Showing 90001 words to 93000 words out of 135404 words

Chapter 31 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46337

zata tarar basa nan amma tana fitowa Mami tayi kanta tana kai mata bugu sai dai khairy ta zame. “Ke don ubanki har ina miki magana kina ji zaki mayar da ni mahaukaciya” Murmushi kawai khairy tayi tare da raba Mamin zata wuce, jin ta kara jawota yasa ta juyo tace “Baiwar Allah nifah bani da mutunci ga babban da ya zubar da kimarsa kin gane?” daga haka tayi kokarin kwacewa daga rikon da Mami tayi mata.

Fauzy ce tace “Yau sai naci abu ta kazar ubanki tunda kika mare ni don ni ba saarki bace” murmushi kawai khairy tayi zai dai har lokacin Mami na rike da ita. “Ni kike cewa marar mutunci ko?” ta fada a hasale “To ni da mutunci na sai dai ubanki ko uwarki, ashe rainon gidan da yata ta fado kenan” muryar khairy taji ta doki kunnenta “Ki tsaya kaina madam amma kika tabo iyayena wollah sai na baki mamaki”

Sai da Mami ta kankance ido tace “Uhm haka kikace ko? Ba shakka yau na san ina tare da rasa kunya amma babu komai yau zaki tattara ki bar gidan nan” wata mahaukaciyar dariya khairy tayi tace “To fah! Sunan wani wai gadarau, to ke a matsayinki na wa?”
“A matsayi na na uwar matar gidan kuma uwarki!”
Bata ji hauahin zagin ba sai ma dariya da tayi tace “Wai har da su kaza a cin chewing gum? Uhm to Hajiya ai ko matar gidan bata da hurumi da zama na tunda ba ita ta kawo ni ba bare kuma uwarta”

Fauzy fa tunda taga abun ya fara wuce tunaninta ta lallaba ta wuce waje. Khairy ta dubi Mami tace “Madam ki fita zan rufe kofa ko? Ko a nan zaki kwana ne?”
“A uwarki zan kwana, nace a uwarki zan kwana, shegiya mai kama da mayu kawai, wallahi sai kin bar gidan nan don ni rayuwar da nayi ni daya...” bata karasa ba taji an yiwa bakinta mahaukaciyar damka har ta kai ga da kyar take jan numfashi.

Khairy ta kara matse bakin tace “Wannan ne bakin naki mai zagar min uwa ko? To wallahi ahir dinki madam, kinci sa'a ina girmama manya wallahi da yau kashinki sai ya hura wuta, kuma ina miki kashedi wallahi har ki tafi kada ki kara shiga sabga ta, in banda ma rashin ta ido ki kwaso kizo gidan ya ki zauna kamar a garin marasa kunya, mu dai fulani mun gaji kunya bari ki ji, da na sake ki kuma ki bar min daki”

Sakin bakin Mami tayi wacce taja gefe tana sauke numfashi tace “Amma ke kam Allah yayi tambadaddiya ko?”
“Kar ki kara fada” khairy ta katseta. Shiru kuwa tayi tana aikin jefawa khairy harara, cikin ranta tana fadin “Yau naga ta kaina, dole na dage ganin yata ta kubuta daga sharrin wannan yarinya” tunanonta ya katse ne da jin muryar khairy tana fadin “Madam get out, i wanna close the door” a sabule kuwa ta fito babu kunya.

Ko da ta koma dakin pretty ta tarar da Fauzy a can, Fauzy kuwa bata sanar da pretty abunda ke wakana ba saboda yanayin jiki irin na mai jego, ta san zata iya cewa sai taje.

Ganin Mamin na haki tana kuma sauke numfashi yasa pretty fadin “Lafiya Mami?, ba dai dukanta kika yi ba ko?” Zazzare ido Mami ta fara tana fadin “Ai kin riga kin dauko masifa gidanki, har yaushe zaki tsaya a kawo ta tun wuri baki korata ba eh?, to bari kiji don baki san irin diban albarkar da yarinyar nan tayi min bane shiyasa, wallaho tun wuri ki samu mafita”.
Kasa-kasa Fauzy tayi dariya sannan ta dago cike da kulawa tace “Gaskiya Pretty kisan matakin dauka, kinga irin kallon da take jifan Mami da shi?, ni niyya ta sai dare zan far mata saboda naco ubanta”

Ai kuwa pretty fa an harzuka don kuwa jikinta har tsuma yake yi harda kokarin tashi alamun wurin Khairyn zata je, da sauri suka riketa suna fadin “Ya haka pretty? ”
“Rabu da ni naje naci mutuncinta please”

_To jama'a yau ake wata ga wata, bari muji pretty me zata je yiwa khairy?, shin khairy zata bar gidan Hamma Zaki ne?, follow my ink and find out, Diamond Bhatool ce!_

*COMMENT & SHARE PLEASE!*

*COMMENT & SHARE PLEASE!*
[07/09, 2:21 p.m.] 💎Diamond_Bhatool💎:


🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““91&92”””

"A'a daughter, rabu da ita zan faɗa miki hanyar da zaki bi ta bar gidan zuwa gobe" A kunnenta ta raɗa mata magana can kuma suka kwashe da dariya.

*KHAIRY POV*

Ko da Mami ta fita murmushi Khairy ta yi lokaci ɗaya kuma ta haɗe rai tana riƙe haɓa "Lallai ku gode Allah da khairy kuka haɗu ba ƳAR IYA ba, amma ba komai ido na a kanku wallahi kuma duk mugun nufinku sai na tarwatsa shi, annob ne irin ku wallahi, a ce mata ganɗamemiya tazo tana tunkatar ƙaramar yarinya da sunan faɗa? Allah wadaran naka ya lalace" tsaki tayi sannan tace "Yanzu zaku ga salon YAR IYA, ta yadda nan gaba ko suna na kuka ji sai kun tsorata, shashashu."

Wayarta ta ɗakko tana sakin wani shu'umin murmushi. Number granny ta laluɓo tare da danna mata ƙira. Tana fara ringing granny ta ɗaga, kuka khairy ta saka tana faɗin "Na shiga uku granny, ki taimake ni don Allah nikam na shiga uku" a rikice granny tace " Lafiyarki Ummul-Khairy?, me ya faru da ke haka ne? kinga yimin bayani baki da lafiya ne?"
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jan majina "Granny don Allah ki saka Hamma yau ɗin nan yazo ya mayar da ni gida wallahi in ba haka ba kafin safiya zasu kashe ni"
"Inna lillahi, su waye haka? kinga yi min bayani na shiga uku ni Shatu" granny ta faɗa a rikice.
Kuka ta ƙara sawa tace "Allah ni dai granny tun yanzu ki ƙira shi" ta faɗa tana bubbuga ƙofar ɗakin da hannunta "Wayyo granny kinji basu daina bugu ba, don Allah ki ƙira shi kafin su ida karya ƙofar"

Hankalin Granny in yayi million to ya tashi, da ƙyar ta furta "Kinga kiyi sauri ki faɗa min sai na ƙira shi"
"Granny Aunty Nabila ce da mamanta suka zo, don Allah ki taimake ni daga baya sai nayi miki bayani"

Da sauri tayi ƙit ta kashe ƙiran tana sakin wata mahaukaciyar dariya. " Da YAR IYA kuke maganar, wallahi sai dai ku bar min gidan."

Ko da Granny taga ƙiran ya katse tuni cikinta ya ɗura ruwa, ai da sauri ta nufi part ɗin Mom tana ƙwalla ƙira "Ke Rahamatu, fito da sauri ki dubo min lambar wayar maza, kiyi sauri don Allah kar ayi kisan kai, yi maza Rahamatu.
Muryar Granng tasa Mom fitowa da sauri, haka Fauzah.
"Hajiya me yake faruwa?"
Cikin kaɗuwa granny tace "Daga baya na muku bayani yanzu maza dubo lambar maza ki maka masa ƙira, yi maza" ta faɗa tana miƙa mata wayar tata.

Da sauri Mom ta ƙira number Hamma Zaki tare da miƙawa Gtanny, da sauri ta karɓa tana mannata a kunnenta.
Jin sallamarsa ko amsawa bata yi ba tace "Kai maza kana gidanka ne ko kuwa?" mamaki cike da firgici suka sauƙar masa, dakewa yayi yace "Granny lafiya?" a tsawace tace "Amsa zaka bani ba tambaya ba kaji"
Mamakin da ya kama shi ya wuce misali don tunda suke da ita bata taɓa ɗaga masa murya haka ba, kwantar da murya yayi yace "Sorry Granny, bana gida amma yanzu zan koma"
"To maza ka koma don yarinyar nan Ummul-Khairy na can uwar matarka da matarka sun hau mata ga saj buga ƙofa suke kamar zasu cireta." daga haka ta yanke wayar tana duban su Mom da suka yi carko-carko suna dubanta don jin cikakken bayani.

"Ku kuma kun sani gaba ai sai ku koma ko?" ta faɗa tana duban Mom, a hankali Mom tace "Hajiya ai duk hankalinmu ya tashi ne, ko me tayi musu haka?" Granny tace "Ai kema kya tambaya la'alla ko ta gano suna soyayya ne yasa suka far mata?" Granny ta faɗa, cike da tabbatar da maganar da granny ta faɗa Mom tace "La'alla" Granng tayi tsaki tace "Ai kuwa sai dai su mutu, auren maza da Ummul-Khairy kam babu fashi", daga haka ta kaɗa bujenta da iska. Mom kam ajiyar zuciya ta sauƙe tare da komawa ciki. Fauzah dai murmushi tayi tana faɗin "Ta fara tsami kenan, bari na sanar da su Ayrah"

Ɓangaren khairy ko da ta gama kwasar dariyarta sai ta sakawa ƙofarta key ta koma ta zauna.
Ba zato ba tsammani taji muryar Hamma Zaki yana knocking "Ummul-Khairy" ya faɗa cikin wata irin murya har sai da numfashinta ya ɗauke don ji tayi babu wadda ya iya ƙiran sunan kamarsa. Muryarsa da taji a karo na biyu yasa ta yafa wani yanayi tana faɗin "Wallahi ba zan buɗe muku ba, me nayi muku zaku hau ni da duka, Allah bazan buɗe ba"
Ta faɗa cikin wata irin murya da in kaji zaka tabbatar tsoro ne a tattare da ita.

"Kinga Ummul-Khairy nine, ki buɗe kinji"
"Wallahi bazan buɗe su kasheni ba, ka korasu tukunna"
Cike da ƙosawa da maganar yace "Babu kowa ki buɗe nace"
"Allah bana buɗewa" bai san lokacin da ya haɗe rai yace "Open the door i said" ai ba shiri ta buɗe ƙofar tare da ɓuya a bayanta jikinta sai karkarwa yake.

Tausayi ta bashi hakan yasa ya ƙarasa cikin ɗakin babu shiri, hannunta ya riƙo yana faɗin "Kinga Khairy calm down, nine me ya faru kuma su waye?" wane kuka mai tsuma zuciya ta saki tana faɗin "Ni dai ka mayar da ni wurin granny in ba haka ba wallahi kashe ni zasu yi"

Irin kukan da take bai san lokacin da ya rungumeta jikinsa ba, a duniya idan akwai abunda baya so kuka, kukan ma yau na mai son kyautata masa. Sai da yaji kukan ya lafa ya saketa yana zaunar da ita bakin bed ɗin, ita dai kanta ƙasa don tunda take bata taɓa haɗa jiki da kowanne namiji ba, amma a wannan karon ji tayi kamar kar ya raba jikinsa da nata, ajiyar zuciya ta ci gaba da sauƙewa shi kuma sai aikin kallonta yake yana nazartarta.

Can dai yace "Ummul Khairy su waye haka?"
wani kukan ta saki tace "Aunty Nabila ce da mamanta sai kuma ƙanwarta na gama abinci na jera a dining shine suka tsayar da ni wai nazo gidan mutane na fake da aiki na musu zaune, shine nace ai granny ce tace na zauna zuwa Aunty Nabila ta haihu, shine maman nata tace min munafuka wai ni da wanda ya turo ni ma dole na bar gidan, ganɗamemiya da ni na shigo cikin ma'aurata. Da ban kulasu ba sai ƙanwar tata ta kawo min duka tana faɗin wai su ci uwa ta, shine na saka gudu na dawo ɗaki na amma basu daina bugun ƙofar ba wai sai na bar gidan, nikam dan Allah ka mayar da ni kada su kashe ni."

Ran Hamma Zaki in yayi dubu ya ɓaci amma sai ya dake yace "Kiyi haƙuri kinji zan musu magana, kiyi shiru ki kwanta ki huta"
kai ta ɗaga daga nan ya ja mata ƙofar, sai da ta tabbatar yayi nisa ta sheƙe da dariya tace "Wallahi kaɗan ma tunda kuka shiga gona ta, kuma ni da gidan nan sai aure".



Ko da ya fita ɗakinsa ya wuce, ko ruwa bai watsa ba ya ƙira number Pretty, tana ɗagawa cikin shagwaɓaɓɓiyar fuska tace "Sweetheart...." bata kai ga ƙarasawa ba ya katse ta "Me kuka aikata haka eh?, to wallahi in ba so kike ranki ya ɓaci ba ki tattara baƙinki su bar gidan nan" baki ta buɗe tace "Swestheart me kuma ya faru, ni da yau yini guda ban ci komai ba, ƙanwarka ma yau ko ruwa bata bani sai baƙin nawa ne suka yi order na abunda muka ci"

Mamaki ya hana shi cewa komai, ganin yayi shiru yasa pretty tunanin ya hau layi, hakan yasa tace "Sweetheart kawai ta koma gida tunda ta gaji da kulawa da mu"
Katse ƙiran yayi yana tunani, can ya sauƙo ƙasa ya nufi dining, abincin da ya gani jere yasa ya tabbatar khairy bata yi masa ƙarya ba. Shima zaman yayi yaci abincin cikin ransa kuma yana tuna moment ɗinsu na ɗazu.

Mamakin kansa yake wai shi ke lallamin mace? kai gaskiya yarinyar nan tana so ta sauya ni, zuciyarsa tace "Tana kyautata maka dole ka damu da damuwarta" can dai da ya gaji ya koma bedroom ɗinsa.

Washegari sassafe khairy ta tashi, breakfast ta fara ɗaura musu daga nan ta shiga wanka cike da zumuɗi.

Tun 8:56am ta gama shirinta cikin wani black expensive lace da ya gama haɗuwa, jikinsa flower ce pink colour, bata yi wata kwalliya ba sai ɗaurin kwalin da tayi, pink veil ta yafa tare da riƙo pink jakarta. Masha Allah kamar ka sace ka gudu. black flat shoe ta saka tare da fesa turare.

Wayarta ta ɗauko tana shirin ƙiran su Fauzah sai ga kiranta. "Hello" Khairy ta faɗa, ban ji me aka ce daga ɗaya ɓangaren ba tace "Ok gani nan fitowa nimah". Daga haka ta miƙe tayi waje. Motar tasu ta shiga tana faɗin "Wow! babes kunyi kyau" haka dai suka yi ta shirmen su wannan na yaba kyan wannan har suka isa makarantar tasu.

Daidai wurin da aka tanada dominsu suka nufa kowa fuskar nan nasha-nasha da farin ciki. Cikin iko da ƙudurar ubangiji Taro yayi sai son barka, manya-manyan baƙi sun halarta Kuma sun gabatar da speech kala-kala. An bayyana irin nasororin da ɗalibai suka samu a ɓangarori mabanbanta daga nan aka bawa ɗalibai masu ƙwazo kyaututtuka na ban mamaki tun daga kan karamin aji zuwa semi-final year.

Daga nan aka fara gwangwaje ɗaliban da ake yayewa da awards, Khairy manya awards huɗu ta karɓa, ta samu jinjina da yabo na musaman wurin malamai haka zalika Ayrah, Fauzah, da Kuma Yesmeen.
Bayan kammala bayar da awards ga waɗanda suka cancanta aka bawa outgoing students damar yin farewell speech. Nan Khairy ta fito tayi cike da burgewa ta dawo wurin zamanta. An rufe Taro da addu'ah daga nan baƙi suka fita, nan students ma suka fara ɗaukar hotuna.

Sai wajajen 2:00pm suka wuce GIDA a gajiye, Ayrah uwar son jiki sai complain ɗin gajiya suke yi. Bayan sun ci abinci suka fara shirye-shiryen tafiya farewell dinner da suka haɗa da malamansu. Ko da misalin ƙarfe Takwas na dare suka wuce.

Anyi shagali iya shagali, anyi rawa kuma anci an sha a wurin. Ba su suka koma gida ba sai 11pm nan ma Granny ce ta saka lallai lallai su dawo.
Yau Kam Khairy an dawo wajen Granny, dukkansu a room ɗin Khairyn suka kwana bayan doguwar Hira da suka yi.

Washegari suna yin sallar subh suka koma bacci, wajajen ƙarfe goma suka tashi. Nan Kuma aka fara duba pictures ɗin da aka yi dare da ranar jiya, kowa sai posting yake. Babu laifi duk sunyi kyau abunsu. Cikin status viewers ɗinsu fa kar ku manta akwai Wanda ya Siya musu wayar don ya ajiye number a kowacce waye ko me yasa?

Comments Nasha-nasha har sai da suka gaji da replying. Ranar kuma Ya Ishaq, Ya Khalil, da Kuma Hamma Hammad kamar haɗin baki suka shirya tura iyayensu don nema musu auren masoyan nasu.

_Mu haɗu don Jin yadda zata kaya, mu dai burinmu ayi biki Muci musha, ah to, ya kuke tunanin haɗin da Granny da Mom ke shirin yi?, Pretty kuwa zata amince da wannan haɗin, to su iyayen gayyar fa?, zasu yadda ko kuwa?, duk cikin littafin Ƴar Iya ne, kuyi sharhi please tare da Kuma sharing fisabilillah._


[07/09, 2:21 p.m.] 💎Diamond_Bhatool💎:



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““93&94”””

Washegari kuwa ba tare da sanin Ayrah ba Hamma Hammad ya turo Neman aurenta, abun mamaki baa jima ba Kuma sai ga Iyayen Yaya Khalil, daga ƙarshe Kuma sai ga Yaya Ishaq. Shi dai Dad abun ya ɗaure mas Kai gashi Kuma Uncle Suraj da Uncle Bello duka basa gari. Su dai basu san me ake toyawa ba, yauu Khairy ma ta koma gidan Hamma Zaki saboda batun wannan maganganu da Mamin Pretty ta faɗa ranar basu kwanta a ranta ba.

Ranar da ta koma ta tarar da Parlourn kamar ba shi ba a iya kwana ɗaya da bata nan, ta ƙara tabbatar da cewa ana gadon ƙazanta. A zahiri ta furta “Wallahi ƙazanta dai irin wannan bata yi ba” tana yamutsa fuskar ta buɗe ɗakinta ta shiga. Ko kaya bata sauya ba ta hau aiki, sai da ta gyara Parlourn tass sai ƙamshi ke tashi tukun ta nufi kitchen ta ɗaura girki. Few minutes ta kammala girkin daga nan ta nufi sama don duba sarauniyar gidan, har ta nufi ɗakin sai ta juya ta tura ƙofar ɗakinsa, ganin baya ciki ta sauya masa bedsheets tare da fillow cases, daga nan ta nufi toilet ta wanke tas.

Shigowarsa gidan ya tarar da abinci a dining, Hakan ya tabbatar masa silly girl ta dawo. Har zai wuce sama sai Kuma yayi knocking, cikin baccinta ta Farka tana faɗin “Yes come in” dariya ma abun ya bashi yace “Hey! Silly girl zo” ko da ta fito manta ƙasa ta gaishe shi, maimakon ya amsa sai ya jeho mata tambayar “Da izinin wa kika fita a gidan nan jiya har kika kwana?” cikin ranta tace “Ji min mutum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login