Showing 78001 words to 81000 words out of 135404 words

Chapter 27 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46365

kyau suke duk da akwai yaro ma, amma ki ga Hamma Zaki, miskilamcinsa ma kullum karywa yake” ta karasa hawaye na silalowa daga idanuwanta.

Khairy ce ta goge mata hawayen cike da kulawa tace “I'm sorry sister, Allah yana tare da my haka Hamma Zaki ma, addu'a kawai zamu ke yi masa ok?” kaibta gyada khairy tace “Now babes to work, mu gyara parloun nan irin wanda baa taba yimasa ba”
“Yea” suka hada baki tare da fara tattare parloun.

Mintuna ashirin suka bata kafin su kammala gyara parloun, “wato tsafta tayi a rayuwa” Yesmeen ta fada tana mika. “Gaskiya da sakyal babes, mu huta please”. Har zuwa lokacin pretty bata fito ba bare suyi tsammanin gaisawa da ita, wannam dai matsiyacin kallon da kuma tsakin tana nufin sune tarbarsu. To Allah ya kyauta.
Kallo suka kunna suna dan tadinsu, idan aka yi wani abu da ya burgesu sai sun tsaya sun magantu.

A bangaren pretty tun juyawarta ta haye upstairs tana sakin tsaki. Zama tayi bakin bed tana fadin “Allah na gode maka, nayi zaton ma iyayensa ne ashe wadannan masu siffar aljanun ne” tsaki tayi tana fadin “Amma wacece wannan matashiyar?” ta tambayi kanta tana mai daga kai sama alamun tunani. Can kamar wacce aka tsikara tace “Oh!!! Wannan wannan yarinyar da na taba zuwa na samu kakarsu na nan da nan da ita ne!, to wacece?” ganin babu mai bata amsa yasa ta jawo wayarta tana fadon “I'll ask sweetheart in ya dawo” daga nan taci gaba da tadinta ba tare da tuna cewa tayi baki ba talkless of ayi musu girki.

Kallonsu suke hankali kwance har wajajen Karfe biyu, yunwa ce ta fara dawainiya da khairy, kalkon yan uwanta tayi tana fadin “Babes i'm hungry!, wollah ba alamar zamu samu wani abu a gidan nan muje kawai mu samarwa kanmu abun tabawa”. Su ma duk yunwar ta ishesu dama shiyasa suka mike suka nufi kitchen. Mamaki ne ya kama su ganin kamar baa taba amfani da kitchen din ba, komai kura ga uban plates zube a sink. Basu fara girkin ba sai da suka tabbatar sun gyara ko ina, plates ma tsaf suka tsaftace su tukun suka hau kan girki.

Hadaddiyar fried rice suka hada wacce kamshinta kadai mai karatu ya samu a matsayin rabo to ya gode Allah, sai chicken pepper, Sai kuma Tigernut drink da kana gani zaka fara hadiyar miyau.

Cikin tsadaddun food flask suka zuba fried rice din sannan suka saka shima chicken pepper din, daga nan suka zuba tigernut drink din duka nufi dining, isarsu kenan suka zaro idanuwa. Khairy tace “Tab! Sunan wani abu wai shi badakala” babu yadda suka iya dining din ma sai da yasha dusting.

Sauran suka debo suma suka ci, kiraye kirayen sallar asr yasa suka yi alwala, a parloun suka yi sallah. Ita dai khairy hamshakiyar take jira ta fito tasan dole zata nemi abin tabawa. Ai kamar ta sani ashr tunda suka fara girkin kamshi ya cika mata hanci, tunani take ko daga ina?, tunawa da kannen mijin nata da ta manta da zuwansu ma yasa tace laalla sune, tana lashe baki ta fito daga dakin, sallar ma bata samu damar yi ba. Downstairs ta nufa ai tana fara taka steps din bata san me ta taka ba taji ta a kasa yarrrrrr. Wani mahaukacin ihu ta saje tana fadin “Na shiga uku shikenan nikam na karye, wayyo sweetheart ” cike da jin haushinta suka saka dariya kamar zasu yi kuka yayinda ita kuma take famar ihu tana ta shiga uku.

Sai da suka yi mai isarsu tukun suka je gareta, bs tare da sunce komai ba suka ja ta zuwa sama har zuwa dakinta, khairy ce tayiwa Ayra alama da ido ita kuma suka daura pretty kan gado daga nan suka dawo parloun ba tare da sunce mata uffan ba.

Suna zaune a parloun yayi sallama, kamar koyaushe cikin uniform da suka mugun karbi jikinsa. Cikin takunsa na kasaita ya shigo. Sunkuyar da kai suka yi suna gaida shi a tare. “Ina yini Hamma Zaki ”
Can kasan makoshi yace “Lafiya” yana bin parloun da kallo, cikin ransa kuma tunani yake “Waye ya gyara parloun? ” yasan dai ba pretty bace, “then who?” ganin yana tsaye yasa Fauzah yin gyaran murya tace “Hamma ga Abinci a dining. Bai ce uffan ba itama bata yi tsammanin zai fadi ba, cike da takama ya fara takawa zuwa sama. Wanka ya fara yi ya sanya wasu ligjt blue pyjamas sannan ya fito.

Ba tare da ya kallesu ba ya nufi dining din don dama yunwa yake ji rabonsa da abinci tun daren jiya da yaje gida. Sanin ko a gida mom ke serving dinsa yasa fara mikewa taje ta zuba masa komai daga nan ta dawo wurin zamansu. Bayan yaci na plate din sai da ya kara kadan tukun ya goge bakinsa da tissue, tigernut drink din ma ya sha sai dai ba zaka iya gane yanayin fuskarsa ba.

Sama ya kara komawa ba tare da ya kara kallonsu ba, bedroom din pretty ya shiga da niyyar nuna mata kuskurenta na wulakanta danginsa don ranar da Hamma Salim da matarsa Aunty Waheeda suka zo haka ta musu. Fuska daure ya shiga, ganinta kwance yasa ya karasa wurinta. Cike da shagwaba ta fara magana “Oh sweetheart sai yanzu ka dawo, wallahi yunwa nake ji kamar naci babu, kaga naji kamshin girki inaga yan uwanka ne suka yi sai da naje ci nayi missing step na fadi, sweetheart duba kaga har ya kumbura” fuska daure ya duba ganin bai ga komai ba yasa yace “Nabila!, Nabila! Nabila! ” dagowa tayi tana kallonsa tasan babu wasa “Sau nawa na kira sunanki?” a shagwabe tace “Uku sweetheart ”
“Gargadi a karo na karshe ki daina wulakanta yan uwana idan sun zo in ba haka ba kuma zan baki mamaki” daga haka ya fice ya barta. Downstairs yq sauko yana nufi wurinsu. Cikin dakakkiyar murya yace “Yaushe zaku koma”. Khairy da ta gama kosawa da gidan tace “Yanzu muke son komawa”. Minti biyu tukun yace “Ku bari kuyi sallah sai mu wuce tare” babu yadda zasu yi haka suka zauna suna jiran in anyi sallar sa wuce amma sun kosa.

Ita dai khairy haushi yau dinnan ya bata duk da cewa ba don shi suka yi hakan ba amma atleast ya kamata yayi appreciating effort dinsu, cikin ranta tace “Har da zama ya kwaahi girkin bayan ko nuna yaji dadi bai yi ba”

(Nidai ina gefe nace khairy so kike Hamma Zakin yayi ta washe miki baki yana fadin ya gode???).

*COMMENT & SHARE PLEASE*


[29/08, 2:36 PM] 💎Diamond_Bhatool💎:

🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““79&80”””

Bayan sunyi sallah Hamma Zaki ya shigo alamun daga maajid yake, da ido yayi musu alamun su tashi, thank God kowa yayi sallah hakan yasa suka fito dukkansu.

Shiga suka yi cikin sauri kamar wani zai riga su, Fauzah, Ayrah da Yesmeen suka shige gidan baya, isowar khairy kamar zata yi kuka ta shiga gaba amma ta shirya yi musu rashin mutunci idan suka isa gida.

Maimakon ya nufi gida Shopping Mall ya mika su, suna isa yace musu “10 minutes na baku ku fito, take this” ya mikawa khairy ATM card dinshi. Basu kai 10minutes din ba suka fito daga nan suka wuce gida zuciyoyinsu wasai don tuni sun mance da iya shegen da aka tsula musu a can.

Bayan ya daidaita parking suka fita suna masa godiya. Da gudu khairy tayi part din granny.
“Ina kike ne granny ta”
Cikin sakin fuska granny tace “yar albarka sai yanzu, aah wannan kuma fa?” granny ta tambaya tana mai kai dubanta ga ledar dake hannun khairy. Murmushi tayi tace “Granny Hamma Zaki ne ya kaimu muka yi shopping, kema na siyo miki naki. Nan ta fito da turaren daki da na jiki da ta siyowa grannyn. Murmushi granny tayi tana fadin “Allah yayi albarka, madalla madalla ummul khairy ”. Daga nan ta kwashe sauran ta kai bedroom dinta. Bata san lokacin da ya shigo ba coz bacci ne ma ya dauke ta.

Hamma Zaki tunda ya koma gida bai kuma leka bangaren pretty ba don mugun haushinta ma yake ji. Ko da yayi wanka ya kwanta baccin ma kin zuwa masa yayi, banda tunanin wannan muryar babu abunda yake, ya kasa tantance wacece cikin yaran nan ta kira shi. Lokaci daya kuma zuciyarsa tace “Khairy! Ita kadai granny zata iya bawa wayarta, Amma gaskiya muryarta akwai sanyi ga nutsuwa” ajiyar zuciya yayi yace “Su suka gyara parloun sannan suka girka abinci mai dadin nan, kai gaskiya yau kam na kara yabawa tarbiyyar gida, see how kananan yara suka gyara waje amma wannan katuwar sai ci da chat, mtss”
Wata zuciyar kuma tace “Tabbas Dr. Farouk yayi gaskiya, zan kara aure amma fa bazan auri wacce ta gama wayewa ba, naga ishara” daya zuciyar tace “To wa zaka aura kai da baka san soyayya ba bare ka taba yinta” amsa dayar ta bayar da fadin “Ai ba sai anyi soyayya ba kawai dai in tana sona fine” wata zuciyar tace “To wacece?” amsa dayar ta bashi da “I dont know”
Ganin tunani zai haukata shi yasa ya kunna wayarsa yana duba messages nashi.

Washegari duka yan matan suka taho part din granny kamar yadda suka saba a yanzu. Tare da granny suka baje dandalin hirarsu. Fauzah kuwa tas abunda ya faru gidan Hamma Zaki sai da ta fadawa granny, nan fa hau fada da masifa sai da ta gaji tayi shiru don kanta, abunda suka so kenan dama. Bayan ta tafi khairy ta kalli Ayrah tace “Mutuniyar basu san fa me muka yi ba!” tafawa suka yi Ayrah tace “Me kika yi dai, ni ai taimaka miki nayi” dariya khairy taui tace “Ai duk da haka kinyi participating a ciki dai” ta karasa tana daga mata gira. Cike da kaguwa Yesmeen tace “Kunga kun samu a duhu fa, ku fada mana me ya faru”
“Ai kam” Fauzah ta fada.
Dariya suka kara yi suna tafawa. Khairy tace “Kai babes kunsan nace sai mun rama duk tsiyar da aka yi mana idan muka je, do u know what?” kai suka jijjiga
“Bayan mun gama gyaran gida munyi girki nasan kamshin ya isa hancin wannan fifgaggiyar Aunty Nabilar, sai da na fakaici idonku na watsa morning fresh a staircase shine fa da ta fito ta wuntsilo” dariya dukkansu suak saka can suak tsagaita.
Fauzah tace “Wallahi kin kyauta kuwa, wannan shegiyar maganinta ke ce, ashe har yanzu yar iya kike” ta fada tana dariya. Khairy ma dariyar tayi tace “Ai abun a jini ne, wollah da ace gida daya muke da ita da taga tsiya”. Idanuwa suka hada su uku sannan suka kwashe da dariya. Kallon mamaki khairy ke binsu da shi tana fadin “Meye kuma ”
Kamar hadin baki suka ce “In tayi tsami zata fito kiji”

Nan suka yi son ransu daga bisani duk suka wuce bangaren su. khairy dai littafanta ta fitar tana biyawa har lokacin lunch.

Ranar monday ne su khairy aka je competition din da ta wahalar da kanta a kai. Alhamdulillahi kuma an samu nasara dob har award school nasu ya samu. An karrama ta ranar a gaban assembly, sosai taji dadin yadda bata bawa malamanta kunya ba, haka a musabaka ma da aka yi na daya tazo a hizb 50, su ma su Ayra daga na biyu sai na uku.

Sun yi farin ciki sosai da wannan nasarar, kowa sai son barka. yanzu gabadaya hankalinsu ya koma ga shirye-shiryen WAEC da NECO suke a daya bangaren kuma shirin saukarsu suke yi.

Cikin nasara kuwa suka kammala WAEC & NECO sai kuma jira result, meanwhile, abubuwa sun faru ciki harda haihuwar Adda Najma da Adda Salma, anyi shagalin suna lafiya kuma Babes fa sun sha kyau a ranakun sunan da suka kasance mabanbanta. A nan ne kuma Fauzah da Ayrah suka yi catch, da farko basu biye su ba sai da su Yesmeen suka saka su gaba tukun suka yarda, Khalil wanda brothern mijin Adda Salma ne kuma ya kammala karatunsa aiki ma yake yi a Dubai, da kyar ya samu amincewar Fauzah, sai kuma Ishaq btothern Mijin Adda Salma ne, shi kuma a nan yola yake aiki a katafaren companyn mahaifinsa.

Su da suke ki sai gashi yanzu sunfi kowa so, Allah Allah suke daddy ya saya musu waya su huta da satar wayar granny suna waya da masoyansu. Su dai Yesmeen da Khairy nasu ido ne.

A cikin hutun nan ne kuma khairy ta je Gallara, a nan ta riski labarin mutuwar Inna Zaliha wacce sai da ta sha jinya a gidansu don tuni Baba ya sallame ta, satinta biyu ta dawo.

Dawowarta ne kuma abun farin ciki ya samu, pretty ta samu juna biyu, ganda ta karu, ga shegen fi'ilin tsiya da ta samo.

A yau Laraba suna zaune suna hirarsu kamar koyaushe Hamma Zaki ya shigo, duk irin yadda zuciyarsu shi da Khairy ke bugawa sai suka meze, gaidashi suka yi ya amsa daga nan Granny ta fito. Sun dadr suna hira kafin yayi mata sallama ta koma bedroom dinta. Har lokacin su khairy na nan suna hirarsu. Can kasan makoshi yace “Kai kuzo” Yesmeen kadai taji yayi magana sai ta rada musu. Addu'a auke Allah yasa ba laifi suka yi masa ba.

A gabansa suka durkusa suna fadin “Gamu” kamsu kuma na kallon kasa. Sai da ya share 3minutes kafin ya janyo ledar dake gefensa. A hankali ya zaro wayoyin kirar Iphone 14 guda hudu, Daya bayan daya ya bawa kowaccensu. Karba suka yi cikin ransu kamar su tashi su taka amma ba hali.

Kamar baya son magana yace “Ba an baku waya ba kuma, bana son rawar kai, banda tara numbers din samari kunji ko?”
A tare suka ce “Munji Hamma, Allah ya saka da alkhairi ya kara bude”
Cikin ransa ya amsa daga nan ya mike yana nufar waje, har ya kai bakin kofa ya dawo yace, “Ke!” ganin ita daya ce a wurin su sun koma wurin zamamsu yasa ta dago kyawawan idanuwanta tana kallonsa yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Mikewa tayi ta nufi wurinsa tace “Gani”
“Idan granny ta tashi kice ta fada miki sakona” daga haka ya tasa keyarsa gaba.

Kafin Zuhr kuwa sun saita wayoyinsu komai zam, duk social media handles kowa sai da ta bude account, don a cewarsu ba zaa yi babu su ba.

Bayan granny ta tashi ne take sanar da ita wai zata koma gidan Hamma Zaki tana taimakawa matarsa da aiki saboda cikin dake gareta. Babu yadda ta iya amma ranta bai so ba saboda zaa raba ta da ababen kaunarta wato babes.

Kamar yadda granny ta fada mata tare dasu Fauzah suka hada kayan Khairyn cikin trolley, da daddare kuwa sai gashi yazo. Da zai koma auka wuce da Khairy.

Tun a parloun ta fara tsinewa kazanta irin ta matar gidan Cikin ranta, in banda karni babu abunda yake tashi. Shima ba iya zaman zai yi ba yasa ya nuna mata daki.

Itama bata ce komai ba ta nufi daki, karkadewa tayi sannan ta wanke toilet daga nan kuma ta janyo wayarta. Ba ita tayi bacci ba sai wajajen 1pm bayan gama latsa wayar da tayi cike da annashuwa da farin ciki.

Washegari ko da tayi sallar asuba bata koma ba don aikin dake gabanta yana da yawa, ta kudiri cewa zata yi aiki kam amma wallahi sai ta saita matar gidan. Parloun kasan ta gyara fess kamar ba shi ba, duk kurar nan babu ita, ta feshe parloun da room freshner daga nan kuma ta wuce kitchen. Ba ita ta gama gyaran kitchen din ba sai wajajen 9am, har lokacin kuna masu gidan babu wanda ya fito. Ko da ta gama gyarawa sai ta daura breakfast daidai yadfa zai ishi dukkansu. Tana gamawa ta jera a dining daga nan ta koma bedroom dinta ta shiga wanka, wata Black atamfa mai flower green da ja, dinkin doguwar riga fitted ta sanya wanda tuni ya amshi jikinta, cikakkiar surarta ta bayyana kamar ka sace ka gudu. Powder da wet lipa kawai ta shafa daga nan ta fito don zuwa ta tayar da majiya dadin.

A hankali take taka steps din har ta iso jerin dakunan da bata san wannene nasa da matar tasa ba, har ta kai hannu zata yi knocking sai ta fasa ta wuce na gaba, knocking tayi daga ciki ta jiyo muryarta tana fadin “Yes come in”
A hankali ta murda handle din ta shiga, wani irin karni ya ziyarci hancinta tuni ta fara yamutsa fuska, dakewa tayi ta karasa gaban bed din tace “Madam, breakfast is ready” sai a lokacin pretty tasan wanda ya shigo don duk tunaninta sweetheart dinta ne.
“Kan uba!” ta furta tana tsirawa Khairy ido, ganin irin kyan da yarinyar ke da yasa taji ta tsaneta. Har khairy ta kai bakin kofa taji muryar pretty na fadin “Uban waye ya kawo ki gidana?”
Murmushin da ya karawa fuskarta kyau har sai da dimples dinta suka lotsa tayi sannan tace “Dan uwana mai gidan shi zaki je ki tambaya, mtss”

Daga haka ta fice, a harzuke pretty ta mike tana nufo Khairyn wacce ta riga ta fice ma daga dakin. Matar da bata iya komai sai gashi ta biyo wata fa gudu.

Khairy kuwa bata damu ba ta cigaba da tafiyarta cikin takunta mai daukar hankali. Pretty kuwa bata hakura ba saboda ganin takun da yarinyar ke yi kamar da gayya yasa ta bi bayanta har ta sauko daga steps din ta shige dakinta tana rufe kofar, wani banzan murmushi tayi tace “Wallahi sai nayi maganinki Auntu Nabila”.

Isowar pretty kuwa ganin parloun a tsaftace kamar na shi ba yasa ta furta “Wow!, ko dai munyi mai aiki ne?” kamshin girkin da ya nugi hancinta yasa ta leka dining area, ganin abinci a jere yasa ta yunkura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login