Showing 105001 words to 108000 words out of 135404 words

Chapter 36 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46360

ɗanyi hira kaɗan kafin ya sanar da ita cewa shi da son ta yake amma da aure, caraf Abulbashar yace “Nimah haka” ba tare da sanin ya faɗa ba. Murmushin takaici tayi cikin ranta tace “Guys kun makaro, don har an sa min rana”. Jin shirun yayi yawa yasa Abulbashar tunanin ko ya ɓata mata rai hakan yasa ya ce “I'm sorry Sister, ban san na faɗi ba.” wani murmushi ta ƙara yi tace “La babu komai, na gode sosai da ƙaunarku gare Ni, Allah ya ƙaunace ku fiye da yadda kuke ƙauna ta” da “Amin suka amsa kowa na fargabar amsar da zata fito daga bakinta, Prince na addu'ar Allah yasa ta so shi, shi kuma Abulbashar na addu'ar Allah yasa ta zaɓe shi.

“Dukkannin ku babu na jefarwa duk da yau na fara ganin ku but i guess Ku ɗin mutanen kirki ne, sai dai zan sanar da ku cewa akwai shamaki tsakanin mu don nima an saka rana ta kamar dai yadda aka saka wa ƴan uwa na.” dumm gaban su ya buga amma sai suka yi murmushi tare da saka albarka suna masu juyayin rashin cikakkiyar mace kyakkyawa kuma wayayya irinta.

Bayan sun tafi ne Suke ce tambayarta wane events da wanne zasu yi?, amsa ta basu da “Ni Babu fa” tabbas sun fahimci ba son auren nan take ba kamar yadda su suke yi, sai suka fara lallashinta nan kuma ta ɓarke da kuka, to dama me neman kuka ne aka jefe shi da ɓawon gyaɗa (Allah ya sa dai-dai nayi Hausar).

Allah sarki Hamma Zaki a ɓangarenshi shima ya mugun damuwa da wannan aure da za'a yi masa, in ya tuna zaɓin iyayensa ne kuma sai ya sanya albarka kawai. Abun da ma yake mantar da shi shine shiryawarsa da matarsa, duk da ba zai ce yana jin son ta a ransa ba amma dai yadda take nuna concern ɗinta a kanshi yasa yake matawa da batun auren.


**********************

*A GURGUJE*

Rayuwar ta ci gaba da tafiya yadda ya kamata tsawon wata ɗaya, tun ranar da aka sanar da ita batun aurensu bata ƙara bari ya ganta ba duk da shi kanshi yana son ganinta at least zai ɗan ji relief akan yadda yake ji.

Biki ya rage saura watanni biyu, Daddy da kanshi yayi booking musu Flight zuwa Bauchi, sannan ya ba wa Hamma Zaki key na katafaren gidan shi dake Bauchin so that in sun isa sai ya ɗauki one of the cars there su ƙarasa.

Duk gidan in ka cire iyaye mata sai da suka yi mata rakiya zuwa airport, shi kuma Hamma Zaki Pretty ce tare da baby Humaira suka kawo shi, daga nan suka juyo suna kewar Khairy da ta zama wani sashe na jikinsu, haka pretty ma ta juya da motar tana kewar mijinta don yanzu babu laifi komai normal normal zata ce. Ko da suka shiga jirgin bayan gaisuwa babu abunda ya haɗa ta da shi duk da cewa seat nasu maƙwabtan juna ne, kowa tunanin abunda ke damusa kawai yake yi.

Bayan sun isa ya ƙira Attahir, the governor's son Wanda shima abokinsa ne don ya miƙa shi gidan da Daddy yace su bi su ɗauki sayyarah!. Ko da ya miƙa su ma babu wanda ya cewa ɗan uwansa ƙala, to kowa ma da kalar tasa damuwar ina zai ke tuna na wasu?.

Ko da suka isa gallara ya sha mamaki ƙwarai da gaske, ba yau ya fara ganin ƙauye ba saboda tun bai kai matsayin da yake ba akan tura su idan akwai matsaltsalu amma a wannan karan, mamakin da yake shine dama anan Khairy ta tashi?, gaskiya ta ga rayuwa kam ga kuma irin ƙakubalen da ta fuskanta, ninki akan tausayinta da yake ji da ya rufe shi. Da taimakonsa da suka shigar da tsarabar da suka saya bayan isarsu Bauchi, sannan ta ja trolley nata. Har ta kusa shiga kuma sai ta juyo jin bata jin alamun mutum na biye da ita ba. Shi kuwa hankalinsa na kan waya don jira yake in ta shiga tayi masa iso.

Tsayar da trolley nata tayi tare da dawowa, “Hamma” ta ƙira sunansa cikin wata irin murya da ta sa babu shiri ya ɗago yana mata alamar ya dai?” ɗan kwaɓe fuska tayi tace “Mu shig mana” kamar ba zai ce komai ba kuma sai yace “No ki min iso kafin nan” hararar wasa ta jefa masa wacce bata san lokacin da tayi ba ita kanta, shi kuwa hakan ya matuƙar burge sa sosai har sai da yayi murmushin gefen baki.
“Don Allah ka shigo, iya Iya ce fa ina ga sai kuma Baffi idan ya dawo” ta faɗa a shagwaɓe, bai san lokacin da ya ƙara dubanta ba yana ayyana wasu abubuwan a ransa sai kuma ya ɗan kau da kansa gefe yace “Ok”.

Cikin ranta kuwa sai da tayi mitar amsar tasa wai ok, sai kuma ta juya, har ta isa ga trolley nata bai taho ba, sai kawai ta kawar tayi ciki.
Cike da girmamawa Iya ta tarbe su tana ta famar washe baki, ruwa ta kawo musu daga nan kuma ta ƙwalla ƙiran Nafisa ɗiyar ƙanwarta, bayan ta zo ta gaida baƙi Iya tace ta ƙira Baffi. Ko da bafffi ya dawo suka gaisa da Hamma cike da girmamawa, nan yake ce masa ai yanzu ma babanta zai dawo coz yayi aure kuma ya dawo kusa da Iyarsa tare da matarsa Hafsatu da ɗiyarsu Faɗimatu ƴar kimanin shekaru biyu.

Sai da suka huta tukun suka shiga ɓangaren Inna Hafsatu. Sun kuwa samu tarba mai kyau don kuwa dai ta nuna tsantsar kulawarta gare su. Cikin ran Khaibar kuwa tayi mamakin yadda Hamma ya sake har suke wasu da iya, tunda suke da shi bata taɓa ganin dariyarsa ba amma sai gashi yana yiwa Iya, Faɗinatu ma dai a hannunsa ya riƙe ta yana ta mata wasa yayinda ya bar Khairy da ɗumbun mamaki da al'ajabi.

Shi kansa ya rasa me yasa ya sake haka da wuri but ya jingina hakan da irin kulawar da ya samu daga khairi. Da dare yayi gidan sauƙar baƙi Baffi yaraka shi sannan yayi masa mu kwana lafiya. Washegari da safe kuma ya ɗau hanya saboda Khairy zata yi sati biyu ne kafin ta dawo.

Ko da ya koma Mom tayi masa magana akan lefen biki da yace ya je sun gana da matar da zai aura, yayi hakan ne ba don komai ba kawai sai don baya jin ya haɗu da ko ma wacece tunda ba Rouhy ɗin sa ba ce. Shawarar da ya yanke in anyi auren an kawo ta sa haɗu.

Tsawon satikai biyu kenan Khairy tana gallara. Kulawa ta na samu sosai daga wurin Iya da kuma Inna Hafsatu, gyara dai da suke yi wa amare a ƙauye anyi mata don cimarta ma sai da aka sauya mata.

Yau ta kama Khairy zata koma Adamawa wanda yayi dai-dai da satikai biyu to bikin ƴan matan. Sassafe ta tashi don haɗa kayanta amma Inna Hafsatu wacce take mata kallon uwa ta hana ta, a cewarta ita da kanta zata shirya mata. Bayan sun karya kuwa ta haɗa mata kayanta tsaf sannan ta haɗa mata da wasu abubuwan a matsayin kyauta, Khairy har da kukanta don sai a lokacin ne ma ta ji ina ma ace itama ta rayu da Innarta wacce ta haife ta. Iya ma ba a barta baya ba ta tanadi tsaraba ta musamman wa mutanen Adamawa, sai da ta zaga gida Arɗo da sauran abokan arziƙi tayi musu sallama, nan suka yi mata alƙawarin za su halarci bikin ta da izinin Allah tunda a can Adamawa ɗin za'a yi. Arɗo ma ya ware kayan gona irin su vegetables yace a tafi da shi wa mutanen Adamawa.

Sai wajen sha ɗaya na safe Hamma Zaki ya iso garin gallara don irin yadda Daddy ya azalzale shi tun jiya ya kwana a Bauchi, sassafe kuma ya kama hanyar Gallara. Ko da ya iso nono Iya ta dama masa ya sha kafin a fara loada kayan arziƙi da aka yi guzirinsu wa mutanen Adamawa. Tas aka shigar da su daga nan suka ɗauki hanya.

Sai bayan Hamma Zaki ya tayar da mota Khairy ta gaida shi, ya amsa mata yana ɗan nazarinta. Ba tsammani taji yace “Kuka kike yi don zaki koma?” kamar ba zata amsa masa ba sai ta ga rashin dacewar hakan kawai sai tace “Ba kuka nayi ba” murmushin gefen Baki yayi yace “Uhm, ke da zaki yi aure ma ai kuka ba naki bane yanzu” sai da Khairy ta zaro ido, cikin ranta tana faɗin “Dama Hamma Zaki ya iya magana haka?” bata dawo daga tunanin ba ta tsinkayi muryarsa yana faɗin “E mana na iya, sai dai in nayi da yawa yana sa min ciwon kai”
Tsabar mamakin da ya bata sai kawai ta saki baki. Da hannunsa na dama ya ɗan bige ta yace “Ki daina mamaki Ummul Khairy, duk ke kika jawo na zama mai surutu, yanzu kuma kinyi shiru, kiyi magana Please”

Kanta ta kawar ta ce “Hamma Ni kuma na koya maka surutu?”

_Share Please_

[15/09, 10:07 p.m.] Famanté 💎:



🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*









SHAFI NA “““107&108”””

Ba tare da ya kalle ta ba yace “E” jinjina kai tayi tana faɗin “Ai nima bani da surutu” ƴar dariya yayi yace “Kamar ban san ki ba?” shiru suka yi daga nan ya ƙara maida Hankalinsa kan tuƙin da yake cikin ransa yana jin wani farin ciki maras misaltawa. Tunaninsa kwacakom ya koma ga masoyiyarsa wanda lokaci ɗaya ya kamu da matsananciyar ƙaunarta ba tare da ya shirya ba, wani lokacin ya kwaɓe fuska kamar wani ƙaramin yaro wani lokacin kuma yayi murmushi.

Shirun da ya ishe ta ne ya sa ta ɗauko wayarta ta saka charge daga nan kuma ta fara danna kayarta cike da ƙwarewa. Lokaci zuwa lokaci kuma yakan ɗago ya dube ta ganin hankalinta na kan wayar shima sai ya maida nasa ga titi. A nata ɓangaren ita ma takan ɗago ta saci kallonsa sai kuma ta koma danna wayarta. Shirin da ya ishe shi ne yasa ya kunna Ƙira'ar Muhammad Ayyub yana ɗan bin baki.

Ita kam cikin ranta take bin baki saboda yadda take tsananin son karatunsa. Haka tafiyar tasu ta kasance, da suka kai Bauchi kuma suka tsaya suka ci abinci a restaurant daga nan kuma suka ƙara ɗaukar hanya. Ba su suka isa ba sai wuraren la'asar don ma suna tsayawa su yi salla.

Sai da ya daidaita parking tukun ya fito, gateman da ya rufe gate yayi wa nuni da ya zo ya shiga da kayan dake cikin Boot, ita kuwa saboda kewa da ɗaulin ganin mutanen gidan da gudu ta shiga ɓangaren Granny tana ƙwalla mata ƙira. Jin Muryar shalelenta yasa ita ma ta fito da sauri tana washe baki.

Bayan ta huta kuma ta zaga sauran part ɗin gaida su tare da isar da gaisuwar mutanen Gallara gare su. Ɓangareb Nenne ne ƙarshen zuwa ai kuwa can ta tarar da Babes an sha kyau don tuntuni an fara yi musu gyaran jiki. Don Aunty Baraka ba baya ba wurin sanin Sirrin gyaran jiki. Rungume juna suka yi suna murna yayin da take koɗa yadda suka sauya sosai, sunyi kyau da haske ga fatarsu kamar ba a Nigeria suke rayuwa ba.

Hayaniyarsu ne yasa Aunty Baraka fitowa don ta san halin ƴaƴan nata, ko da ta fito ganin Khairy sai ta tsaya tana bin ta da wani kallo, ita ma Khairy nata ɓangaren kallonta take yi don babu shakka ta san fuskar amma ta gagara tuna ina ta santa. Ganin tunanin yana shirin yin tsayi yasa ta ɗan kau da kai tare da gaida Aunty Barakar da take mata kama da wata fuska da ta sani.

Cikin sakin fuska Aunty Baraka ma ta amsa, tana murmushi ta ce “Da gani wannan ita ce Khairy ko” murmushi tayi tana gyaɗa kanta. Yesmeen tace “Kin kuwa canka dai-dai ita ce Khairy, cikon quadruplets kenan” dariya dukkansu suka yi, Aunty Baraka ta ce “Matso nan Khairy” babu musu ta ƙarasa kujerar da Aunty baraka ta ke, ganin hakkan yasa suka fara shagwaɓa wai khairy ta ƙwace musu Aunty Baraka, ita dai Khairy mamaki take ganin irin wannan sauyi bata san lesson ɗin da aka ɗaura musu bane bayan tafiyarta.

Cikin ƙanƙanin lokaci Khairy ta sake da Aunty Baraka wacce ta ja ta a jiki, hirarsu suka kasa bayan sunyi sallah. Nan Aunty Baraka ta fara kawo musu abubuwa iri-iri suna ci da sha amma na Khairy haɗin daban ne saboda ita ma ta kamo ƴan uwan nata, sai da Aunty Baraka ta tashi Khairy ta ke tambayar su murya ƙasa-ƙasa. “Kai Babes irin wannan sauyi haka daga tafiya ta? Meye Sirrin ne?” Fauzah ta ce “Ai babu wani sirri da kike gani sai abunda yanzu kema kika fara amsa” ta ƙarass tana ɗage mata gira.

Dukan wasa Khairy ta kai mata tana faɗin “Ke meye haka kina wani ɗage min gira?” Ayrah ta ce “Kin ga Fauzah ki ɗan bawa Khairy lokaci naga yanzu bata samu karatun ba amma tunda ga Aunty Baraka lafiya lau zata fahimta” dariya Dukansu ukun suka yi Yesmeen na faɗinn “Ai kuwa dai Ayrah haka ne, mu jira muga nata....” shiru tayi ganin Aunty Baraka ta shigo.

Wani haɗin ta ƙara basu daga nan Khairy ta ce zata wuce kada Granny tayi zaman kaɗaici. Cike da tsokala Yesmeen ta ce “Uhm ke da kin kusa ma ki rabu da Grannyn?” zuciyarta ne ta yanke lokaci ɗaya don ita har ga Allah ta ma manta da batun auren, waskewa tayi kawai tace “Ku dai kayan mamakinku baya karewa, kunga mu kwan lafiya nikam”

Daga haka ta wuce part ɗin Granny da sauri har tana harɗewa kamar zata faɗi, ko da ta shiga ɗakinta hawaye ta sake tana faɗawa kan gadonta. A hankali yayin da hawaye ke zubowa daga idanuwanta tace “Allah sarki Ni Aishatu, wannan wanne irin aure ne za'a yi min?, ace two weeks ya rage ayi biki amma bansa ango a idanuwa na ba! To in ma baya kusa ne ba zai nemi number na ya ƙira ni ba at least na San ko da sunansa ne” hawayen fuskarta ta share tana mai ƙarfafawa kanta guiwa tace “Ko ma waye ne tunda yayi silar rashin cikar burin zuciya ta kuma muradi na sannan ya zama shamaki tsakaninmu da wanda na ke so dole ne ya karɓi kowanne hukunci na yanke masa” daga haka tayi alwala tare da gabatar da shafa'i da kuma witr daga nan tayi shirin bacci tana mai gabatar da addu'ar ta.


************************

A daren yau ne Hamma Zaki ya shirya sanar da shalelensa kuma uwar ƴarsa wato pretty game da auren nasa da ke zuwa cikin wasu makonni masu zuwa. Har ga Allah baya son tashin hankalinta a halin yanzu musamman da take ƙoƙarin ganin ta gyara wasu banzayen ɗabi'unta, uwa uba yana jin daɗin rayuwarsu da suka fara ginawa baya son a samu wani abu da zai zama shamaki da zaman lafiyarsa da abokan rayuwa.

Ganin tunda ya shigo yana cikin damuwa yasa ta kawo masa drink a cikin glass cup tare da zaunawa gefensa tana ɗaura hannunta a kafaɗarsa. “Sweetheart!” ɗan ɗago kansa yayi yana dubanta tare da sanya fuskar murmushi don gudun kada ta gano sai ya sanar da ita. Sajen fuskarsa ta shafa tana faɗin “Watz wrong with u sweetheart?, kana cikin damuwa don Allah ka faɗa min”
Bai ce komai ba duk da cewa tana jiran amsarsa sai ta ɗan sharar. Sai da suka wuce bedroom tukun ta Kai baby Humairah cot nata suka kwanta tukun ya ƙira sunanta a sanyaye. “Nabila” sai kuma ya ɗanyi shiru kafin ya ci gaba “Ina so ki saurare Ni da kunnenki na basira ki ji me zan ce” zuciyarta ne ta tsinke don kuwa ta tabbatar wannan babban al'amari ne yake son sanar da ita.

Ajiyar zuciya ya sauƙe sannan ya ce “Nan da sati biyu in sha Allah za'a ɗaura aure na” dumm gabanta ya faɗi, a zabure ta tashi ta zauna tana dubansa “A'a sweetheart wasa kawai kake min na sani, babu wacce zata shigo rayuwarmu, wasa kake yi ka faɗa min” ta faɗa tana tsayar da kallonta a kansa babu ƙiftawa.

Dama ya san za'a yi haka tabbas sai dai kuma ba zai bata damar tasiri akan hakan ba, shi ne mijin ai ba ita ba. Ɗan dakewa yayi yana faɗin “Yadda kika ji zan ƙara aure ne, kuma nan da sati biyu” jin maimaicin abunda ta ji a maimakon amsar da tayi tunani yasa ta sauƙa a gadon babu shiri tana tsaye gabansa idonta kuma na kansa tace “Ai wallahi ba zai taɓa yiyuwa ba!, ta ya ma zan yi sharing miji da wata banza, Allah sweetheart tun wuri ma ka ce ka fasa don kuwa ko wacece ta kuskura ta shigo zan iya kashe ta a kan miji na”

Hayaniyar tata ne ta fara damunsa hakan yasa ya ɗaure fuska yana faɗin “Sai ki kashe ta ai tunda ke kika yi ta!, bari ki ji aure babu fashi kamar anyi, babu gudu babu ja da baya cikinsa, in kin so ki nutsu ki zauna da ita lafiya in kin so kiyi hauka lafiya lau kika aikata wani laifin duk hukuncin da aka miki babu abunda zan ce.”
Kan sa ne ya sara saboda doguwar maganar da yayi hakan yasa ya ja blanket ya juya gefe ya kwanta abunsa yayin da ita kuma take tsaye tana huci kamar mayunwacin zaki. Ganin tsayuwar ba zata fisshe ta ba yasa ta faɗa gadon kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login