Showing 87001 words to 90000 words out of 135404 words
duniya da kuma hadama ma baa barinsa a baya. Tunda ya samu wannan mukami sai ya fara kokarin daura Hon. Dr. Umar Sani Danja kan muguwar akida ta satar kudin gwamnati, sai dai Allah ya so mai girma governor ya fahimci ba shawarar kwarai Alhaji Saminu ke bashi ba.
Tsawon lokaci Governor ya bawa Alhaji Saminu ko zai sauya dabi'u amma inaa kullum abunsa gaba yake karawa. A haka suka ci shekarar farko cikin tenure nasa aka shiga ta biyu. Munanan halin Alhaji Saminu kullum kara bayyana suke, hakan yasa daga karshe Mai girma governor ya tsigeshi daga mukaminsa ya daura wani a maimakonsa.
Wannan abu ba karamin bata ran Alhaji Saminu yayi ba don a cewarsa bai cancanci haka daga governor ba tunda tare da shi suka yi fadi tashi ganin ya samu kujerar. Dalilin bakar zuciya irin ta Alhaji Saminu yasa ya rura wutar daukar fansa cikin ransa, ya kuma yi alkawarin duk wanda yayi kokarin dakatar da shi zai fuskanci hukunci.
Ganin dukiyar da ya fara tarawa ta ja baya ga kuma uwargidansa da take damunsa da bukatar kudi, kusan kullum sai sunyi fada gashi kuma yana bala'in sonta, baya tunanin zai ita rabuwa da ita ko da kuwa kullum sai ta zane shi da tsumanguya kafin ya fita.
A lokacin ne kuma suka hadu da Alhaji Yunusa Boss, wanda yake da dukiya maras adadi, yaji dadi sosai don kuwa basu rabu da Boss ba sai da yayi masa Alkawarin zai sama masa aikin yi daga nan suka yi exchanging contact.
Ranar da suka hadu Boss yayiwa Alhaji Saminu bayani akan aikin da zai bashi, da farko yaki saboda tsoro amma da Boss yayi masa bayanin shima da ita ya tara dukiyar nan yasa ya amince. Ba kowacce irin sana'a bace sai safarar miyagun kwayoyi da kuma makamai. Boss mugun dan ta'adda ne da sunansa yayi kamari cikin Nigeria, duk ko hukuma ta kama shi bata iyawa shiyasa yake tsula tsiyarsa son ransa.
Shekaru kusan bakwai Alhaji Saminu ya shafe yana aiki da Boss din, tuni shi ma ya samu nasa yaran. Sun shagala da iya shegensu ne kuma kwatsam sabon shugaban sojoji wato Gen. Muhammad Naira ya daura musu banten nema tun ranar da ya kama su hannu da hannu suna bude bandles na makamai masu hatsarin gaske a lokacin da yaje Katsina wurin amininsa Prof. Mansur Usman.
Tun daga wannan rana ya samu jami'an sirri suka fara bibiyar Alhaji Saminu, da suka tabbatar sai aka sanar da jami'an yan sanda, baa dade ba kuma aka shigar da kararsu a kotu. Ana cikin shari'ar ne kuma wani munafikin dan sanda ya sanar da shi ai sabon general ne yasa aka kamo su.
Zo kuga yadda ran Alhaji Saminu ya baci akan wannan abu sai dai rubutaccen al'amari gidan kaso aka tura shi don yayi serving 3years aciki with hard labour da kuma kwatar kaso hamsin 50% na dukiyar sa ya tara, yayi kuka iya kuka amma yayi alkawarin fitowa kafin lokacin. Abun mamaki cikin sati Boss yayi cuku-cuku aka fitar da Alhaji Saminu. Tun daga wannan rana ya dauki aniyar daukar fansar abunda General yayi masa, kason dukiyar da yasa ya rasa yayi alkawarin shima sai ya ruguza tashi dukiyar da ya tara.
Sau tari yakan tura yaransa daga Katsina zuwa Adamawa don kaiwa General hari amma basa cin riba, daga karshe sai ya fara kokarin hada alaka da ma'aikatan gidan amma bai samu hadin kai ba. Shekaru kusan biyar ya bata yana wannan farautar sai dai ubangiji bai vashi sa'a ba, ana cikin hakan kuma pretty wato diyarsa daya gwal da ya dora soyayyarsa a kanta ta bullo da zancen auren dan General. Yayi farin ciki sosai don a tunaninsa wannan babbar dama ya samu ta cika muradinsa akan General Naira.
Tunda auren ya dauru suke tunanin yaya zasu tsara abun har ta kai ga sun tsayaa matsayar saka explusive device a gidan amma basu samu hadin kai daga wurin maaikatan gidan ba.
Shawararsu ta karshe itace matsayarsu, zasu dauken shalelen da General Naira yake da sannan su saka masa tara mai dan karen yawa da suke tunanin zasu kwashi kaso 60% na dukiyarsa.
★★★★★★★★★★
*DAWOWA CIKIN LABARI*
Sai yamma lis suka kammala hada komai nasu, daga nan driver ya maida khairy gidan Hamma Zaki, ko da ta isa ta tarar da Fauzy a parlourn ga sunyi kaca kaca da shi kamar shanu. Tsaki tayi tace “Ashe abun gado ne” don a tunaninta Fauzy ma kanwar pretty ce.
Dakinta ta wuce tana mika, sai da ta watsa ruwa daga nan ta dan mike tana karanta Alqur'an har bacci ya sace ta. Cikin bacci taji alamar mutum na taba ta, a firgice ta mike, ganin kanwar pretty yasa tace “Lafiya kike tashi na?” Fauzy da alamun rashin gaskiya ya bayyana tattate da ita tace “Dama zan ce miki azo a shirya abincin dare ne” hade fuska khairy tayi tace “To fice mun, in nayi niyya zan yi in naga dama kuma bana yi saboda wa kattai zan girkawa”.
Fauzy na fita ta rike haba tana mamakin rashin kunya irin na wannan kyakkyawar yatonya da ta kwallafa ranta akanta, baki ta cije tace “Ai dole na same ki yarinya”.
Khairy kuwa da kyar ta fito tayi musu taliya da manja sai tayi warming sauran farfesu wa pretty, bata kai musu saman ba ta ajiye a dining idan suna so suzo su dauka.
Shiru suna jiran abinci babu shi babu alamunsa babu kuma na mai kawowa yasa Mami saukowa da niyyar cin mutuncin yarinyar nan don ita a son ranta ta bar gidan. (Nace kamar wata kishiyarki?).
A tare da Fauzy suka fito, Mami ta tambayi Fauzy dakin yarinyar, Fauzy ta nuna mata don itama yarinyar ta bata haushi dazu. Babu knocking kawai Mami ta kutsa ciki, lokacin Khairy ta fito daga wanka tana kwalliya gaban mirror. Ashar Mami ta lailayo tana fadin “Bura uba! Yau naga isa da mallaka a gurin yarinya, ke ko kunya baki ji ba” sai a lokacin Khairy tasan an shigo dakin, idan da mirror din da khairy ke gani suke magana sa saka ran amsawa. Ko kallonsu bata yi ba ta bude trolleynta ta ciro doguwar riga, ta juya zata shiga toilet ta saka kawai taji an jawota, ba kowa bace sai fauzy. Tana juyowa ta wanketa da mari tuni Fauzy ta sake ta tana binta da kallon al'ajabi ita kuwa ta mike ta shige toilet din.
A tunaninta in ta fito zata tarar basa nan amma tana fitowa Mami tayi kanta tana kai mata bugu sai dai khairy ta zame. “Ke don ubanki har ina miki magana kina ji zaki mayar da ni mahaukaciya” Murmushi kawai khairy tayi tare da raba Mamin zata wuce, jin ta kara jawota yasa ta juyo tace “Baiwar Allah nifah bani da mutunci ga babban da ya zubar da kimarsa kin gane?” daga haka tayi kokarin kwacewa daga rikon da Mami tayi mata.
Fauzy ce tace “Yau sai naci abu ta kazar ubanki tunda kika mare ni don ni ba saarki bace” murmushi kawai khairy tayi zai dai har lokacin Mami na rike da ita. “Ni kike cewa marar mutunci ko?” ta fada a hasale “To ni da mutunci na sai dai ubanki ko uwarki, ashe rainon gidan da yata ta fado kenan” muryar khairy taji ta doki kunnenta “Ki tsaya kaina madam amma kika tabo iyayena wollah sai na baki mamaki”
Sai da Mami ta kankance ido tace “Uhm haka kikace ko? Ba shakka yau na san ina tare da rasa kunya amma babu komai yau zaki tattara ki bar gidan nan” wata mahaukaciyar dariya khairy tayi tace “To fah! Sunan wani wai gadarau, to ke a matsayinki na wa?”
“A matsayi na na uwar matar gidan kuma uwarki!”
Bata ji hauahin zagin ba sai ma dariya da tayi tace “Wai har da su kaza a cin chewing gum? Uhm to Hajiya ai ko matar gidan bata da hurumi da zama na tunda ba ita ta kawo ni ba bare kuma uwarta”
Fauzy fa tunda taga abun ya fara wuce tunaninta ta lallaba ta wuce waje. Khairy ta dubi Mami tace “Madam ki fita zan rufe kofa ko? Ko a nan zaki kwana ne?”
“A uwarki zan kwana, nace a uwarki zan kwana, shegiya mai kama da mayu kawai, wallahi sai kin bar gidan nan don ni rayuwar da nayi ni daya...” bata karasa ba taji an yiwa bakinta mahaukaciyar damka har ta kai ga da kyar take jan numfashi.
Khairy ta kara matse bakin tace “Wannan ne bakin naki mai zagar min uwa ko? To wallahi ahir dinki madam, kinci sa'a ina girmama manya wallahi da yau kashinki sai ya hura wuta, kuma ina miki kashedi wallahi har ki tafi kada ki kara shiga sabga ta, in banda ma rashin ta ido ki kwaso kizo gidan ya ki zauna kamar a garin marasa kunya, mu dai fulani mun gaji kunya bari ki ji, da na sake ki kuma ki bar min daki”
Sakin bakin Mami tayi wacce taja gefe tana sauke numfashi tace “Amma ke kam Allah yayi tambadaddiya ko?”
“Kar ki kara fada” khairy ta katseta. Shiru kuwa tayi tana aikin jefawa khairy harara, cikin ranta tana fadin “Yau naga ta kaina, dole na dage ganin yata ta kubuta daga sharrin wannan yarinya” tunanonta ya katse ne da jin muryar khairy tana fadin “Madam get out, i wanna close the door” a sabule kuwa ta fito babu kunya.
Ko da ta koma dakin pretty ta tarar da Fauzy a can, Fauzy kuwa bata sanar da pretty abunda ke wakana ba saboda yanayin jiki irin na mai jego, ta san zata iya cewa sai taje.
Ganin Mamin na haki tana kuma sauke numfashi yasa pretty fadin “Lafiya Mami?, ba dai dukanta kika yi ba ko?” Zazzare ido Mami ta fara tana fadin “Ai kin riga kin dauko masifa gidanki, har yaushe zaki tsaya a kawo ta tun wuri baki korata ba eh?, to bari kiji don baki san irin diban albarkar da yarinyar nan tayi min bane shiyasa, wallaho tun wuri ki samu mafita”.
Kasa-kasa Fauzy tayi dariya sannan ta dago cike da kulawa tace “Gaskiya Pretty kisan matakin dauka, kinga irin kallon da take jifan Mami da shi?, ni niyya ta sai dare zan far mata saboda naco ubanta”
Ai kuwa pretty fa an harzuka don kuwa jikinta har tsuma yake yi harda kokarin tashi alamun wurin Khairyn zata je, da sauri suka riketa suna fadin “Ya haka pretty? ”
“Rabu da ni naje naci mutuncinta please”
_To jama'a yau ake wata ga wata, bari muji pretty me zata je yiwa khairy?, shin khairy zata bar gidan Hamma Zaki ne?, follow my ink and find out, Diamond Bhatool ce!_
*COMMENT & SHARE PLEASE*
[07/09, 2:17 p.m.] 💎Diamond_Bhatool💎: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““89&90”””
Washegari khairy bata yini a gidan ba, tare da babes suka wuce don karasa hada abubuwan bukatarsu. A daya bangaren kuma pretty ta kudiri aniyar korar khairy saboda hudubar shaidanci da mahaifiyarta tayi mata.
*FLASH BACK*
A shekarar 2005, lokacin Alhaji Saminu Hambali na rike da mukamin Special adviser na Maigirma governor of Katsina state, matashin dan siyasar yana da son abun duniya da kuma hadama ma baa barinsa a baya. Tunda ya samu wannan mukami sai ya fara kokarin daura Hon. Dr. Umar Sani Danja kan muguwar akida ta satar kudin gwamnati, sai dai Allah ya so mai girma governor ya fahimci ba shawarar kwarai Alhaji Saminu ke bashi ba.
Tsawon lokaci Governor ya bawa Alhaji Saminu ko zai sauya dabi'u amma inaa kullum abunsa gaba yake karawa. A haka suka ci shekarar farko cikin tenure nasa aka shiga ta biyu. Munanan halin Alhaji Saminu kullum kara bayyana suke, hakan yasa daga karshe Mai girma governor ya tsigeshi daga mukaminsa ya daura wani a maimakonsa.
Wannan abu ba karamin bata ran Alhaji Saminu yayi ba don a cewarsa bai cancanci haka daga governor ba tunda tare da shi suka yi fadi tashi ganin ya samu kujerar. Dalilin bakar zuciya irin ta Alhaji Saminu yasa ya rura wutar daukar fansa cikin ransa, ya kuma yi alkawarin duk wanda yayi kokarin dakatar da shi zai fuskanci hukunci.
Ganin dukiyar da ya fara tarawa ta ja baya ga kuma uwargidansa da take damunsa da bukatar kudi, kusan kullum sai sunyi fada gashi kuma yana bala'in sonta, baya tunanin zai ita rabuwa da ita ko da kuwa kullum sai ta zane shi da tsumanguya kafin ya fita.
A lokacin ne kuma suka hadu da Alhaji Yunusa Boss, wanda yake da dukiya maras adadi, yaji dadi sosai don kuwa basu rabu da Boss ba sai da yayi masa Alkawarin zai sama masa aikin yi daga nan suka yi exchanging contact.
Ranar da suka hadu Boss yayiwa Alhaji Saminu bayani akan aikin da zai bashi, da farko yaki saboda tsoro amma da Boss yayi masa bayanin shima da ita ya tara dukiyar nan yasa ya amince. Ba kowacce irin sana'a bace sai safarar miyagun kwayoyi da kuma makamai. Boss mugun dan ta'adda ne da sunansa yayi kamari cikin Nigeria, duk ko hukuma ta kama shi bata iyawa shiyasa yake tsula tsiyarsa son ransa.
Shekaru kusan bakwai Alhaji Saminu ya shafe yana aiki da Boss din, tuni shi ma ya samu nasa yaran. Sun shagala da iya shegensu ne kuma kwatsam sabon shugaban sojoji wato Gen. Muhammad Naira ya daura musu banten nema tun ranar da ya kama su hannu da hannu suna bude bandles na makamai masu hatsarin gaske a lokacin da yaje Katsina wurin amininsa Prof. Mansur Usman.
Tun daga wannan rana ya samu jami'an sirri suka fara bibiyar Alhaji Saminu, da suka tabbatar sai aka sanar da jami'an yan sanda, baa dade ba kuma aka shigar da kararsu a kotu. Ana cikin shari'ar ne kuma wani munafikin dan sanda ya sanar da shi ai sabon general ne yasa aka kamo su.
Zo kuga yadda ran Alhaji Saminu ya baci akan wannan abu sai dai rubutaccen al'amari gidan kaso aka tura shi don yayi serving 3years aciki with hard labour da kuma kwatar kaso hamsin 50% na dukiyar sa ya tara, yayi kuka iya kuka amma yayi alkawarin fitowa kafin lokacin. Abun mamaki cikin sati Boss yayi cuku-cuku aka fitar da Alhaji Saminu. Tun daga wannan rana ya dauki aniyar daukar fansar abunda General yayi masa, kason dukiyar da yasa ya rasa yayi alkawarin shima sai ya ruguza tashi dukiyar da ya tara.
Sau tari yakan tura yaransa daga Katsina zuwa Adamawa don kaiwa General hari amma basa cin riba, daga karshe sai ya fara kokarin hada alaka da ma'aikatan gidan amma bai samu hadin kai ba. Shekaru kusan biyar ya bata yana wannan farautar sai dai ubangiji bai vashi sa'a ba, ana cikin hakan kuma pretty wato diyarsa daya gwal da ya dora soyayyarsa a kanta ta bullo da zancen auren dan General. Yayi farin ciki sosai don a tunaninsa wannan babbar dama ya samu ta cika muradinsa akan General Naira.
Tunda auren ya dauru suke tunanin yaya zasu tsara abun har ta kai ga sun tsayaa matsayar saka explusive device a gidan amma basu samu hadin kai daga wurin maaikatan gidan ba.
Shawararsu ta karshe itace matsayarsu, zasu dauken shalelen da General Naira yake da sannan su saka masa tara mai dan karen yawa da suke tunanin zasu kwashi kaso 60% na dukiyarsa.
★★★★★★★★★★
*DAWOWA CIKIN LABARI*
Sai yamma lis suka kammala hada komai nasu, daga nan driver ya maida khairy gidan Hamma Zaki, ko da ta isa ta tarar da Fauzy a parlourn ga sunyi kaca kaca da shi kamar shanu. Tsaki tayi tace “Ashe abun gado ne” don a tunaninta Fauzy ma kanwar pretty ce.
Dakinta ta wuce tana mika, sai da ta watsa ruwa daga nan ta dan mike tana karanta Alqur'an har bacci ya sace ta. Cikin bacci taji alamar mutum na taba ta, a firgice ta mike, ganin kanwar pretty yasa tace “Lafiya kike tashi na?” Fauzy da alamun rashin gaskiya ya bayyana tattate da ita tace “Dama zan ce miki azo a shirya abincin dare ne” hade fuska khairy tayi tace “To fice mun, in nayi niyya zan yi in naga dama kuma bana yi saboda wa kattai zan girkawa”.
Fauzy na fita ta rike haba tana mamakin rashin kunya irin na wannan kyakkyawar yatonya da ta kwallafa ranta akanta, baki ta cije tace “Ai dole na same ki yarinya”.
Khairy kuwa da kyar ta fito tayi musu taliya da manja sai tayi warming sauran farfesu wa pretty, bata kai musu saman ba ta ajiye a dining idan suna so suzo su dauka.
Shiru suna jiran abinci babu shi babu alamunsa babu kuma na mai kawowa yasa Mami saukowa da niyyar cin mutuncin yarinyar nan don ita a son ranta ta bar gidan. (Nace kamar wata kishiyarki?).
A tare da Fauzy suka fito, Mami ta tambayi Fauzy dakin yarinyar, Fauzy ta nuna mata don itama yarinyar ta bata haushi dazu. Babu knocking kawai Mami ta kutsa ciki, lokacin Khairy ta fito daga wanka tana kwalliya gaban mirror. Ashar Mami ta lailayo tana fadin “Bura uba! Yau naga isa da mallaka a gurin yarinya, ke ko kunya baki ji ba” sai a lokacin Khairy tasan an shigo dakin, idan da mirror din da khairy ke gani suke magana sa saka ran amsawa. Ko kallonsu bata yi ba ta bude trolleynta ta ciro doguwar riga, ta juya zata shiga toilet ta saka kawai taji an jawota, ba kowa bace sai fauzy. Tana juyowa ta wanketa da mari tuni Fauzy ta sake ta tana binta da kallon al'ajabi ita kuwa ta mike ta shige toilet din.
A tunaninta in ta fito