Showing 6001 words to 9000 words out of 135404 words
*(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘7&8’’’’’
Shiru ne ya wanzu yayin da kowa kallon sa ya koma kan Ƴar Iya da ta tsaya a gaban su ƙyam ko tsoro babu a tattare da ita, nan da nan wasu suka sha jinin jikin su yayin da wasu kuma suke miƙewa tare da yunƙurin kamo ta....
Kan uba, yadda zaratan matasa da magidanta ke yunƙurin kawo ma ƙaramar yarinya hari ammah ko gizau bata yi ba yasa masu hankali daga cikin su faɗawa duniyar mamaki.. Sai da taga rabin su sun yo kanta ta zaro silifas ɗin ta guda biyu ta fara buga musu ɗaya bayan ɗaya.
Duk wanda aka bugawa sai kaga ya ja baya ya koma gefe yana shafa kansa, ganin suna watsewa yasa ta gyara tsayuwar ta tana kallon yadda jini ke ɓulɓulowa daga kawunan su wanda hakan ba ƙaramin burge ta yayi ba.
“Hhhhhhh....dama na faɗa muku ai, shegu manyan banja kawai ku a dole jaku ci jalin yalinya kalama ko?, Toh in kun faca” ta ƙarasa tana sakin dariyar mugunta.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka fara zamewa ɗaya bayan ɗaya suna wucewa gida saboda jinin da yake zubowa.
Shi kanshi Arɗo ya tsorata da lamarin wannan yarinya, an daɗe ana kawo ƙarar ta yakan ce suyi haƙuri yarinya ce ammah yau ta riga ta goge masa hadda. Idanuwan Ƴar Iya dake yawo kan Arɗo da Baffi da su kaɗai suka rage don tuni dogarai ma suka cika bujen su da iska.
“Baffi ka tashi mu tafi Iya na can tana jiran ka, kai ma Alɗo kana biye wa makalyatan mutanen nan sai na maka naka” ta faɗa tana kallon Baffi.
Da ido Arɗo yayi wa Baffi izinin tafiya don ya sare da al'amarin wannan aljanar yarinya. Bayan sun yi ƴar tafiya Baffi ya ɗan dakata yana Kallo Jikar tashi. Ganin ya tsaya yasa ta juyo tana kallon shi.
“Baffi mu tafi manah”
“A'ah Ƴar Iyan ta sai kin faɗa min me kika yiwa Shayibu kuma da me kika jiwa mutane ciwo”
Dariyar da ta ɗaurewa Baffi kai Ƴar Iya tayi sannan ta maida kallon ta kanshi. Nan ta bashi labarin abun da ya haɗa ta da Ishiyaku, nan Baffi yayi mata faɗa sanann yace.
“Toh da me kika ji musu ciwo kuma”
A hankali ta ciro silifas ɗin ta daga ƙafar ta ta nuna mishi ƙasan su. Wasu Allurai ne a cake sun fi hamsin a cikin kowanne. Abun ya ɗaurewa Baffi kai ganin irin waɗannan allurai a ƙasan takalmin kuma abun mamaki takalmin na ƙafarta ammah ita basu cake ta ba in fact ko leƙowa basu yi ba.
A haka suka wuce gida zuciyar Baffi babu daɗi ga kuma abun da ya ajiye a ranshi na gano dalilin wanann ɗabi'u na Jikar tashi.
Bayan sun je gida bai faɗawa Iya komai ba ammah ya ƙuduri aniyar bincike akan jikar ta sa, haka ranar dai sukuku Baffi yayi ta har dare. Nan tunani ya hana shi sukuni ƙarshe ya fice daga bukkar. Wuri ya samu yana tunanin mafita ga Ƴar Iya daga ƙarshe ya yanke shawar fara ɗaura mata karatun Alqur'ani tunda shi Qur'ani haske ne kuma waraka ga kowacce jinya.
Washegari kuwa Baffi yayi ɗamarar koyar da Ƴar Iya. Bayan gari ya waye ya ƙwalla kiran ta daga bukkar shi jin shiru yasa ya ƙwalla kiran Iya. A nan take sanar da shi Ƴar Iya ta fice sassafe.
Cike da takaici ya koma ya kwanta, sai wajajen Azahar Ƴar Iya ta dawo saboda yunwar da ta koro ta, abincin da yarinyar ke ci kuwa ko samari masu aikin noma biyu iyaka.
Bayan taci abinci Baffi ya tsayar ta ya fara mata karatu sai dai abun haushi ko bismillah ta kasa haddacewa.
Haka Baffi yayi ta ɗawainiya da ita don ganin ta koyi karatu ammah ina ƙwaƙwalwar bata ja, babu abun da ta iya sai neman tsokala.
Kullum cikin addabar mutane take, yau itace wannnan gobe wannan, yau ta illata wannan gobe ta illata wannan gashi babu damar hukunta ta don kuwa duk ƙauyen Gallara da kewaye babu wanda baya shayin Ƴar Iya. Hakan ne ya bata damar tsula tsiyar ta son ranta ita da shaƙiƙiyar ta A'i wacce gidan su ke ɗan gaba da gidan su Ƴar Iya.
A'i ma dai ba baya ba wajen rashin ji shiyasa Ƴar Iya ta zaɓe ta don ta kasance ƙawa gare ta, tare suke fita ko ina da A'i, idan tsokala ne tare idan damfara da ƙwace ne ma dai tare suke yi. Iyayen A'i kan su shakkar waɗannan ƴan barandar ƴaƴan nasu suke yi kullum fatan su bai wuce Allah ya shirye su ba.
Tunda ya fahimci akwai ɓoyayyen al'amari dangane da Ƴar Iya ya ɗan samu sauƙi, addu'ar sa kullum Allah ya shirye ta.
Ana cikin haka lokacin Ƴar Iya ta ƙara girma, shekarun ta sun kai Tara lokacin. Wata rana wani mai magani ya zo ƙauyen Gallara, bayan ya samu karɓuwa wurin Arɗo aka bashi wurin zama nan ya kafa amsa ƙuwwar sa (Loudspeaker) ya fara talla r maganin sa.
Inna Zaliha ne ta jiyo bayanin da Mai maganin yake yi ai kuwa ta saka Malam Umaru gaba kan ya kai Ƴar Iya tunda su ma bata ƙyale ba in ƴan ɓarnar ta suka motsa takan je ta yanka masa kaji ko agwagi ko kuma zabin da yake kiwo, wasu lokutan har akuya takan ja ta gudu da ita zuwa mahauta.....😀 Babu yadda suka iya dole su yanka ta kai Iyar ta ta soya ko ta musu farfesu wanda kaso tamanin na naman Ƴar Iya ke cinyewa.
Shawarar Inna Zaliha ya ɗauka ai kuwa Yaje har gidan Iya ya kamo hannun Ƴar Iya tare da mata wayon zata raka shi birni ne.
Bayan sun isa mai magani ya fara ƴan dube-duben shi irin na ƴan tsibbu, can ya fuskanci Malam Umaru yana faɗin
“Lallai wannan yarinyar taka ba mutum nace, hannun ta bana mutane bane kuma bazata taɓa bari a zauna lafiya a wuri ba matsawar tana nan.”
Bayan Mallam Umaru ya buƙaci maslaha ga batun Ƴar Iya mai maganin yace.
“Maslaha ɗaya ita ce ku ɗauke ta ku mayar da ita wurin Ƴan uwanta aljanu ko kuma ku kawo ta gobe a yanke hannun ta”
Ba tare da yayi shawara da Iya ba washegari ya ɗauko ƴar Iya da niyyar a maida ta can wurin ƴan uwan ta sheɗanu idan hakan bai yi aiki ba sai ya kawo ta a cire hannun kowa ya huta.
(Nace ku jiye mun mutumin nan wai kowa ya huta, sai kace ya damu da rayuwar yarinyar ko yana hidimta mata).
Bayan sun je Mai magani yayi surkullen shi sannan ya ɗauko wani makeken ganye wanda ya kai girman bargo duniyar kule guda biyu, wata garin magani ya watsawa Ƴar Iya ai kuwa lokaci ɗaya ta faɗi yashe kamar gawa.
Duk wannan Shagalin da ake yi Iya da Baffi basu da masaniya haka mutanen gari basu sani ba ai da tuni sun fara haɗa ƴar ƙwar-ƙwaryan shagali na rabuwa da annoba.
Bayan wani lokacin Mai maganin ya ɗauko wannan ganye ya ware shi sannan ya ɗaga Ƴar Iya ya jefa ciki ya naɗe abun kamar ƙuƙulen cabbage. Bayan ya gama wannan aiki ya ɗauko wani ruwa ya watsa mata daga nan ya umarci Malam Umaru da ya wuce da ita kai tsaye bakin kogi.
Bai Musa ba kuwa ya ɗauki wannan ƙulƙule raf ya tafi da shi kogin da yake kusa da su kaɗan wanda yake cikin garin Zubo. A bakin ruwan ya ajiye ƙulƙulen abun ya juyo gida hankalin sa kwance don ya gamawa gimbiyar sa aikin ta.
(Nace zaka sani idan aikin bai daidaitu ba ta dawo gida don nasan ba zata ƙyale ka ba).
Bayan ya koma ya sanar da Inna Zaliha duk abinda ya faru da kuma maida Ƴar Iya ga ƴan uwanta shaiɗanu da yayi. Tuni farin ciki ya kewaye birnin zuciyar ta. Bayan ya fita bata tsaya wata-wata ba ta nemo Larai saboda ta sanar da ita abun da ke faruwa. Nan suka fara murna saboda su kaɗai suka san dalilin da yasa suke son ɗauke Ƴar Iya a kusa da su bayan jawabin da bokan su yayi musu.
Can cikin gari kuwa shiru basu ga giftawar halittar da suke wa take da annobar su ba kusan ko ina ka wuce in dai daba ce walau ta maza ko mata zaka ji suna jajen Ƴar Iya yau basu ga wulgawar ta ba.
Akace ko yaya wata alaƙa ta gifta tsakanin wasu zukata walau so ko ƙi toh duk ranar da wani sashi ya samu matsala ɗayan sashin dole ya ji abun a zuciyar shi.. Irin haka ce ta faru da mutanen garin Gallara, ta ko ina ka wulga zancen kawai ake yi, wasu har sun yanke shawarar zuwa dubo Ƴar Iya ko lafiya.
Ɓangaren Iya ma da tun ficewar Ƴar shalelen ta bata ƙara ganin ta shigo gidan ba bayan kuma ta saba da in sun kewaya sun kewaya toh sai sun leƙo gidan Iya ko don cin abinci ma ammah yau shiru har Yamma tayi. Wannan dalilin ne yasa Iya zaro zanin yafawar ta ta fito cikin gari don neman shalelen ta.
Yawo sosai tayi amma bata ga ko alamar ta ba, gidan su A'i ma da taje A'i cewa tayi yau Ƴar Iya bata zo ba da yake dama mafi yawancin lokaci ita ke bi takan A'i sai su wuce gantalin su.
Nan da nan hankalin Iya ya tashi ta fara bin kowacce daba tana tambaya sai dai amsa ɗaya suke bata “Muma yau jajen ta muke bata leƙo mana ba”.
Tun Iya na ɗaurewa har ta fara sheƙa kuka abun tausayi, Baffi da ƙyar ya shawo kanta ta haƙura yana ce mata
“Ai zata dawo in dai shalelen ki ce, kin santa da rigima da shegen yawo wataƙila tana nan ƙauyukan maƙwabta kuma zata dawo ai ko dan saboda ke”
Da haka dai Iya tayi shiru ba don ta yadda da jawabin Baffi ba.
★★★★★★★★★★★
Ɓangaren Ƴar Iya tunda Mai magani ya fara karanta wannan dalasimai shikenan taji an ɗauke ta gaba ɗaya, bayan Baffi ya kai ta bakin ruwa ya koma abun sa can bayan sallar Ishã wata tsohuwa ta biyo ta wajen don ta ciri alayyahu a lambun dake kusa da ruwan. Tunda ta hango abun ai kuwa ta isa don ganin menene wannan a bakin ruwa.
Sai da ta duba sosai ta gano ganyen da ake naɗe ƴaƴan shaiɗanu ne idan za'a mayar da su. Toh idan hakaneh me yasa har yanzu basu ɗauke ta ba?, Lallai wannan mutum ce, saboda haka ta je ta buɗe ta bata tsaya ko ina da ita ba sai gidan ta.
A nan ta jiƙa jiƙe-jiƙen ta ta ɗurawa Ƴar Iya ba jimawa kuwa ta dawo hayyacin ta. Duk yadda tsohuwa taso Ƴar Iya ta zauna taƙi a daren kuwa ta koma sai gidan Iya, bata kula kowa ba ta wuce bukkar ta washegari kuwa ta shiga gari don ci gaba da halin.
Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan Mallam Umaru ya ganta cikin gari, bai yi ƙasa a guiwa ba ya sanar da Inna Zaliha nan tasa shi gaba wai ya faɗawa mai maganin.
Bayan ya faɗa masa yace gobe ga zo da ita a yanke hannun sai kowa ya huta. Washegari kuwa hakan ta faru da ƙyar Ƴar Iya ta bi shi ba tare da ta masa jayayya ba hakan kuma yana alaƙa ne da surkullen da mai maganin yayi mata daga nan inda yake.
Tunda suka nufi hanyar ƴar Iya ke turjewa alamun bata so ammah saboda Inna Zaliha ce ta bashi aikin ai dole ya kai ta. Bayan sun isa mai magani ya fara haɗa kayan aiki.
Wata sharɓeɓiyar wuƙa da yayi wa laƙabi da wuƙar shaiɗanu na gefen sa. Zaunar da Ƴar Iya aka yi a tsakiyar wata shimfiɗa daga nan ya fara karanta wasu dalasimai wanda nake kyautata zaton na tsafi ne. Cike da rashin imani Mai magani ya dubi wuƙar sannan ya karanta wani abu, da kanta wuƙar ta taso ta taho sai hannun sa.
Bayan wuƙar ta dawo hannun Mai magani ya karkato ta yana mai riƙe hannun Ƴar Iya na dama. Ya ɗaga kenan zai buga mata.......
TOH FAH, ANA WATA GA WATA!
ƳAR IYA FANS KUNJI ME BABAN ƳAR IYA YA AIKATA MATA?
GASHI KUMA ZA'A YANKE HANNUN ƁARNA! KO HAKAN ZAI FARU?
ITA KUMA INNA ZALIHA KO MEYEH ƘUDIRIN TA?
*Just follow Diamond Lady's pen and find out*
COMMENT &SHARE FISABILILLAH.
MU HAƊU GOBE DA SAFE, AMMA SAI NAGA YAWAN COMMENTS, INA NUFIN SHARHI FAH! IN BA HAKA BA KUWA SAI JIBI TUNDA YAU UPDATE UKU NAYI MUKU.
NA GODE FANS NA INA MATUKAR SON KU DA YAWA ƊIN NAN!!!
[4/27, 6:03 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘9&10’’’’’
Bayan wuƙar ta dawo hannun Mai magani ya karkato ta yana mai riƙe hannun Ƴar Iya na dama. Ya ɗaga kenan zai sara mata wani mahaukacin ƙarfi ya zo wa Ƴar Iya, a lokacin kuwa tayi wa wannan wuƙar wata irin wawura, cikin ƙanƙanin lokaci tayi nasarar amshe wuƙar daga hannun shi.
Kamar mayunwacin zaki haka Ƴar Iya tayi kan Mai Maganin, duk iya ƙoƙarin shi na ƙwacewa abun yaci tura, ƙarshe cike da rashin tsoro Ƴar Iya ta datse hannun Mai Maganin, bata bar shi haka ba ta fara shata masa fuskar shi da wuƙar...wasu dogayen Bille marasa kan gado ta shata daga nan ta juyo tuni Mallam Umaru ya sa ta tunda yaga ta amshe wuƙar.
Wannan zance kuwa tuni ya bazu cikin Gallara da kewaye, Ƴar Iya ta yanke wa wannan Mai Maganin hannu har da guzurin bille ai kuwa girma da tsoron Ƴar Iya ya hauhawa a idon mutane, kowa kaffa-kaffa yake da ita.
Tun daga ranar Ƴar Iya ta samu salama daga wurin Mallam Umaru, shegantaka irin tata kuwa sai abun da ya ƙaru, idan nama take son ci sai ta wuce can gidan tsohon ta ta yanko zabi biyu ko uku......
*_CI GABAN LABARI_* *(BACK TO STORY)*
Ƴar Iya ne da A'i ke tafiya cikin gari suna ƴan waƙe-waƙen su na yara. Suna cikin tafiya suka hango wani mai rake.
“Mai rakeeee”
Ƴar Iya ta ƙwala mishi ƙira, jin Muryar ta yasa ya fara tura kurar taken sa da sauri saboda ya tsere mata. Ba tare da sun ƙara mishi magana ba suka ɗora bayan shi da gudu. Bayan sun isa Ƴar Iya ta tare gaban kurar tana bin shi da mugun kallon, shi kuwa mai take ya sunkuyar da kan shi ƙasa zuciyar sa na bugawa.
“Kai uban wa ka fi da Ƴar Iya ke ƙwala maka ƙira shine zaka gudu”
A'i ta faɗa tana bangaje shi.
Idanuwan mai rake tuni suka raina fata saboda irin kallon da Ƴar Iya ke aika mishi, tsoron sa ma bai san wacce irin mugunta zata ƙunduma mishi ba.
“Hhhhhh...” dariya ta kwashe da ita sannan ta maida kallon ta ga mai rake da ya gagara ko da bada haƙuri ne.
“Baka ji me ƙawa ta tace bane?” ta aika mishi da tambaya.
Cikin ƙiƙina mai raken yace:
“Ranki....shi... daɗe kiyi.....haƙuri....ban..ban san ke bace ai da...zan..tsaya”
Dariya suka kwashe da ita a tare ita da A'i lokaci ɗaya kuma ta ɓata ran ta.
“Ƴar Iya bata yafiya kuma bata haƙuri, saboda haka yanzu ba anjima ba sai ka shanye raken nan tasss”
Ƙwalalo idanuwan shi yayi yana tunanin ta ina zai iya shanye kura guda na rake ai kuwa taji muryar A'i na faɗin:
“Wallahi yanzu zaka shanye Bismillah, shege marowaci tunda rowa ne yanzu shanye abunka”
Babu yadda mai raken ya iya haka ya fara gaftarar raken yana sha har cikin sa ya cika ya ɗan dakata.
Ganin ya tsaya yasa Ƴar Iya daka mishi tsawa
“Aradu yau sai ka shanye wannan raken tunda ka min rowa a kan shi”
Babu yadda ya iya tun yana sha a matsayin ƙari har ya fara kuka yana roƙon su da suyi haƙuri bazai ƙara ba ammah inaaaah sai da suka tabbatar ya jigata kuma sun san raken yayi mishi yawa tukunna suka sallame shi.
Basu tsaya ko ina ba suka yi cikin kasuwa. Ba tare da sun kula kowa ba suke tafiyar su suna haɗawa da ƴar waƙar su. Ganin yunwa ta fara addabar su yasa Ƴar Iya yanke hukuncin nema musu abun da zasu rage zafi da shi.
★★★★★★★★★★★★
Convoy na motocin sojojin da zasu kai goma ne suka shararo titin yayin da wata expensive white mota ƙirar Zenvo ST1 ta kasance tsakiyar su.
Dai-dai Murtala Mohammed International Airport dake Lagos State suka ja can gefe suka yi parking. Ganin har lokacin Flight ɗin da Shugaban nasu ya biyo bai yi landing ba yasa wasu daga cikin sojojin fitowa daga cikin nasu motocin.
At exactly 11:00am flight ɗin yayi landing . Few minutes bayan sauƙar jirgin sojojin nan suka dawo kusa-kusa so that their master will recognize their presence.
Ƙafarsa da ke sanye da Black luxury covershoe ya fara zirowa bisa steps ɗin. A hankali yake takowa yayin da idanuwan mutane duk ya koma kan shi.
(Nimah Bhatool nace bari na ɗaukowa fans ɗina report).
Sanye yake cikin wasu expensive brand na Armani. White T-SHIRT ce wacce tsabar farin ta har wani ɗaukar ido take yi, sai Black three-quarter jeans da ya bayyana