Showing 81001 words to 84000 words out of 135404 words
zata nufi wurin. Ji tayi an dakatar da ita ta hanyar rike hannunta ana juyo da ita.
_COMMENT & SHARE PLEASE_
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““81&82”””
Juyowa tayi tana fuskantarta, ita dai Khairy wani shu'umin murmushi take saki yayin da pretty ta saki baki tana kallonta.
Lokaci daya ta hade rai tace “Kallon fa?, eh? Ke da kike tambayar uban waye ya kawo ni gidan kuma kike nufar abunda na girka?, madam koma daki tukun idan wanda nayi dominsa yaci in nayi niyya na baki guntun”
Mamaki ne ya cika pretty ganin yarinyar da ta bata kusan shekaru biyar zuwa shida tana fada mata son ranta. A harzuke ta kawowa khairy duka, gocewa tayi tana sakin wani mahaukacin ihu wanda yayi daidai da fitowar Hamma Zaki daga dakinsa. Da sauri ya sauko kasa ganin Khairy kwance a kasa sai famar ihu take yasa ya iso yana tsugunnawa a gabanta.
“Me yake faruwa?” ya tambaya.
Cikin muryar kuka Khairy tace “Wai don na tashi da wuri na gyara gidan nayi girki shine ta fito ci, don nace ta jira ka fito shine ta hau ni da duka” ta karasa tana kyallawa pretty ido.
Cike da kulawa Hamma Zaki yace “Sannu yi hakuri, zaki iya tashi ai?” murmushin gefen baki tayi, cikin wani yanayi dake nuna tasha wahala tace ,“Zan iya”.
Jin amsarta yasa ya mike tsaye yana duba wurin da pretty take sai dai babu ita babu alamunta, murmushi kawai yayi yace “Ki bi a hankaki da ita kinji”
Kai ta gyada tana mikewa tsaye. Ganin ya nufi dining yasa ta bi bayansa.
Sai da tayi serving dinsa ta bar wajen tare da komawa dakinta tana shekewa da dariya, “Yau dole babes su san me ya faru, hhh”. Tabbatarwa da ya tafi yasa ta fito tayi breakfast, da ta gama ta zuba a plate ta nufi sama. Ba tare da tayi knocking ba ta shiga dakin pretty fuskarta dauke da wannan murmushin. A bakin gadon ta zauna tana yamutsa fuska, hannunta ta kai tana taba pretty. “Ki tashi kiyi breakfast mai ciki”
Kamar zata yi hauka haka ta tashi don kamshin yayi mata dadi sosai. Karba tayi ta fara ci hakan yasa Khairy fitowa ta nufi bedroom din da take kyautata zaton na Hamna Zakin ne.
Tas ta gyara masa, ta sauya curtains, bedsheet sannan ta fesa freshners mabanbanta wadanda suka bada wani sassanyan kamshi daga nan ta dauko plate din da pretty taci abinci ta nufi kitchen, sai da ta wanke komai kafin ta dawo dakinta tana daukar wayarta. Cikin whatsapp group nasu ba babes ta shiga ta fara zuba musu voice note, da ta gama ta sauka tana murmushi ita kadai cikin ranta tana fadin “He's not bad as i thought”.
Bangaren Hamma Zaki tsaf ya gano yarinyar nan da gangan ta fadi amma sai ya tsinci kansa da murmusawa. “Silly girl” ya furta a bayyane . “I don't know that se's so nice like this” cikin ransa kuma yabawa da aikin da tayi yake, girkin ma yayi a bayyane yace “Delicious indeed”. Haka yayi ta tunaninta a office nashi har ya gaji ya fara jin haushin kansa, “Why did i so much care about her? Mtss” yayi tsaki yana kwaso wasu files.
Sai around 1:30pm ta fito bayan tayi sallah, daga nan kuma ta nufi kitchen tana tunanin me zata girka. Murmushi tayi ta nufi bedroom din pretty. Da ta shiga kamar dazu a keance take tana danna waya. A hankali tace “Aunty Nabila me zaki ci a dafa miki?”
Da mamaki ta dago tana kallonta cikin ranta tana fadin “Wannan kuwa lafiyarta kalau?” sai kuma tayi murmushi tace “Kiyi hakuri kanwata da abunda ya faru dazu, raina ne ya baci”
Gira ta daga tace “Babu komai, me zan dafo miki?”
“Taliya da manja ma yayi”
Bata ce komai ba ta fita ta girka daidai cikin prettyn ta juye ta kai mata bedroom dinta, ita kuwa sai godiya take rafka mata. Ba tare da ta kulata ba ta taho kitchen ta hau girki, sai da tayi tunani kafin ta yanke shawarar yin White vegetables rice and stew, bata wani bata lokaci ba ta kammala, tas ta kwaso ta jera a dining ta koma ta juye sauran a plate. Daga nan ta bude fridge taga akwai kwakwa ta hada coconut juice shima ta saka shi a jug ta ajiye a dining daga nan ta fito taci nata.
Sallar la'asar tayi sannan ta dawo parlour ta dawo tayi zamanta tana danna wayarta. Misalin 4:06pm ya shigo gidan, ganin parlourn fess sai yaji ransa fayau, bata kula da shi ba kamar yadda shima bai kula da ita ba, bedroom dinsa ya nufa, yana bude kofar wani sassanyan kamshi ya bugi hancinsa, lumshe ido yayi yace “Wow!”, a hankali ya shiga kamar mai jin tsoro, ganin ko ina kamar ba bedroom dinsa ba yasa ya kara sakin murmushi yace “Oh this silly girl”. Sosai dakin ya burge shi, zai iya cewa tunda suka taro gidan baa taba gyara dakin nan ba in ka cire sauya bedsheet idan yayi datti da yake yi.
Bai gama mamaki ba sai da ya shiga bayi yin wanka, idanuwa ya kwalalo jin wani irin kamshi da bayin yake yi ga kuma gyara da yasha ko ina sai shining yake yi. Cikin wani irin farin ciki da ya gagara gane na miye yayi wankan ya fito. Bayan ya shirya cikin brown jallabiya ya sauko kasa don yana da tabbacin cewa yauma akwai abinci.
Kai tsaye ya nufi dining din lokacin tana kwance, ganinsa yasa ta mike tabi bayansa, “Ina yini Hamma Zaki ” tsintar kansa yayi da fadin “Lafiya”. Serving dinsa tayi kamar dazu ta koma bedroom dinta. Yaci ya koshi yayi hamdala yana kara yabon girkin nata. Daga nan ya nufi gym room nashi ya motsa jiki. Sauran abincin ta dauka ta nufi dakin pretty tare da kai mata ko zata ci.
Da daddare ma haka ta shirya musu dinner daga nan bata kara fitowa ba.
Haka rayuwar taci gab da kasancewa tsawon sati daya, a lokacin ne kuma result na WAEC ya fito, sunyi matukar farin ciki da sakamakonsu kowacce perform well, daidai wannan lokacin ne kuma aka sanya ranar bikin saukarsu akan watanni biyu masu zuwa.
Tun daga ranar suka saro zuwa gidan Hamma Zakin suna fakewa da shirye-shirye suke yi, babu laifi sun ga sauyi kadan daga matar gidan musamman yadda takewa Khairy magana.
Yanzu watannin cikin pretty bakwai, lafiya lou kuma take saboda babu laifi Khairy na kulawa da ita.
Ana gobe saukarsu ne suka biyo ta kan Khairy, bayan tayi girki ta ajiye musu tayi wanka ta shirya. Lalle aka yi musu na gani na fada ja da kuma baki sannan aka gyara musu kai da jiki, sunyi kyau abunsu gwanin ban sha'awa. A can Naira family house anyi musu kaya na gani na fada.
Washegari da misalin 2:00pm suka iso gidan Hamma Zakin dauke da wata jaka. Bayan sun gama cin abinci suka zauna suna fitar da kayayyakinsu daya bayan daya suna yaba irin haduwar kayan. Sai wajajen 3:30pm suka fara shirin tafiya. Kowacce tayi kyau kamar ba ita ba, cikin purple colored Hijab suka fito. Suna isa wurin da aka tanadar dominsu suka wuce tare da zama.
Taro yayi babu laifi, bayan anyi saukar ne aka fara ba kyaututtuka da certificate wa hazikai daga ciki. Alhamdulillah duk cikin Yan matan kowa ya amsa nasa. Nan aka fara raba kayayyakin ciye-ciye daga nan kuma kowa da ahalinsa suka ja gefe ana daukar hotuna. Kowa ka gani fuskarsa cike da farin ciki maras iyaka, ana cikin yin hotunan kamar daga sama Khairy ta hango fuskar da batayi tsammani ba.
Sanye yake cikin wata Blue Gezner wacce tayi matukar amsar jikinsa, cikin takunsa mai daukar hankalin nan ya karaso wurin da suke. Ganin hankalinta ya koma wurin yasa fauzah bin idon nata, baki bude cike da mamaki take kallonsa, tayi farin ciki da hakan amma ai basu sanar da shi da zancen saukar ba.
Mom da sauran matan gidan tare da granny duk sunyi mamaki, nam wani sabon farin cikin ya barke. Sabon shafin daukar photos aka bude, Hamma Zaki ya mika wayarsa aka yi musu da su a tare, sai kuma aka yi musu individually. Kasancewarsa maras son hayaniya yasa yana gamawa ya fice ba tare da kowa ya kalleshi ba.
Alhamdulillah! Taro yayi anyi an gama lafiya, kowa sun koma gida lafiya. Suna fita suka tarar da motar Hamma Zaki, mom kasa yin shiru tayi tace “Kun kuwa ga me na gani?”
Nenne tayi murmushi don ta dasa ayar tambaya akansa tace “Ai duk mun gani, Allah dai yasa sauyi ne ya samu har abada”
“Amin” suke ce.
Kowa motar da yazo ya nufa, Khairy ma niyyarta ta wuce guda kawai taji muryar Mom na fadin "Khairy inaga fa Hammanku ke yake jira ku wuce ” kamar zata yi kuka tace “Mom don Allah kice ya barni yau kam na biyo ku, iya yau don Allah ”
Mom tayi murmushi tace “Kije ki tambaye shi da kanki ko kina ciwon baki ne?”
“a'a” karasawa wurin motar tasa tayi tana Allah yasa ya barta. Glass din tayi knocking, bayan ya sauke kamar wata maras gaskiya tace “Hamma Zaki don Allah zan bi su mom na kwana gobe da safe sai driver ya maiso ni” kamar ba zai amsa ba taji yace “To wa kike so ya bamu abinci kuma?” cikin ranta tace “Dube shi to da da bana nan kuma waye yake bashi?” sai kuma tayi alamar tana bukatar ya tausaya mata tace “Don Allah iya yau, akwai abinci nayi fa kafin mu fito” ta fada tana mamaki dama Hamma Zaki yana magana haka? Bata gama tunanin ba taji yace “Ajiyayye kuma zamu ci? Ki wuce mu tafi kina bata min lokaci ” kamar zata yi hauka ko kallon su mom din bata yi ba ta zagaya ta shiga.
Su dai su mom ikon Allah kawai suke gani, tambaya shine aka bata wannan lokacin, ai basu ida zancen ba suka ga ta shige ciki. Mamaki duk ya cikasu. Haka motar Hamma Zaki ta nausa bisa titi. Ko kallo bai samu daga gareta ba saboda yadda take jin haushinsa.
Daidai gate din gidansa yayi horn, bayan gateman ya bude ya cusa hancin motar zuwa ciki. Ko daidaita parking bai yi ba tayi azamar fita sai dai taji ya rike hannunta. Ba tare da ya juyo ba yace “Ina kuma zaki je? Ki tsaya mu shiga tare” mamaki ne ya kamata har ta gagara boye hakan.
Sakin hannunta yayi suka shiga a tare kamar yadda ya fada din. A fusace tayi hanyar dajinta ya rike hannunta, juyowa tayi tana jiran taji ta ina yanzu kuma zai bullo “Kiyi wanka ki shirya fita zamu yi” daga haka ya wuce.
Kamar yadda ya fada hakan tayi amma wani kololon bakin cikinsa take ji kamar ta kama ta daka. Wanka tayi sannan ta gabatar da sallar magrib, daga nan ta nufi dining, ganin babu abunda suka taba yasa tayi godiya, warming abincin tayi ta dawo da shi sanan ta koma bedroom dinta. Powder ta shafa sai wani pink lip gloss da ta shafa, ko kwalli bata saka ba ta ciro wata Violet purple doguwar riga wacce ta gama haduwa.
_COMMENT & SHARE_
[30/08, 11:57 AM] 💎Diamond_Bhatool💎:
🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““83&84”””
Violet purple riga wacce ta gama haduwa ta dauko, a nutse ta shirya, masha Allah tayi kyau sosai don ko makiyi ya gani sai ya yaba.
Tana zaune taji knocking, da kanta ta mike tazo ta bude, kashinsa ne ya fara bugar hancinta nan ta lumshe idanuwa sai kuma ta bude tana sunkuyar da kanta kasa, “Kin gama shirin?” kai ta gyada masa don ita wani kusanci da suke samu bata so sai ta ji kanta so uncomfortable. Muryarsa taji yace “Ok ki fito mu wuce”
Light purple veil kawai tayi rolling tare da daukar light purple bag dinta sannan ta fito. A parking lot ta tarar da shi har ya shiga motar hakan yasa ta nufi gefen mai zaman banza ta shiga. Duk irin kamahin da take tuni nasa ya danne nata sai taji kamar bata saka komai ba.
Motar yaja zuwa kan titi yayin da muryar qari'in nan Muhammad Ayyubi ke tashi. Cikin ranta ta fara bibiyar karatun sai dai tunani ya dauke ta. Ta rasa me yasa a kwanankin nan take yawan tunaninsa, mutumin da sai da daliki magana ta fara shiga tsakaninsu amma tunaninsa ya bi ya takurawa sahihiyar zuciyarta. Ajiyar zuciya ta sauke shima kuma daidai lokacin ya sauke tasa. Cikin ranta tace “He's handsome and qualified to be called precious, duk macen da ta same shi ai wallahi cass da ita amma wata ta samu tana wasa da damarta”. Daya bangare na zuciyarta yace “To ai dama duk wanda ya samu haka yake da ballagazanci” da sauri dayar tace “A'ah Khairy to ke da kike taki ce miki yayi yana sonki ne sai wani yabonsa kike?” da sauri ta furta “Nooooooo”.
Cike da mamaki ya dago yana kallonta jin ita kadai tana magana sai kuma ya juya yana maida hankalinsa ga tukinsa. Bata lura da hanyar ba sai ganinsu tayi gaban gidansu, ai kuwa bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba. Har ga Allah ya mugun bata mamaki, tuni haushinsa da take ji ya gushe. Yana daidaita parking ta mika hannu zata bude taji muryarsa yana fadin “Ki shiga kuyi sallah, ana idarwa zamu fita, ok?” kai ta daga masa daga nan ta fice a motar ta nufi gidan cikin farin ciki.
Tana fita ya saki wani shu'umin murmushi yace “Everything she do fits her” daga haka ya fice ya nufi part din Mom. Bayan sun gaisa ya shiga sauran bangarorin suka gaisa amma bai shiga na granny ba.
Ana idar da sallah kamar yadda ya fada ya shigo part din granny don yafi kyautata zaton a can suke, bayan sun gaisa fa granny nan ta fara mitar yanzu ya sauya. Har da fadin ni dazu daga cewa taje ta tambayo ka kawai sai ka wuce da baiwar Allah bayan tana son zama da yan uwanta” fuska ya hade saboda baya so suji zancen da suke shida granny, cikin ransa yace “Ai sai su raina ni”. A zahiri kuma yace “Is ok granny, ni zamu wuce ne fa!”
“Kai!” ya fada daga wurin da yake, a tare suka zo kamar wasu sojoji suka tsaya “Gamu”. Granny ya kalla yace sai anjima granny ta sannan ya dawo da kallonsa gare su “Kunsan bana jira ko?”
Ai bai gama fada ba suka yi waje, a parking space suka ga motar da ya zo da ita saboda haka kowa ta kama mazauni, frknt seat kam yanzu sun yafewa khairy shi don su wani tunani ma suke akanta.
Bai tsaya ko ina ba sai katafaren shopping mall da baa dade da lunching nashi ba, su basu ma taba zuwa ba sun dai ji yadda ake zuzuta wurin a gun classmates nasu. Abun mamki ko da suka isa maimakon ya basu lokaci kamar yadda suka saba sai ya mike yayi gaba, ba tare da sunce komai ba suka bi bayansa don sun san suka tsaya magana ma laifi zasu yi.
Kewayawa suka yi suka zabi abunda suke bukata, sosai suka kwashi abubuwa coz wurin latest ne ba karya. Bayan sun gama yayi payment daga nan kuma suka zuba kayan a boot, maimakon su wuce gida sai suka ga ya nufi wani restaurant da su. Baki bude Ayrah kam ke kallonsa cikin ranta tana fadin “Anya Hamma Zaki ne?” haka sauran ma, ita dai Fauzah tunaninta ko zai siya ne tunda matarsa bata girki, mai yi yanzu kuma yau bata samu yi ba sai dai dukkansu sai da suka kwalalo ido jin yace “Letz go” bayansa suka bi sannan suka samu wurin zama, kowa tambayarsa me taje so yayi duk sai suka ce a koshe suke, cupcake yayi sai tea.
Tare suka ci suka sha suka kara da hamdala daga nan kuma yasa aka yi masa take away. Maimakon su tafi sau suka ji muryarsa yana fadin “Ina matukar tayaku murnar wannan nasara kannena, Allah yasawa abunda aka koya albarka” “Amin” suka ce, sai suka ji ya daura da “Abunda nake so da ku shine ku tsaya ku kula da rayuwarku a wannan lokacin don mutane da yawa zasu yi kokarib kutsa kansu cikin rayuwarku yayinda da yawa daga cikinsu suka kasance ba boge, ina nufin ba saboda Allah ba. So yanzu kunga jami'a zaku faea zuwa tunda babu wasu tsayayyu, ku rike tarbiyyar da kuka samu daidai iyawarku, banda tara samari, duk wanda yace yana son ki kice yazo ya gana da iyayenki, wannan shibe ideal way kun gane?”
“Eh mun gane” suka hada baki. Yace “Good, are we good to go?” kai suka daga daga haka suka kwashi jiki suka bi bayansa.
Kowa dai da abunda je ransa, Allah Allah suke a koma gida a dan guntsa a fetsar. Ko a hanyar bai yi magana ba saboda yadda kansa ya sara sabida maganar da yayi.
Ko da suka isa boot ya bude musu yace su kwashe iya nasu, ita kuma tayuwa granny sallama tazo su wuce. Ba haka ta so ba amma babu yadda zata yi. Da ta dawo yaja motar suka wuce gida. “mun gode Hamma, Mu kwana lafiya” kawai ta tsinci kanta da