Showing 24001 words to 27000 words out of 135404 words
yarinyar. Gani suke yi kamar ƙaramar mahaukaciya ce shiyasa kowa yayi ƙyam.
Ba tare da wani tunani ba Ƴar Iya ta sa hannu cikin aljihun ta da ta cika shi da yashi ta watsa a fuskar su. Nan fa suka farga zasu fara guduwa, ƙara ciko hannun ta tayi ta watsa musu.
Sai da ta tabbatar idanuwan su sun raunana ta janyo na baki-baki tare da buga mishi katakon a ƙafar hagu, ta juyar da shi dama ta ƙara buga mishi nan da nan ya cilla ƙara tare da faɗuwa yana sowa.
“Wayyo ƙafa ta na shiga uku wayyoh Allah wayyoh shikenan ta karya Ni wayyo”
Jin ihun da ɗan uwan su ke yi yasa suka far lalume zasu buɗe office ɗin da ke kusa sai dai ina ta riga ta far musu da shiri.
Haka ta ringa bugun ƙafafuwan su da katako tana yasar da su, polisawan da ke bakin Gate ne suka jiyo ihu nan da nan suka shigo ciki don ganin me yake faruwa.
Kafin shigowar su kuwa ta gano fuskar mugayen da suka buge ta ai kuwa tayi kan na farko. Hannun sa na dama ta samu ta buga mishi katakon da ƙarfi sannan na hagu daga nan ta buge masa ƙafafuwa kamar yadda ta bugawa sauran.
Haka ta jawo ɗayan shima ta fara bugun shi kamar yadda tayi wa ɗayan sannan ta bar shi ƙasa ta dawo gefe tana maida numfashi.
Ganin aika-aikar da yarinyar tayi yasa duk suka fara jin shakkun ta. Kallon su tayi tace.
“In ba zaku kai ni gun Baffi na ba to ku mayar da ni sukul ni wurin Iya ta zan koma Aradu birni duk mungaye ne”
Kuka ta raushe da shi kamar ba ita ce wacce ta nakasa waɗannan tarin ƴan sanda da sun kai takwas ba.
A gaggauce suka fara kwasar ƴan sandan suna jera su cikin mota ba tare da sun bi ta kan Ƴar Iya ba. Kai tsaye asibiti suka wuce a nan aka tabbatar musu da cewa duk sun samu karaya a ƙafafuwan su biyu biyu sai waɗannan biyun da suka karye a hannayen su.
Ƙiran DPO suka yi suka sanar da shi, nan da nan shima ya tsorata da al'amarin yarinyar yace su mayar da ita makarantar su kafin ya zo asibitin zasu yi magana da shugaban makarantar su.
Ba musu da suka koma police station suka nemo Ƴar Iya suka saka ta a mota sai school.................
Ina godiya sosai da addu'oin ku masoya na, masu ƙira da masu tura saƙo duk na gode Allah ya bar ƙauna. Babu daɗin yadda kuka damu da Ni, ina matuƙar son ku da yawa da yawa.
MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA.
KUN JI ƘUDURIN ƳAR IYA NA KOMAWA GUN IYAR TA DA BAFFI BAYAN TA KWASHI KASHI GURIN POLISAWA.
TOH FAH, GA KUMA DAI AN FARA SAMUN SAUYI TA ƁULLO DA TSIYA.
KU CI GAVA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎 DON NISHAƊANTUWA DA KUMA WA'AZANTUWA.
DIAMOND LADY 💎 CE
TOH ƳAR IYA NACE ALLAH YA TAIMAKA.
COMMENT AND SHARE FISABILILLAH!
[5/2, 9:03 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘25&26’’’’’
[Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata gare shi yace: «Akwai wasu kalmomi guda biyu masu soyuwa wurin Ubangiji, masu sauƙi akan harshe, masu nauyi akan mizani, sune _subhanallahi wabihamdihi subhanallahil azeem». Bukhari da Muslim suka ruwaito.
Ya ke Ƴar uwa mai albarka ki lazimci furta waɗannan kalmomi da basu da nauyi da wahala wurin faɗi domin mizanin ki ya nauyaya ranar sakamako]
Ba musu suna komawa police station suka Iya suka saka ta a mota sai school.
Kafin Isar su DPO ya ƙira Principal, ranshi a ɓace bayan Principal yayi picking call ɗin ya fara magana
“Haba Misbahu, fisabilillahi wa rasulihi me ka aikata haka?”
Kwantar da murya Principal yayi yace
“I'm sorry sir, wallahi an samu matsala ne”
“Matsala kake cewa eh, matsala koh?, To bari kaji in faɗi maka Yarinyar nan ba full mutum bace”
“Ban gane ba full mutum bace, kaga kofato ne a ƙafarta” Principal ya faɗa yana rarraba idanuwa.
Jin batun Principal yasa ran DPO ƙara ɓaci yace
“Eh kofato kake magana Misbahu?, Ana maka magana ta aika-aikar da yarinyar tayi kana batun kofato?”
“I'm sorry sir, kayi haƙuri ka faɗa min me tayi don Allah” Principal ya faɗa yana kwantar da murya.
“Toh bari kaji na faɗa maka yanzu polisawa takwas ne a karye, shida ƙafafuwan su biyu kuma hannu da ƙafa” ya faɗa cike da ƙosawa da jin zancen.
Principal da yabi ya ɗimauce, rasa abun faɗa yayi sai kawai yayi shiru.
“Ohk ba zaka ce komai ba Misbahu, lemme hang off the call” ya faɗa cikin hasala.
“Aaah ehma sir mamaki kawai nake yi wallahi, how can that small creature defeat nearly 8police officers?, Da farko ina tunanin dabara ce da ita ammah yanzu na gano tabbas ba mutum ɗin bace.”
Nan Principal ya bawa DPO dabarin Ƴar Iya Tun ranar zuwan ta zuwa wannan lokaci. Cike da fargaban abun da zai ƙara faruwa DPO ya bawa Principal shawara kan ya mayar da ita gida lallai-lallai in ba haka ba duk matsalar da ya shiga shi ya jawo ma kan shi.
Yana katse ƙiran ya ƙira Baffi kan cewa ana neman shi da gaggawa. Duk da cewa yammaci ne hakan bai hana shi amsawa da Toh ba. Nan da nan ya ƙira Shayibu don ya kai shi makarantar.
★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Tun kafin motar ta gama daidaita tsayuwa Ƴar Iya dire tana wani muzurai.
Da gudu ta arta sai hostel ɗin su, tana shiga ta faɗa kan Aunty Ajiram dake zaune alamun karatu ta gama.
Kukan da take yi kuwa har abun tausayi nan fa kowa ya zubowa Angel Ido ganin. Yadda take kuka bilhaƙƙi, wasu na tunanin taci wahala ne wurin polisawa wasu kuma suna tunanin ta cutar da polisawan. Kowa dai jira yake yaji me ya faru haka.
“Aishatu?” Aunty Ajiram ta ƙira ta cikin sanyin murya. Kukan da take yi ta ɗan tsagaita tana sauƙe ajiyar zuciya.
“Aishatu me ya same ki kike kuka haka?”
Shiru tayi in banda ajihae zuciya babu abinda take sauƙewa. Sai da ta koma dai-dai ta fara ƙoƙarin cire rigar ta babu ko ɓata lokaci, tana cirewa zanen dorinar da ta sha wurin polisawa ya bayyana.
Ƙwalalo idanuwan su mutanen da ke room ɗin suka yi. Aunty Ajiram da ta rikice ganin irin shafin bulalar yasa hawaye fara zubo mata. Cikin raunatacciyar murya tace
“Aishatu dukan ki suka yi?”
Sai a lokacin Ƴar Iya ta samu bakin magana.
“Ni wurin Iya na zan koma Aradu, duk Ƴan birni mugaye ne saboda haka na haƙura yanzu da ABCD ɗin in na ƙara girma a can ƙauyen mu sai na dawo.”
“Yi haƙuri A'ishah kiyi zamanki, babu wanda ya isa ya ƙara taɓa ki har ji gama. In Kika koma wurin Iya yi ba zaki zama Ƴar Gayu ba”
“Ni na fasa zama Aradu, in kuwa. Ba'a kai Ni wurin Iya ta ba Aradu kashe mutane zan far...” Rufe mata baki Aunty Ajiram tayi saying
“Is ok za'a kai ki wurin Iya tunda baki son zama kusa da Aunty Ajiram” ta ƙarasa tana juya mata baya.
“Halan kin ci wani abun a can koh?”
Sai a lokacin cikin ta ya fara ƙugin yunwa, tuni ta jawo Bagco nata ta ciro wani ƙunshin ƙanzo,bata tsaya jiƙa shi ba kuwa ta cinye shi tas.
Tana gama ci kuma ta tayar da rigima ita fa yanzu zata tafi, da ƙyar Aunty Ajiram ta lallaɓa ta ta Zauna kafin Baffi yazo su tafi.
, ★★★★★★★
*ALEE POV*
Tunda ya dawo ya zama busy, gaba ɗaya ayyukan da yake son kammalawa sun yi mishi yawa. Batun wani attack da aka bar case ɗin a hannun shi yasa ya zama kamar mahaukaci sai dai ba zaka taɓa fahimtar wani aiki yayi mishi yawa saboda irin yadda koyaushe fuskar shi take a kame.
Motar shi ce ta danno hanci zuwa mansion nasu. Ko jiran Joseph bai yi ba ya fice abun shi. A parlour ya tarar da Sarah taci ado, ba laifi Sarah kyakkyawa ce kamar Mommyn ta. Sanye take cikin traditional kayan su na blue sari, hannun ta fari tas sai jan lallen da ya ƙara haska su.
Kallo ɗaya yayi mata ya kau da kan shi tare da wucewa bedroom ɗin Mom. Ganin tana toilet yasa ya fito ya wuce bedroom ɗin shi. Wanka yayi ya sanya light kaya tare da fesa turare. Ya zo zai fito har ya murɗa handle na ƙofar wayar shi tayi ringing.
Ganin number Major Kabir Joda yasa yayi picking da sauri.
“Hello, Is Captain Alee on the line”
“Yes sir, anything wrong?”
Cikin muryar tashin hankali yace
“Waɗannan mutanen sun ƙara attacking ƙauyen nan yanzu nayi recieving call daga sojojin da muka tura, sun ce abun babu kyau”
“On my way, yanzu zamu shirya tafiya mu far musu”
Daga haka yayi hanging call ɗin. Komawa bedroom ɗin shi yayi ya sauya dressing nashi zuwa uniform ɗin su na sojoji. Bai wani ɓata lokaci ba ya rataya bindigar sa ya fice.
Mom da ta bi ta damu tun ɗazu take zaman jiran dawowar shi ammah shiru yasa ta fito. A parlour ta tarar da Sarah zaune kan sofa.
Murmushi Mom tayi mata, cikin harshen Hindu tace,
“Sarah, brothern ki bai shigo bane”
“Ya shigo har bedroom naki sai ya fito ya wuce sama. Bai ma daɗe ba ya fito inaga wanka yayi sai kuma ya sanya uniform ya fita cikin tashin hankali”
Hankalin Mom in yayi dubu to ya tashi, fara jera mishi calls tayi ammah baya picking daga ƙarahe ma wayar ta daina shiga. Tuni zancen ya bazu.
Duk irin tashin hankalin da suke ciki haka granny ta sanya su gaba tana kuka duk ta ƙara ɗaga musu hankali.
“Hande enbone, Ni Shatu yau shikenan ɗan jikan nawa aka rasa, wayyo ni ƴar nan, wallahi Muhammadu, Suraja har da kai Bello ku nemo min jika. In ba haka ba wallahi kar ku dawo min gida”
Haka tayi ta surutai tana ƙara ɗaga musu hankali.
Lokaci ɗaya gidan ya koma tamkar maƙabarta, Yaya Saleem ma a ranar ya diro hankali tashe.
Har dare shiru number Hamma Zaki baya tafiya, su Fauzah da ƙyar aka lallashe su suka yi shiru coz duk irin yadda yake haɗe musu da tsare musu suna matuƙar ji da su saboda yadda yake hidimta musu.
Ɓangaren Hamma Zaki yana zuwa can Barrack a nan ya haɗa tawagar sojoji sannan ya haɗa musu kayan aiki. Kai tsaye wucewa suka yi zuwa ƙauyen da tun kafin su shiga suke jin ihun yara ga kuma ƙarar bindigu dake tashi.
Suna cikin tafiya basu kai ga ƙarasawa ƙauyen ba suka ji tsit kamar ba daga nan hayaniya da ƙarar ke tashi ba ɗazu.
Hamma Zaki da shine commander a wannan gwagwarmaya, tsayar da shigar su ƙauyen yayi, wasu har suna a shiga ya dakatar da su saying
“Suna da matuƙar wayo Ƴan ta'addan nan saboda haka ba zamu shiga yanzu ba, idan muka shiga yanzu ba ma samun su zamu yi ba saboda sun gama na yau. So we'll stay here kamar bamu zo ba, hakan zai sa su ƙara samun kwanciyar hankali gobe ma su kai hari, ammah yanzu...” ya faɗa pointing to motar farko da a ciki akwai likitici sannan yaci gaba
“Ku zaku shiga ku fara treating waɗanda suka raunata, mu zamu jira a nan. And kuyi taka tsan-tsan kada su fahimci mun zo da ku”
Basu yi musu ba suka shiga suka fara treating waɗanda suka raunata. A nan suka tabbatar da cewa waɗannan ƴan ta'adda ba ƙananan mugaye bane, sun kashe mutane da yawa wanda yawancin su maza ne sai kuma waɗanda aka raunata suma kuma da yawa.
Gaskiyar Hamma Zaki ƴan ta'addar na da basira don kuwa babu wanda ya ƙara taɓa kowa cikin ƙauyen sai ma samun maɓoya da suka yi.
Dr. Faruq yana ta saka musu ido ba tare da sun sani ba bare su fahimta coz yana shiga ya cire labcoat da wndon shi ya sanya riga ƴar shara da wando da ya ara a wani gida bayan sanar da su shi ɗin likitane.
Haka ya yawata cikin ƙauyen yana ganin maɓoyar ƴan ta'addar ba tare da sun gane ba. Sai yamma ya dawo zuwa gidan da aka basu don kula da majinyatan.
Da yamma su Hamma Zaki ma suka samu shigowa ƙauyen su ma ammah basu shigo da mtar su ba sai bindigun su da suka shigo da su. Wani ɗan gidan kara suka samu suka maƙale a ciki har lokacin sallar maghrib, a nan kuwa suka yi sallah sannan suka yada zango.
Su kan su jama'ar ƙauyen basu san da shigowar su ba bare kuma ƴan ta'addar su fahimta.
Irin daidai lokacin da suka tada tsiyar au jiya irin shi suka fara yau. Sun fara sake bindigu suna kashe mazajen ƙauyen ai kuwa sojojin nan suma suka afka musu.
Nan da nan fili ya kacame, waɗannan na kaiwa wannan farmaki har dai suka daina farmakar ƴan ƙauyen. An shafe fiye da Hour uku ana wannan faɗa yayin da Hamma Zaki ya nuna ainihin jarumtar sa, yadda yake harbi a dabarance kaɗai zai sa ka fahimci shi ɗin ƙwararre ne ga kuma yadda yake sa ƙarfin shi wani lokacin.
Duk irin raunin da ya samu bai sa ya sare ba sai ma ƙara ƙaimi da yayi, tuni suka ƙarar da ƴan ta'addan tass. Sai a lokacin suka lura da Commander nasu, nan aka fara treating raunukan shi daga nan suka kwashi hanya har inda motocin su suke ba tare da an rasa rayuwar soja ko ɗaya ba.
(Ya ubangiji ka ƙarawa sojojin mu lafiya tare da imani ka kuma kare su daga sharrin waɗanda Basu Son kawo cigaba, Amin).
★★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Rikicin da ta tayar ne yasa Aunty Ajiram ɗaukar da suka wuce office ɗin Principal.
Jin batun Ƴar Iya yasa ranshi yin wasai ko ba komai yasar da wannan ƙwallon mangwaro zai zo da sauƙi.
Baffi bai iso ba sai wuraren yammacin ranar basu wani ɓata lokaci ba saboda yadda Ƴar Iya da kan ta ta nuna tana son tafiya. Aunty Ajiram kuwa kamar ta tsala ihu haka ta je ta kwaso Bagco na Ƴar Iya bisa umarnin Principal.
Bayan ta kawo ta ja hannun Ƴar Iya gefe ta sanya mata wani zobe mai kyan gaske sannan ta riƙe hannun ta. Idanuwa Ƴar Iya ta zuba mata yayin da zuciyar ta ke mata wani iri ammah kewar Iya yasa dole zata bar Aunty Ajiram.
Hawayen fuskar ta ta goge sannan ta fara magana cikin sanyin murna
“Aishatu, ga wannan zoben na baki kyautar sa kasancewar bani da wani abun da zan baki yanzu, kimin alƙawarin kasancewa da zoben har zuwa ranar da Allah zai ƙara haɗa fuskokin mu. Ki gaishe da Iya”
Tana kaiwa nan ta goge hawayen da ya ƙara zubo mata sannan ta saki hannun Ƴar Iya ta juya.
Daga nan babur ɗin su Ƴar Iya yayi horn, juyawa tayi ta ɗale kamar yadda suka yi a zuwa daga nan mashin ya tashi sai Gallara.........
*WANNAN SHI AKE ƘIRA KOMA BAYA, BAHAUSHE YA CE WAI GA CI GA KWANAN YUNWA, TOH ƳAR IYA, SADUWAR ALKHAIRI, IN DA RABO KUMA WATA RANA KI ƘARA HAƊUWA DA AUNTY AJIRAM ƊIN KI.*
*MU HAƊU GOBE DON JIN YA RAYUWAR ƳAR IYA ZATA ƘARE A GALLARA, SAUYIN DA TA FARA SAMU KO ZAI TAFI OHO...*
*INA INNA ZALIHA NE?*
*DUK AMSOSHIN KU NA TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎* *KUCI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMI NA*
*COMMENT AND SHARE FISABILILLAHI!*
[5/3, 7:23 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘27&28’’'’’
*[Gare ki ƴar uwa, ko kin san cewa na ɗaya daga cikin dalilin da yasa mata suka yi rinjaye cikin wuta butulcewa kyautatawar da mijin ki ke masu?*
*Matso kiji ƴar uwa, butulcewa kyautatawar miji kamar dai yadda mata yanzu muka ɗauki abun kamar hali ..kowa tana da shi.*
*Mijin ki zai jima yana ɗawainiya dake yana ƙoƙarin kyautata miki ammah da an samu matsala na rana ɗaya sai ki butulce kina faɗin _me ka taɓa yi min a rayuwa?_*
*Wannan abu yanzu mata sun ɗauke shi sun yafa har wani tinƙaho suke yi...TOH maza ƴar uwa tun kina da sauran lokaci maza ko yada wannan ɗabi'ar domin kasancewa cikin ahlul jannah*
*Allah Ubangijin yasa muna da rabo baki ɗaya*.
Daga nan babur ɗin su Ƴar Iya yayi horn, juyawa tayi ta ɗale kamar yadda suka yi a zuwa daga nan mashin ya tashi sai Gallara.
Tunda suka ɗauki hanya take famar zare ido tare da juya zoben da Aunty Ajiram ta bata yayin da wani ɓangare na zuciyar ta ke jin babu daɗi.
Har ƙofar gida Shayibu ya kai su, daga suka dire. Ƴar Iya bata samu damar shiga da Bagco nata ba tayi ciki da gudu.
A zaune ta tarar da iya bisa kujerar tsakar gida, da gudu ta faɗa kanta tana sakin kuka.
“Iya ta bakiyi kewa ta ba neh?” ta faɗa bayan ta tsagaita da kukan da take yi.
“Haba shalelen Iya ni ɗin ne kuwa nayi kewar ki, kullum sai nayi hawaye ina tunanin shalele na”
Murmushi tayi tare da sakin Iya
“Iya birni babu daɗi, akwai mugaye a sukul ɗin mu”
Zare ido yayi tayi tace
“Miye sukul kuma shalelen iya?”
Dariya da shewa Iya ta saki lokaci guda.
“Ayyiriri nanaye....lallai Iya na manta ashe fa ke ƴar