Showing 93001 words to 96000 words out of 135404 words

Chapter 32 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46363

don Allah, sai kace wani baba na” ganin tayi shiru yasa yace “A'ah Amma a ƙarƙashin kulawa ta kike” idanuwa ta ƙwalalo cikin rawar murya tace “I'm sorry, baka nan lokacin Kuma ai speech and prize giving day namu muka je and a gida na kwana” har zai yi magana ko me ya tuna kawai yaja ƙeyarsa ya nufi sama. Yamutsa fuskar tayi itama tare da komawa cikin ɗakin.

Washegari ta kama ranar suna, jaririya Kam taci sunan Granny wato “A'isha” za'a yi mata alkunya Kuma da Humairah. Baa Daɗe ba dangin pretty da Kuma Hamma Zaki suka fara zuwa tuni GIDA ya fara cika.

A can Naira Family House kuma Uncle Suraj da Kuma Kuma Uncle Bello sun dawo. Daddy ne ya sanar da su tattaunawa a ɓangaren Granny don sun saba basu yanke hukunci sai da sahalewar Granny. Cikin muryarsa Mai cike da mutunci yace “To ba komai yasa na nemeku ba sai batun yaran nan da suka gama makaranta, shekaranjiya anzo Neman auren dukkansu ukun Banda ita Mai sunan Hajiya Amma fa ban ce komai ba na dai ce musu zanyi bincike sabboda na samu damar magantuwa da ku duk da cewa ko na bayar ɗin ba zan samu wani tsaiko daga gareku ba, to ya kuke gani”
Murmushi Granny tayi tace “kai Masha Allahu, na gode Allah da ya nuna min wannan Rana, nufa dama karatun nan bai wani dame ni ba, idan sunje gidan miji sa yi, Kuma batun ita Ummul Khairy itama akwai wadda suke soyayya da shi ai, sai duka a haɗa.”
Uncle Bello yace “To Hamma mu dai komaai yana hannunka tumda yaran nan dai kaima naka ne, wallahi duk yadda kayi mu masu maka biyayya ne.”

Murmushi Daddy yayi yace “To Hajiya ita Mai sunan naki kince ai tana da Wanda take so ko?, kawai sai ayi masa magana dukkansu kawai ranar laraba su zo sai a saka ranar auren”
Baki Granny ta washe tana faɗin “Affafai! Ai na GIDA ne wannan Kam, Maza dai Maza shine suke soyayya da yarinyar duk da suna ɓoye mana Amma mun tabbatar, Kai ko Babu soyayya ma Ummul Khairy ɗiyar kirki ce zata amince da zaɓin mu, Maza yana buƙatar mata don kuwa ta gidan nan Kam ba mace bace”

Shiru dukkansu suka yi suna sauraron zancen mahaifiyar tasu, tabbas sunyi farin ciki sosai da wannan haɗi da za'a yi, wannan abun alkhairi da ya tunkarosu duk sun rungume shi Babu wasa, a wurin Daddy ya ƙira iyayen yaran da suka zo shekaranjiya duka ya faɗa musu cewa su zo ranar laraba don saka ranar bikin. Daga nan Kuma Taron ya watse.

Ko da angwayen (to be Amma fah😂) suka ji zancen kamar suyi rawa, kowa ya ƙira sahibarsa ya sanar da ita ranar laraba fa za'a saka musu ranar biki. Duk da cewa basu so Hakan ba Amma tsananin soyayyar da suka ƙulla yasa suka haƙura.

Nan fa aka fara raya group ɗin babes. A lokacin Khairy na online kuwa Taga Ayrah ta turo “To babes, nifa na kusa shigewa daga ciki don kuwa ranar laraba za'a saka ranar bikinmu” Tuni Khairy ta fara recording voice, ko gamawa bata yi ba sai ga message ɗin Fauzah.
“To Hajiyata ba ke ɗaya ba, nima nawa masoyin bai yi ƙasa a guiwa ba kuma ranar laraba shima zai turo a saka rana”
Khairy tace “Yau nake ga rashi kunya a gun yaran nan, to Allah ya tabbatar da alkhairi”
Fauzah sai Taga kamar Khairyn bata ji daɗi ba hakan Kuma na da nasaba da ita Babu wand ya turo, sai tayi replying mata da “Sha kuruminki matar soja, ba iya mu bane kema ki tsumayi Jira kwanan nan ƙwanku zai fashe”
“wane ƙwai Kuma ana zaune lafiya, Kai babes, wai ba zaku zo gidan sunan bane?”
“Zamu zo fa” Ayrah ta faɗa. “Don Allah dai kuzo da wuri lunga Babu Wanda na sani cikin mutanen da suka zo. Kuzo mu ɗan guntsa Hira please ” daga nan ta sauƙa offline.


Da misalin ƙarfe biyar na yamma suka dira gidan Hamma Zaki, sunci ado sun sha kyau. A compound ɗin kuwa Mai jego ce ta cakare cikin wata dakakkiyyar shadda da ta amsa sunanta wacce aka yi mata ɗinkin doguwar riga da ta dace da ita, fuskar nan ta sha make up, Babu laifi tayi kyau Kuma ta ciko ba kamar da ba da ta kasance kamar iska zata kaɗe ta.

Ko da suka shiga nan kallo ya dawo kansu don yanzu iya dangin pretty ne da suka zo, sai Kuma tarukucen friends ɗinta, su Ishy ma duk sun zo. Masha Allahu kowa yake furtawa don kyawawan ƴan matan sun burge su. Ƙasa ƙasa ake tambayarta ko su wanene? Yamutsa fuskarta tayi tace “Ƙannensa ne fa” wata a cikinsu tace “gaskiya suna da kyau gaskiya, kigansu fa, ga farin ga kyau Kuma ga diri” gwaɓeta pretty tayi tace “Dallah madam a gaba na?”
“To in a gabanki ne sai kawai kar na yabi abunda ya burge ni?”
Duka ta kaii mata tace “Ke fa Zooshoot baki da dama, wai baki fahimci pretty bane, ita Zaki yaba ba su ba don yau ranarta ne” dariya Dukansu suka saka nan suka Maida hankalinsu ga hidimar gabansu.

Wucewa su Ayrah suka yi direct zuwa bedroom ɗin Khairy, rungume juna suka yi nan suka fara hirarsu.
Yesmeen ce tace “Mu fita muɗanyi snapping pictures please ” basu Musa ba Khairy ta jaeo veil ɗinta suka fita. Basu bi ta kan mutanen ba suka wuce suka fara hotunansu da wayoyinsu, wasu daga cikin mutanen wurin sai kallonsu suke ganin ba wasu manya bane Amma ga phones ɗin hannunsu.

Cikin friends ɗin Pretty wata ta hango ana daga latest iphones, da sauri ta sanar da sauran nan kallonsu ya dawo zuwa su Khairy. Ganin matasan ɗazu yasa suka juya, Zooshoot da ba zata iya Jira ba ta ƙaraso tace “Sister nima azo a ɗan yi min ko uku ne tare da jaririn”
Khairy tayi niyyar gasa mata Amma Jin irin lafazin da tayi amfani da shi yasa ta amsa da “To, ki ɗauko shi ”

Kamar raƙuma ta je aka bata yaro, ganin ta nufi wurin yaran wasu suka fara mata magana. Ba tare da ta jisu ba ta wuce aka yi mata pictures, Khairy tace “Ki kawo wayar ki a tura Miki ko?” miƙowa tayi suka tura mata.
Pretty kam kamar ta kamasu ta hau su da duka musamman wannan shegiyar Khairyn. Haka dai aka yi taro aka gama sai wajajen maghrib suka dawo ciki, Khairy kuwa tun kafin lokacin ta sulale ta shiga ciki, sama ta nufa kamar yadda tayi tsammani Kuma taji murya a ɗakin pretty alamun waya ake “Ok an kama shi, good, shikenan” sai Kuma aka sheƙe da dariya.

Da sauri Khairy ta sauƙo ƙasa, “Babes ku bani number Hamma Zaki please ” dariya ma ta basu Yesmeen tace “Wai me kike nufi, ke ma baki da ita ballanta mu?” cike da tashin hankali tace “Kunga babes ba batun wasa ba please ku bani, ina ji a jiki n wani Abu zai fari da shi don Allah ku ƙira min shi” dariya suka yi Ayrah tace “Yauwah ko ke fa! Gwanda ki fito Muji zancen da kyau, Ashe dai” ba tare da ta damu ba tace “Ko ma meye dai ku bani”. Nan suka fara suka amshi wayar suka fara sakawa zuciyarsu ɗaya Babu Number tasa, Ayrah na farawa Taga number ɓaro-ɓaro sai dai ba suna. Tace. “Dallah Madam karɓi wayarki, ga number a ciki nan” b tare da ɓata lokaci ba tayi dialling number tayi ringing Amma baa ɗaga ba, ta ƙara jarrabawa shiru, sau gom ta ƙira har suka yi sallah bata Daina ƙira ba sai dariya suke mata.

Haka ta haƙura ta zubawa sarautar Allah Ido. Daga nan Kuma tace “ku zauna don Allah babes tare da ni kunga Babu kowa, idan Hamma ya dawo sai ku ƙira driver ya wuce da ku”
Da to suka amsa don Suma yanayin nata ya sa sun fara shiga wani irin yanayi”.

Ƙarfe Tara, goma shiru Babu Hamma Zaki Babu labarinsa, Hakan yasa ta ƙira Granny tace don Allah abarsu su kwana yau Hamma baya nan. Su dai bacci ne ya ɗauke su Amma ita ta gagara bacci, sai gwada number tasa take yi Amma yanzu switched off. Zagaya ɗakin ta fara tana nazari, daga haka tayi sama zuwa cikin ɗakinsa.

A nan ta zauna tana ta tunanin ko Ina ya tafi yau Amma shiru, wata envelope ta hango kawai hanunta ya isa Kai. Tana buɗewa ta buɗe idanuwa tace “Wow!”. Pictures ɗinsu ne na sauƙa Wanda suka yi in ba zata manta ba ma da wayarsa aka yi, Amma an cire su, wasu ita kaɗai, wasu Ayrah, Fauzah, Yesmeen suma su ɗaɗɗaya, sai Wanda aka yi musu su biyar, Hamma Zaki a tsakiyarsu, ita a gefensa na dama, Fauzah a na hagu. Yayi kyau sosai don iya ranar ta taɓa kallonsa da shigar manyan kaya, daga uniform sai jallabiyas sai kuma haka pyjamas tasan ta taɓa kallonsa da su.

A ranta tana ƙara yaba kyau irin nasa, kyan da ya kasance na jiki da Kuma zuciya, tabbas Hamma Zaki mutumin kirki ne, duk da kasancewarta ƴar ƙauye, bai taɓa banbanta su da ƴan uwansa na jini ba tsawon zamansu, ko zama a gidansa ma ita ya zaɓa, tabbas ya cancanci ta damu da shi ko don Hakan.

Haka ta bi pictures ɗin ɗaya bayan ɗaya tana dubawa, na ƙarshen yafi yi mata kyau Kuma ya tsaya mata a rai. Ita da Hamma Zaki ne aka yi musu. Sunyi kyau sosai kamar ba gobe. Gwanin ban shaawa haka take dubawa tana murmushi. Ko me ta tuna sai ta tura baki gaba.
Ta rasa me yasa suke kwatanta ta da Hamma Zaki da sunan soyayya, ko giyar hauka ta sha tasan ya wuce tunaninta, sai macen da ta Kai zata samu irinsa. Tana fatan dai Allah ya bata kwatankwacinsa.

_Comment and share fisabilillah_



[07/09, 2:23 p.m.] 💎Diamond_Bhatool💎:



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““95&96”””

Haka dai Daren nan ya kasancewa Khairy, bayan ta gama kallon pics ɗin ta mayar da su ma'ajiyarsu daga nan ta jingina jikin gadon nan bacci ɓarawo ya sace ta.

Kiraye-kirayen sallar subh ya tayar da ita a firgice. Da sauri ta sauƙa ƙasa tana addu'ah Allah yasa babes basu tashi ba. Da sauri ta buɗe ƙofar a hankali ta shiga. Hamdala tayi cikin ranta sannan ta ɗauro Alwala, bayan tayi sallah tayi addu'ar Allah yasa Hamma Zaki na cikin aminci a duk yadda yake. Daga nan Kuma ta tayar dasu Suma suka yi.

Ƙara jarraba ƙiran tayi Amma kamar jiya switched off, tuni ta shiga cikin wani irin yanayi Mai wuyar fassara, haka ta zauna har safiya tayi su Kuma suka koma baccin safensu. A haka ta fito tayi warming dinner ɗin jiya saboda babu Wanda yaci daga nan ta shiga musu da shi ciki cikin ranta tana faɗin “Ba zata ƙara yiwa ƙarti girki ba”.

Wajajen ƙarfe goma suka Farka bayan sunyi breakfast suka kafa dandalin Hira amma hankalin Khairy baya kansu, lokaci bayan lokaci takan saci idonsu ta leƙo Taga ko zata ga motarsa Amma Babu. Ganin Hakan yasa taci gaba da gwada number tasa Amma still switched off.

Bayan sunci abinci suka ƙira driver itama ta bisu suka wuce tare. Ko da ta isa ta bi ta gaida mutan gidan daga nan ta wuce ɓangaren Granny. Wayar Grannyn ta ɗauka ba tare da saninta ba ta doka ƙiran number tasa Amma amsar ɗaya switched off.

A dabarance ta nufi ɓangaren Mom ko zata ga alamun yaje, cikin hikina ta tambaye Fauzah tace ai bai zo ba. Haka ta faru a ɓangaren Nenne ma saboda haka Khairy fa ta shiga wani yanayi Mai wuyar fassara.

★★★★★★★

Tuƙi yake cikin nutsuwa don ya matsu ya dawo duk da cewa Babu tunanin zuwa gidansa, tsarin da yayi shine ya wuce GIDA. Tun da ya hu Kan titin da motarsa ya lura da wata black jeep Mai tinted glasses kamar bibiyar wani take sai dai a ransa ya ɗauki alwashin tallafawa Wanda ake bi, a hankali ya rage gudun da yake yi da ya zo mararrabar titin Hakan ya bawa motar damar wuce shi. A daidai farkon corner tayi parking, ganin Hakan yasa da ya iso ya wuce abunsa.

A daidai titin da zai sada ka da Stadium Kuma ya ƙara hango wannan motar still na biye da shi, ganin titin sham yasa yayi parking. Motar da ta iso itama tayi parking. Shi ya fara fitowa ai kuwa wasu manya-manyan mutane kamar samudawa suka fito, su shida ne sannan sanye suke da black trouser, da black shirt sai Kuma black cap da suka saka fuskarsu sanye da takunkumi, nufo shi suka yi gadan-gadan Hakan yasa ya fahimci don shi suka zo, da Ido ya bisu har suka ƙaraso, ko ƙala basu ce ba suka Kai hannayensu gareshi. Da farko ya fara depending ƙanshi Amma hausawa suka ce sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Hari gabaɗayansu suka fara Kai masa yayin da ɗayansu Kuma ya sheƙa masa wani farin Abu a takarda nan Hamma Zaki ya saki ji ya faɗi.

Dariya mutanen suka yi daga nan suka jefa shi a motarsa, uku a cikinsu suka shiga, daga nan suka ja motar ɗayar na biye da su. Babban cikinsu Wanda nake kyautata zaton ogansu ne ya ɗauko wata wayarsa da ta sha manni da gum, a kunnensa ya karata, sai da ya saka a handsfree sannan naji ance “Yah Aljan Kun kama shi ɗin ne?” dariya yayi kamar mahaukaci cikin muryarsa maras daɗin sauraro yace “Oga gamu nan zuwa forest ɗin naka ma, ka ajiye mana la'adarmu kawai Kuma ka bar ƙofar a buɗe zamu saka shi ciki don yaji Hoda 😂” daga haka ya katse ƙiran.

Tafiya sosai suka yi har wajen maghrib kafin su karya cikin wani jeje, nan ma sun yi doguwar tafiya kamar Wanda zasu bar duniyar, bayan sun gama da yanki Mai ɗauke da bishiyoyin suka iso wani fili da Babu komai cikinsa sai wani ɗan Gini madaidaici. A daidai wurin suka yi parking.

Kamar yadda suka yi wayar haka suka tarar wurin a buɗe, da ƙyar suka ɗauke shi tare da nufar cikin Ginin da shi. Wani ɗaki suka shiga da shi suka ajiye daga nan suka fice. A filin wajen Kuma suka tarar da wata jaka wadda suke da tabbacin tasu ce, daga haka suka ja jeep ɗinsu suka bar wurin.

★★★★★★


Har yamma bata ga ya shogo gidan ba Hakan yasa hankalinta ya ƙara tashi. Nan ta fara tunano maganganun da ta Jiyo a ɗakin Pretty. Cikin ranta tace “Zanyi abunda ya kamata kuwa, kenan shi ake cewa zaayi kidnapping asa kuɗi da yawa?, to me yayi musu?, poor Hamma Zaki da baya shiga rayuwar mutane?”
Me zata gani?, hawaye ne ke zuba daga idanuwanta, Hakan Kuma yayi daidai da shogowar Ayrah.

Idanuwa ta ƙwalalo tana faɗin “Ya Salam! Khairy me yake damunki haka?” saurin goge hawayen tayi tana kame-kame tace “Ah Ayrah Kinga ƙwaro ne ya faɗa min cikin Ido tun ɗazu” cike da kulawa Ayrah tace “Haba Khairy, a zaman da muka yi da ke Babu yadda za'a yi ki ɓoye damuwarki gare mu, Khairy wani abun ne ya faru? Wallahi tun jiya na lura baki cikin mood” murmushi tayi don bata so ta faɗa musu, tana Jira ne ma ta tabbatar da zarginta shiyasa. “Haba Ayrah, me zai sa na ɓoye muku damuwata?, Kinga ki hure min idon dan Allah”
Babu yadda Ayrah ta iya ta hure mata, nan take faɗa mata cewa “Khairy Hamma Hammad yau yace min zai zo da dare, ki faɗa min me zamu shirya masa?”

Murmushi tayi tace “Inaga muyi masa tuwon gero Kinga ai bafulatani ne shima, sai ahaɗa masa da buredi” ta faɗa tana kashe mata Ido Kuma tayi Hakan ne saboda ta gusar da zargin da Ayrah ke da shi a kanta.
Duka Ayrah ta kawo mata tace “Kut! Dan ma duk kanwar ja ce, muje mu tuƙa tuwon yanzu saboda yayi sanyi ko?”
Dariya dukkansu suka kwashe da ita.
Ayrah ta tsagaita tace “Kinga ni dai muyi magana please ”
Khairy tace “Toh naji muyi magana, shi Hamma Hammad me yafi so kika ce?”
Kanta ta ɗaga tana fari da Ido can tace “Yauwah kwanaki yace min dai da dare baya cin heavy foods, me kike ganin zamu yi masa?”
Khairy tace “Inaga a soya masa chips mana, sai Kuma a soya ƙwai sai ayi masa hot tea ko?”
Rungume ta tayi tare da sumbatar goshinta tace “U're better than a sister to mie, thanks...tashi muje mu duba idan komai available ne”

Tare suka wuce part ɗin Mommah, Zulai na girki bayan sun gaisa suka shiga suka duba komai tare da haɗa komai wurin da ya dace. Sai da Zulai ta gama girkinta ta jera dining suka kwashi kayan buƙatarsu suka nufi ɓangaren Granny. Bayan sunyi sallar Maghrib Khairy ta kora Ayrah. “Madam kije ki fara wanka tun yanzu kin ji ni ko?”
“Ki bari mu gama aikin mana”
“Aah Kinga ni zanyi aikin ke ki wuce ki fara shiri Kinga Babu jimawa isha zata yi, Kuma Ina da tabbacin yana kusa da anyi sallah zai shigo, kije please”

Daga haka ta bar Khairy tana soya chips ɗin, bayan ta gama ta soya ƙwai daga nan Kuma ta ɗaura tea ɗin. Lokacin har an fara kiraye-kirayen sallar isha, Hakan yasa ita ma ta wuce tayi sallah tare da roƙarwa Hamma Zaki aminci wurin ubangiji. Daga nan part ɗin Mommah ta koma, ganin Ayrah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login