Showing 75001 words to 78000 words out of 135404 words
sai ka je wajen boka, sai su fake da ai wane malami ne, duk wani malami da zai yi duba, bugun ƙasa shima boka ne, saboda haramun ne hakan, akwai hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama, inda yake cewa “Duk wanda yaje wurin boka ko ɗan duba, to haƙiƙa ya kafurcewa abinda muka sauƙarwa Manzon Allah”. Mata muji tsoron Allah, duk wata buƙata ko buri da kike son cimmawa to ki roƙi Ubangiji, babu abinda yafi ƙarfinsa in kika ga ya Hana ki ko bai biya miki ba to ki saka a ranki ba alkhairi bane abun kamar yadda yazo cikin suratul baƙara, Allah maɗaukakin sarki yace “Zaka ga kana ƙin abu yayinda abun ya kasance alkhairi a gare ka, zaka ga kana ƙaunar abu yayinda abun ya kasance sharri gareka, Allah shine mafi sanin abinda ku baku sani ba”. Don Allah ƴan uwa na mu guji zuwa wurin irin malaman nan ko ince yan duba, in Zaki yi addu'a kiyi da kanki ba sai wani yayi miki ba, babu wani hijabi ko shamaki tsakanin ki da mahaliccinki, so ki roƙe shi duk abinda kike so kina mai ƙaskantar da kai, sai kiga addu'ar ki ta karɓu wurinsa, idan shawara ne ma kiyi istikhara zaki ga kin dace_
_Mu haɗu gobe don jin yadda zata kaya_
_Taku Diamond Bhatool ta gargajiya, ina ƙaunarku fans ɗina_
[8/26, 8:15 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎: Follow the DIAMOND BHATOOL'S LIBRARY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VamEf2Y4dTnFmjl4Dv1Z
https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““77&78 ”””
Idanuwa ta ƙwalalo kamar zata yi kuka yayinda su Fauzah ke kwasar dariyarsu.
“Haba ƙawa ta duk kin sauya kamar ɗiyar Indiyawa taya zan gane ki?, Matso kusa da ni don Allah, yaushe gamo?”
Kusa da juna suka zauna nan Khairy tace “Fauzah, Ayrah, Yesmeen, ku haɗu da ƙawata ta yarinta abokiyar ƙiriniyata kuma mai suna na A'i” ta faɗa tana nuna A'i da yatsa fuskarta ɗauke da murmushi. Ta juya kuma ta kama kafaɗar A'i “Ƙawata A'i ki haɗu da ƴan uwana kuma ƙawayena wannan Fauzah,wannan Ayrah wannan kuma Yesmeen”.
Nan kowa yaji daɗin haɗuwa da ƴan uwansa don Ai ma ba baya ba wurin sabo, tsiyarsu ta da dai ta bari amma akwai barkwanci ta shega. Nan suka fara hirar yaushe gamo.
Ƙiran sallar Ishã yasa Ai faɗin “Gashi ban girka komai ba saboda nauyin jiki, bari ya shigo sai ya nemo muku shayi da bredi don ba iya cin girkinmu zaku yi ba”
Harararta Khairy tayi tace “Ba sai kin faɗa mana kina da ciki ba ai mun gani, kin faɗa kin maimaita”
“To ke ina ruwanki don ke baki da shi kuwa baki isa hana Ni faɗa ba" nan dai suka yi ta jan magana Khairy team ɗin ta ita kaɗai su suma duk suna bayan A'i.
Shigowar Iliya mijin A'i ta sanar da shi game da baƙinta, ai bai manta lokacin bikinsu ba tuni ya fita ya nemo musu bread bisa umarnin uwar gida. Tare da ita suka tasa tsire da bread ɗin a gaba suna ci suna hira har suka kammala.
Bayan sun kammala ne Fauzah tace “Ƙawarmu ki taya ƴar uwarmu murna, ta samu lafiya” nan suka kwashe komai suka faɗa mata dom a cewarsu ciwon su ne duka, A'i tayi kuka kam sai tsinewa Inna Zaliha take, daga baya kuma ta dawo lafta mata godiya da albarka tunda yanzu tayi sanadin wayewar ƙawar mu ga kuma wani mahaukacin kyau da kika yi”.
Sai da suka yi sallah tukun suka miƙe suka ce sai watarana zasu kara zuwa, nan suka rabu suna sharar ƙwalla. Har sun kama hanyar gida Khairy tace “Zamuje dandali? Don nasan gobe za'a wuce”
“Eh muje mu gani”
Ba su suka koma gida ba sai wajajen goma na dare. Suna komawa kuwa suka yashe sai bacci.
Bayan tafiyarsu granny ta so abar Khairy tayi ko sati ɗaya ne sai dai saboda makaranta yasa tace in anyi hutu zata zo ko sati ne tayi. Suma su Baffi da iya tare da Baba duk basu ji haushi ba, sunji daɗi da zancen ma saboda Khairy ce mutum ta farko da ta fara yin karatun boko.
Washegari bayan sun karya dukkansu harda iya suka ɗunguma sai gidan Arɗo, nan suka yi masa sallama ya haɗa su da tsaraba irinta ƙauye. Sunyi matuƙar farin ciki tare da yaba halacci da karamci irin na ƴan ƙauyen. Iya da Baba harda kukan su kafin su rabu, daga nan motar su ta tashi sai Adamawa.
Wuraren la'asar suka isa kowa jikinsa yayi tsami, sai da Daddy ya ajiye Sheikh Imam kafin su zarce gida baki ɗayansu. Babu wanda yasan da dawowarsu sai dai horn ɗin motar da suka ji ya tabbatar musu da cewa sune.
Tuni kowa ya fito ana musu sannu da hanya. Kafin maghrib an cika dining ɗin granny da abinciccika. A nan aka yi dinner gabaɗaya ranar. Bayan an kammala Daddy yayi addu'a tare da fara musu bayanin abinda ya faru a can, bai ɓoye musu ba don yanzu an riga an zama ɗaya. Bayan ya kammala wasu harda kukansu, kowa yaji kabarin ajikinshi. Kamar wancan lokacin Daddy ya ƙara jan hankalinsu akan rayuwa daga nan kowa ya koma bangarensa.
_______________________________________________
Hamma Zaki ya shigo gaida granny Amma bai sameta ba, da ya tambayi mom.ta faɗa masa ai sun tafi garinsu Khairy don kammala aikin da Sheikh Imam ya fara. Haka kawai ya tsinci kansa a damuwa yana ta fatan Allah yasa a dace. Zuwansa uku bai semeta ba, gashi numbers ɗin su duka basa tafiya.
Bayan sunyi waya da Mom ne ya tambaye ta ko granny ta dawo? Tace masa eh, bai san MEH yasa duk ya damu da yarinyar ba, “Ko dan ta cancanci a tausaya mata ne” ya bawa kashi amsa. Wanka yayi ya shirya cikin Farar jallabiya tas tare da feshe jikinsa da turarensa da har yau bai daina amfani da irinsa ba wato _Imperior majéste._
Ganin irin wankan da yasha yasa Pretty tsayawa tana binsa da kallon mamaki.
“Sweetheaft ina zuwa haka?”
Ko kallonta bai yi ba ya ɗauko key ɗin motarsa ya fito, bayansa ta biyo tana faɗin “In dai hira kaje da kai da ita duk Allah yana ganin ku ” ta faɗa tana komawa.
Shi fa har yau mamakin irin ɗabi'unta yake, ace mijinka zai fita ba zaka yi masa addu'a ba sai ma mita da rashin ɗa'a.
Jan motar yayi zuwa gidansu. Bayan sun gaisa da mom ya bi ko ina suka gaisa kamar yadda ya saba. Party ɗin granny shine ƙarshen zuwa. Yana shiga ya tarar da granny zaune bisa lallausan carpet ɗin dake parlourn sai Khairy da kanta ke cinyar grannyn. Sallamar da yayi dama ba ji suka yi ba sai da ya doso cikin ɗakin ƙamshinsa ya karaɗe ƙofofin hancinsu.
Zama yayi kan kujera yana faɗin “Granny sallamar ma ba zaki amsa bane?”
“I haƙuri maza, wallahi duk na gaji ne, jiki na ma ciwo yake, ina irin maganin zafin nan da ka taɓa bani, da zan samu ma shi nake so”.
Haka kawai ta kasa ɗaga ido taga fuskar da ta saba gani jikin photo a zahiri. Kanta ƙasa tace “Ina yini” kamar bazai amsa ba yace “Lafiya, ya jikin ki?”
Tayi mamaki sosai jin ya tambaya ta, don a yadda su Fauzah ke bata labarinsa ba ya son wargi ko kaɗan”
Murya a sanyaye ta amsa da “Alhamdulillahi, naji sauƙi”
Daga haka ta fara ƙoƙarin miƙewa don tafiya ɗakinta, har ga Allah ba zata iya zama wuri ɗaya da shi ba.
Zata fara tafiya taji yace “Ina zakije, ni tafiya ma zanyi, Allah ya sauuwaƙe”
Kunya ce ta lulluɓeta tace “Ameen na gode” ba tare da ta kalleshi ba yayin da shima hankalinsa yake kan wayarsa. Daga haka ta koma ta kwanta akan cinyar grannyn.
Miƙewa yayi yana faɗin “To granny mu tashi lafiya, man zafin zan bayar a shigo miki da shi”
Amsa masa tayi da faɗin “To maza, mu tashi lafiya, ka gaishe da ifritiyar matarka”
Murmushi yayi yace “Granny dai”. Daga haka ya wuce ba tare da ya amsa mata ba.
Sun sha hirar su sosai duk da sun gaji kafin su kwanta, ɓangaren sauran ma daren ranar kowa sun sha hirar da mahaifiyarta, wanda duk a
_________________________________________________
*A GURGUJE*
Haka rayuwa taci gaba da kasancewa, Khairy ma ta shiga islamiyya kuma karatun nan abun mamaki shiga yake yi har sai da tazo ta wuce su Fauzah, a bangaren boko ma ba a barta a baya ba, don in kaje kana fadan sunanta kowa ya santa ba dan komai ba sai don ƙwazonta da kuma shiga rai da take da shi uwa uba iya mu'amala da mutane, abun mamaki kuma idan mutum ya nuna mata wargi sai ta cire rigar muunci tayi masa tas tamkar dai *ƳAR IYA*
*TWO YEARS LATER (Bayan shekara biyu)*
Wasu kyawawan Ƴan mata ne da suka gaji da haɗuwa da kyau su huɗu tsaye a bakin gate ɗin Islamiyya, kowaccen su sanye take da hijabi babba brown colour sai kuma wando coffee brown yayinda ba'a iya ganin colour na rigar don yadda hijabin ya sauƙo
Duk cikinsu babu baƙa, farare ne tas wanda in kayi musu kallo ɗaya bazaka so dainawa ba sai ka kai wani duban garesu.
Ta biyunsu a ɓangaren dama ne tace “Ya Ilahi, wollah yau ɗin nan I'm exhausted sisters, gashi drivern ma yaƙi zuwa da wuri, don Allah ku samar mun wurin zama in ba haka ba anjima zan faɗi muku”
Ta farkon tace “Sorry Khairy Ai dole ki gaji, rabonki da runtsawa tun jiya, and all this is bcuz of so called competition ɗin da zaku ce, ga kuma musabaƙar da kika makalawa kanki” ta ukunsu ce tace “Ni wallahi Fauzah na rasa Khairy wace irin mata ce, in tasa abu gaba ko abinci bata ci, Allah dai ya shirya ki”
Tare suka ce “Amin” ta ƙarshen ne bata ce uffan ba dai-dai da zuwa driver Yana parking gabansu tace “Oyah! Letz go babes”
Ai kuwa nan suka shige motar sai gida, suna parking dukkansu suka wuce part ɗin granny, bayan sunyi wanka kowaccen su ta ɗauko Alqur'ani tare da shimfiɗa sallaya. Baka iya jin muryoyinsu har lokacin sallar maghrib suna karatun. Alwala suka ɗauro tare da tayar da sallah.
Har zuwa lokacin babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana, bayan sun idar da sallah Khairy ta kwaso mordern biology textbook, new school chemistry textbook, new general mathematics da kuma okeke's Physics. Nan ta baje tana karanta su tare da warware matsalolin da dama, ni Bhatool ido kawai na bita da shi don abun ya bani mamaki musamman yadda take ragargaza equations, tana solving mathematics ba tare da amfani da calculator ba.
(Allahu akbar).
Sauran ƴan matan a ɗaya ɓangaren suna karanta Alqur'ani ne cikin ransu ba tare da mai karatu yana iya jiyo muryoyinsu ba.
Ƙiran sallar Ishã ya tayar da su suka gabatar, bayan sunyi sallah kuma suka ɓarke da hira tare da komawa parlourn. Granny dai sai mita take wai sun shige jikin jikarta yanzu bata samun kusanci da ita.
Ƙyalƙaylewa da dariya yesmeem tayi tace “Kai granny ba dai kishi ba, na so an haife ni lokacin da kike matashiya da naga salon love ɗin ki” duka grannyn ta kai mata ita kuma tana zamewa, sauran dariya kawai suke yi. Granny tace “Wannan yarinya ba dai iskanci ba, kuyi dai ku gama makarantar nan duk aure za'a yi muku, yara sai shege faɗin lob kamar akansu aka fara” ta ƙarasa tana sakin tsaki.
Dining gabaɗayansu suka nufa, bayan sunyi dinner kowa tayiwa granny sallama tare da wucewa ɓangarensu.
Washegari weekend ne, da safe suka shirya don yau Mom ta tasa su gaba sai sunje gidan Hamma Zaki coz Basu taɓa zuwa ba tsawon lokacin nan, a cewarsu kar suje Aunty Nabila tayi dambunsu.
Cikin Expensive abayas da suka gaji da haɗuwa ƴan matan suka shirya, sunyi kyau kam kamar ka sace ka gudu, ba zaka san da irin kyan da suka yi ba sai kun kai dubanku ga tauraruwarsu wacce kamanninta suka juye tamkar wata ɗiyar larabawa, i doubt not Fulani ba ba baya ba a kyau. Handbag ɗin hannunta ta gyarawa zama tare da gyara veil ɗin da tayi rolling. Cikin muryarta mai daɗin sauraro tace “hey Babes...mu wuce ko,”
Murmushi suka yi kamar haɗin baki suka ce “wow! Khairy kin gaji da haɗuwa fa”
Hararar wasa ta jefa musu tace “Babes ai kuma kun gama haɗewa, Ni inaga ma zan daina yawo da ku don zaku sa kasuwata ta yi sanyi” ta ƙarasa tana kanne ido ɗaya tana dariya”
Yesmeem ce ta kawo mata dukan wasa tana faɗin “Wallahy Khairy ke kike kashe mana kasuwa, kin tuna wannan Khalifa mai ɗinkin?”
Duka ta kaiwa Yesmeen ɗin, Fauzah tace “Muje Babes, Kuna ɓata mana lokaci, Allah dai yasa mu dawo lafiya”
Kyaɓe baki dukkansu suka yi suna faɗin “Ameen”.
_Toh jama'a me kuke tunanin zai faru a gidan Pretty?, Ku dai ku ci gaba da bibiyar alƙalamin Diamond Bhatool, loads of love_
[28/08, 9:07 PM] 💎Diamond_Bhatool💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““78&79 ”””
Mota suka shige daga nan driver yaja motar, bakin wani tafkeken gate yayi horn, babu bata lokaci aka bude musa, “Masha Allah” dukansu suka furta, sai da driver ya daidaita parking suka fito.
Entrance door din suka nufa suna zazzare idanuwa kamar wasu barayi. Doorbell suka danna amma tsawon wani lokaci babu alamar zaa bude har sai da suka kosa da tsayuwa.
Khairy tayi tsaki tace “Nifah babes na gaji wollah, tunda nazo da wayar granny kawai mu kira Hamma Zakin ko bata nan. Amma kafin nan muyi ta danna doorbell in ta gaji da ji hala ta bude ”
Duk sunyi na'am da shawarar Khairyn suka fara danna doorbell din ba kakkautawa. Tsawon mintuna bakwai amma babu wani yunkurin budewar, in banda tsaki babu abunda suke saki.
A hankali taja gefe tare da shiga contacts na wayar, _Maza_ ta fara dubawa don tunaninta ga hakan ya tsaya, abun mamaki numbernsa wanda special ne ya bayyana. (Bari dai na bawa readers numbern Hamma Zaki in da mai sonsa to.....0707777....).
Dialling tayi tare da karawa a kunnenta, a lokacin kuma sauran suma suka iso gareta. Ajiyar zuciya khairu ta sauke jin numbern ya shiga, sai dai yana fara ringing akayi rejecting, bata kai ga kara kira ba kuma kiransa ya shigo wayar. Picking tayi tare da saka wayar a handsfree. Cikin mutyarta mai dadin sauraro tayo sallama, shima amsawa yayi sai dai ya shiga wani yanayi jin wata daddadar mutya wacce take dauke da wani sinadari da bai aan na menene ba. A gefe daya kuma yana tunanin lafiya? Numbern granny kuma wata ta daga don shi har ya manta akwai wata khairy a gidan.
Tsawon lokacin da suka shafe babu mai magana a ciki alamun dukkansu sun shiga wani yanayi ne, don ita khairy a nata bangaren zuciyarta ne ke wani irin bugu, Fauzah ce ta tabo ta nan ta dawo hankakinta, cike da inda-inda tace “Ehm eh dama su Fauzah ne, mom tace muzo kuma muna ta jira a bude mana kamar babu kowa a gidan”
“Shikenan ku tsaya yanzu zaa bude kunji” daga haka yayi rejecting kiran. Numbern Pretty ya lalubo tana picking ta furta “Hello sweetheart...” katseta yayi yana fadin “Ki wuce ki bude kofa tun dazu kina nufin baki ji karar doorbell ba?” bai jira amsarta ba ya katse kiran yana sakin tsaki.
Lokaci daya kuma ya tuna da wannan daddadar murya, “Fauzah” ya furta, “Noo that should not be Fauzah, then who?” ganin zai bata wa kansa lokaci yasa ya mike tsaye.
A bangaren su khairy ko 3minutes basu kara ba suka ji karar bude kofa, waiwoyawa dukkansu suka yi suna duban kofar. Pretty ce tsaye cikin wasu tsinannnun kaya, ganin wadannan cousins din Hamma Zakin yasa ta saki tsaki tsaki tana jifansu da wani matsiyacin kallo, tayu yunkurin konawa idonta ya sauka kan Wata kyakkyawar yarinyar da bata santa cikin familyn ba, dumm zuciyarta ta buga amma ta kafse tare da shigewa abunta tana juyi kamat wata macijiya. Dariya khairy ta kwashe da ita tana fadin “Babes don Allah baku ga muciya bane, hhhhh kinga yanda take wani juyi don Allah”
Dukkansu dariyar suka yi kamar zasu yi kuka, daga hakan khairy tace musu “Mu shige ciki mana babes” ta karasa tana kanne musu ido daya.
Dukkansu suka dunguma zuwa parlourn, cak suka tsaya saboda kurar da parloun yayi, ta can gefe kuma ga datti alamun dai matar gidan ba girki take yi ba order take. Cikin ransu duk Allah wadai suke da hali irin na in-law din tasu wacce babu wani kyakkyawan hali daga gareta da ya isa garesu, tabbas jarrabawar Hamma Zakin ne amma ina mutum mai nagarta itinsa da mace irin Aunty nabila?. Ganin babu inda zasu yi gashi kuma Mom tace yini zasu yi wallahi da ba zasu zauna a wannan kazamin parloun ba.
Khairy ce tayi tsaki tace “Babes mu nemo kayan aiki mu tsaftace parloun don wollah ni bana iya zama a cikin kazantar nan”
Yamutsa fuska Ayrah tayi tana fadin “Ai dolenmu, amma wai dagaske Hamma Zaki kuwa yana iya rayuwa a hakan?”
Fauzah tace “Nima abun ya tsaya a raina, mutumin da tsabagen tsafta wani lokacin har mamaki muke yi”
Yesmeen ta cafke da fadin “Kin manta kullum cikin kiranmu da kazamai yake yi bayan babu wani abun kazanta da muka yi”
Fayzah tace “Ai wollah dole mom taji, haba no wonder Hamma ke ramewa, ku tuna lokacin da Hamma Salim yayi aure yanda kullum kara