Showing 33001 words to 36000 words out of 135404 words
ba*
*Allah yasa mu gane*]
*3:03pm*
Wasu kyawawan motoci kusan guda bakwai suka Kunno Kai cikin tamfatsetsen gidan nasu, dai-dai parking lot suka yi parking. Samari ne da suka kai su goma suka fito daga cikin motocin, cikin waɗannan samari kuwa har da masu jajayen kunnuwa.
Dr. Faruq shine jagoran su kuma shi yayi musu iso zuwa main parlour na gidan. A nutse suka kutsa kawunan su cikin parlourn da ya sha gyara ƙamshi kawai ke tashi. Bayan sun zauna da kanshi ya wuce ɓangaren masu aiki ya sanar da su su kawo refreshments Mai ɗan yawa daga haka ya wuce sama. Directly bedroom ɗin Hamma zaki ya nufa wanda yayi dai-dai da fitowar shi daga toilet, Sanye yake cikin bathrobe kamar ko yaushe yana drying sumar shi da ta jiƙe da wani pink towel yayin da jikin shi ke fitar da daddaɗan ƙamshi na shower gel ɗin sa.
Cike da mamaki yake kallon Dr. Faruq da ke sanye cikin Black expensive jeans da kuma suite ɗin shi white colour da necktie black, ya kuma ɗaura newly white labcoat da ta ƙara haskaka shi. Ba tare da yace mishi komai ba kai tsaye ya nufi gaban mirror ɗin shi.
“To Sarkin miskilanci a taimaka a shirya da wuri friends namu na can parlour suna jiran ka....saura ka ɓata lokaci kasan masu jajayen kunnuwan nan basu san african time ehe”
Ba tare da ya jira amsar shi ba ya wuce zuwa wurin friends ɗin su dake parlourn, hirar su suka ci gaba suna raha bayan ya sanar da su Alee ɗin na zuwa.
Sai da yayi drying sumar nan tas daga nan ya fara gyara ta haɗe da zuba mata mayuka iri iri. A nutse ya koma kan body creams da lotions dake jere gaban mirror ɗin, cikin ƙwarewa da gayancewa ya gama shafa mayukan tukun ya nufi closet nashi, bag ɗin da Dr. Faruq ya amso wurin major Kabir ya ɗauko. A daidai gaban mirror ɗin ya ajiye tare da zuge ta a hankali.
Kayan sojoji ne a ciki sabbi, tundaga boxer, singlet, riga, wando, wristwatch, handkerchief, da kuma cap. A hankali ya sanya kayan tas. Yana gama saka kayan Dr. Faruq yayi Knocking tare da shigowa, ganin ya shirya ma yasa ya juya coz dama ƙiran shi yazo yi coz lokaci ya kusa.
Turaruka ya fesa lastly ya fesa favourite nashi wato _Majesté impériale_ tuni daddaɗan ƙamshi ya buɗe ko ina. A hankali ya faro tako ƙafarsa da ke sanye cikin takalmin sojojin yayin da ainihin izza da kuma ƙasaita tashi irin ta zaratan maza da bayyana.
Tunda ya murɗa handle na ƙofar ya jawo ta suka jiyo ƙamshin sa. Tun kafin ya ƙaraso yadda suke suka fara sakar mishi murmushi, shima murmushin kawai yake aika musu har ya isa wurin da suke. A tsattsaye suka gaisa ga in lokaci ya kusa cikawa, hakan yasa duka suka ɗunguma zuwa wurin da za'a yi taron.
Makeken hall ne mai ɗan karen girma, aƙalla hall ɗin zai ɗauki mutane dubu biyu. Ta ko ina ya tsaru don ba ƙananan masu decoration ne suka ƙayata hall ɗin ba. Gwanin ban sha'awa multi colored lights ɗin ke ƙara haskaka ɗakin taron.
Maimakon hayaniya wurin tsit ko da yake abun na zarata ne wato sojoji, ɓangare ɗaya Governor ne da kanshi tare da wasu commissioners , manya manyan sojoji ne dake faɗin ƙasar, manya manyan masu kuɗi da sauran su. Ɓangare guda kuma mata ne waɗanda keda muƙami cikin gwamnati tare da sanannun mata waɗanda ke da burin Kawo sauyi. Akwai ɓangaren da kuma samari ne matasa sai kuma ɓangare ƴan mata wanda kowacce tayi wanka na kece raini.
Shigowar wanda aka shirya taron domin sa wato Captain Alee Muhammad Naira yasa aka ƙara nutsuwa kowa na bawa idon sa abinci. Cikin takunsa na zaratan maza yake tafiya har ya kai zuwa wurin da aka tanada domin sa.
Nan da nan MC ya fara magana tare da welcoming manyan mutane da suka halarci wurin. Bayan ya gama da su ya dawo kan mai gayya mai taro.
Cikin harshen turanci yace:
“Hausawa suka ce barewa ba zata yi gudu kuma ɗanta yayi rarrafe ba...dole dai shima gudun nan zai, kamar dai haka, ɗa ga General Muhammad Naira Shugaban sojojin wannan ƙasa ta Nigeria yake take sawun mahaifin sa, tabbas mahaifin sa mutum ne jarumi wanda kowa yasan shi tun kafin ya kai wannan mataki yake hidimtawa ƙasa da ƙarfin sa da kuma dukiyar sa....ga kuma ɗan sa nan Captain Alee Muhammad Naira Wanda ya gado halin mahaifin shi”
Nan fa aka sake tafi taf taf taf. MC yaci gaba
“Ba tare da ɓata lokaci ba zan miƙa abun magana ga mai gayya shugaban sojojin ƙasar wato General Muhammad Naira.”
Taf taf taf taf
Bayan General yayi jawabin sa ne aka bawa mai girma gwamna abun magana, a nan ya yabawa ƙoƙari da ƙwazo irin na wannan soja tare da jan hankalin sauran sojoji da suyi koyi da sadaukarwa irin ta wannan soja.
Duk wannan hidima da ake yi babu wanda zai ce yaga ko da murmushin Hamma Zaki ne bare kuma azo gandin sanin kalar haƙorin sa, fuskar nan tamau amma hakan bai hana sihirtaccen kyau da kwarjini irin nasa bayyana ba.
Nan MC yace za'a bada damar ci da sha daga nan kuma akwai speech da Hamma Zaki zai yi sai kyaututtuka na musamman da za'a bayarwa wanɗanda suka halarci dagar da aka yi cikin ƙauyen nan.
Bayan an kammala jawabai daga wurare daban-daban ne aka fara ciye-ciye da shaye-shaye.
Bayan an gama ci da kuma sha MC ya gabatar da abu na gaba a matsayin speech Wanda Captain Shareef Zai gabatar. Ran shi bai so ba haka ya miƙe daga wurin zaman shi nan fa ƴan mata aka ƙara ruɗewa musamman waɗanda Basu ga shigowar sa ba. Ƙarasawa yayi karɓi abun magana tare da riƙe shi.
Mintuna 5mins ya share ba tare da yace komai ba, fuskar nan kuwa a haɗe kamar me. Can ya buɗe baki a hankali ya fara magana.
“Good day to u all” nan fa hall ya ƙara ɗaukan shiru jin yadda amo da sautin Muryar shi ke karaɗe wurin. Minti 1min yayi yana magana daga nan ya miƙa abun taro. Kowa mamakin rashin magana irin na haɗaɗɗen guy ɗin yake musamman irin yadda mutane ke matuƙar ƙaunar sa.
Bayan ya gana nan aka fara basu kyaututtukan su, su Dr. Faruq duk sun karɓi nasu kyaututtukan da ban girma har aka zo kanshi. Ko da zai karɓa masu hotuna ƙyas ƙyas ƙyas ɗin camera kawai ke tashi.
Alhamdulillah! Cikin ikon Allah aka yi taro lafiya har aka kammala, daga nan baƙin Hamma Zaki suka lallame shi akan ya tsaya suyi pictures. Babu yadda ya iya aka fara yi musu pictures. Daga family ma suka fito aka fara.
Hamma Zaki an sha hoto don kuwa sai da suka yi da kowa, kada kuso kuga yadda suka yi mugun match da Sarah wacce ta sanya army green sari, suna cikin snapping pictures ɗin wata farar matashiyar budurwa ta tunkaro su.
Fara ce, kyakkyawa babu laifi, ta saka fitted English gown Wanda suka bayyana ainihin suffar jikin ta, bata cika tsayi sosai ba kuma bata da jiki, haka take zuit kamar alifun, fuskar nan kuwa shaɓe-shaɓe da make up Kamar aljanar roba. Ga wani high hill shoe da ta saka, attachment ɗin da tayi kitso da shi bai samu arziƙin rufuwa ba.
Tafiya take tana kwalmaɗewa kamar macijiya har ta iso wurin nasu, lokacin Sarah na gefen Hamma Zaki ta hagu sai Fauzah ta ɓangaren dama. Tana isowa ta ƙaraso tare da miƙa hannun ta tana riƙo hannun Hamma Zaki.
Babu zato babu tsammani yaji an riƙo hannun sa, hakan yasa ya ɗago yana duba waye ne don shi tunanin sa ma Dr. Faruq ne. Ido cikin ido ta wani ɗaga mishi gira saying “Hi handsome” tare da kissing hannun nashi.
Fuzge hannun sa yayi tare da watsa mata wani dirty look haɗi da tsirta yawu yana yamutsa fuska, a lokacin ne Sarah ta lura da yarinyar ai kuwa ta kifa mata mari ji kake tasss. Hamma Zaki kuwa daga wurin ya wuce zuwa motar da yazo cikin ta. Babu ɓata lokaci ya fuzgi motar sai waje.
Ɗagowa tayi da niyyar ganin habibyn nata ne ya mareta ai kuwa taci karo da Sarah da ke watsa mata wani banzan kallo. Ba shiri budurwar tayo kanta wanda yayi dai-dai da zuwan Captain Sulaiman, yana ɗaya daga cikin abokan Hamma Zaki da suka yi aiki da shi Lokacin yana Jigawa State. Captain Sulaiman kuwa tunda yaga Sarah ya faɗa mata.
“Keee! How dare You zaki ɗauki wani koɗaɗen hannun ki ki mare ni? Wallahi yau sai naga wanda ya tsaya miki a ƙasar nan har kika samu damar mari na”
Captain Sulaiman yaja hannun Sarah da ta juya a fusace tana faɗin
“Ubanki ne ya tsaya min nace” ta faɗa cikin Hausar ta da kana ji kasan ba Yarenta bane.
Budurwar ta hasala tare da bin bayan su, jawo gashin Sarah tayi nan Sarah ta saki wata irin ƙara. Cike da ɓacin rai Captain Sulaiman ya juya ya ƙara wanke budurwar da mari. Duk da uniform ɗin dake jikin shi hakan bai sa tayi shiru ba sai ma hawayen da ta goge
“Wallahi duk ku biyun sai naga uban da ya tsaya muku cikin ƙasar nan, har Ni wasu zasu saka hannu su mara?, Wallahi sai kun san kun taɓa shalelen Dad.” Ta faɗa tare da ɗauko wayar ta ƙirar iPhone 14 promax, snapping ɗin su tayi sannan ta ja gefe tana haki.
Ƙawayen ta ne suka kewaye ta tare da ɗago ta
“Pretty ya haka?, Kin dace kuwa”
Ɗagowa tayi tana kallon su, ganin shatin yatsu a fuskar ta yada duk suka zaro ido
“Kutmelesi....this guy do u shege abi?, Dama irin kyawawan samarin nan basu san ƙimar mutum ba”
Ɗaga musu hannu tayi alamar ya isa
“Ba Sweetheart bane ya mare ni, wata baindiya ce da ban san uban me ya kawo ta ba ta mare ni, ban Kai ga hukunta taba wani soja yaja hannun ta....bayan na bisu na ja gashin ta kawai shima ya mare ni”
Tayi shiru tana haki
“Wallahi duk sai sun san wa suka mara, ko Dad bai taɓa ɗaukar hannu ya taɓa Ni ba, talk less of Mommy ammah yau wasu shegu sun saka hannayen su a fuska ta, wallahi sai na koya wa rayuwar su darasi”
Ɗaya daga cikin ƴan matan da suka shigar tasu duk irin tata ce tace “Gaskiya ya kamata ki ɗauki matakin da ya dace....ke da kike taka uban kowa ya za'a yi yau wasu banzayen su taɓa ki, wallahi ina bayani ptty ki hukunta su yadda ta dace”
“Ke dai Ishy ki bari, wai yau wasu shegu sun mari pretty da alama dai basu san wacece ba” daya budurwar ta faɗa.
Ishy ta karɓe zancen da faɗin
“Lallai kam ai ko mu bazamu bari ba Wallahi, sai da nace mata mu bi bayan ta kada matsala ta faru tace a'a”
Murmushin mugunta Pretty tayi tare da faɗin “Ki rabu da ni wallahi duk sai sun yabawa aya zaƙin ta, ku tashi mu wuce wurin da muka sauƙa, bazan bar Adamawa ba har sai na sace zuciyar mutumin nan”
Daga haka su Pretty suka shiga motar da suka zo da ita tare da figar ta zuwa hotel ɗin da suka sauƙa.
TOH FAH, WAI JAMA'AH INA ƳAR IYA NE?
HAMMA ZAKI AN NUNA HALI
KO WANNAN PRETTY A TUNANIN KU ZATA YI NASARAR SACE QALB ƊIN HAMMA ZAKI KUWA?
WACECE MA TUKUNNA PRETTY?
DUK AMSOSHIN NA A TARE DA DIAMOND LADY, KU CI FABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY.
ZAMU HAƊU GOBE IN SHA ALLAH
COMMENT & SHARE PLEASE!
[5/18, 10:45 AM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘35&36’’’’’
Ɓangaren Hamma Zaki a hasale yaja motar tare da barin wurin. Yana cikin tafiya babu abunda yake sai huci farar fuskar nan tashi ta koma ja, haka fararen idanuwan shi duk sun sauya kala tsabar ɓacin rai.
“Why all this!”
Ya faɗa tare da buga steering wheel na motar. Da taimakon Allah da kuma dai Addu'a ya samu isa gida lafiya, yana shiga yayi wanka ko zai rage jin ɓacin ran da yake ji.
Yana fitowa bai shafa komai ba ya zura jallabiya tare da ficewa garden. Mom kuwa tun fitar da yayi suma suka biyo bayan sa da yake lokacin da yana ƙarami in an ɓata masa rai toh duk abun da ya gani a kusan shi sai ya hallaka shi.
Ganin motar tasa lafiya lafiya yasa Mom shigewa ciki tare da shiga bedroom nashi sai dai bata ga ko alamarsa ba, ta duba Toilet nan ma dai shiru, hakan yasa ta fita hankali tashe tare da sanar da sauran ahalin gidan da suka yi tsaye babu mai cewa uffan.
★★★★★★★
*ƳAR IYA POV*
Tunda ta fito bata kula kowa ba har ta iso gidan Iya, shigewa tayi abunta tare da janyo daron da ta zuba kashin shanun haka nan na awakin da tumakin ma. Ganin ciyawarta ma ta bushe yasa ta haɗa su cikin babban daro tare da ficewa daga gidan.
Kai tsaye gidan Arɗo ta wuce, daga baƙin ƙofa Babu wanda ya kulata haka itama bata kula kowa ba. Tana shiga ta wuce ɓangaren Saratu amaryar Arɗo tare da janyo turmi. Saratu da ke ɓangaren madafan ta jiyo alamun ana taɓa turmi. Daga wurin da take ta ƙwala ihu “Waye a nan?”
Ƴar Iya ta amsa da “Ubanki ne!, Daka zanyi”. Saratu na jin Muryar Ƴar Iya ta lallaɓa ta wuce can ɓangaren Innani ba tare da ta kuma cewa komai ba.
Tass ta daga ciyawar nan har ta zama gari, daga nan ta juye ta zuba kashin shanun.....shima dai kamar ciyawa sai da ya koma gari, haka ta zuba kashin awakin nan da nan shima ya zama gari.
Kai ta ɗan jijjiga alamar ne zata yi next, can kuwa tayi murmushi na samo solution. Haɗe abubuwan da ta daka tayi cikin turmin tare da gauraya. Cikin ikon Allah ta kammala nan kuwa dakan nan ya bada colour mai kyau kamar dai ba kashi ne da ciyawa ba.
Kaɗan ta lakuto a hannun ta tare kaiwa hanci tana shinshina kamar mayya. Zaro ido tayi Jin warin still na nan.
“Kutumelesin uban can” ta faɗa tare da ƙara dandalowa tana ƙara kai hanci
“Aradu warin sa har yanzu na nan, to uban me zan saka ya daina warin”
Lokaci ɗaya ta saki murmushi....
Juye abunda ta daka tayi tare da ficewa daga gidan Arɗo don neman abun da zai kashe warin. Gonar Baba Haro ta wuce tare da. Tsinto ganyen mangwaro, ganyen kashu busassu ta koma gidan Arɗo.
Suma sai da ta daka su sannan ta haɗe su baki ɗaya. Kamar yadda tayi ɗazu Yanzu ma Sai da ta shinshina haɗin nata, jin warin ya ragu sosai yanzu sai ma ƙamshi ƙamshin ganye yake yasa tayi dariya.
Har ta saka hannu Zata kwashe tace “A'ah, akwai ciyawar lemon tsami a bayan ɗakin Arɗo bari na ƙara sai ƙamshin yayi yawa”
Tsam taje tare da ciro ɗanyar lemon grass da ƙamshin ta ke fita lokaci guda.
Da yake a jiƙe take tuni ta fara haɗe garin maganin waje ɗaya, sai da ta tabbatar ya daku da kyau ta janyo ludayi tare da ɓanɓaro haɗin kayan sana'ar ta. Ba tare da tayiwa kowa magana ba ta wuce tana ƴar waƙarta har gidan Iya.
A kan rumfar yayi da kara da aka yi don rufe madafa ta ajiye. Tana ajiyewa ta juyo, bata kai ga fara tafiya ba ta kama baki tare da faɗin:
“Na fan gulmar Iya, tana gani sai ta tambaya, mtss” ta ƙarasa da sakin wani dogon tsaki tare da janyo daron ta ta wuce da shi bukkar ta.
Wani baccin wahala ne yayi gaba da Ƴar Iya ko dan guje-gujen da tayi a lambun Baba Haro, ga yawon neman kayan haɗin ta.
Ba ita ta tashi ba sai da yamma, miƙa tayi tana hamma, ba tare da ta rufe baki ba ta miƙe ta zagaya baya don kama ruwa. Ko tsarki bata samu damar yi ba ta fice da guduuuuuu.
Kasuwa ta shiga yayin da wasu ke miƙa gaisuwar su saboda tsoron kada ta ci zalin kayayyakin su. Ganin mutumin Salisu mai burodi tuni ta saki murmushi. Har da wani sunkunyar da kai kafin ta shige rumfar.
“Ah Salisu kana nan abun ka!”
Murmushin da bai kai zuciya ba yayi yace
“Eh wallahi, aka ce mana kin je birni ke kam, yaushe kika dawo rai”
Ƴar Iya tace
“Ai nayi kwana biyu da dawowa nan ɗin ne ban fiye shigowa ba”
“Ayya sannu da dawowa” ya faɗa tare da miƙa mata burodi biyu cikin leda. Murmushi tayi ta ce
“Nagode Salisu, kamar ka san yunwa ce ta kawo ni”
Mamaki duk ya cika Salisu jin mutuniyar tashi da godiya, abun da tunda suke bai taɓa jin tayi ba. Maganar ta ne ta dawo dashi hankalin sa
“To Salisu na tafi, sai na kewayo”
Ta faɗa tana wucewa
“To toh toh” shima ya faɗa a ɗan firgice.
Tana barin wurin Salisu ta ƙara kutsa kai cikin kasuwar. Can da ta gaji da kewaya wa ta fito tare da komawa gida. Gwaten shinkafa da wake Iya tayi musu, daron da ake saka mata ta janyo ba tare da wanke hannu ba ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya kamar wacce bata taɓa ci ba, few minutes ta haɗa cinyewa tare da janyo burodin ta, tas ta cinye tana yin gatsa .
Shaf ta manta fa ashe bata da abun ƙulla kayan neman halal ɗin ta. Ai kuwa a zabure ta miƙe ta fice a guje, tana isa kasuwa ta shiga shagon Baban Balki. Ganin yana salla kuma ga ledodi nan a baje fara da baƙa kan teburin shagon ai kuwa ta wawusa tare da cikawa bujen