Showing 27001 words to 30000 words out of 135404 words
ƙauye ce” ta dakata tana wani fari da ido kamar wacce ke gaban saurayin ta.
Iya kam dariya tayi tana faɗin
“Yo Ni kam ai nan ne iyaka ta sai ƙauyukan kewaye, ban taɓa zuwa birni ba shiyasa naso ke ki tashi a can kinga wata rana sai ki kai ni”
Ta ƙarasa sounding serious.
Dariya Ƴar Iya tayi tace
“Iya kenan, to Aradu ƴan birnin nan mugaye ne barin ma masu baƙin kayan na, hegu kingan su ƙataye da su ammah sai da na basu kashi”
Ta ƙarasa tare da kaɗa yatsa.
Cike da ƙosawa iya tace
“Yanzu faɗa min suku ne Kika ce ko sumul?”
“Hhhh..... Kiji Iya wai suku😒😂, to ai ba haka ake faɗa ba, in Kika faɗa a gaban ƴan birni to dariya zasu yi miki” ta faɗa tana wani kaɗa kai ita ala dole ƴar birni.
“Toh ai sai ki gyara min yadda nima in na shiga maƙwabta zanyi musu su san Shalele na taje birni”
Murmushi Ƴar Iya tayi tace
“Ai kuwa, to Iya ai sukul ake cewa ba suku ba”
“Ayya sukwal”
“Hahhhh. Iya ba sukwal ba sukul”
“Ai to sukul”
“Yauwa Iya ta yanzu dai-dai kika faɗa”
Dariyar farin ciki iya tayi tace
“Toh shi sukul ɗin me yake nufi?”
Ta tambaya cike da ƙaguwa.
Sai da ta juya kai kafin tace
“Makaranta shine sukul ɗin”
Haka suka yi ta shirmen su yayin da cikin gari ya ɗauka ai Ƴar Iya ta dawo. Wasu na farin ciki musamman A'i wasu kuma har sun fara kuka da kansu.
★★★★★★★★★
*ALEE POV*
Bayan sun isa wurin da suka bar motocin su, kai tsaye suka shige tare da wucewa. Bayan sun isa waɗanda suka samu rauni aka miƙa su asibitin dake can for effective treatment yayin da Hamma Zaki yaƙi tsayawa.
Bai samu kunna wayar shi ba ko da bayan sun dawo, saboda haka ya kunna tare da ƙiran Joseph, cikin mintuna kaɗan Joseph ya ƙaraso yayi driving Hamma Zaki gida.
Tun kafin motar ta gama packing gaba ɗaya mutanen gidan suka iso wurin,p Mom da fuskar ta ke ɗauke da tsantsan damuwa da sauri ta shige gaba ganin Joseph ya buɗe mishi motar, cikin zafin nama taje tayi hugging nashi tana sakin wani irin kuka.
Zuciyar shi ce ta karye ganin yadda Mom ɗin shi ke kuka.
Granny ma ba a bar ta baya ba,
“Ku bani waje nagan shi don Allah, lafiya ƙalau yake ai koh?” ta faɗa tana Matsowa kusa da shi.
Ganin raunin da ya samu yasa jikin kowa yin sanyi. Nan take Mom tace su wuce Hospital, bai iya yi mata musu ba haka suka ɗunguma zuwa Hospital. Bayan an yi treating raunukan likita ya buƙaci su koma don yana buƙatar hutawa.
★★★★★★★★★
Yammacin ranar kuwa Ƴar Iya tayi wanka har da wanke baki da gawayi da kuma alimun, aka saka kaya masu kyau ita ala dole an je birni.
Ko sallama bata yiwa Iya ba ta fito abun ta tana taku tana yauƙi kamar wata kuɓaiwa. Kai tsaye gidan su Aminiyar ta A'i ta wuce, kafin isar ta kuwa duk wurin da ta gifta sai anyi gulmar ta wai Ƴar Iya taje birni baku ga har sauya tafiya tayi Baneh irin ta ƴan birni?.
Sai da suka sha hirar yaushe gamo da kuma labarin bayan rabuwa a nan A'i ke faɗa mata tsiyar da ƴan garin suke mata bayan tafiyar ta.
“Hmm ƙawata dai tunda kika sa ƙafa kika bar Gallara shikenan ƴan gari suka tsaneni,”
“Ban gane ba”
“Ina faɗi miki Aradu har duka na wasu suke yi wai zasu huce tsiyar da muka tsula duka a kaina”
Mamaki ne ya kama Ƴar Iya jin abun da ƴan garin suka yi wa Aminiyar ta kuma ta ɗaukar mata alƙawarin ɗaukar mata fansa.
Daga haka suka fice don yawata gari. Gulma ko ina Ƴar Iya annoba, Ƴar Iya mai hannun ɓarna ta dawo, wasu wurin kuma gulmar su bata wuce yadda Ƴar Iya ta sauya tafiya ba ga kuma kaya masu kyau da suka gani a jikin ta saɓanin da da sai tayi wata da kaya a jikin ta.
(Nace ah toh, don ma makaranta taje da ace wani gidan ƴan gayun taje da tafi haka).
A dai-dai wata corner suka ga wani yaro ɗauke da kaji a hannun shi alamun sayar da su zai yi.
Ƴar Iya kuwa murmushin mugunta tayi sannan ta dakatar da shi.
“Dauda ina ne zaka je haka a yammacin nan da kaji?”
Dauda da duk ya tsorata ya duburburce saboda ya san karon sun da Ƴar Iya mai hannun ɓarna ya fara magana cikin ƙiƙina.
“da...da...dama...innnn...innna ta...ce...ta..ta...ce..na..je ka...ka..kasuwa na..sa..sa..yar da...kajin...sai...na.auno...geron tuwa”.
Murmushi kawai tayi tace shikenan jeka abun ka ammah kace kada a ƙara aiken ka da kaji kaji ko?”
Kai ya gyaɗa daga nan suka bar shi ya wuce.
Nausawa cikin kasuwar suka yi still Ƴar Iya na kwalmaɗewa kamar wata kara tana ƙara gyara tafiya.
Dai-dai wurin Bala Mai kifi suka tsaya ganin lokacin yake soya kifin.
Fari Ƴar Iya tayi da ido sannan ta gaida Bala wanda take zuciyar sa ta fara wani irin bugu.
“Ina wuni mai kifi”
Cikin ƙarfin hali Bala ya amsa yace
“Ina wuni Ƴar Iya ya gida?, Kin dawo ashe”
“Eh wallahi mun dawo jiya da Yamma, akwai kifin ne?”
Ta faɗa tana ƙara leƙa kifin dake zube kan teburin.
Bala ya amsa mata da
“Eh akwai”
Ai da tunda suka zo bata ce uffan ba ta ce
“Mai zafi zaka saka muna”
Da “Toh ” ya amsa sannan ya jawo leda ya cika ta da kifi daga nan ya miƙa musu. Godiya suka yi mishi sannan suka ja ƙafafuwan su sai gidan Iya.
Bayan sallar maghrib A'i ta yi sallah a ɗakin Iya, don ita duk tsiyar ta tana yi ne idan mai tare mata tana nan kuma ba laifi tana bubbuga sallar ta duk da cewa ba yadda ake yi ba abun ku da mutanen ƙauye.
Kai tsaye gidan wata Halima suka shiga. Duk da cewa basu taɓa shiga gidan ba ammah haka Ƴar Iya ta jagoranci A'i zuwan cikin gidan saboda ta jiyo ƙamshin dahuwar da ke tashi ta jikin zana.
Ƴar Iya ce ta fara kwaɗa Salama
“Salamu Alekum, Salamu Alekum ga baƙin maghriba”
Halima da bata san waye ba ta amsa tana gyara murya da alamar a makewayi take.
Shigowa suka yi suka zauna kamar mutanen kirki a kan taburmar da ta shimfiɗa kusa da murhun.
Halima mace ce mai son gayu, fara ce kakkaura kuma ba ƴar cikin Gallara bane, daga Azare aka auro ta. Da yake tayi zama cikin birni kuma irin matan nan ne masu kutsawa cikin manya babu wahala ta san abubuwa da dama. Sana'ar ta a nan Gallara shine sayar da maganin mata iri iri kuma babu laifi ana siya saboda kowa so take ta zama gwana wurin mijin ta. Hakan yasa Halima ta saba da ƴan garin cikin ƙanƙanin lokaci, da wuya kazo gidan ta baka tarar da baƙi ba wasu sun zo ayi musu irin dahuwar nan ne wasu kuma siyan maganin mata suke yi.
Ɗaure da zani a ƙirjin ta ta fito daga makewayi tana kallon su Ƴar Iya da suka make a kan taburma tana aika musu kallon tambaya.
“Sannun ku da zuwa Ƴan mata”
“Yauwah sannu” Ƴar Iya ta amsa tana ƙara kame kanta wuri guda kamar ta ƙwarai.
“Bari na sako kaya sai nazo”
Bayan mintuna 30 sai ga Halima ta fito cikin wata koɗaɗɗiyar atamfa sai dai tas-tas take babu alamun datti. Tayi kwalliyar ta ta kuma shafa janbaki har da eyeshadow. KO ƙifta ido Ƴar Iya bata yi ganin irin adon da matar ta caɓa. Haka nan taji matar ta burge ta kuma tana son su ƙulla zumunci.
“Kuyi haƙuri ƴan mata na ɗan ɓata muku lokaci, wacce ce amaryar a ciki?” ta faɗa tana yin wani murmushi tare da zama kusa da su bisa taburmar.
Kallon mamaki Ƴar Iya ke bin ta da shi jin wai wacece amarya?. A'i da yake an riga an sanya bikin ta bayan tafiyar Ƴar Iya birni saboda dama tun kwanaki aka fara auren sa'annin su.
Sunkuyar da kai ƙasa tayi tace
“Nice, Ina wuni”
Murmushi Halima tayi tace
“Lafiya ƙalau ai na ɗauka wannan ce amaryar”
Ta faɗa tana nuna Ƴar Iya da yatsa.
Kamar ta Allah Ƴar Iya bata ce komai ba sai murmushi kawai take saki nace anya kuwa wannan murmushi babu biyu a ƙasa kuwa?.
Bayan sun gaisa tace
“Bari na sauƙe dahuwar nan don Allah, kema ya kamata ki fara shirin auren nan fa, in kin je gida ki cewa Innar ki ta fara shirya ki kuma ki ce mata ina gyara sosai da kuma bada magungunan mata masu kyau”
Caraf Ƴar Iya tace
“Gyara kuma na me?”
Halima da yake irin matan nan ne marasa kunya kuma babu ruwan su da yaro ko babba tace
“Bari na sauƙe na dawo”
Sauƙe tukunyar tayi tare da ɗaura wata tukunyar da alamar abincin dare zata girka. Wurin su ta dawo ta zauna sannan ta maida kallon ta ga Ƴar Iya.
“Yauwah Ƙawar amarya kike tambaya kan batun gyara koh?” kai Ƴar Iya ta gyaɗa tare da maida hankalin ta ga Halima.
“Toh kafin nan dai ya kamata na san sunan amarya da ƙawar ta ko?”
A'i tace
“Ni suna na A'i wannan kuma Aminiya ta ce Ƴar Iya, halan zaki ji ana labarin ta ko da yake mu ma kan mu bamu san ki ba a ƙauyen duk irin yawon mu”
Murmushi Halima tayi tace
“Yoh ai dole na san Ƴar Iya mai hannun ɓarna, ai naji ance ma taje birni, halan yaushe kika dawo?”
Duk irin tsiyar Ƴar Iya da yake nema take bata ce komai ba sai ma murmushi da tayi tace
“Jiya na iso, ammah nima na kusa yin auren ai tunda ƙawa ta zata yi, sai dai ina son ki min bayani akan gyaran da kuma maganin mata da kike magana a kai”
Halima ta gyara zama tace
“Babu damuwa zan miki bayani kamar yadda kika buƙata sai dai bari na kammala girka mana abinci muci, idan muka yi sallah sai mu fara bayanin don zamu kai zuwa gobe bamu gama ba. Tunda mai gidan baya nan ai zaku jima koh?”
Gyaɗa kai Ƴar Iya tayi haka nan A'i ma.
Halima ta tashi ta gyara wuta ganin ruwan ya riga da ya tafasa yasa ta wuce ɗaki ta ɗauko taliyar murji mai ɗan yawan gaske, zubawa tayi a tafasasshen ruwan daga nan ta gauraya da muciya.
Har taliyar ta dahu cikin su babu wadda yayi magana, da kan ta ta kwashe taliyar cikin matacin ta na ƙarfe.
Sai da ta soya manja ta ɗauko yaji sannan ta fito. A tray ɗin silver ta juye duka taliyar sannan ta saka musu manja da yaji, nan aka hau taliya aka cinye ta tsaf.....
(Masoya littafin Ƴar Iya ina matuƙar godiya da irin haɗin kai da kuke bani ta hanyar suburbuɗo comments don ƙarfafa min guiwa.
Ina godiya sosai ƙawayen Ƴar Iya, su AMEERAN MAMA, HINDATU HASSAN, da sauran da ban ambace ku ba, ina fatan samun haɗin kan ku har abada, Allah ya bar ƙauna.
ME KUKE TUNANI GAME DA ALAƘAR HALIMA DA ƳAR IYA?
MENENE DALILIN TAMBAYAR ƳAR IYA GA HALIMA?
SHIN WANE IRIN SALO NE ƳAR IYA TA DAWO DA SHI GALLARA?
MU HAƊU DA SAFE IN SHA ALLAH DON JIN CIGABAN LABARIN.
DUK AMSOSHIN KU NA TARE DA ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎, KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMI NA DON YANZU NE ZA'A FARA WASAN!
TAKU HAR KULLUM, DIAMOND LADY 💎
[5/5, 7:13 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __
SHAFI NA ‘‘‘‘‘29&30’’’’’
*ALEE POV*
Ana kaishi asibiti kuwa aka fara bashi kulawa, kwanan su ɗaya suka koma can gida da shi saboda yadda Ƴan jarida suke sintiri a bakin asibitin, ga kuma mutane kamar tururuwa safe, rana yamma, dare basu bar asibitin ba.
Kulawar da ya samu yasa cikin two days ya warke sumul da yake dama ciwon a iya jiki ne zuciyar na nan ƙalau.
Kowa nan da nan yake da shi kamar wani ƙwai, duk irin yadda yake takurawa ƙannen sa hakan bai sa sun gajiya wurin yi mishi addu'a ba. Musamman waɗanda suke jin kaunar shi daban cikin zukatan su.
Ɓangaren kulawar nan ba'a bar kowa baya ba, Granny, ƴaƴan ta, jikokin ta da sirikan ta musamman Nenne ga kuma Sarah da itama take iyawar iyawar ta, Allah these ko Allah zai sa Hamma Zaki ya so ta ne.
Ƙira kuwa ta ko ina, wasu na ƙiran Mom wasu kuma Daddy yayin da wasu ke ƙiran wani daga cikin ahalin suna tambayar jikin sa don tuni labari ya karaɗe Nigeria ta ko ina zancen ake.
In ka hau facebook, IG har da Tiktok kowa abun da yake wallafawa a shafin sa kenan. Dr. Faruq ne yayi Video ɗin a lokacin da suke kan aiki. Ai kuwa a ranar da suka dawo ya wallafa Video ɗin a shafin sa na Facebook, Instagram, Twitter, YouTube, da sauran su. Kafin kace me kowa sai tofa albarkacin bakin sa yake. Kowa na yabawa wannan zarton matashi da yake aikin sa babu ƙakkautawa.
Comments ɗin wasu kuma bai wuce kan yanayin shi ba, wasu na faɗin wannan ai baindiye ne irin waɗanda ake nuna su a indian film ɗin nan. Ashe dai da gaske akwai masu irin ƙarfin nan. Kowa dai da abun da yake faɗa, ƴan uwa mata kuwa santi ne kawai ke jansu.
Videon nan fah tun da mata suka gani suka rikice, su ba jarumtar shi ce ta burge su ba kaɗai siffar shi kawai ita taja hankalin su.
Daga nan batun zai fara, Ƴan mata a ko ina a faɗin ƙasar mu Nigeria burin su yanzu bai wuce su mallaki wannan Lion ɗin ba. Ga kyau ga kuma jarumta.
Tuni ƴaƴan mommy da Daddy (Ina nufin ƴan gayu, shagwaɓaɓɓu ƴaƴan manya) suka fara yiwa iyayen su daru su fa ga wanda suke so, sun ji sun gani in Babu shi ba zasu rayu ba.
Ana wannan drama ne kuma hukumar sojoji ta ƙasa ta shirya gagarumin bikin cin nasara da suka samu bisa jajircewar Commander da ya jagoranci aikin wato Hamma Zaki.
Flyer na taron ma kar ku so kuga yanda yake trending a yanar gizo. Ai kuwa mata fa sunyi shiri tsaf don halartar wannan taro kowa da irin tata aniyar don jawo hankalin samɓalen saurayin nan.
(Wannan kenan, nimah gaskiya na haɗa sabbin kaya na don ina so nimah nasamu matsuguni a zuciyar Hamma Zaki na).
*ƳAR IYA POV*
Bayan sun samu cinye taliya da manja kowa tasha ruwa aka wanke hannu.
Halima tace “Toh sabbin abokai na, da farko zan fara amsawa Ƴar Iya tambayar ta.” tayi shiru tana maida duban ta ga Ƴar Iya.
“Tabbas akwai gyara na musamman da ake yiwa amarya idan zata yi aure. Wannan gyara kuma ana yin sa ne dai-dai al'adun kowa. Gyaran nan na da matuƙar muhimmanci musamman saboda shi kanshi ango ya son amarya tayi, yana don ya ji ta daban. Ana gyaran jiki, tun daga fuska zuwa ƙafa, gyaran gashi da kuma sauran gyararraki.
Kin gane, misali da zan baki yanzu saboda baki kai ɗaukar bayanan ba shine, kamar ke yanzu in Zaki yi aure, ni da kai na zan gyara ki fes, kinga fatar nan taki da gani Allah ya zuba mata kyau da haske datti ne kawai ya ɓata ta, To zan gyara ta ta koma fes da ita irin ta ƴan gayu ko ba komai ango ya gani zai yi mamakin hakan.
Sannan wannan bakin naki ma da kike gani in Zaki yi aure tas zai koma in yasha gyara ....”
Haka Halima ta fayyace musu gyaran jiki da ake yi.
“Sai kuma batun maganin mata, ku da yake ƙananan yara ne ba zaku fahimta ba amma dai zan faɗi muku abu kaɗan”
Halima ta faɗa musu batun sex idan anyi aure tare da muhimmancin da ayyukan waɗannan magungunan matan.
Daga haka suka koma normal hirar su. Ƴar Iya tace
“Oh Ni Halima kika ce za'a iya gyara baki na?, To da me za'a ke gyara shi?”
“Ƙwarai Ƴar Iya Tun yanzu ma ki fara,idan kika samu gawayi, ko don ashe ku da kara kuke girki, to in kun tashi tafiya ga gawayi a nan sai ki tafi da shi.
Ki daka gawayin nan da gishiri da kuma lalle, sai ki daka kanunfari da kuma alimun ki haɗe da wannan dakakken gawayin, kullum sai durje bakin ki, ina tabbatar miki bazaki jima ba zai koma fes kamar farin wata”
Sai da dare ya fara duka suka yiwa Halima sallama tare da alƙawarin zasu ke shigo mata.
Ɓangaren Angel Ƴar Iya kam ba'a magana, haka kawai taji tana son yin sana'a cikin ƙauyen, tou yanzu tunda an mata bayani kan maganin mata shi ta yanke zata fara siyarwa ba tare da ta san menene da menene constituents na maganin matan ba.
Sassafiya kamar kullum Ƴar Iya ta tashi, bata, tana miƙewa ta fito daga bukkar ta, bata tsaya ko ina ba sai wurin kiwon Baffi, kashin shanu ta tsinta akan faifayin busa, ta hau kan turmi ta ɗaura shi bisa bukka.
Tana ɗaurawa ta diro tare da ɗaukar langa ta fice abun ta. A dai-dai gonar wani mutumi da yake kiwon tumaki da awaki ta tsaya. Ciki ta tsallaka saboda an riga an kewaye wurin da fence. Sai da Ƴar Iya ta kusa cika langar nan da kashin tumaki da awakin nan ta fito abun ta.
Gida taje shima ta ɗaura shi a sama daga nan ta ƙara fitowa, wannan karan ciyawa taje ta tsigo a buhu, ta sanya ta kamar yadda tayi wa sauran abubuwan.
Gidan su A'i ta wuce suka fita yawon su. Suna fitowa Ƴar Iya tace wa A'i
“Ke A'i yau kwaɗayin mangwaro da kashu nake yi, muje lambun Baba Haro mu ciro”
Bata Musa ba su ka ɗebi ƙafafuwan su suka wuce lambun Baba Haro. Sun ci Sa'a kuwa kamar baya nan har da murnar su don sun riga sun san Bala'in wannan tsoho, don duk maitar ka ko zata fito tayi rawa ba zai bayar ba.
Sai da suka kewaye ko ina suka