Showing 63001 words to 66000 words out of 135404 words

Chapter 22 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46344

da kika ganni”
Ayrah ta sheƙe da dariya tace “gaskiya Khairy baki da dama, to wallahi duk iya shegen ki da zaki ga Hamma Zaki wollah sai kin jijjiga”
Itama dariyar tayi tana miƙewa tsaye
“Inma Hamma Namun daji ne ba zaki ba wollah bai kai naji tsoronsa ba, ni naga Alama koma waye shi tsoronshi kuke, hala malamin kune?”
Janyo ta Yesmeen tayi ta zauna tace “Ke Khairy wallahi ki godewa Allah Hamma Zaki baya nan yanzu, kina cewa malamin mu ne shine fa na jikin picture ɗin parlourn Mom, ƴaƴan Fauzah ne”
Dumm gabanta ya faɗin cikin ranta tace “Wannan mai siffar aljanun tsabagen kyau?” zahiri kuma ta cillawa Yesmeen harara
“Ke kar ki wani dame ni, ina ruwa na da shi, nidai abunda na sani shine ko shi waye bazan ji tsoronsa ba”.
“hmm” Fauzah ta faɗa “Zanso naga ƙarshen iyashegen ki Khairy, wollah zan so naga karon ki da Hamma Zaki”
“Mtss sai kiyi kuma, don baki san wacece Ƴar Iya ba shiyasa kike tunanin zanji tsoron wani mahaluki, ni nan da kike gani duk ƙauyen mu kowa tsoro na yake, b don komai ba wasu kam sai saboda hannu na”
Ta faɗa tana pointing hannun nata.

Cike da son kawar da zancen Ayrah tace “Allah sarki Hamma Zaki, wallahi Ni yanzu fa tausayi yake bani” ta ƙarasa kamar zata yi kuka.
Fauzah tace “Wallahi kullum sai nayi mafarkin ɗan uwa na, kin san Mom fa kullum sai tayi kuka”
Yesmeen tace “Ai dole tayi, ni kan wannan matar tasa mai siffar aljanun dama daga ganin ta ai shaiɗaniya ce”
“Ke dai kibari Yesmeen, wallahi da Hamma Zaki zai barmu gidan shi zamu koma muci uban shegiya ko kuma a haɗa shi aure kawai da Adda Salma tunda tana son shi”
“Toh ƴan Manzon manyance, ku tashi ku bani wuri munafikan yara, ƙanana da ku kun iya gulma” Muryar granny ce ta katse su.
“Kai don Allah granny, ke matsalar mu dake kenan wollah, don kawai mun jajanta abun dake damun mu” Ayrah ta faɗa tana tura baki.
Baki Granny ta kama da hannunta ɗaya, ɗayan kuma ta riƙe kunkumi tana bin Ayrah da kallo
“Toh rasa kunya ɓeran tanka, kin Isa ƙwarai, to ko ubanki Bello bai isa na faɗa ya faɗa ba, shashasha kawai, shi Mazan ne damuwar ku?”
Fauzah tace “Yi haƙuri ƴar tsohuwar mu me ran ƙarfe, nasan kema dai kina kewar Wannan jikan naki da mace ta ƙwace shi ta hana shi zuwa kallon ki”
Ai jin batun Fauzah sai granny ta ɓare baki tana kuka
“Ƴar nan fauziyya ai dole, wannan shaiɗaniyar matar tasa kullum sai na tofa mata yasin ƙafa goma don ta cuce mu, shegiya mai fuskar aljanu” ta faɗa tana fyace majina da gefen zanin ta.
Khairy da bata fahimtar komai gashi granny da kuma ƴan uwan ta sai ƙwalla suke zubarwa yasa ta ƙarasa tana rungume granny “Ki shiru haka nan granny, Ni nan nayi miki alƙawarin dawo miki da Maza (kamar yadda taji granny ta faɗa) garemu, ƴan uwa na kuyi haƙuri kunji?”

*Hamma zaki da Khairy*
_Ya kuke tunanin za'a kaya, kuyi comment an jima nayi update, Ina son mu kammala littafin nan kwanan nan ne_

COMMENT & SHARE PLEASE


[8/18, 5:46 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA””” “““65&66

Granny tace “Shikenan ɗiyar kirki, na yarda dake sosai, Allah yayi muku albarka”
“Ameen dukan su suka amsa mata” daga nan suka ɗunguma sai part ɗin Mommah. Lokacin Madam Ajimola tazo, dole Khairy ta tsaya yin karatu wanda suke yi a parlourn Granny.

Tafe yake cikin takunshi mai nuna tsantsar haiba da kamala irin tashi. Can ƙasan maƙoshi sallamar tasa ta fita, Madam Ajimola dake ƙoƙarin koyawa Khairy karatu ta ɗago, kasa haɗa ido dashi tayi hakan yasa ta sunkuyar da kai.
“Good Morning sir”
Kai kawai ya ɗaga alamar iya amsar da zai iya bata kenan. Ganin yarinya zaune amma bata yi ko gigin gaisar da shi ba yasa ranshi ɓaci. Cikin ranshi yace
“Koma wacece, I'll teach her a lesson” daga haka ya wuce Bedroom ɗin granny.

Lokacin da ya shiga granny na sallar walaha saboda haka ya fito da niyyar komawa anjima. Sauran parts ɗin gidan yabi ya gaida su kamar yadda ya saba kafin ya koma bedroom ɗin shi yana mamakin wannan ƴar yarinya mai zarra da har zai shiga ta gagara gaida shi sai dai malamar ta.
“silly girl” ya faɗa yana juyawa zuwa ɗaya ɓangaren. Madam Ajimola na gama yi mata Lesson ta wuce abunta. Granny da ta idar da salla ta fito tana faɗin “Maza ina ka shiga ne”
Da kallon mamaki Khairy ke binta, ko ina taga mazan?. “Ke Khairy ina maza?”
“granny wani maza kuma?”
“Ke bana son shiririta, yanzu ya shigo ina sallah ko ya fita ne?”
“Eh ya fita amma ina ga zai dawo”

Bata rufe baki ba taji irin ƙamshin da ya bugi hancinta ɗazu, babu shakka wannan shine mazan granny Kuma Hamma Zakin ƴan uwanta.
A hankali ta ɗago da idonta don kallon mamallakin wannan ƙamshi. Ganin granny ajikinshi tana share ƙwalla yasa ta nufi Bedroom ɗinta.

“Maza sai yau ake ganin idon ka?, Yau wata nawa da auren ka sai yau ka tuna da mu?”
“kiyi haƙuri granny, nasan Ni me laifi ne a wajen ku, Wallahi ban san me yasha kaina ba ne”.
Ya faɗa yana yamutsa fuska alamar maganar da yayi tayi tsayi.
“Ai dama na san wannan matar taka mai kama da tsatson bokaye ita ta raba mu, shikenan na haƙura, ina ita matar taka?”
“Gida can abuja”
“Hohoho dole ma ta dawo nan Adamawa da zama, don bazata raba mu da kai ba ita kuma tana tare da nata iyayen ba”
Cike da ƙosawa da zancen granny yace “wacece wannan yarinyar?”
Washe Baki granny tayi jin an ambaci Khairyn ta.
“Ayyo, ƴar wajena wai?, Ummul Khairy ce sabuwar ƙanwar ka”
Cikin ransa yace “Wannan fitsararriyar?, Ai sai na koya mata hankali”.

“Amma dai tana da taɓin ƙwaƙwalwa?”
“haba maza ya za'ayi kana cin mutuncin yarinya, to bata da taɓin hankali ko kaɗan, ragas take Kamar kai”
Cikin ransa yace “In kuwa ragas take tabbas zan koya mata hankali”.
Cike da jin haushin yadda granny ta nuna son fitsararriyar yarinyar da ko kallo bata isheshi ba yasa yayi mata sallama ya koma ransa babu daɗi yana tunanin ta yadda zai yi maganin ta.

Da yamma sunje part ɗin su Ayrah Adda Salma ta tsokalo Khairy. Suna zaune a parlour suna hirar su wacce rabi da quater akan Hamma Zaki ne, ita dai bata cewa uffan saboda har yanzu bata taɓa ganin fuskarsa ido da ido ba, iyaka dai bata taɓa ganin mutum mai girman jiki kuma mai ɗaukar hankali ba irinsa.
“Kai dallah ku rufawa mutane baki, idiots. Kun wani saka wannan gidahumar baƙauyiyar kuna mata zancen Hamma Zaki, oya ku tashi ku bar parlourn nan”
Adda Salma ta faɗa tana cilla musu harara, cike da kallon da ke nuna ƙyama.

Tunda Khairy take baa taɓa ci mata fuska irin na yau ba, kuma yau ne karo na farko a rayuwarta da wani ya taɓa nuna ƙyamarta. Har ta juya zata fita ta juyo ta kalli Adda Salma tace “Kada ki ƙara ƙira na da bagidajiya, ƙauye kuma tushen kowane” daga haka ta saka kai zata fita, babu tsammani taji hannun Adda Salma ya damƙi wuyanta. Duk abinda suke Mommah na kallon su, ita kanta ta gaji da mugun hali irin na Salma, shiyasa ko da yarinyar tayi mata rashin kunya bata ce komai ba.

A hasale Khairy ta juya tana taskawa Adda Salma Mari, Marin da tunda Mommah tahaife ta bata taɓa jin irin sa ba coz sai da tayi loosing sight ɗin ta na wani lokacin.
Da yatsa take nuna ta tace “Wannan shine karo na farko da kika saka na karyar alƙawarin da na ɗaukar wa Iya ta, kin sa haƙuri na ya ƙare, to Wallahi ki fita sabga ta”
Daga haka ta arta a wani irin speed kamar wata iska, bata tsaya ko ina ba sai Bedroom ɗin ta, tana isa ta kulle ta faɗa kan bed sai wani irin numfashi take fitarwa.

Gabaɗayan su basu bi ta kan Adda Salma dake zaune a ƙasa ba dirshan, sai ma bin bayan Khairy da suka yi. Hankalin su yayi mummunan tashi, gurnanin da ke tashi daga rufaffen ɗakin ya matuƙar razana su. Granny kuwa kuka take tana faɗin “Kuje ku ƙira maza yazo, nashiga uku ni Aishatu, ke Najma karɓi waya ta ki ƙira min Daddyn ku”
Da ƙyar ta laluɓo number Daddy, cikin tashin hankali ya shigo gidan, ko parking bai daidaita ba ya fito ya nufi part ɗin granny. Tun daga bakin part ɗin yake jin gurnanin kamar an sake mayunwacin zaki.

Ƙarasawa yayi, bai gama shiga tashin hankali ba sai da ya ga Hajiyarsu na kuka.
“Maza ɗan nan a fito mun da yarinya, in ba haka ba zan bar gidan nan nima”
Cikin ɗimuwa ya tambayi Fauzah dake kuka shabe-shabe coz tunda take bata taɓa jin irin wannan kukan ba. Bayani tayi masa, cikin ɓacin rai yace “Shikenan yanzu ya za'a yi ta fito?”
Granny tace “Ka ƙira min maza nasan shi kaɗai ne zai fito da ita, wallahi yarinyar nan ta illata sai na saɓa muku”
Daddy wayarsa ya ɗauko ya ƙira Hamma Zaki, thank God Yana ma gidan ashe.

Kasancewarsa maras son hayaniya yasa gurnanin nata ya fara sauƙar mishi da ciwon kai, a haka ya daure ya ƙaraso zuwa ƙiran Daddy.
Nan yayi masa bayani kamar yadda Fauzah tayi masa. Takaici ne ya kama Hamma Zaki amma ya dake yace “Daddy to a ƙira Sheikh Imam mana”
Murmushi Daddyn yayi don shi har ga Allah kansa ya kulle.
Number ya Sheikh ya danna amma bata shiga, hakan yasa ya ƙarasa bakin ƙofar yana ƙiran sunan ta
“Khairy, Khairy”
Babu alamun za'a amsa kuma gurnanin bai daina fita ba. Cikin ransa ya ɗauki aniyar hada ta da Sheikh Imam ko ma meyeh in sha Allah ba zai gagare shi ba.

Har lokacin azahar ya kusa wucewa shiru, hakan yasa Nenne lallaɓa su suje suyi sallah. Bayan tafiyar su kowa zuciyar sa babu daɗi Nenne ta ƙaraso jikin ƙofar ta kafa kanta ta fara magana “Yarinya ta kiyi haƙuri ki buɗe kinji, Kinga ni da grannyn ku ga ƴan uwanki duk muna cikin damuwa, ki taimaka ki buɗe”
Cikin wata razananniyar murya da amon ta ya zaga ko ina na gidan tace “Meyesa Nenne, ki tafi kema, ba ita bace, ku tafi in mun gaji zata buɗe”
Jikin Nenne karkarwa kawai yake, cikin ƙarfin hali tace “Toh kada ku cutar da ita don Allah”
Tsawa aka daka mata wanda sai da kowacce kusurwa ta gidan ta jijjiga.
“keeee, ki tashi ki tafi muka ce, wannan ba damuwar ki bane, tun tana ciki muke tare da ita, da munyi niyyar cutar da ita da munyi”
Ai tun kafin maganar ta kai karshe Nenne ta fice da gudu, duk gidan a ɗimauce suke, musamman yadda Muryar ke tashi ga kuma tsawar da ta jijjiga ginin gidan.
Allah Sarki granny kuka take, ta kasa cin abincin ma, gwanda yaran an saka su dole sun ci.

Adda Salma ana can ana zaryar shiga toilet, don tunda ta fara jin wannan sautin cikinta ya juya, ga kuma wani surutu da ake yi mata a cikin kunne, gashi kowa ya gudu ya barta ita kaɗai, kuka take kamar zata mutu amma babu mai rarrashi. Tayi da-na-sanin tsanar yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Gashi yanzu ta jawowa kanta, Mommah sai ta hukunta ta, gashi kuma sai ta shiga uku da bareɗeɗen granny.
Da haka tayi sallah tana roƙon Allah ya kawo abun da sauƙi.

Sai wajajen maghrib gurnanin ya lufa, sannu A hankali kuma ya disashe kamar ba a gidan ba. Can kuma sai suka ji ƙarar ƙofa ƙiiiii, Khairy ce idon ta a kumbure, fuskar nan tayi jawur da ita. Dukkan su kanta suka yi suna rungume ta. Granny ta janye ta gefenta tace “Haba ɗiyar nan, kiyi haƙuri faɗa min wadda ya taɓa ki”
Nenne tace “Ysnzu dai ba wannan ba Hajiya, tayi sallah taci abinci”
Babu musu tayi sallarta kamar yadda ta saba. Granny da kanta tayi feeding ɗin ta, ƴan uwanta kuwa na kewaye da ita don har ga Allah su suna jinta a jikin su.

Ɓangaren Hamma Zaki abun ya ɗaure masa kai cikin ransa yake faɗin “Dama nasan yarinyar nan ba lafiya take ba granny ta kafe har take kwatanta lafiya ta da tata” yamutsa fuska yayi yace “So disgusting”.
Ƙiran pretty ne ya dawo da shi daga duniyar da ya dulmiya, tsaki yayi ya ɗaga.
“Aliyu shine ko kira na bazaka yi ba saboda kana tare da ahalin ka?”
A hankali yace “Kinga Nabila meyasa kike hakane, ke da ko nuna kulawarki gare Ni bakya yi don yanzu ina samun kulawa sai ki ɗaga hankalinki”
Cikin ɗaga murya tace “Dakata Aliyu, iyayenka sun fini ai?, Gaskiya ka dawo ma in zaka dawo don ba zaka shiga hakki naba” tsaki yaja Yana hanging call ɗin. Cikin ranshi yana tunanin meyasa yarinyar ta raina shi, tabbas sai ya saita ta.

Da daddare Daddy ya ƙara gwada numbern Sheikh Imam, and luckily ya same shi, bayan sun gaisa cike da mutuntawa yake sanar da shi game da Khairy, da irin yadda tayi yinin yau.
Sheikh Imam yace “Tabbas akwai abun dubawa a game da yarinyar, sai dai bana Nigeria yanzu haka, kuma zan kai wani satin kafin na dawo,amma da na dawo in Sha Allah zan taimaka da taimakon Ubangiji mu ceto yarinyar nan.”
“Yauwah ya Sheikh, Allah ya dawo da kai lafiya, na gode sosai”
“Babu godiya tsakanin mu, sai na dawo, kafin nan ake yawan karanta Alqur'ani a wurin da take, kuma a guji duk wani abu da zai tada hankalin ta na wannan lokaci”
“In sha Allah za'a kiyaye”
Daga nan suka yi sallama.

Nan yake sanar da Mom akan yadda suka yi da Sheikh Imam, da kuma shawarar da yanke idan Sheikh Imam ɗin ya dawo a haɗa shi da Alee, don Yana da tabbacin akwai sihiri a tattare da shi. Mom taji daɗin hakan kuma ta shawarci Daddy a kan Hamma Zakin ya dawo Adamawa da aikin gabaɗaya don hakan ne kaɗai kwanciyar hankalin su.

_Toh Fans, ya kuke tunanin wasan zai kaya?, mom da Daddy suna yunƙurin lalata shirinta, ko kuna tunanin zata yadda kuwa?, Ya kuke tunanin haɗuwar Hamma Zaki da Pretty?, Kuci gaba da bibiyar alƙalamin diamond bhatool ta hanya yimin comments da share_



[8/21, 11:00 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:


🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*










SHAFI NA “““67&68”””

Sheikh Imam yasha wahala ƙwarai dagaske kafin ɗaya daga cikin shaiɗanun suka amince da batun shi.
Gyaran murya yayi ya fara magana kamar haka:
“Mu ma ba yin kanmu bane, mun kasance muna aiki da wani bil'adama wanda yake aikin bokanci a can Gallara. Hatsabibin boka ne wanda ba abinda baya iyawa da taimakon shaiɗanu.”

“Wata rana, shekaru goma sha biyar da suka gabata, wata mata mai suna Zaliha taje ga bokan don yayi mata aiki. Tana son a raba auren Wani mutum mai suna Umaru da matarsa Barira, wanda hakan ba abu ne da zai yiwu ba. Bayan sanar da ita da hakan da boka yayi, bata sare ba tace da shi yayi yadda yake ganin zai yi don ita so take ya aure ta. Boka yace ba zai yiwu ba saboda tauraron matar na da matuƙar ƙarfi, kashe ta ba abu mai sauƙi bane. Ammah akwai mafita, dole zata sadaukar da jinin yarinya wacce zasu sarrafa, sannan kuma zata sadaukar da mahaifarta ga baƙin aljani. Duk da haka matar bata sare ba ta amince da hakan. Boka yayi mata alƙawarin zai kashe matar kuma zai haɗa aurenta da Umaru”.

“Bayan wani lokaci taji shiru sai ta dawo wurin bokan, take masa ƙorafin ya taji shiru?, A lokacin ne kuma boka yake sanar da ita ai Barira na da ciki, amma kuma da zarar ta rabu da cikin kashe ta zai zama abu mai sauƙi. Zaliha tayi murna sosai saboda haka bata yi ƙasa a guiwa ba duk bayan sati sai ta ziyarci boka yayi mu'amala da ita. Bayan an haife yarinyar, wacce boka ya musanya hannun ta da hannun ɗan guigui, sai ya bawa Zaliha mutunmutumi wanda da shi zata hallaka Barira. Kamar yadda ya bata haka tayi amfani da shi, ta soka allura a jiki, nan Barira ta fara jinya, ta soka na biyu, jinya tayi tsamari, tana soka na ukun Barira tace ga garinku nan, a ranar kuma boka ya zuba tsantar soyayyar Zaliha cikin ran Umaru, tun a ranar ya fara samun uwarsa cewa shi aure zai yi, sati da mutuwar Barira kuwa ya auro ” Zaliha wacce ta mallake shi, bashi da ikon yin abu sai da izinin ta”.

“A lokacin da Barira ta fara jinya, sanin cewa Umaru mutum ne wanda zai iya wargaza aikin, yasa boka ya tura masa shaiɗanu ciki har da Mantau, gaba ɗaya ya manta da ita, har tayi jinya ta rasu kai har yanzu da nake maka magana Umaru bai san mutuwar Barira ba. Ranar da Barira ta mutu ranar boka ya amshi mahaifar Zaliha kamar yadda suka yi alƙawari. Nan kuma boka ya binciko wannan yarinya ta Barira tana da matuƙar tasiri, kuma ita zata kawo ƙarshen taaddancin Zaliha, saboda haka ya zaɓo mu cikin ma'aikatan sa ya sa mu kasance tare a ita, kada mu barta ta samu sukuni, muke saka ta aikata munanan abubuwa da taimakon hannun ɗanguigui da aka musanya mata. Tun daga ranar muke tare da yarinyar, ba ma barinta tayi wani abu mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login