Showing 39001 words to 42000 words out of 135404 words

Chapter 14 - ƳAR IYA complete hausa Novel

13 Oct 2024

46370


*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*







__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __

SHAFI NA “““39&40”””

Sanyin asuba da ke busawa yayin da alfijir ya keto, Babu abunda ke tashi sai kiraye-kirayen sallah wanda ake jin sa daga can nesa. Miƙa yayi ɗauke da addu'a a bakin sa.

(الحمد لله الذي أحيانا بعد ما أماتنا و إليه النشور).

Sai da ya shafe wasu sakanni kafin ya ziro sawayen shi ƙasa. Toilet ya nufa tare da alwala sannan ya gabatar da sallar sa. Yana idarwa ya yi azkar ɗin sa na safiya tare da karanta wasu ayoyi daga cikin Alqur'ani. Ba shi ya tashi daga praying mat ɗin ba sai around 6:00am. Bayan ya naɗe ta ya haye gado tare da komawa baccin sa saboda har yanzu bai gama cinye hutun da aka bashi ba.

(*Ko kun san cewa miƙewa tsaye immediately bayan tashi daga bacci ne ahaifar da matsaloli da dama?, Idan baki sani ba toh daga hau in kin farka daga bacci ki tabbatar kin cigaba da kasancewa a kwance na wani lokaci kafin ki miƙe domin kiyaye lafiyar ki*)

*PRETTY POV*


Directly Cikin tuƙin ganganci suka fizgi motar sai hotel ɗin ransu a matuƙar ɓace. Bakin kowa tsit banda sautin waƙar _Rush_ babu abinda ke tashi cikin motar.

Bayan sun isa Pretty ta buɗe musu ɗakin tare da shigewa. Pretty dake wani hura hanci ga fuskar nan tayi ja jawur kamar an watsa mata ruwan zafi (nace ai kusan hakan, ga marin Sarah ga na Capt Sulaiman). Kayan dake jikin ta ta fara cirewa. Tas sai da ta cire komai tukun ta ɗaura towel ɗin dake lanƙaye jikin hanger. Toilet ta shiga ta sakarwa kanta ruwa ko zata ji sauƙin raɗaɗin da ke damun ta.

Ishy, Fauzy, da kuma sumy suma a lokacin suka tuɓe suna jiran fitowar ta, sai da ta ɗan ɓata lokaci kafin ta fito, Ishy da Fauzy suka shige abun su a tare yayi da sumy ta tsaya taya Pretty shiryawa tana lallashin ta. Su biyun tare suka fito sannan sumy ma ta samu ta shiga. Cikin wasu tsinannun kaya suka shirya waɗanda ko a zaman gida wanda ba kai ɗaya ba bai dace ka sanya su ba.
Bayan sun shirya Pretty ta ƙira aka aiko musu da abinci.

Sai da suka yi hani'an suka yi brush, batun sallah kuwa babu shi, turare suka fesa tare da miƙewa suka yi waje.

Motar su suka nufa but this time around Sumy ke driving, duk irin yadda kiɗa ke tashi a motar basu daina hirar da suka fara ba.
Pretty da kanta ke lafe jikin kujerar motar tace “Guys yau ban san ya zanyi ba, yet zuciya na bai daina zafi ba”
“Sorry Pretty, yanzu zuciyar ki zata sauƙa for a while, ance Adamawa akwai sweetboys wadanda suka san harƙa, just relax kiyi mankas muyi rawa abun mu, all this sadness will fade away.” Sumy ta faɗa tana juyo gefen ta da Pretty ke zaune.
“Uhmm” Pretty ta faɗa tana sakin wani killer smile “Ban jin zan iya mantawa da wulaƙancin nan da wuri fah”
“Ke dai ki bari” inji Ishy dake sit na baya ita da Fauzy.
Fauzy tace “Just relax babe, ko baki mance ba in mun dawo we'll make u forget it”
“Toh Allah yasa”

Suna isa suka samu wani ɓangare tare da parking motar su. Tun daga fitowar su suka ci karo da wasu gang ɗin samari suna busa shisha.
“Payo....ɗago kaga wasu hot babes a nan” ya faɗa yana tsaida kallon sa kan su Pretty dake sanye cikin wasu tsinannun transparent gowns da basu da maraba da babu.
“Bura uba” payo ya faɗa yana muƙewa tsaye “Alquran yau akwai shagali Subato” ya faɗa tare da miƙa wa subato hannu.
Miƙewa suka yi tare da nufan su Ishy da suke daf da isowa yadda suke.

Kallon banza su Pretty suka aikawa su subato tare da raɓawa ta gefen su suka shige ciki. Sauran gang members ɗin kuwa dariya suka saka suna musu gwalo.

Directly hall ɗin suka nufa, a daidai entrance door ɗin suka ci karo da wata budurwa samanta wani ƙato sai haƙarta yake yi (Authubillah ko kunyar ido babu). Raɓa su suka yi sannan suka shige cikin hall ɗin. Suna zama waitress ɗin ta miƙa musu alcohol Wanda brand ɗin ta ana hana mutane ta'ammali da ita.

Sai da suka yi mankas daga nan kowacce ta manta yadda take, sautin waƙar dake tashi sai a lokacin yake ɗibar su, Pretty da Ishy suka nufi stage ɗin suna tangal-tangal. Rawar da sukeyi kaɗai ya isa ta bawa mutum haushi, su gasu kamar macizai saboda lanƙwashewa amma haka suka yi tayi.

Payo da ya shigo yaga mutanen nasu sunyi mankas yasa ya janyo hannun Pretty suka shige room ɗin da ya kama.
Suna shiga ya fuzge mata rigar da da ita Gara babu nan ya cafki boobs ɗin ta ya fara sucking, tuni salo ya canza aka wuce zuwa wata duniyar.

Ishy kuwa tare da subato suma suka baje tasu hajar. Fauzy da Sumy kuwa dama sun fi ƙwarewa a fannin lesbian hakan yasa da suka samu partner suma suka shige nasu room ɗin tare da ci gaba da masha'ar su.

(Innalillahi wa inna ilayhi rajiuun, wannan itace rayuwar da matasan wannan zamani suka ɗauka a matsayin wayewa, zina ta zama ruwan dare, maɗigo (lesbian) da kuma luwaɗi (homosex) sun zama jiki a wurin matasan mu. Subhanallah, ayyukan da suke samarda fushin Allah su bayi suke aikatawa hankalin su kwance?, Ina zamu je ne?, Ina zamu saka rayuwar mu ne?, Shin mun manta akwai mutuwa ne?, Lallai ya kamata mu farka mu san ne muke yi, ba fa komai ce wayewa ba! Mu tuna zamu mutu, ya muke tunani idan mutuwa ta riske mu a irin wannan hali?, Me zamu faɗawa Ubangijin mu?.
Ƴan uwa ya kamata mu san cewa aikata waɗannan abubuwan baya daga cikin wayewa sam sai dai ma taɓewa, kuma masu aikata waɗannan ayyuka in Basu tuba ba kafin mutuwar su toh Ubangiji ya tanada musu azaba mai raɗaɗi tun daga mutuwa har zuwa hisabi da kuma miƙa kowa gidansa na har abada. Allah yasa mu dace).

Su Pretty basu bar club ɗin nan ba sai around 2:00am, lokacin alcohol ɗin ya saki sumy da yake ita ba wani da yawa ta sha ba, hannun Fauzy ta kama tare da miƙa ta cikin motar su sannan tabi rooms ɗin da Ishy da kuma Pretty suke, suma ta ɗsuko su ba tare da ta mayar musu da kayan jikin nasu ba ta miƙa su motar.

A haka ta fuzgi motar sai hotel ɗin su, da ƙyar ta taya su suka shigo ciki saboda har yanzu suna kan network. Nan duk suka baje wasu ƙasa wasu suka haye bed.

Sai around 10:00am suka tashi, bayan sunyi wanka suke tambayar taya suka dawo. Dariya sumy tayi tace
“Dole kuce haka babes, irin wannan dare da gani U guys enjoy it”
Su duka suka kwashe da dariya, Pretty tace “Tuni na manta da maganar Sweetheart, sai yanzu na tuna, hope zaku ƙara raka ni tunda sai gobe mu wuce ko?”
Ishy tace
“Shegiya Pretty dole ki manta da shi mana, kinje kin buɗe xender ya tura Miki bahubali!” ta faɗa tana sakin dariyar shaƙiyyanci.
Fauzy da har yanzu ke dariya tace
“Babes baku da dama gaskiya, kiji wai xender!” ta faɗa tana miƙa wa Sumy hannu wacce itama dariyar take tsulawa.
“Ke dai ki bari sumy, ai gwanda xender wai kinji bahubali!” itama ta faɗa suna cigaba da dariya.

Bayan sunyi breakfast kuma suka ja motar su neman pretty's Sweetheart.


★★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*
Yau tunda ta tashi daga bacci tayi wanka tare da sheƙa kwalliyar ta irin ta Aljanu. Janbaki kamar zai yi magana haka powder kamar wata dodanniya.

Neman halal ɗin ta ta fita, yau ma dai bata biya ta gidan su A'i ba saboda ita ta a can tana shirye-shiryen bikinta ne.

Tana fita ta fara zagayawa daga gidan dake maƙwabta da su. Da sallama ta shiga kamar dai ba Ƴar Iya ba.
“Salamu Alekum, ina mutan gidan ko sun fita ne”
Goggo hari dake cin ɗumamen tuwon dawa tace, “A'ah yau kuma mu aka tuna shalelen Iya?, Maraba lale iso muci ɗumame”
Zama Ƴar Iya tayi kan taburmar tana sinne kai. “Iy Aradu inna Hari yau ke na tuna, talla na kawowa sirikan ki, bari na shiga ciki”
“Tallen me kuma shalelen Iya?” Goggo hari ta jefa mata tambaya.
“Maganin mata ne, ku fa tsofin nan kun fiye tambaya, haka iya ma ta sani gaba da tambaya to Sarkin Aljanu da kansa ya koya min, kuma duk wanda bai siya ba Aradu mijin ta sai ya sake ta”
Ta faɗa tana miƙewa tsaye. Goggo Hari jin ambaton Aljanu da Ƴar Iya tayi yasa ba shiri ta bata hanya.
“Allah ya kawo kasuwa” Gaba Ƴar Iya tayi abunta ba tare da amsawa ba.

Lirwanu ɗan Goggo Hari na farko ya fito zai fita suka ci karo da Ƴar Iya. Dakatar da shi tayi ta hanyar faɗin “Mallam ka bawa matarka kuɗin siyan magani”
“A'a shalelen Iya ce?, Ya Iya ɗin tana lafiya”
Katse shi tayi da cewa
“Ba shi na tambaye ka ba in ka damu da Iyar ka je ka gaishe ta ai, mtsss ka bawa matar ka jaka biyu da rabi kaji”
“Toh toh babu damuwa” ya faɗa tare da bin bayan Ƴar Iya har suka isa, su Ƴar Iya ashe akwai hankali a bakin ƙofa ta tsaya jira, bayan ya fito ta tambaye shi ko ya bayar, da ya bata amsa ta barshi ya wuce ita kuma ta kutsa cikin ɗakin.

Ala dole haka tabi sirikan Goggo Hari duk suka siya tukun ta fito daga gidan. Tunani ta fara ina zata kuma nufa?
“Gidan Baba na!” ta faɗa tana murmurshi. Bata tsaya ko ina ba sai gidansu. A lokacin Inna Zaliha na zaune a kan kujerar zaman gida tana wanke-wanke tana rera ƴan waƙen ta. Ko sallama Ƴar Iya bata yi ba ta kutsa cikin gidan sai wani hura hanci take tana ɗaga shi sama, bakin nan yayi gaba kamar bututu.

Inna Zaliha da fuskar ta ke nuna tsantsan mamaki ta kalli Ƴar Iya tana yatsina fuska
“Ke kuma rasa kunya daga ina?”
Ƴar Iya bata amsa mata ba sai ma ƙoƙarin sauƙe kayan tallar ta da take.
“Wai ba magana nike maki ba?, Me Kika zo yi gidana?”
Duk rashin hankali irin na Ƴar Iya sai da ta tsaya ta maimaita me kike yi a gidana cikin ƙwaƙwalwar ta. Can ta kalle Inna Zaliha tace “Gidan ubanki ne ko nawa?”
Baki buɗe Inna Zaliha ke kallon Ƴar Iya tace “Eh ba shakka gidan ubanki ne kam..eh babu shakka haka ne”
Ƴar Iya ta harare ta tace “In baki sa na dawo gidan da zama ba, shegiya mai shegen baƙin hali da baƙar zuciya”
Inna Zaliha tuni ta tsure da zancen Ƴar Iya tunawa da sharaɗin da Bokan ta ya bata....hakan yasa tayi murmushi tana sunkuyar da kai.
“Wa ya isa ya hana shalelen Iya guda?, Yanzu dai me ya kawo ki maza ki faɗamin” Ta faɗa cike da ƙosawa coz zaman ta a tare da su akwai matsala.
Sai da ta gama shan ƙamshin ta tace
“Maganim mata na kawo miki ki saya, ai nasan kina amfani dashi”
“Maganin mata kuma Ƴar Iya?” ta watsa mata tambayar.
“Eh shi dai, ko kin fi so nayi ta maimaita magana kamar jaka?”
“Aah ba sai kin maimaita ba, wane iri ne”
“Irin wadda kike amfani da shi ki mallake min tsoho na har kika raba mu da shi gaba ɗaya, Aljanu da kansu suka bani wannan maganin bari kiji, Kuma in Kika karɓa bakiyi amfani da shi ba Aradu sai kin mutu, shegiya mai raba ɗa da uwa”
Cikin sanyin murya Inna Zaliha tace “Nawa ne?”
Ƴar Iya tace “Naira dubu biyu ne babu yawa, kuma zan dawo don kullum sai kin siya Aradu”
Zaro ido Inna Zaliha tayi tana kallon Ƴar Iya
“Dubu biyu fa kika ce shalelen Iya?”
“Eh haka nace!” ta bata amsa a fusace, “Kina amsar fiye da haka ma daga wurin Baba na ki hallaka a wurin ƙato ai”
“Shikenan yi haƙuri, bari na ɗauko miki kuɗi” ta faɗa tana miƙewa don ta ƙosa Ƴar Iya ta bar gidan zata shiga ɗakin taji Muryar Ƴar Iya “Ki taho min da dubu ɗaya zan biya na siya burodi”
Kamar inna Zaliha zata yi kuka haka ta amsa da to tare da shigewa ɗaki.

LIKE PLEASE


[5/18, 10:52 AM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀




_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*








__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __


SHAFI NA “““41&42”””

Dubu uku cas Inna Zaliha ta ɗauko tare da damƙawa Ƴar Iya tana zuba godiya. A yatsine Ƴar Iya ta amshi kuɗin sannan tace
“Idan Baba na ya dawo kice masa inji ni ya bani wasu kuɗaɗe za'a yi bikin ƙawata daga nan kuma nima za'a yi nawa ba daɗewa.
“to to zan faɗa masa, sai anjima”
Harara Ƴar Iya ta Banka mata tare da ɗago daron ta ta aza shi bisa kayin ta, nan ta fice abun ta tana murna. Ganin tayi ciniki yasa ta yanke shawarar komawa gida ta adana kuɗin ta.

★★★★★★★★★★★★★★★★

*PRETTY POV*

Yammacin yau Laraba Pretty ta shirya kaima Sweetheart nata ziyara bayan ta binciko bayanai game da shi.

Sanye take ciki wasu expensive English wears, Wanda suka ɗame ta sosai, surar jikin ta ana gani kamar dai babu. Kitson attachment da tazo da shi ta sa aka sauya duk da ta kashe kuɗi mai yawa kafin ayi mata, ƙwaƙuyayyen kan nata ta ɗaurawa wata cap na gashin doki tare da gyara ta tsam, nan sai ka rantse gashin ta ne.

Fauzy ce ta mata makeup wacce ta mayar da ita mutum-mutumi, in ka ganta babu abinda zai hana ka guduwa, hankali kwance ta fesa uban turare tare da yiwa ƙawayen nata alama da suzo su wuce, suma da shigar tasu babu gwanda, sai dai ita sumy Abaya ta saka tare da rolling veil.

Cikin motar kuwa Pretty farin ciki ya hana ta sukuni, zata ga Sweetheart ɗin ta, babu abunda ke tashi sai sautin waƙar India tuni ta manta duniyar da take.

Dai-dai Gate ɗin gidan General Muhammad Naira suka yi horn, gateman ya buɗe, sai da suka kai dai-dai parking space suka yi parking motar. Ba tare da sun fito ba suka tsaya ƙarewa motocin dake wurin kallo, ga kuma tsarin gidan da tuni ya tafi da su.
Pretty da ta tuna mai ya kawo ta ta ce “Babes wanne part ɗaya zamu shiga ne?”
Fauzy tace “Mu shiga na farkon idan ma ba nan bane ai za'a tura mu wani”
“ƙwarai yadda Fauzy ta faɗa haka za'a yi” Sumy ta amsa mata.

A gadarance cike da yauƙi suka fito daga motar tare da nufar entrance na part ɗin. Ganin door ɗin a buɗe yasa suka kutsa kayuwan su ciki. Ƙamshin da ya daki hancin su kaɗai yasa su lumshe ido, bisa latsa-latsan kujerun suka yiwa kansu masauƙi.

Ganin babu wadda ya ko gifta yasa Ishy faɗin “Pretty wai zaman me muke yi ne?, Letz just get in mun tsaya a nan babu mai fitowa fa” Sumy kam da kallo ta busu don tuni gidan ya matuƙar burge ta, sai taji inama ace tana da wata alaƙa da gidan. Su Fauzy ma dai zuciyar nan a cunkushe ana bawa ido abinci.

“Assalamu Alykum” sallamar Fauzah da ta doki kunnuwan su yasa su waiwayowa don ganin waye”
Mutuwar tsaye taso yi ganin baƙi a parlourn Mom, baƙin ma Christian, sai da ta hango Sumy tukun taga ita kamar musulma ce. A hankali ta ƙara sa tare da faɗin “Ina yinin ku”
Murmushi duka suka yi mata tare da faɗin “lafiya ƙalau a tare”
“Bari na sanar da Mom tayi baƙi to”
Daga haka bata jira amsar su ba ta wuce bedroom ɗin Mom.
“Good evening Mom.... I'm back oh sorry u've visitor outside”
Cike da mamaki tace “Visitors kuma Fauzah, su waye”
“I don't know them but it seems like Christians ne, suna jiran ki” ta ƙarashe tare da nufar hanya zata fice.
“Wait Fauzah, ask Laraba to bring something for them, Ina fitowa”
“Ok Mom”

Kamar yadda Mom ta umarce ta haka ta wuce ɓangaren su Laraba ta sanar da ita saƙon Mom kafin ta wuce bedroom nata ta cire uniform tare da yin wanka. Sai da Mom ta ƙara kusan five minutes ta fito sanye cikin kayan al'adar su, sari ce blue wacce tayi matuƙar ƙara bayyanar da kyau da kuma izza irin ta Mom ga kuma kyakkyawar kwantacciyar baƙar sumar ta da ta zubo da ita ta baya.

Jin takun takalmi yasa duka suka waiwayo..... idanuwan su suka zaro tare da sakin baki kowa na ayyana abun da ke zuciyar sa. Cike da mamaki ganin duk ciki babu wanda ta sani yasa ta ƙara ƙure su da ido ko zata tuna su. Su kuwa kallon da Mom ke jifan su dashi ya sauƙar musu da shakkar ta na lokacin.

Tana ƙarasowa ta zauna tare dayin murmushi. Ganin kamar ba kansu ɗaya ba yasa Mom fara gaida su.
“Ƴan mata ina yinin ku?”
Cikin ƙiƙina suka amsa babu kunya da
“Lafiya Mom,”
Mom! Mom ta ƙara nanata sunan cikin zuciyar ta, “Ikon Allah, wai mom ko wace Mom ɗin rai?” ta faɗa a ranta a fili kuma tayi murmushi tare da faɗin
“Sannun ku da zuwa, sai dai ban gane ku ba fah”
Sumy ce tayi ƙarfin halin faɗin
“Laa Mom yaranki ne ai”
Ishy ta cafke da faɗin
“Mun zo wurin Captain ne Mom”
Mom kam sun ɗaure ta da abun mamaki, ita dai iya sanin ta Son nata baya ma kula mata bare yayi mu'amala da waɗannan masu kama da Ashawos ɗin nan, murmushi kawai tayi tace
“Ku ƙira shi kuce kuna jiran shi parlourn”
Jin hakan yasa fitsararriya Pretty faɗin
“Ji rainin wayo...” bakin ta Ishy tayi saurin rufewa da hannun ta tare da fatan Allah yasa Mom Bata ji ba, sai dai aikin gama ya gama.

Fauzy ce tayi ƙarfin halin faɗin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login