Showing 132001 words to 135000 words out of 135404 words

Chapter 45 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46341

da matar wacce ke zaune a gindin wata bishiya kowa sai toshe hancinsa yake yi, da mutane sun isa wurin suna tarar da abinda ke faruwa suke kaucewa.

Ƙarasawa nayi na kutsa kaina don ganin me ake yi, wata mata ce ƴar babba da ita wacce ke zaune dirshan tana kuka, kayan jikinta duk sun yayyage ga kuma uban datti da ke jiki. Roba ce a gabanta tana kuka ta na nuna musu amma babu mahalukin da ya jefa mata komai cikin robar. Ko da na matsa kusa don ganin waye ba kowa bace sai Mami, Mamin Pretty dai ta rame ta ƙara baƙi kamar ba ita ba, fatar nan kamar wacce aka kai prison ta shekara talatin duk ta yanƙwane “Ku taimaka ku saka saboda Allah ba don Ni ba, ku taimaka don darajar ubangiji ba dai Ni ba” da ta gama faɗar haka kuma sai ta fara faɗin “Ni ce silar komai”. Idan ta faɗi haka ko mutane sun yi niyyar ajiyewa sai su tafi. Da ƙyar dai ta tara 2k daga haka ta miƙe tana murna ta nufi wata rumfa da ke can gefen hanya. “Tashi shalele, bari yanzu zan siyo abinci ki jira Ni, babu inda zamu sai ya dawo mun nemi yafiyarsa, haƙƙinsa ne kanmu” daga haka ta wuce tayi gaba.

Daidai rumfar na tsaya ina zuba idanu, wata matashiyar budurwa ce da ba zata wuce kimanin shekaru 28-29 ba amma fatarta duk wasu ƙuraje ne sun farfashe suna fitar da wani irin ruwa mai warin gaske. Ba kowa bace pretty ce, amma fatar nan tayi baƙi kamar ba wannan ƴar gayen ba wato pretty. Mamin ta ce ta dawo da leda a hannunta daga nan ta ƙaraso.
“Shalele tashi na siyo Miki taliya”
Da ƙyar ta ɗaga ta ta jinginar da ita, duk irin warin da ke fita bata damu ba ta bata abincin ta ci, daga nan ta mayar da ita ta kwanta ita ma ta ci sauran.

_Waiwaye_

Kafon Namouru ya cillo su sai da ya ɗauke pretty ya Tara da ita tukun, bayan ya cilla su da ƙyar Mamin ta tuƙo su suka baro ƙauyen zuwa Niamey, dama ba da Flight suka zo ba da mota ne, haka suka ɗau hanya kusan sati biyu suka kai ga Adamawan Yola bisa sharaɗin pretty na idan Mami bata Kaita wurin Captain ta nemi yafiyarsa ba har ta mutu wallahi bata yafe mata ba, hakan kuma duk cikin azaba ne don kuwa fuskar ta tayi baƙi ta lalace kamar kanwa, babu yadda ta iya haka tayi ta niƙar hanya, ga kuɗaɗen da suka shiga da shi Namouru ya kwashe su tas ya bar su da la haula iya wasu kuɗaɗen da ba zasu haura 200k ba suka bari a motar tasu, da su kaɗai suka tsira, kuɗin mai da suka yi ga kuma matsalar da motar ta basu sai da aka gyara ta. Tuni kuɗin ya cinye.

Ƙarin abun haushin suna isowa Adamawa suka rafkata accident Allah yaso duk motar ta cilla su gefe kafin ta kama da wuta, su kuma basu buƙatar wani agaji ko taimakon gaggawa yasa baa bi ta kansu ba. Mami sai da ta zama ƙaramar mahaukaciya a lokacin saboda ko wayar da zata ƙira Daddyn pretty bata da shi, gashi taƙamaimai gidan basu sani ba.

Haka zata fita yin Bara kowa ya hana ta don basu yadda da ita ba, wasu kuma basu jin ma Yaren da take maganar da shi bare su fahimci me take so.

_Comment, react and cimment_
[27/09, 6:15 p.m.] Famanté 💎: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““129&130”””

Da ƙyar ta samu wasu masu jin Hausa suka bata sadaka, shine ta tambaye su me zata ke faɗi don a bata, da harshen fillanci suka faɗa mata har ta haddace kafin suka wuce nan tayi ta musu godiya.

Kwanaki biyu duk ta jigata, sai a lokacin ma ta fara tuna irin iyashegen da ta tsula a rayuwarta, a hakan ma ba risina tayi ba, jira take wannan ɗan iska in ji ta da faɗa ya dawo ƙasar daga nan zasu wuce Abuja abunsu, daddyn pretty have everything Amma suna wahaltuwa, ita kuma pretty bayan kwana biyu wasu ƙuraje suka fiffito mata a jiki, masu ruwa ne kuma in sun fashe wari suke fitarwa.
Basu da kuɗin da zasu je ko da chemist ne su sayo magani shiyasa tunda suka samu wata rumfa suka fake wurin har zuwa lokacin da suke jira.

*********💎********💎*******💎********💎

*AMMAN, JORDAN*

Breakfast suka yi daga nan suka fara shirin ficewa don zaga gari, cikin shigar da ta mugun amsarsu suka fito nan suka haɗu da sauran, through kowa da wurin zuwanshi haka suka fita. Da da zasu dawo sai da suka biya ta wani park suka ƙara enjoying ranar, sun ɗan huta sosai kafin su kwashi tarkacen da suka saya suka nufi masauƙinsu kuma.

Tunda suka koma take jin ta high high wasa wasa temperature na jikinta rises, Hamma ne yayi tapid sponging nata sannan ya bata hot tea amma still bai sauƙa ba. Yayi yayi ta tashi su tafi hospital ta ƙi haka ya sa ya haƙura don baya son takura mata. Abincin da ya yi feeding nata ma duk sai da ta fitar da shi, hakan yasa ya sa ta gaba suka nufi hospital. After all the examinations and tests Dr ya dubi Hamma Zaki cikin harshen Urdu wanda ita khairy bata fahimtar komai ya ce “Congratulations, your partner is two weeks pregnant shiyasa, temperature na jikinta da yayi rising is because of the foreing embryo da ke cikin nata, amai ma da tayi is normal, most pregnant women come up with it.” daga ƙarshe dai yayi masa bayanin yadda zai kula da ita, things she supposed to be doing and those she's contraindicated to. Daga nan yayi prescribing drugs nata aka sallame su suka wuce.

Ita dai ba abinda ta ji ganin Hamman ta cikin farin ciki yasa da suka koma gida take tambayar shi “Me yasa kake farin ciki?”
Ɗaga ta yayi kwacakom kamar wata teddy bear ya juya round uku kafin ya tsaya yayi kissing nata deeply har sai da suka kusa wuce hanya sai kuma ya ajiye ta kan kujerar shaƙatawar da ke balcony na apartment nasu tare da zama gefenta. Ƙara kissing nata yayi hugging her tightly ya ce “Thank You soulmate, Allah yayi Miki albarka soon zan ƙara zama Daddy”
Bata fahimci me yake nufi ba yasa ta ɗan zare jikinta daga nasa a hankali ta ce “I don't get you Heartbeat ”
Cikinta ya shafa yana faɗin “Akwai ajiyata a nan” sai kuma ya kanne mata ido ɗaya. Dariya tayi sosai don tunaninta he's only joking, tsayawa tayi tana riƙe kansa tare da ƙura mai idanuwa sai kuma ta kwaɓe fuska “Don Allah Heartbeat me Dr ya faɗa maka, kaga bana jin Yaren da kuka yi magana da shi”

Murmushi ya kuma yi yace “Youre pregnant khairy, kina ɗauke da Baby na” sai kuma ya ɗaga ta kwacakom suka koma massuƙinsa, abincin da aka kawo ya amso yana tambayarta ko zata iya ci?, ta ce masa “Eh” da kansa yayi feeding nata, few spoons ta ci ta kauda kai, daga nan tayi brush ta shalla wanka sai zuba ƙamshi take kamar dai yadda ya zame mata jiki, ƙarasowa wurinta yayi sai ta gauce tana mai hararar wasa “Take bath before you touch me and my baby” sai kuma ta gwaliye sa. Dariya yayi ya ce “Zan rama ne” daga nan ya wuce toilet shima yayi wankan sa.

Sosai suka yi making love, sannan suka yi wanka. Tun lokacin Hamma ya takura mata wai gobe zasu yi shopping tunda sati mai zuwa they'll be leaving zuwa Mecca, the holy city. Washegari kuwa suka nufi _City Mall_ da ke nan Amman, sosai suka yi siyayyar kayan baby kamar basu san ciwon kuɗi ba, kayan kuma suka sa a wuce musu da shi masauƙinsu.

Basu koma gida ba sai suka wuce _Darat Al funun_ , a nan suka sha coffee da kuma biscuits sai suka sayi ticket na shiga theatre don su ma suyi kallo yau. Komawa masauƙinsu daga nan suka yi suka shiga da kayayyakin da suka siya suka harhaɗa su wuri ɗaya saboda ko lokacin tafiya ya zo ba zasu sha wahalar haɗawa ba.

Da yamma suka ƙara yin wani wankan suka nufi _Orient Gallery_ a nan ma sai da suka ƙara kwasar kayan baby da suka ga Kid's collection Site, bayan sun gama ne Hamma Zaki ya tambayi masu wurin ko ina ake sayar da expensive jewelleries, location na _Al Galleria mall_ wurin zobuna ya ja ta suka yi, ko da suka dudduba bai ga irin wadda yake so ba, ya juya ɗauke da ita a hannunsa saboda gajiyar da tayi idonsa ya sauka kan wani pink pack da aka nade shi da zare mai white rose a sama. Da sauri cike da kulawa yace “Soulmate let's check that one”. Ko da ya buɗe wasu ring ne guda biyu wanda ido na yin tozali da su zai san ba na wasa bane. Ko da suka nunawa roomkeeper ɗin sai da ya zaro ido. Kallon Hamma Zaki yayi yana faɗin “Wannan zoben shekararsa biyu yanzu a nan an rasa mai siya saboda tsadarsa”
Price nashi Hamma Zaki ya tambaya, mutumin ya faɗa masa, a kuɗin mu na Nigeria daidai yake da 1.9billion, babu tsammani suka ga Hamma ya miƙa card nasa yace “Ina buƙatarsa” ba iya khairy ba duk mutanen da ke a store ɗin nan sai da suka juya suna kallonsu, zoben ne ya haɗa iya haɗuwa, in dai mutum ya gani zai so mallakarsa bayan sunyi payment suka dawo masauƙinsu.

Satin nan dai duk a siyayya ya ƙare musu, thank God cikin Khairyn ba me wahalar wa bane. Ana gobe zasu wuce Saudiyya kuma. Suka gama komai nasu, bayan ya dawo daga booking musu Flight ya tattara komai nasu in place. Washegari suka wuce Saudiyya.
Sosai suka yi addu'a wa kansu da kuma ƴan uwansu, suka yi addu'a sosai Allah ya raya cikin jikinta, Ana saura kwana biyu su koma, Hamma ya ƙira ya sanar da gida cewa zasu dawo amma Lagos dai zai yi landing, kafin su koma kuma ya tura kudade an kara modernizing gidan nasa.

********💎*********💎********💎*********💎
*Nigeria, Adamawa*

A yawace -yawacen Nasu don yanzu an tayar da su daga rumfar har suka shiga cikin gari, babu laifi ƙurajen Prettyn sun bushe yayin da suka bar mata spots har abun ƙyama, tafe suke hannunsu riƙe, ɗaya hannun mami ɗauke da rubber wacce ake saka musu abun sadaka a ciki. Mami ce ta ɗan tsaya tana faɗin “Shalele nifa na gaji da wannan rayuwar, baki san unguwar su Alin ba ne kawai muje mu huta?”
Ɗan tunani tayi can ta tuna kamar dai a Shagari estate suke kafin ta faɗawa Mami. Wani mabaracin Mami ta tambaya ko ina ne Shagari estate, kwatanta mata yi da yake nisan ba can ba ne da yadda suke, in ma akwai dole da ƙafar zasu je tunda ba kuɗi garesu ba, ita dai Mami ta ƙosa su koma Abuja ko da huta sai mita ta ke wai duk pretty ne ta jawo musu Bara da tace su taho Adamawa.

Da ƙyar secury guards na babban gate ɗin suka barsu suka shiga. Sun sha wahala kafin suka gano gidan, ƴar ƙaramar drama aka yi da gateman kafin ya barsu suka shiga. Part ɗin granny suka fara zuwa, ganin su yasa duk ta tsorata musamman pretty da fatarta ta ɓaci da dari spots, ta ƙofar baya granny Kam ta gudu ta fito tana neman taimako wai aljanu ne suka zo part ɗinta. Da ƙyar aka lallaɓata aka ce su je a gani.

Kuka sosai pretty ta fara tunda ta ga su Nenne, Mom da kuma Mommah sai kuma granny ɓoye a bayansu tana laɓewa wai kada su tafi da ita.
Mom ce ta tambaya ko lafiya nan pretty da ke kuka ta ɗan tsaya ta musu bayani ta zo neman yafiyar abinda ta aikata ne. Sai a sannan Mom ta gane ta sai ta faɗawa su Granny ai Nabila ce tsohuwar matar Hamma Zaki. Hailala granny ta fara tana kuka. “Duniya kenan!, Allah ne ya rama mana tun a nan duniya amma wallahi duk irin yadda nayi ta jin haushi ki labila na so na Miki dukan tsiya kafin ki tafi. Yanzu kuma kinzo a abar tausayi ba zan iya ba, to shi dai Maza yanzu haka ina ga gobe zai dawo ƙasar tare da matarsa Ummul Khairy kuma bana jin a nan zai sauƙa sai nan da sati zai shigo nan ɗin, amma kafin nan bari a Baku kuɗi ke uwar banza ki kai ƴar nan asibiti duk ta koma kamar aljana”

Haka dai granny ta basu kuɗi tace su tafi asibiti, nan da sati sa dawo ko yazo. Mamin Pretty ce tayi ta roƙon granny a kan ta taimake su basu da wurin kwana ma. Baki nuɗe granny ta ce “Wai nace ina ƴar nan ne mai suna na, ina nufin jika ta?” da ƙyar pretty ta bata amsa da “Tana can gidansu ƙawata a Abuja ” kamar granny zata daketa ta ce “Ai kuwa ki koma ki taho da ita don in Maza ya dawo yarinyar nan zai karɓa kar ta koyi mugun hali.”

Da haka suka bar gidan, Mami ta ce to kawai su koma Abuja kafin ya dawo su ma sun daidaita ai sai su taho musu da ƴarsu.

*******💎******💎********💎******💎***💎

*MECCA*

Yau juma'a, Six am suka nufi airport bayan sun yi tsaraba sosai. Bayan an gama ƙiran sunayen su da kuma binciken kayayyakin su suka shiga jirgin. Ƙarfe 6:30am na safe kuma jirgin ya ɗage daga ƙasa ya nausa sama zuwa birnin Lagos, Nigeria.

Motocin sojojin da ya hango ya tabbatar masa nasu ne, su ma suna ganinsa suka yo kansa suna sara masa. Khairy da ke manne jikinsa ya ja zuwa motar da zai shiga, bayan ya saka ta shima ya shiga, kayayyakin su kuma sauran motocin ne suka kwaso su.

Bayan kwana biyu da dawowarsu suka wuce Adamawa, kowa yayi farin ciki sosai ganin yadda ma'aurantan suka yi kyau suka yi ɓulɓul alamun dai akwai hutu da zaman lafiya cikin rayuwarsu. Nan labarin zuwan pretty ya riske su, ita dai khairy tayi mamaki saboda kwanakin baya in ta tambaye shi ina take baya nemanta sai yace ta ƙyale shi gashi ira kuma tsoron a tauye haƙƙin wani tana gani take yi amma babu yadda ta iya.

Nan take tambayar granny dama Prettyn tayi tafiya ne? Granny ta washe baki tace “Yo shaiɗaniyar ai dole ta tafi gidansu, ai tun kuna nan Maza ya bata takardarta saboda laifukan da tayi ta aikata masa, ta zubar da ciki ta sa aka sace shi don ma Allah yaso kina nan kika yi yadda aka yi ya dawo. yo ai ko bai sake ta ba Ni sai na sa ya sake ta akan hakan. Gafalalliyar ƴa, ke dai Ummul Khairy ki nutsu ki yi wa mijinki biyayya ki zauna kayanki kinji ko?”
Kai ta gyaɗa mata nan granny ta barta tana jimami, mutuwar aure ai ba wasa bace ko ta auren maƙiyi ne.

_Comment and share_
[27/09, 6:16 p.m.] Famanté 💎: https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““131””” *(Last page)*

A part ɗin Mom suka zauna tsawon sati guda saboda yana son musu sallama zai wuce Canada tare da khairyn har sai bayan 3years kuma su dawo.

Ranar da zasu tafi kuma pretty ta dawo da Baby Humairah. Ta nemi yafiyar Hamma Zaki Nan ya nuna mata babu komai dama shi yace ya yafe mata tuntuni. Tayi kuka sosai a nan ta sanar da shi ai Daddynta yana prison, ashe bayan tafiyarsu Niger ita da Mami aka kama su red handed da safarar makamai, anci tararsu Daddy kam har gidan da suke ciki sai da aka karbe.

Sosai Hamma Zaki ya tausaya mata, nan ya basu wancan gidan da suka zauna da ita, daga nan ya amshi Baby Humairah ya danƙawa Mom ita daga nan suka wuce Lagos.

Suna zuwa suka gama ciku-cukun tafiyarsu Canada, babu jimawa ya kammala daga nan suka wuce.

_A gurguje_
Watansu takwas da tafiya Khairy ta dawo ta haifi ɗanta namiji mai kama da Hamma Zaki sak, ranar suna kuma yaron yaci sunan Daddy Muhammad, ana kiransa da Aman , bayan two months ta koma abunta tare da Baby Anan, sosai suke soyayyarsu sai son Barka.

*BAYAN SHEKARU UKU*

Wani kyakkyawan matashi ne da ya gama haɗuwa yake sauƙowa daga matakalar jirgin, biye da shi kuma wani kyakkyawan yaro ne da ba zai wuce 2-3years ba, kyakkyawa da shi kamar ɗan larabawa, sai kuma ga matashiyar mata a bayan yaron ita ma tana sauƙowa.

A wuri guda suka tsaya, sojojin da suka zo ɗaukarsu ne suka nuna musu hanya, Namijin ya ɗauki yaron ya nufi motar da shi. _Banana island_ convoy na motocin suka nufa, daidai gidan Hamma Zaki suka shige. Bayan sun dai-daita tsayuwar kuma Matashin ya fito ɗauke da yaron sannan ya buɗewa matarsa nata sashen ta fito. Fuska ta yamutsa, hannunta ya riƙe suka shige cikin gidan tare.

Tas gidan yake saboda yanzu akwai ma'aikatan dake kula su. Wanka suka yi suka huta tukun zuwa yamma Hamma Zaki ya nufi Barrack tare da certificate na karramawa da ya samu daga can, daga nan kuma suka barshi ya dawo, sati mai zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login