Showing 48001 words to 51000 words out of 135404 words
Uncle Bello suka je nema wa Hamma Zaki auren Pretty babu Musu aka basu don kuwa shi kanshi uban Pretty akwai wata ajiyar tsakanin shi da wannan ahali.
Wata guda aka sanya ranar bikin, tun daga nan Pretty aka fara shirye-shiryen bikin. Babu wanda ya nunawa Hamma Zaki rashin son auren nasa sai dai granny kullum sai tayi magana in yazo part ɗin ta, in kuma ya zauna har kuka sai tayi wai yaje ya nemo Ƴar mutunci ba wannan da ta haɗa rigima kwanaki ba.
Sarah kuwa babu ruwan ta coz yanzu ta riga da ta cire son Hamma Zaki cikin ranta, yanzu mutum ɗaya ne yake yawo cikin jinin jikin ta wato Captain Sulaiman wanda tuni ya isa gida har an fara shirin yin bikin al'ada irin na indiyawa.
Tunda ya diro ƙasar shi da Aunty Waheeda suka sauƙa a ɓangaren su dake cikin family house ɗin nasu. Labarin auren Hamma Zaki ya dirar musu a kunne su ma dai basu ji daɗi musamman da suka ji babu wanda ke son auren. Fatan Alkhairi tare da addu'oi kawai suka yi musu.
★★★★★★★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Kamar yadda ta buƙata haka arɗo ya sanar da saƙon ta sai dai bai ce Ƴar Iya ke son ganin su ba.
Kafin kace me fada ta cika da samarin garin gaba ɗayan su.
Cikin nuna isa da taƙama tazo ta kama wuri ta zauna sannan tace da arɗo ya sanar da su dalilin taruwar su.
Gyaran murya yayi sannan yace
“To kamar dai yadda kuka gani an haɗa wannan taro na matasa ne ba don kowa ba sai Ƴar Iya, kuma dalili shine zata zaɓi miji cikin matasan ƙauyen nan” daga haka ya dakata yana maida kallon shi ga Ƴar Iya wacce take famar sake murmushi.
“To Ƴar Iya bismillah, ga su nan ki zaɓi duk wanda yayi miki a cikin su”
Sai da ta farfara ido kafin ta fara binsu ɗaya bayan ɗaya tana dubawa, ta shinshini wannan ta yatsina fuska tayi kallon banza daga ƙarshe dai duk ciki babu wanda yayi mata. Dawowa tayi ta zauna tare da yamutsa fuska tace
“Basu yi ba”
Arɗo yace “Shikenan kada ki damu zan gayyato samarin ƙauyukan dake kusa da mu zuwa gobe kinji? Ki kwantar da hankalin ki maza”
Jijjiga kai Ƴar Iya tayi tace
“Aah Arɗo ka barshi ai naga wanda yayi min ma ba sai an gayyato wasu ba”
Jin furucin ta yasa kowa fara zare ido yana sunkuyar da kanshi ƙasa. Cikin zukatan su kuma addu'a suke Allah yasa dai kada ta zaɓe su. Don kuwa babu wanda zai so ya auri Bala'i, a faɗar su ai Ƴar Iya saidai aljani.
Can Ƴar Iya tayi murmushi tace
“Ba kowa ne wanda na fitar a matsayin miji na ba sai kai Arɗo, kai ne zan aura”
Ta faɗa tana pointing nashi da yatsar ta.
(Toh fah, kunji pretty dai ta samu Hamma Zaki na zai aure ta.! I'm jelous fah☹️😥. Su Ƴar Iya kuma ta yadda aka ɓullo kenan! Toh zadai.muji yadda zata kaya!)
COMMENT, LIKE and SHARE FISABILILLAHI!
Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya, comments ɗinku kawai nake buƙata don shine ƙwarin guiwa ta.
[6/22, 12:47 PM] Diamond Bhatool💎🩷✍️:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
Eid Mubarak to you all!
Barkan ku da sallah, muna roƙon Allah ya maimaita mana Amin.
Gaisuwa gareku Ƴar Iya READERs
Faty Sharif~
Ameeran Mama~
Oum Basmat~
Ummi Hafsat~
~And the rest.....Allah ya bar ƙauna.
SHAFI NA “““49&50”””
Arɗo da ya rasa tunaninshi na wucin gadi baki kawai ya sake yana ganin ikon Allah yayin da sauran matasa suka shiga wani irin yanayi mai kama da tsoro, tsoron su Allah tsoron su kada iskanci irin na Ƴar Iya ya ƙaru sakamakon auren arɗon gari.
Bayan wasu mintuna ta ƙara murmushi tare da kallon Arɗon wanda har lokacin bai gama dawowa daidai ba tace.
“Arɗo baka ce komai ba har yanzu”
Cikin wani irin yanayi arɗo yace
“Haba Ƴar Iya ai nayi miki tsufa, ki dube Ni kice ni Zaki aura, Ina laifin Matashi mai jini a jika?”
Haɗe rai tayi tace
“Na gama magana Arɗo, Ni kai ɗin dai nike so”
Irin yadda tayi da fuskar tata yasa Arɗo tsorata cikin karyayyiyar Muryar sa yace
“Shikenan Ƴar Iya babu komai Allah ya kai mu lokacin”
Sai a lokacin Ƴar Iya ta saki fuska tare da faɗin
“Yauwa Arɗo sai a fara shiri, wani satin ne bikin”
Daga haka taro ya baje, kowa mamaki kawai yake wai Arɗo zai auri Ƴar Iya. Abun ka da ƙaramin gari tuni zancen ya bazu, babu shiri Inna Zaliha ta ƙudurta ziyartar Bulebule washegari.
Gidan Arɗo ma an rasa zaman lafiya don kuwa Saratu ihu tayi ta kurmawa jin batun auren Arɗo da Ƴar Iya. Daren ranar dai babu bacci don kuwa Innani ma abun bai mata daɗi ba sai dai babu yadda suka iya dole su bi umarnin Sarauniya Ƴar Iya.
Saratu kuwa mancewa da waye Ƴar Iya tayi, washegari sassafe tayi niyyar wucew kahin ta kwaso Ƴan daba azo aci uban Ƴar Iya.
(😂😂😂, Zamu ga yadda za'a yi dai. Su Ƴar Iya masu bikin manya, an zaɓi miji kuma an saka rana. Hooohohooo).
Inna Zaliha da safe ta wuce wurin Bulebule. Taso a dakatar da auren a cewar ta mahaukaciyar nan bata dace da auren Arɗo ba sai dai Bulebule ya tabbatar mata da cewa auren nan dole za'a yi shi sai dai ba zai yi ƙargo ba. Wannan yasa ta ɗan samu salama cikin ranta ai ko ba komai zata fito daga gidan. Bulebule ya tambaye ta yanzu me take so ayi. Nan ta wangale baki tace tana so Ƴar Iya tayi nesa da gida.
Babu ɓata lokaci Bulebule ya haɗa mata magungunan da yadda zata yi amfani da shi daga nan ta baro wurin zuwa gida.
★★★★★★★★★
*ALEE POV*
Soyayyar Hamma Zaki da kuma Pretty ta kankama don kuwa yanzu babu laifi shima yana jin wani abu game da ita, shi kan shi yanzu ya ƙosa suyi auren nan.
Mom da kuma sauran Familyn Alhaji Naira sun dukufa wurin yiwa Hamma Zakin addu'a don sun tabbatar ba haka kawai future wife din shi ta barshi ba musamman yadda suka san ɗabi'un shi na rashin son mata, matan ma marasa kamun kai sai gashi rana tsaka yace sai ita.
Burin su Allah ya maida mummunan nufin Pretty kanta saboda Hamma Zaki bai cutar da kowa suma basu fatan Ubangiji ya bawa wani izinin cutar da shi.
Ana saura two week bikin Hamma Zaki da kanshi ya wuce Canada ya haɗo lefen gimbiyar shi Pretty. A cikin satin su Nenne suka kai gidan su amarya. Tuni lefen ya karaɗe duniyar sada zumunta don irin yadda ya kashe kuɗi wurin haɗa shi.
*ƳAR IYA POV*
Bayan ta koma gida wurin Iya bata yi ƙoƙarin ɓoye mata ba, tas ta kwashe batun auren ta sanar da ita. Iya tayi farin ciki sosai ko ba komai ƴar ta zata huta tunda a gidan arɗo zata yi auren. Nan fa Iya ma aka fara shirye-shiryen biki, a cewar ta zata yiwa shalelen ta bikin Ƴar gata, irin wadda ba'a taɓa yiwa wata ɗiya Mace ba a cikin garin Gallara da kewaye ba.
Ɓangaren Saratu kamar yadda ta ƙudurta sassafe ta fice daga fada, babu ɓsta lokaci ta nufi hanyar kahin. Da isarta kuwa bata ɓata lokaci ba ta nufi wurin su Balamo da su Hodiyo waɗanda suka kasance gagararru cikin kahin. Da ƙyar suka amince da ƙudurin ta daga nan suka ɗaura bayan ta sai Gallara.
Saratu ce ta nuna musu gidan su Ƴar Iya sannan ta tsaya a ƙofar gidan, wani yaro da yazo wucewa ta ƙira akan ya ƙira mata Ƴar Iya amma kul yace inji ta ne, yace ƙawarta ke neman ta.
Cikin gidan yaron ya rantaɓa sallama tare da isar da aikan matar sarki, daga nan yace da su “Tana zuwa” ya wuce abunsa.
Saratu na cije baki tace “Don Allah in ta fito ku nakasa ta, ku daki banza ku daki wofi... Ta rasa ubanwa zata aura sai miji na, yar bura......”
Bata kai ga ƙarasawa ba taci karo da Ƴar Iya na fitowa, alama tayi wa su Balamo, ai kuwa tana ida fitowa suka fara ɗaga bulalun da sunan bugunta. A nan kuwa suka ga burauba don dukan Kawo wuƙa tayi musu da ƙyar suka samu hanyar fecewa. Kan Saratu tayi ta bugi banza daga nan ta barta ƙofar gidan. Da rarrafe Saratu ta koma gida ta yi jinyar kanta.
Ranar Laraba aka kawo lefen Ƴar Iya, babu laifi kaya sunyi a matsayin ta na sarauniya to be. Washegari aka saka Ƴar Iya a lalle.
Ranar juma'a da misalin karfe biyu na rana aka ɗaura Auren A'isha Umar Gallara da kuma angon ta Alhaji Arɗo Usmanu Jauro. Ɗaurin auren da ya samu halartar mutane masu ɗan karen yawa.
Cikin gidan Iya kuwa cike yake maƙil da jama'a, ƴan uwa da abokan arziƙi kowa sAi shige da fice yake. Shinkafa kuwa an daga sama da kwano ashirin don kuwa zuwa ake ana tafiya.
Wasu daga cikin dangin amarya ne suka ce su zasu yi mata rakiya, ai kuwa babu tsammani suka ji tace
“Ni zan kai kaina ban yadda wata tabini gida na ba”
Miƙit suka yi saboda sun san halin ko zancen basu ƙara tadawa ba.
Sai da aka yi sallah Halima tace Ƴar Iya tazo ayi mata ado, babu musu da yake ƙawarta ce ta amince, kwalliya aka sheƙawa Ƴar Iya ta kuzo mugani. Duk da cewa ba wata hamshaƙiya bace tayi mata amma tayi kyau sosai kamar ba ita ba musamman yadda ainihin kyau da Ubangiji yayi mata ya ƙara bayyana.
Ana gama mata kwalliya ta yi sallama da iya wacce ke riskar kuka kamar ba gobe sannan tayi gaba abun ta. Gidan Arɗo wato mijin ta kenan ta nufa kai tsaye. Bata ga kowa ba hakan yasa ta nufi ƙorarta wacce aka yi mata ginin bildin (block) inji su da faɗa.
A hankali ta tura ƙofar tare da shigewa ciki. Baki ta buɗe sosai tana kallon irin kayan arziƙin da Iyarta tayi mata. Bayan ta gama ƙauyancin ta ta haye gadon ta mai rumfa tare da sheƙarewa nan bacci ya ɗauke ta.
(To amarya Ƴar Iya mai abun mamaki Allah ya bada zaman lafiya, ayi amarci lafiya)
*ALEE POV*
Mom CE ta hana yin duk wasu shagulgula a bikin, da ƙyar ta amince mishi da dinner da gidan su amarya suka shirya. Irin rawar kan da Hamma Zaki yake kaɗai zai ƙara tabbatar maka ba lafiya musamman ga wanda ya sanshi before wannan abu ya auko mishi.
Gidan shi da yake Banana Island ya Sha gyara don kuwa dai ƙarfi da yaji Pretty tasa kuka wai ita ba zata zauna a Adamawa ba. Hakan yasa ya zaɓar musu zama a Lagos ɗin tare da ɗaukar transfer zuwa can ɗin. Ba'a daɗe ba kuwa Mom ta gano take_taken shi, babu shiri kuwa ta dakatar dashi kan cewa su zauna a Abuja tunda bata son Adamawa, dalilin mom na hana hakan shine ba zata bar yarinyar nan tayi rayuwa a Lagos ba yanzu ma ya aka kaya balle ta koma Lagos. (Ni kuwa nace ita da take yawo duk yadda taga dama halan ta yi zaman Lagos ɗin ma Mom). Dalili na biyu kuma irin yadda Mom taci alwashin ƙarawa Hamma Zaki aure koda cikin cousin sisters ɗin shi ne.
A lokacin da Hamma Zaki ya sanar da Pretty cewa a Abuja zasu zauna not lagos ji tayi kamar ta shaƙe Mom ɗin nan nashi don taga alama matar babu sauƙi a tattare da ita kuma zata saita ta ne, bari dai shi mai kankat ɗin.
Ranar Laraba a ɓangaren Pretty sunyi kamu, wanda dai ango dama yace shi baya zuwa, ranar Alhamis suka yi Ladies' party. Cikin duk waɗannan events AMARYA tasha kwalliya abunta kamar mai zuwa gasar kyau, sai dai akace mai hali baya fasawa kayan da ta saka sam basu dace ba. Nan social media ta ɗauka wasu na zaginta wasu kuma na zagin mijin, a cewar su ai laifin shi ne da ya barta ta sanya su.
A daren ne kuma taje wurin party da friends nata suka shirya mata wai farewell party. (Ni kaina Bhatool ban so zuwa wurin ba coz Babu alkhairi a ciki). Duk da cewa Mamin ta tayi mata faɗa kan ta guji maza na wani lokacin in ba haka ba duk gyara da aikin da aka yi mata zai ɓaci amma tayi kunnen uwar shegu da ita don kuwa a nan ta kwana tare da su, wannan yayi ya bawa wannan wannan ma yayi ya bawa wannan a cewar su ai farewell ne. Sai da safe ta koma gida ba tare da wani ya fahimta ba ta nemi wuri ta baje sai bacci......
Washegari juma'a, wadda ta kasance ranar da za'a ɗaura aure.
Da misalin karfe 10:00am na safiya aka ɗaura Auren Captain Aliyu Muhammad Naira da kuma amaryar shi Nabila Saminu Hambali akan sadaki ₦100,000 cif a Central Mosque dake birnin tarayya wato Abuja. Ɗaurin auren da yasamu halartar manyan mutane a faɗin Nigeria kasancewar bikin na ƴaƴan manyan ne.
Bayan an ɗaura aure Hamma Zaki ya ƙira Pretty yake sanar da ita. Wani ihu daga saki saida ta tsoratar da soja marmari daga nesa. Daga baya take sanar da shi ihun murna ne, daga nan suka taɓa Ƴar hirar su.
Can Naira family ma babu yabo babu fallasa haka suka gudanar da hidimar bikin sai dai zukatan dukkannin su cike fal da alhonin auren suke. Granny kuwa tunda aka saka bikin nan ta rikice musu, yau kukq gobe kuka don ma Aunty Waheeda na nan takan kwantar mata da hankali don babu laifi akwai sabo da alaƙa mai kyau tsakanin ta da granny.
Sisters ɗin shi ma dai basu so auren ba musamman su Najma da suka so a cikin su aka aura mishi sai dai sunyi alƙawarin taimaka mishi a karya wannan sihirin.
Nenne da Mommah duk basu so hakan ba suna sai dai babu yadda zasu yi Hamma Zaki na son Auren amma zasu yi maganin wannan mushrika dake shirin kutsowa cikin Naira family.
Ina Sarah kuwa?, Ko a jikin ta tunda itama tayi nata masoyin ga kuma irin yadda Captain Sulaiman ya ke nuna mata kula, soyayya uwa uba yadda ya shagwaɓa ta sai dai tana jin wani iri ko ba komai Hamma Zaki ɗan uwanta ne kuma ba zata so abinda zai cutar da shi ba komai ƙanƙantar sa.
Tun da suka gama wayar da Pretty abokan shi suka fara yi mishi tsiya wai tun ba'a kai masa ba ya fara zakwaɗi irin na angwaye. Hamma Yusuf ne kan gaba shi da Dr. Faruq duk da cewar suma suna baƙin ciki da wanga aure ɗin duk da cewa abokin nasu yana cikin farin ciki shi ɗin.
(Akwai aiki a gaba fa, Naira family sun yi shirin tarwatsa Pretty sai dai ita ma fa shirin take yi. Allah ya bawa mai rabo Sa'a, happy married life Hamma Zaki na, gaskiya nikam ina jin kishin wanga aure.
Ƴar Iya kema Allah bada zaman lafiya).
# Sarauniya Ƴar Iya
# Pretty
# Hamma Zaki
Kowa tayi indicating a wanne team take.
COMMENT & SHARE PLEASE
Diamond Bhatool ce!!!!
[6/22, 12:48 PM] Diamond Bhatool💎🩷✍️:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
Bazan manta da ku ba:
_Baby Unah_
_Murjanatouh_
_Zeely_
Haƙiƙa kuɗin ƙawaye na gari ne, Allah ya kula min da ku.
SHAFI NA “““51&52”””
Ranar Asabat Pretty da kuma Hamma Zaki suka biyo Flight ɗin 9am zuwa Adamawa. Direct Naira family house aka nufa da su. Tun daga entrance door pretty take sheƙa iskancin ta shi kuma ya kasa hana ta.
A nan aka yi musu tarba ta musamman, bayan sunyi lunch taja hannun Hamma Zaki suka wuce bedroom nashi upstairs. Flight ɗin 4pm suka bi suka koma gidan su dake Maitama a can birnin tarayya.
Daren ranar angon ya shigo bayan rakiyar da yasamu daga wurin abokan shi. A lokacin Pretty na Sanya wani tablet cikin coke, ɗauko coke ɗin tayi tana fitowa daga kitchen ɗin zuwa bedroom, kiciɓus ɗin da suka yi da Hamma Zaki wanda ya fito duba ina zai ganta don bata cikin bedroom ɗin.
Da sauri Pretty ta ɓoye coke ɗin a bayan ta tana addu'ar Allah yasa yace ta bashi. A zahiri kuma ta marairaice fuska tace
“Sweetheart ka shigo kenan, na shiga kitchen ne na nemo abun da zan sha. Murmushin sa mai sanyaya zuciya ya saki tare da kamo hannun ta suka wuce bedroom ɗin. Kazar hannun shi ya ajiye tare da komawa kitchen ya ɗauko plate da cups sannan ya dawo, lokacin Pretty har ta cire kayan jikin ta ta shiga toilet ta watso ruwa. Murmushi kawai yayi cikin ranshi yana jaddada rashin kunya irin na Pretty.
“Nabees” ya ƙira sunan ta can ƙasan maƙoshi.
“bari na shirya Sweetheart”
Sai da ta sanya night wear ɗin tukun ta ƙaraso zuwa yadda yake. Gefen shi ta zauna tare da janyo kazar ta saka kan plate ɗin, ganin harda yoghurt yasa tayi saurin janyo coke ɗin ta. Saurin riƙe hannun ta Hamma Zaki yayi tuni taji wani irin yanayi na ziyartar ta. Cike da shagwaɓa tace
“Ni shi nake soooo”
Hamma Zaki yace “Sorrie Nabees, ki haɗa da yoghurt not coke please”
“Kenan asarar coke ɗin za'a yi” ta faɗa tana marairaice fuska.
Cike da ƙosawa da maganar yace “I'll use it”
Farin ciki ya mamaye Pretty don irin yadda ta ƙagu su keɓance sai taji daɗi sosai. Sai da suka ci kazar sannan ta ɗauki yoghurt ɗin ta sha, shi kuma yasha