Showing 117001 words to 120000 words out of 135404 words

Chapter 40 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46367

yayi yana furta “Ya Allah”.

“Sannu” Dr ya furta, “Yanzu me yake damunka?” ƙasa-ƙasa ya nuna masa kansa da hannu. Cikin magungunan dake bedside drawer ɗin ya ɗauko allura yayi masa kafin ya fice. Yana fita Khairy ta ƙaraso kusa da shi fuskarta ɗauke da tsantsar damuwa. “Sannu Hamma”. Kamar ya ce kada tayi shiru saboda yadda Muryar ta ke dukan kunnuwansa yayin da saƙon ke isa zuwa cikin zuciyarsa through the network of blood vessels.

Few minutes bacci ya ƙara kwashe shi, ba shi ya farka ba sai after Asr prayer, Babu laifi he's feeling better, da taimakon Khairy ya shiga toilet yayi alwala, veil ɗin ta Dake cikin jakar ta shimfida masa ya gabatar da Sallar Zuhr da kuma Asr ɗin. A hankali ta furta “Bari na saka maka abinci Hamma”
Kai ya jijjiga alamar a'a. Ɗan kwaɓe fuska tayi a shagwaɓe ta ce “Please Hamma eat something mana” wannan karon ta mugun tafiya da imaninsa sosai har bai san lokacin da ya ɗaura kyawawan idanuwansa a kanta ba. Kwantar da kanta gefe tayi ta ƙara faɗin “Na zuba maka ko?” haka kawai ya tsinci kansa da ɗaga mata kai.

Pepper Soup ɗin da har yanzu yake tiririn ta zuba a bowl 🍜 sannan ta saka spoon, soya beans milk drink ɗin ta tsiyaya a cup ta nufi gefensa ta zauna. Da kanta tayi feeding nasa har sai da ya kauda kai sannan ta bashi drink ɗin ya sha, he so much missed her delicacies, the aroma of her meals, duk irin yarda yake jin bashi da appetite amma ya ci kuma ya ƙoshi. Hamdala yayi kamar wanda aka saka dole yace “Thanks” cike da kulawa, murmushi ta yi masa tare da parking used bowl da cup ɗin.

Kan kujerar ta dawo ta zauna tare da zuba masa idanuwa, shima a nashi ɓangaren duk giftawarta a kan idonsa ne. Tunawa da amaryar da har yau bai ga fuskarta ba yasa ya yamutsa fuska yana kwanciya abunsa, yayi alƙawarin yana komawa gida zai neme ta amma fatansa Allah yasa mutuniyar kirki ce kamar masoyiyarsa.

Sai bayan maghrib aka yi discharge nasu, Dr. Faruq ne ya maida su har gida tare da bawa Khairy medications nasa, ya kuma yi mata cikakken bayani akan yadda za'a ke bashi a kan in ta je tayi wa amarya bayani. Ita kanta Khairy ƙarfin hali ne kawai take gwada wa saboda yadda kanta ya kulle, gashi kuma an kawo Hamma Zaki gidanta, to wai me suke nufi ne? Ko dai suna nufin Hamma ne miji na?”, “Nooo that could not be possible, ina Ni ina Hamma!”

Ganin tsayuwar na gagararta yasa ta daure ta nufi parlourn, kwance ta tarar da shi kan sofa, ba tare da ta kalle shi ba ta kai basket ɗin kitchen. Sai da ta fito ta ce masa ya tashi ta raka shi bedroom nasa. Mamaki ne ya kama shi jin maganar ta ta banbaraƙwai, “me take nufi ne?” sai kuma ya ɗan kawar da kansa gefe yace, “Ki mata magana ta zo ta shiga da ni sai driver ya miƙa ki”.

Wani kallo da bata san tayi ba ta aika masa irin dai wadda ake cewa kallon tara baka cika goma ba. To irin sa ta aika masa har sai da ya sha jinin jikinsa. A ranta tace “Na ƙara tabbatar shine aka ɗaura mana aure da shi amma why yayi min haka?, ko fuska ta fa bai sani ba” hawayen da ke shirin zubowa ta tare tana sosa idonta tace “To ai Ni ce matar gidan, ya son ranka?”

Ɗagowa yayi cike da mamaki jin maganar ta ta, abunda ya ƙara bashi mamaki ma furucin nata. Tsintar kansa yayi da faɗin “Khairy Please ki mata magana, I'm weak ina buƙatar support.”
Tausayi ya bata shi yasa ta haƙura ta ƙarado kusa da shi tare da miƙa masa hannunta don ta taimaka masa ya miƙe tsaye.

Hannunsa ya miƙa mata ta ɗan saka ƙarfi kadan ta taimaka masa ya miƙe tsaye. Ba tare da ta saki hannun nasa ba suka fara takawa har zuwa bedroom ɗin da take da tabbacin nasa ne. Taimaka masa tayi ya kwanta ta ɗan lulluɓa masa blanket.
“Ko kana buƙatar wani abu Hamma?” kai ya gyaɗa mata
“Mene ne?”
Da hannunsa ya nuna mata bakin gadon wato ta zauna. Haɗe fuska ta ɗan yi tace “Ka huta Hamma, bari na je na yi shirin bacci, in kana buƙatar wani abun don't hesitate to call me, ok?”

Daga haka ta ja ƙafarta ta fice zuwa nata bedroom ɗin. Tana fita ya sauƙe ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwansa. Tuno abinda ta faɗa ɗazu yayi “to Ni ce matar gidan” a zahiri ya furta “What!, me hakan yake nufi?”
Zuciyarsa ta bashi amsa da “Yadda aka yi mana, da a ce tun kafin auren ka bi umarnin daddy na zuwa ka ganta da haka bai faru ba ai”
“To yanzu yaya zanyi?” zuciyarsa ta ƙara bashi amsa da “Mafita ɗaya ce tunda dama ita ce wacce kake so ka sauƙar da kanka ka bata haƙuri sannan ka nuna mata soyayya mai tsafta” kai ya jijjiga yana faɗin “Nooo, wata shawarar”
Zuciyarsa ta ce “To in dai ba haka ba kasan dai baka kyauta mata ba, and ba zata zuba ido abinda kayi mata ya tafi banza ba”
“Ya Allah ” ya faɗa yana runtse idanunsa.

Kwanan da yayi kenan da ƙyar bacci ya ɗauke sa, dalilin faɗawarsa wannan yanayin kuma har ya mance don wannan issue ɗin a ganinsa is more harder to be tackled. A nata ɓangaren ita ma haka ta faru, tabbas ta jima da fara son Hamma Zaki, shine mafarkin ta musamman lokacin da babes suka tisa ta gaba tayi tunanin za'a haɗa su aure ne, amma daga baya ta fara haƙura sai dai ko yanzu da ya kasance mijinta ba zata bari ya kuɓuce mata ba don samun ya shi sai an tona, saboda haka zata bi hanyar da ta dace ne ta nuna masa irin kuskuren da ya tafka.

Da asuba ita ta fara tashi, ta ɗauro Alwala sannan ta nufi bedroom nasa, ganin baya kwance ya tabbatar mata da cewa ya tashi ɗin, ita ma bata tsaya ba ta koma tayi Sallarta, tana idarwa tayi azkar ɗinta. Sai around 6:00am ta nufi bedroom ɗin nasa, kwance yake amma ba bacci yake ba sai dai zaka yi tunanin baccin yake saboda idanunsa da ke lumshe. A hankali ta taka har ta isa bakin gadon wanda shi ma isowarta ya sa ya buɗe idanuwansa.
“ina kwana Hamma, ya kwanan jikin?”
“Alhamdulillah”
“Masha Allah, Allah ya ƙara maka lafiya”
“Ameen”
“Me kake son ci na daga maka?”
“Pepper Soup irin na jiyan nan idan zan samu” miƙewa tayi tana faɗin “Ok”.

Mintuna kaɗan ta ɓata sai ga ta tafe da bowl ta zuba pepper Soup ɗin ciki da kuma spoon, a bedside drawer ta ajiye tare da nufar fridge ta ɗauko bottle water. Kamar jiya ita ta bashi sai dai fuskar nan ta ta daure, bayan ya gama ci ta bashi ruwa yasha sannan ta bashi maganinsa sannan ta haɗa mishi ruwan wanka. Ganin ya shiga wannan yasa ta gyara gadon sannan ta fitar masa wata white jallabiya daga closet. Daga nan tayi waje.

Yana fitowa ya saki murmushi ganin yadda ta gyara gadon ga kuma kayan da ta cire masa. Sajensa da bai fiye cika ba saboda yanayin aiki ya shafa yana faɗin “Mar'atussaliha, Allah ya juyo min da hankalinki gare ni”. Daɗin jikinsa da yaji sosai yasa ya shirya a hanzarce, kan bed ya koma shi kaɗai yana ta murmushi. Wayarsa ce tayi ƙara ko da ya duba yaga Dr. Faruq yasa ya ɗanyi murmushi. Picking yayi a ɗaya ɓamgaren Dr. Yayi sallama Hamma Zaki ya amsa masa. “Yaya ƙarfin jikin?”
“Alhamdulillah na ji sauƙi ma”
“Dama zan ce maka gani nan na zo ne ina neman izinin shiga” tsaki Hamma Zaki yayi ya ce “To kayi ta zama”. Ƙiran ta katse yana sakin wani tsakin.

Mintuna uku sai ga shi ya sauƙo ƙasa, fuskarsa sake ya ƙaraso ga abokin nasa. Nan suka gaisa bayan sun gaisa Dr ya ɗan tsira wa Hamma Zaki ido kamar me son gano wani abu.
“Dude!” ya faɗa yana tsayawa. Gira Hamma Zaki ya ɗaga masa alamar what.
Dr faruq yace “Dude, what's wrong with you?”
“Me ka gani?” ya bashi amsa a gajarce.
Hararar wasa Dr ya jefa masa sannan yace “On a serious note mu bar zancen wasa, Please me yake damunka ne?”
Yamutsa fuskarsa yayi yace “Nothing oo”
Shima Dr a wannan karan sai ya ɗaure fuskarsa yace “Stop beating around the bush man, ina da hankali fa, jiya Ni na kai ka asibiti unconsciously Amma yanzu Ka CE min babu, me kake nufi?”

Sassauta fuskarsa yayi don baya son sanar da kowa wannan batun har sai ya yanke hukuncin da ya dace. Dr ya ƙara faɗin “Tunda ka mayar ki mahaukaci ban kai ka samar da ko damuwarka ba fine, sai anjima” daga haka ya miƙe zai fice.

Ganin haka ya sa Hamma Zaki saurin riƙo shi yana faɗin “I'm sorry...”
Katse shi Dr yayi yana faɗin “Shikenan nace, ka riƙe damuwarka, na gode, sake ki na wuce” marairaice fuska Hamma Zaki yayi yace “Ka zauna muyi magana man, I'm sorry” ba tare da ya saki fuskarsa ba ya koma ya zauna yana maida kallonsa ga Hamma Zaki alamar jiran ƙarin bayani.

_Comment, share and react please_


[20/09, 2:47 p.m.] Famanté 💎:



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““117&118”””

A hankali ya buɗe baki ya fara magana cikin raunatacciyar murya ya ce “Man!, it's about the issue of Nabila” sai kuma ya dakata. Dr yace “Ina jin ka”
Wani yawu ya haɗiye sannan yace “Man ka san kidnapping na da aka yi kwanan baya she and her parents were responsible?” zaro idanuwa Dr yayi yace “What?” kansa ya jijjiga alamar tabbatarwa yace “Yes!, she is accountable”
Nan ya bashi labarin kiran wayarsa da aka yi jiya aka sanar da shi, sannan yace “Do You know what?” Kai Dr ya jijjiga alamar a'a.
“Khairy is the one who rescued me from them” nan ya sanar da shi kamar yadda jiya aka faɗa masa.

Kafaɗarsa Dr ya dafa yana tapping bayansa. “Dude!, yanzu to me ye plan ɗin ka?”
Ajiyar zuciya ya sauƙe ya ce “Dama can ba ta hanyar Allah ta saka na aure ta ba, and...” sai kuma yayi shiru tunawa da lokacin da ta zubar da cikin da ba nasa ba, idanunsa ne suka ƙara yin ja yace “Zan rabu da ita saboda ba mace ta gari bace, zan rungumi zaɓin Daddy don ina da tabbacin dacewa”.
Dr ya ce “Is alright nima ban goyi bayan ci gaba da zama da mace irin Nabila ba, sai dai me zaka cewa su Daddy idan suka ji batun rabuwar taki?” Hamma yace “Zan sanar da su gaskiya ne, in ba haka ba Daddy da Mom zasu iya cewa na mayar da ita, and I don't think zan iya ci gaba da rayuwa da ita”

Tapping bayansa Dr ya ƙara yi yana faɗin “Hakam ma yayi, amma ba sai ka hukunta ta ba taje ita da duniya, sannan baby Humairah fa?”
Murmushin takaici yayi yace “Zan karɓe ta da zarar ta kai fice months idan yaso sai ake haɗa mata formula, zata zauna wurin su Mom tunda yanzu gidan babu yara.”

Kansa ya gyaɗa alamar gamsuwa da shawarar Dr ɗin. Nan dai ya ƙara jan hankalinsa yana ƙara tunatar da shi rayuwa. Har ya miƙe zai tafi yaji Muryar Hamma “Ba iya wannan ne issue ɗin ba” komawa yayi ya zauna yana faɗin “Ina sauraronka”.

“Dude matar da Daddy ya aura min”
“Whats wrong with her?” ya tambaya
“eh eh am dama ban san wace ce ba sai jiya?” zaro ido Dr yayi yana ƙara jinjina faɗin rai irin na abokin nasa. “Me kake nufi”
Ajiyar zuciya Hamma Zaki ya sauƙe yace “Eh Dude, Khairyn da nake burin aura ashe ita Daddy ya aura min, nayi watsi da zaɓinsa ashe dai muradi na ya aura min” ya faɗa yayin da idanuwansa suka yi ja kamar garwashi sannan ya ci gaba “Ba na tunanin zata amince ta ci gaba da zama da ni Dude, nayi watsi da ita, na nuna mata halin ko in kula, gashi yanzu na rasa yaya zanyi”.

Kafaɗarsa Dr ya dafa yana faɗin “Is ok now, Kai ma Man Baka kyauta ba, har aka saka rana aka yi bikin ai ya ci ka sauƙo ku daidaita da matarka, Amma aah tsawon satikai da biki a ce baka duba ko ya take ba! Ka tafka kuskure Man, thank god yarinyar tana da hankali da sauƙin kai, shawarar da zan baka duk da bani da tabbacin za kayi amfani da ita amma zan faɗa maka, ka sauƙar da kanka, ka ja ta a jiki ka nuna mata kulawa, ka fahimtar da ita ka fahimci kuskurenka don ina tsorace maka su Daddy su san da wannan batu coz bana tunanin abun zai yi kyau.”
Cike da gamsuwa da shawarar Dr ya jinjina kai yana faɗin “Thank You for always being there for me Dude”
Tapping bayansa yayi yace “Nevermind man, You deserve more”. Daga haka Dr yayi masa sallama kan zai wuce hospital yana mamakin yadda duniya ta juya wa abokinsa mai cike da izza da taƙama, wai yau shi ne yake furta tsananin ƙaunarsa ga wata ɗiya mace a duniyar nan.

Sai da ya ga fitarsa sannan ya juya zuwa bedroom ɗinsa, har zai shiga sai ya tsinci kansa da murɗa handle na ƙofar, tarar da ita yayi zaune a kan gado tana danna wayarta, kamar bata ganshi ba ta ci gaba da abinda ta ke yi, sallama yayi, ba tare da ta ɗago ba ta amsa masa. A sukwane ya ƙaraso bakin gadon ya zauna a kan lallausan carpet ɗin. Zuciyarta ne ta fara bugawa da sauri da sauri kamar yadda ta sa take bugawa idan har sun samu kudanci da juna komai ƙanƙantarsa kuwa.

A hankali ya miƙa hannunsa zuwa ga nata da ke riƙe da waya yayin da yake durƙushe kamar mai roƙon wani abun. Ƙasa hana shi tayi sai ta tsinci kanta da jin kunyarsa. Wayar ya cire ya ajiye a kan bedside drawer tare da haɗe hannun da nasa yana kawo shi saitin ƙirjinsa. Cikin wata murya da bata taɓa jin ta a tattare da shi ba yace “khairyyyy” yana mai jan ƙarshen har sai da tsikar jikinta ta tashi. Har zuwa lokacin kuma ta kasa duban fuskarsa bare ta saka idanunta cikin nasa.

“Ummul khairy” ya ƙara faɗa, cikin ƙarfin hali ta haɗe fuska tare da fuzge hannunta da ya riƙe tana faɗin “Kanq bukatar wani abun ne Hamma?”. Kai ya gyaɗa mata kamar wani ƙaramin yaro yace “Im sorry 😔”.
Idon ta ta buɗe sosai tare bata san lokacin da ya haɗe da nasa ba, ita da tayi shirin faɗar magana sai kuma ta kasa, kau da kan nata tayi gefe tace “you Are sorry for?” marairaice fuska yayi yace “for everything ” juyawa tayi don ba zata iya jurar tsayawar da shi ba, duk da ta so hukunta shi amma soyayyarsa ba zata bari ba, tunda hankalinta ya dawo gare ta ta kamu da ƙaunarsa, ya za'a yi ta iya ƙalubalantarsa ma, taku ɗaya tayi ta ji ya dakatar da ita ta hanyar riƙe kafaɗarta da hannayensa biyu ya juyo da ita suna fuskantar juna.

Ƙoƙarin ƙwace kanta take sai dai ya hana ta wannan damar daga ƙarshe ma sai ya rungume ta tsam a ƙirjinsa, lumshe idanunsa yayi yana shafa kyakkyawar sumar kanta wanda ya sanya ta shiga wani yanayi na daban sai ta lafe a ƙirjin nasa. Ganin ta saki jiki yasa ya buɗe baki cikin wata irin murya da ko da a ce a kwai mutum a gefen su ga zai ji me yake faɗi ba.
“I'm sorry Ummul Khairy, I'm sorry for everything ” sai kuma ya janye ta daga jikinsa ya zaunar da ita a bakin gadon.

Guiwoyinsa ƙasa yace “Kiyi haƙuri ki saurare Ni duk da ban cancanci hakan daga gare ki ba” da sauri ta diro ƙasa daga gadon don ba zata iya jurar hakan ba, gani mutum mau tarin daraja da ƙima gabanta durƙushe sai take ganin rashin ɗa'a ne hakan. Fakar idonsa tayi ta fice daga ɗakin tana sauƙe ajiyar haki.

Ganin ta fice yasa ya runtse idanunsa yana dafe kansa da ya sara, a sukwane ya fice ya koma nashi bedroom ɗin. Ko da ta sauƙa ƙasa kitchen ta nufa ta fara duba me zata haɗa musu.

A ɓangaren Hamma Zaki yana shiga bedroom ɗinsa ya watsa ruwa ya saka wasu kayan tare da fitowa waje, bai ƙara shiga bedroom ɗin nata ba a cewarsa idan ta sauƙo sai su fahimci juna. Ƙasa ta sauƙa a tunaninsa dama ta koma bedroom ɗinta. Farar motarsa dake parking lot ya nufa, yana shiga ya kunna ta, Gate man ya ƙaraso yana miƙa gaisuwarsa gare shi kafin ya buɗe masa.

Dirin motar da ta ji yasa ta ɗan zaro ido tana fitowa zuwa parlourn, ta window ta leƙa ganin dai tabbas shi ɗin ne ya fita sai ta dafe kanta tana faɗin “Ya Allah, I'm idiot Wollah, me yasa na bar shi ya tafi?, me yasa ban tsaya na saurare shi ba?, why? Ya Allah ka kiyaye min shi” daga haka ta koma kitchen ɗin ranta babu daɗi a haka har ta gama girkinta ta jera a dining sannan ta nufi bedroom ɗinta, tass ta gyara shi banda wani sassanyan ƙamshi babu abunda ke tashi, idanuwanta ta lumshe kana tayi regulating sanyin ɗakin, daga nan ta nufi nasa bedroom ɗin, sai da ta gyara komai ta wanke toilet tas, nan ma dai sassanyan kamshi kawai ke tashi.
Murmushi tayi sannan ta jawo ƙofar ta rufe ta koma bedroom nata, wayarta ta ɗauka ta kunna data, ganin messages na babes yasa ta shiga tana dubawa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login