayar da su tayi babu shiri jin sauƙar wani yasa ta buɗe idanuwan babu shiri kuma akan fuskarsa, nazari tayi na ƴan sakanni sannan ta janye idanunta gefe, murmushi master yayi yana faɗin “Nour, zaki iya tashi ko na kai ki ki gyara jikinki kiyi salla?” ba tada ƙarfin tashin yasa ta jijjiga masa kai, kamar wata baby ya ɗauko ta daga bed ɗin ya nufi bedroom da ita, bayan ya bata necessary help da ya kamata ya barta tayi wankan tsarki da alwala sannan ya barta. Ganin ya juya yasa ta ce “Mugu kawai!”

Haka dai tayi alwalar ta fito a daddafe kanta ƙasa sai famar tura baki take, kallonta kawai yake yana murmushi sannan ya ƙarasa gare ta tare da zaunar da ita bakin bed, wasu pyjamas ya dubo mata ya sanya mata kafin ya tallafa mata zuwa wurin sallayar ya saka mata hijab. Ganin ta shiga sallar yasa ya kwashe spoiled linens ɗin ya nufi washing machine da su a take ya kunna sannan ya dawo ya ciro wasu ya shimfiɗa, ganin ta idar da sallar ne yasa Hamma Zaki matsowa kan sallayar kusa da ita ya zauna, kame jikinta tayi saboda yadda jiya yayi riding nata, tayi tunanin ma ta mutu ne, kamar ya san me take faɗa yace “Good morning Noor, how's your night ” ya idasa yana zuba mata idanunsa, kan ta ta ƙara duƙarwa saboda matsananciyar kunyarsa da take ji. Calmly ya Kai hannunsa yana ɗaga haɓarta sama ta yadda zasu haɗa ido sai dai idonta gyam yake amma hawaye na sintiri daga cikinsu.

“Ya Allah!” ya furta yana kwantar da kanta bisa cibiyoyin sa wanda yayi mata matashi da su. A hankali cikin wata murya yace “Ummul khairy!” ba tare da ta buɗe idanun ba ba kuma ta tsayar da hawayen da ke zuba ba ta ɗan motsa. “Kina ji?” nan ma signal kawai ta ɗanyi.
“I'm so sorry for everything, kiyi haƙuri na wahalar da ke” rasa me me zai ƙara cewa yayi hakan yasa ya ɗan ɗaga kansa sama can kuma ya ce “Kiyi haƙuri Khairy, yanzu me zaki ci nayi mana order?, ina ke Miki ciwo?”

_Comment Please_
[27/09, 6:09 p.m.] Famanté 💎: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““123&124”””

_Ina matuƙar godiya gare ku:_

_Ameena Uthman (Ameeran Mama)_
_Fatima Abubakar Sherif_
_Sumaiya Abdullahi_
_Fatima Zarah_
_Maryam Muhammad_
_Nafisatoul ilmu_
_Queen Bee_
_Mrs Bilal_
_Hauwau Idris_
_Bareera Muhammad Lawal_
_Maman Aslam_
_Thanks for always being there for me, your love and support always empower the Diamond Bhatool's ink 🔏, thanks for your amazing and wonderful comments, Allah ya bar ƙauna Ameen_ 😘 💕

Da Kuka ta fashe mishi wanda ya tayar da hankalinsa, kwacakom ya ɗaga ta daga kan sallayar yayi kan gadon ta ita still not looking calm, “Please say a word Nour, wurin ne yake zafi har yanzu?” kai ta ɗan gyaɗa masa, “Shikenan to muje na ƙara haɗa Miki ruwa masu zafi?” “Ni aaaaa” ta faɗa a shagwaɓe kuma idanunta na rufe.
Ɗan dafe kansa yayi yace “Then tell me what do I wanna chop?” shiru ta ƙara yi masa. Ƙoƙarin zare mata Hijab ɗin da yayi yasa ta ƙanƙame shi da kyau, shi dariya ma ta bashi hakan yasa yayi ta babu ƙaƙƙautawa.

“Allah bana so Hamma, You are wicked man ka mayar da Ni bedroom ɗina”
“An ƙi a maida ke, kin taɓa ganin yadda aka raba hanta da jini?”
Turo baki gaba tayi tana yamutsa fuska yace “To zan sha tea”
“Bari na sa a kawo mana” duk ita tunaninta zai fita ya haɗo ne, sai ta gudu tayi locking door nata, jin amsarsa yasa ta saki wani kukan shagwaɓar wanda ya sa shi kusan zaucewa.
A ransa ya furta “This girl want to kill me”
Ɗam dafe kansa yayi yana mamakin yadda khairy ta iya rigima kamar wata baby girl.
“What again Nour?”
“Ni yanzu zan sha ka tashi ka haɗa min”
“Na ƙi wayon” ya bata amsa yana sakin wata dariya “In Kinga na tashi Nan to kin warke ne, ko barrack ba na ƙara zuwa sai nan da 3weeks.”
Bata san lokacin da ta buɗe idonta tana kallonsa ba.

He can't afford to maintain silent Hakan yasa yayi dariyarsa son fans kafin yace “Kinga Nour please kada ki wahalar da Ni, I'm sorry me zan sa a kawo Miki?” cikin ranta tace “Wai shi zai ce ma kada na wahalar shi bayan jiya duk ya rikita Ni yadda Inna ta ta haife ni” kamar yasan me ta faɗi yace “Eh mana, kina bani wahala Khairy, say something please ”
Kamar zata yi kuka tace “Ni ɗanwake nake so” zaro ido yayi yace “What!” a shagwaɓe ta ƙara cewa “Ɗan wake”. Tunanin ma ina zai samu ɗanwake yake yi can ya tuna da Aunty Waheeda In-law ɗinshi na gari, da sauri yayi dialling number Hamma Saleem, nan ya faɗa masa don Allah ya sa Aunty tayi ma khairy ɗanwake, dariya Hamma Saleem yayi yana tsokanarsa wai an samu cikar buri, kar dai ya kashe yarinya.

Katse ƙiran yayi tunda ya isar da saƙonsa nan ya ci gaba da kulawa da Baby girl ɗin nasa. An hour later Hamma Saleem ya iso, daga bakin gate ya bawa gateman sannan ya ƙira ya sanar da maza cewa ya kawo abinci. Kwantar da Khairy yayi gefe ya sauƙo, bayan ya amsa ya koma ciki. Plate ya ɗauka da spoon ya wuce yana murmushi ya ƙarasa yana faɗin “Nour, tashi na kawo ɗanwaken, bari na haɗo Miki tea” Kai ta jijjiga alamar bata so, bai takura mata ba ya ɗauko wasu minerals don bai san nata choice ɗin ba, da kanshi yayi feeding nata duk irin yadda ya so su haɗa ido ta ƙi ba shi dama. A haka har ta ƙoshi tukun shima ya ci, bayan ya gama ya tattara ya fita, miƙewa tayi da niyyar guduwa ta gagara, hakan ya sa ta koma ta zauna.

Da yamma hamma zaki ya fita, direct barrack nasu ya wuce ya gama renewing transfer da ya so yi kwanakin baya, he want to enjoy this short lire with his Nour, bayan ya kammala yq biya wurin Dr. Shi dai baki buɗe yake kallonsa don in ka ga ya taka masa fa to.. bayan sun gaisa Dr ya bi Hamma Zaki da kallon ƙurilla, ganin ya na son takura shi yasa yace “Cinye ni zaka yi ne?” dariya Dr. Yayi yace “Ina Ni ina cinye ƙatoton soja, sojan ma ango wanda kwana ɗaya ne rabo na da shi amma naga duk ya sauya, Please man meye Sirrin ne?” ya idasa yana kanne masa ido. Hararar wasa ya galla masa saying “Abun sirri ne” dariya Dr yayi yace “Ka faɗawa baƙo a garin, ka ga wallahi ka ga yadda kayi wani fresh yau ɗin nan” jin an gwaɗa shi yasa yace “Shi yasa zan ɗan bar garin na kwanaki kaɗan,” ya faɗa yana nuna masa takardun hannunsa
Ko kaɗan baya son yin nesa da abokin nasa amma tunda ya riga ya kammala cikewa ai shikenan.
“To yanzu yaushe ne zaku keta hazon?”
“In a day time in sha Allah ”
“Ok safe journey, Amma Ka daure ka kawo mana amaryar gobe ko kuma mu muzo”
“Sai dai ku zo ɗin kawai, zan wuce gida, bye”

Daga nan ya wuce Naira Family House, nan ya sanar da su batun transfer da ya nema zuwa Lagos but before zasu wuce honeymoon tare da khairy, Mom dai bata so ba ta ce “Ita kuma Nabilar fa?” sai lokacin ma ya tuna ashe bai faɗa musu ba. Ƙeya ya fara sosawa alamar rashin gaskiya sannan yace “Dama Mom, eh dama i divorced her 2days before” ya idasa yana sunkuyar da kanshi, baki buɗe Mom ke kallonsa tace “Toooo, what do you mean son, yaushe kuma me yasa”
Bayani yayi mata bayani daki-daki, sosai ran Mom ya ɓaci har tana faɗin sai ta haɗa su Pretty da hukuma, rarrashinta yayi tukun ta yadda daga nan ta ɗaura masa da nasiha sosai kafin ta ce Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, bayan nan ya shiga sauran sassan gidan ya sanar da su, Mom da kanta ta sanar da Granny. Granny tayi ƴan surutanta tana faɗin bai fi ma Khairyn ta tayi zaman daɗi ba.

Yana gamawa ya wuce Restaurant yayi musu takeaway na abinci da abun sha daga nan ya nufi gida. Yini tayi tana shiga ruwan zafi shi yasa ma ta ɗan ji dama-dama amma tayi alƙawarin ba zata ƙara bashi chance ba har sai ya bayyana Sirrin da ke ransa. Ko da ya dawo haka ya sa ta gaba sai ta ci wani abu ganin taƙi ci yasa ya koma lallashi, da ƙyar ta ci, daga nan ta maƙale wai ita bacci zata yi. Shi ma da rigima haka ya saka ta gaba sai da tayi wanka tukun, nan ta tada rigimar ita gaskiya ba zata shirya a nan ba sai dai ya Kaita bedroom nata, kayan bacci ya nema mata ya kawo mata kafin nan ya ce zai wuce toilet ta shirya kafin ya fito, sai da ta tabbatar ya shiga tukun ta shirya a hanzarce daga nan ta haye can ƙarshen gadon ta kwanta.

Dariya yayi ƙasa-ƙasa da ya fito ganin yadda ta kwanta, bayan ya gama shirinsa yayi shafa'i da witri kafin ya haye gadon. Ganin yana shirin ƙara nuna mata shi shi ne yasa ta fashe masa da kuka mai ban tausayi, a halin da yake ciki kuwa lokacin gani yake kamar in ta hana shi zai rasa rayuwarsa ne, roƙonta yayi har sai da ya kusa haƙura tukun ta basa dama. Bayan ya samu natsuwa ya jawota jikinsa ya rungume ta sosai yana sauƙe ajiyar zuciya. Da kansa ya gasa mata jiki sannan ya barta tayi wankan tsarki, bedroom nata ya koma ya ƙara ɗauko mata wasu kayan baccin lokacin ta gama ta fito sta shirya shima ya shiga, nan suka koma suka kwanta.

Cikin wata sassanyar murya yace “Na gode Ummu khairy, Allah yayi Miki albarka, tabbas kin matuƙar kasance ta musamman da kika kawo budurcin ki zuwa gidan mijinki, kin saka ni cikin farin cikin da na daɗr ban ji shi ba, Nour” ya ɗan dakata yayi pecking gefen fuskarta da ke lafe da jikinsa. “You Are special to me, special in the sense that I can sacrifice everything I owned for you, thank you Khairy, ki ce wani abu kin bar Ni ina ta zuba”.

A shagwaɓe ta ce “Bayan ba ka so na kuma shine shine...”
“Shhh!” ya katse ta “Who told you that!, ɗago ki kalle ni ki faɗa min” ya idasa yana ɗago fuskarta tana Fuskantar sa, ido rufe ta Turo baki, kissing bakin yayi yace “Tell me Mah friend, Wye yace Miki Bana son ki?”
“To to ai haka ne, ko da aka saka bikin mu baka taɓa zuwa ko sau ɗaya ka duba Ni ba!”
Dariya yayi yace “I'm sorry Nour, ba haka bane, I don't know that you the one, da ace na san ke ce ai da tun ranar da aka sanar da Ni batun sai nayi kyautar kujerar Makka ga waɗanda suka haɗa bikin ”
Tace “Ba wani nan, don't cover off Hamma, you don't love me, kawai ka karɓi auren ne saboda su Granny,”
Yatsarsa yasa a bakinta yace “Shhh Haba Nour, don't say that please ” ƙunƙuni ta ɗan fara yi hakan yasa ya ɗan dafa kansa don ya kasa sanar da ita irin yadda yake son ta. A hankali ya daidaici kunnenta ya furta mata “I love You Khairy!” a ɗan zabure ta buɗe ido tana kallonsa, har ta ma manta da batun kunyarsa.

“Hamma Wasa kake ko?, kana so na irin na ƴarn uwantaka ne” ta faɗa tana maida idonta rufe.
“Ya Salam, Habibatur-rhouh, You wanna make me cry abi?, I love you and I mean it, kin san tun yaushe na fara dakon soyayyarki?”
“Tun ranar da muka kaiki gidan Sheikh Imam na fara tausayawa rayuwarki, hakan ya sa na karɓe duk wata hidima taku ke da su Fauzah, a lokacin ban san ina son ki ba har sai da kika dawo gida na don ki taya pretty zama” ya ɗan tsaya yana haɗiye wani abu da ya tsaya mai.
“Annabi yace ‘Zuciya tana son mai kyautata mata, sannan tana gudun mai munana mata’, Ummul Khairy kulawarki gare Ni Ko matar da nake aure a lokacin bata nuna min ita, zuwan ki gidan an samu sauyi da dama, rai da ruhi, jiki da jini ban san son ki ya kama mi ba har lokacin sai dai na kan tsinci kaina da yawan tunane-tunanen ki lokuta da dama, ban danganta hakan da so ba tunda ban san shi ba kuma ban taɓa ba.”

“Akwai wasu suprise da nake son Miki, kina ji?, haka kawai saboda irin kyautatawar ki da kuma kyawawan halayen ki naji kina burge Ni, a lokacin ne kuma naji labarin kina cikin masu sauƙe Alqur'ani duk da cewa baki fara kan lokaci ba, ƙwazon ki ya sa kika ƙara samun fantasy daga gare Ni, kin tuna na je taron har muka yi pics?”

Tunawa da pictures ɗin da ta gani a lokacin da aka yi kidnapping nasa tayi, sai ta ƙara lafewa jikinsa, “Waɗannan pictures ɗin kowannen lokaci ina cikin kallonsu, har wata rana aboki na Captain Sulaiman ya kama ni, ya yi diagnosing na wai I'm in love, da farko I don't believe him because i know nothing about it, gradually the feelings upgrades to the highest level in the sense that komai zanyi i must think of you.” ɗan saurarawa yayi ganin kamar tayi bacci cikin wata irin murya yace “Are you asleep?” “Yet to” ta bashi amsa
Murmushi yayi yace kina ji na ina?”
Kai ta gyaɗa masa. Daga haka ya ci gaba da zubo mata bayani kamar dai ba wannan miskilin Hamma Zaki da muka sani wanda kewa kowa kwarjini, Zaki shugaban dawa kuma babban matashin sojan nan and then....the most handsome and adorable partner ɗin Khairy wato Ƴar Iya ta mu uwar ta'adi da ɓarna, Ƴar Iya tamu ta Gallara Mutuniyar Aunty Ajiram Kuma.

*Comment Please*
[27/09, 6:11 p.m.] Famanté 💎: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““125&126”””

_Special thanks to my fellow colleagues and tutors:_
_Matar Dear, marubuciyar littafin Duhun Daji, Uncle J da Kuma albasa._
_Salma Ahmad Isa, the writer of the book Juyin kwaɗo, knowledge and wisdom were invested there, awwn😘_
_Nainar Kd, the writer of Ba tabbas._
More ink to your amazing pens and I pray for Allah's Baraka and Noor toward you guys, you mean so much to me._

“A lokacin da aka yi kidnapping na kuma bayan na dawo ina da niyyar bayyanar da soyayya ta ga Granny na San zata so hakan kawai sai naji wani zance wai an riga an saka Miki Rana da wani, and the worst part of it is ni ma an zaɓar min mata, zabar takaici yasa ban taɓa dubo matar ba tunda aka saka ranar don har zuwa lokacin na kasa mantawa da ke duk iya ƙoƙari na, ina son ki sosai Ummul Khairy don tsawon lokacin nan da nayi bana da cikakkiyar lafiya kawai ina yawo ne and wearing smiley face just because ban son masoya na shiga damuwa. I love You khairy, and I hope you will love me ko da rabin yadda nake son ki ne don i believe that ba zaki so ni kamar yadda nake sonki ba”.

Bata yi niyyar fallasa asirin zuciyarta kwana kusa ba amma jin kalamansa yasa ta ce “ Noooo i no gree, wata ƙila soyayyar da nake maka ma ta ninka wacce kake min Hamma., ka san tun yaushe nake dakon soyayyarki?, at first i was in love with your pictures, nima ban san so ba Hamma, Tashi na babu wanda ya taɓa nuna ƙaunarsa ga rayuwa ta bayan Iya ta da Baffi na duk saboda dalilin da ba shi da tushe, ba ni nayi kaina ba bare ace ni na so na zama haka, nayi rayuwa tsawon lokaci a matsayin rabi mutum rabi aljan, ina aikata abubuwa kamar ba bil'adama ba, lokaci daya kaddara mai kyau ta hadu da Ni, sanadiyyar zuwan haske rayuwa ta, sanadin da rayuwa ta ta sauya, Uncle Suraj, bai ƙyamace ni ba ya saka ni cikin ahalinsa, suma babu wadda ke nuna min tsana, lokaci guda na san so da kuma zan sani sai na fara a kan picture naka!”

Hugging nata tightly yayi jin wannan batu ashe ba komai ya sani game da ita ba, gaskiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login