Showing 66001 words to 69000 words out of 135404 words
kyau tun tana yarinya, mugunta, ta'adi sune abinda tasa gaba, kakanta da kuma kakarta da suka raine ta duk sunyi iyakar iyawarsu don ganin sun kawar da mu sai dai munfi ƙarfin su. Bayan ta kai girman ta ne muka juya ƙwaƙwalwar ta saboda muna tsoron ta sauya daga turbar da muka ɗaura ta. Bata duk wani abu da ya shafi addini, babu abunda ta tsana sama da sallah, karatun Alqur'ani kuma mun riga mun juya ƙwaƙwalwar ta ko sau million za'a yi bazata taɓa haddata ba. Mun fara samun tsaiko ne ta hanyar wasu fararen shaiɗanu da suka shafe ta, da yake mun fi ƙarfin su yasa tasirin su baiyi ƙaimi a tattare da ita ba.”
“Yanzu haka ba mu bane muka zo ba, waɗannan fararen shaiɗanun ne da suka fara tasiri a tattare da ita saboda irin kyautatawar da mutanen da suke rainon ta ke nuna mata, har ta fara sanyi kuma ta daina ɓarna kamar yadda ta saba, hannun ɗanguigui ma yayi sanyi. Ko a lokacin da suka samu hatsari, mun so hallaka ta a lokacin saboda mu huta da wannan aiki mai dogon zango sai dai fararen shaiɗanun sunyi galaba a kan mu, duk da mu muka haɗa hatsarin ko ƙwarzane bata samu a jikin ta ba”
“Yanzu maganar da nake maka muna kan aikin mu, indai muka ce zamu rabu da goɗiyar nan boka zai mummunan hukunta mu, saboda haka babu yadda zamu je”
Sheikh Imam ya share hawayen dake fita da idanuwan sa yace “Lallai kun cika azzalumai, kuma Ubangiji ba zai barku ba, ita Zaliha kuma tun a nan duniya zata ga sakamakon ta. Barin yarinya kuma dolen ku ne”.
Cike da hasala shaiɗanun suka tada wata baƙar guguwa wacce ta zo da girgizar ƙasar gidan, tuni gidan ya fara rawa kamar zai rushe, duk da haka Sheikh Imam bai tsorata ba yaci gaba da karanta Alqur'ani, can guguwar ta lafa suka fara ihu suna faɗin ya dakata, zasu fita amma har sai an since ƙullin da aka yi a lokacin aikin, wnada yanzu haka yana tare da Inna Zaliha a bayan gidan ta. Dole aje a ɗauko wannan ƙullin a since, daga nan zasu bar yarinyar”.
Murmushi Sheikh Imam yayi yace “Shikenan zamu je a since ƙullin amma kafin nan ina so kuyi imani da Allah ku tuba daga irin waɗannan ayyukan da kuke yi, don kuwa Allah baya zulunci kuma baya goyon bayan zalunci”.
Nan Christins na ciki suka musulunta , musulman mah suka yi alkawarin sauya sheƙa daga miyagu zuwa nagari. Sheikh Imam yayi matukar farin ciki. Daga nan jikin Khairy ya sake.
Wani ruwan magani ya watsa mata daga nan ya wuce zuwa ɓangaren baccinsa ya kwanta.
Washegari kuwa sai ga Daddy sassafe tare da Hamma Zaki, har lokacin Khairy na kwance bata tashi ba. Bayan Sheikh Imam sun gaisa da Daddy nan ya sanar da shi komai kamar yadda ya wakana daren jiya. Daddy sai da ya zubar da ƙwalla, Hamma Zaki ma ya tausaya wa yarinyar cikin ranshi yace “Ashe ba banza ba”.
Daddy ya umarci Hamma Zaki ya basu wuri za suyi magana da Sheikh Imam. Bayan fitarsa Daddyn ya sanar da Sheikh Imam game da Hamma Zakin. Murmushi irin na manya wanda yanzu na fahimci ɗabi'ar Sheikh Imam ɗin ne yayi. Ya fuskanci Daddy yace
“Tabbas tun jiya da kuka zo na fuskanci hakan, alamomin wanda sihiri ya kama sun bayyana a tattare da shi. Amma babu komai zan bashi wani magani, da izinin Allah zai samu waraka. Akwai wasu addu'oi ma da zai lazimci karanta su, bi'idhnillah zai samu kariya daga wurin Ubangiji, Allah ya kiyaye gaba”.
Hirar su suka ci gaba da yi can Daddy ya tambayi ina Khairyn?, Sai a lokacin Sheikh Imam ya sanar da shi cewa “Ba lallai ta farka a yau ba, saboda shaiɗanun manya ne kuma baƙaƙe, amma akwai maganin da zan baku, ruwan addu'a da kuma wasu addu'oi da za'a ke karanta mata. Idan ta farka za'a iya samun sauyin yanayi game da ita saboda rayuwar da tayi a da duk bata da hankali, don Allah a kula da maganin nan. In ta ware zamu je can garin nasu tunda sun faɗa, sai a tono bisnen a ware shi, daga nan baƙaƙen aljanun zasu bar jikin ta.”
Da “Toh Daddy ya amsa yana ajajjaɓin abun cikin ransa,”.
Sai wajajen Zuhr Daddy ya nemi Hamma Zaki, bayan sunyi sallah a masallacin dake jikin gidan Sheikh Imam ɗin Daddy yasa Hamma Zaki ya ɗauki Khairy ya kaita mota. Da ya dawo Sheikh Imam ya bashi magungunan da kuma addu'oin kamar yadda ya faɗa, ya bawa Daddy ma na Khairy sannan yayi wa Hamma Zaki tunatar wa akan kula da ambaton Allah musamman zikirorin safiya da maraice. Nan suka yi sallama suka dawo gida.
Allah Sarki granny tunda aka tafi da Khairy hankalin ta bai kwanta ba, haka Nenne da sauran mutanen gidan. Horn ɗin motar da suka ji yasa duka suka fito waje suka yi tsaye. Hamma zaki har ya miƙe zai shige part ɗin su Daddy ya dakatar da shi
“Waye kuma zai shiga da ita?”
Ba tare da sanin yadda zai kaita ba ya ɗauko ta sai part ɗin granny, sauran mutanen gidan ma duk suka biyo bayansa cike da alhinin Allah yasa Khairy ba mutuwa tayi ba.
Granny, Nenne, Mommah da kuma Mom duk saida suka zubar da hawaye, Adda Najma uwar tausayi Kam kuka take shaɓe-shaɓe. Su Ayrah dama sun wuce islamiyya.
Har yau Adda Salma a suƙure take, a cewarta itace silar komai, Mommah ma bata sake mata kuma tace duk abinda ya samu yarinyar ta kuka da kanta.
A kan gadon granny ya fire ta daga nan ya fito, magungunan sa ya ɗauka ya wuce part ɗin su.
Granny dake ta famar sharar ƙwalla tana fyace hanci sai haƙuri suke bata.
“Dole nayi kuka mana, yarinyar nan jinta nake kamar yadda nake jin maza, wallahi wani abu ya same ta bazan yafewa kaina ba. Allah Sarki Ummul Khairy”
Daddy ne yayi gyaran murya yace
“Yanzu dai ba wannan ba Hajiya, kiyi haƙuri Allah zai bata lafiya. Sannan waɗannan magungunan ta ne,”
Nan ya faɗa mata yadda za'a yi mata amfani da shi. Mom tace
“Sai naga kamar Hajiya zata takura, ko za'a kaita waje na na kula da ita”
Da sauri granny tayi caraf tace
“Aah Ramatu, barni nayi jinyar Ummul Khairy da kaina, babu wani takurawa”
Kowa sai da ya murmusa don dama da biyu mom tayi maganar.
Nan Daddy yayi musu sharhin yadda abun ya wakana, dagar da aka sha kafin kai ga wannan mataki, kuka dukkan su suke yi, granny tace
“Allah sarki shiyasa nake jin tausayin yarinyar ashe, amma wannan mata in munje can Mai Hana ni muƙe ta da ice ma sai naji dalili”
Fyace hanci tayi tace “Allah sarki ɗaya ta ”
Jikin su Nenne duk yayi sanyi. Nan Daddy ya ɗaura da yi musu nasiha akan suji tsoron Allah su kuma guji shirka, domin mafi munin zunubi itace shirka. Daga nan suka watse granny aka fara jinyar Khairy.
Ɓangaren Hamma Zaki kamar yadda Sheikh Imam yayi masa bayani haka ya fara amfani da maganin, addu'oin ma ya karanta su, tunda ya fara yake ji kamar ana sauƙe masa wani nauyi daga kansa, mugun ɓacin rai da baƙin rai da yake fuskanta tun bikin sa tuni ya fara jin sassauci.
Tunani kuma ya fara kama shi tun bayan yin addu'oin da kuma shafa magani da ruwan addu'ar. Ba abinda ya fara faɗo masa a rai sai batun auren sa, taya ma aka yi ya fara son yarinyar da ta so nuna masa raini ranar bikin girmamawa da akayi masa, wai anya shi yace yana son Auren kuwa shida ko kaɗan baya son tashin hankali?”
Ganin kansa ya fara sarawa yasa ya shiga Toilet ya watsa ruwa tare da ɗauro alwala, daga nan bacci ya ɗauke shi.
_Toh, ko ya zata kaya tsakanin Hamma zaki da Pretty?, Zai ci gaba da zama da ita?, In baku manta ba akwai fansar da iyayen Pretty ke son ɗauka, ko meye dalili?, Khairy fa? Wane irin sauyi kuke tunanin rayuwar ta zata samu?, Su inna Zaliha fa?, Duk cikin littafin ƴar Iya ne, ku ci gaba da bibiyar alƙalamin diamond bhatool_
_In har ba'a comments zan ƙara rage yawan post gaskiya, kuyi comments ni kuma nayi ta Baku update_
Comment & Share Please.
[8/21, 10:36 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:
🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
_NA_
*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*
SHAFI NA “““69&70”””
Sai wajajen ƙarfe goma na dare Khairy ta fara mutauniyar tashi, granny da idonta ke kanta tayi maza ta ƙara matsawa kusa da ita. Shafa bayanta ta fara tana faɗin “Ummul Khairy kin tashi?” shiru babu amsa hakan yasa granny kunna bulb na ɗakin. Idanuwanta sun sauƙa ne akan fuskar Khairy da tayi Fayau da ita sai yamutsa fuskar take.
“Khairy” granny ta ƙara ƙiran sunanta a karo na biyu. Ganin ba zata amsa ba yasa granny yin shiru tana zubawa sarautar Allah ido tare da jin ɗumbun tausayin Khairyn na yawo cikin jininta. Tabbas ko maƙiyinta ne yaga irin yanayin da take ciki zai tausaya mata.
Ɓangaren Hamma Zaki sai da yayi amfani da maganin kafin ya kwanta bisa katafaren gadonsa, addu'oin bacci ya karanta sai dai baccin sam yaƙi zuwa masa in banda tunani babu abunda yake yi, wanda kaso 40 ya tafi ne akan sauyin da ya samu a cikin rayuwarsa. This sudden change yasa shi shiga cikin wani yanayi. “Ya Allah” ya furta yana ƙara juyawa akan faffaɗan gadon nashi.
Ganin tunanin yana shirin sanya shi shiga cikin wani mugun yanayi yasa ya fara tunanin maslaha ga rayuwarsa. Tabbas akwai baƙon al'amarin da ya ziyarce shi kwanakin baya, in ba haka ba me yasa zai yi aure so sudden haka?, Bashi da mai bashi amsar yasa yayi tsaki “And the worst part of it mahaukaciya ce matar tawa” ya faɗa cikin ɗacin rai. “Allah sarki yarinyar nan! Ko ta farka kuwa?, I pity the little creature”.
Miƙewa yayi yana sauƙa a kan gadon, direct part ɗin granny ya nufa. Da sallama a bakinshi ya shiga. Granny ta amsa amsa masa cikin sakin fuska lokaci ɗaya kuma fuskar damuwa ta bayyana tattare da ita “Maza kaga yarinyar nan Khairy har yanzu bata tashi ba, anya ba mutuwa ma tayi ba?, Ɗan duba min” sai da ya murmusa kafin ya dube ta yace “Granny ba dai anyi miki bayanin abinda ke damunta ba?” gyaɗa kai tayi sannan yace “To tana da rai, addu'r ki kawai take buƙata a yanzun sannan Sheikh Imam yace ake kunna karatun Alqur'ani a wurin da take”
Da sauri granny ta miƙe ta nufi wayarta ƙirar tecno mai madannai. Ƙira'ar babban ƙari'in nan Sheikh Muhammad Ayyubi ta kunna wanda tuni sautin ya karaɗe ɗakin.
Murmushi yayi cikin ransa yace “She too much care about the little creature”
Mintuna biyar suka shafe babu mai magana, mutsu-mutsunta ne ya dawo da hankalinsu gare ta.
“Ash, kaina!, Iya ta kaina zai cire” da sauri granny ta matsa kusa da ita tana faɗin “Kin tashi, sannu maza bari na kawo miki abinci”
Da ido Hamma Zaki ya nunawa granny ruwan addu'a ai kuwa tayi sauri ta ɗebo ta shafa mata a goahinta sannan ta shafe mata a sauran jikinta sai famar sannu take jera mata.
“Wollah yunwa nake ji, wai haka zan zauna” murmushi yayi yana miƙewa cikin ransa yana ayyana “Wannan da gani dama foodie ce”
Granny ce tayi feeding ɗin ta daga nan ta koma baccin ta.
Washegari Hamma Zaki yayi shirinsa na zuwa Abuja don samarwa kanshi transfer bisa umarnin iyayensa. Bayan ya isa kamar koyaushe ya tarar da gidan cikin datti kamar ba sabon gida ba. Tsaki yayi ya nufi ɗakinta don babu shakka bacci take sai kace kasa. Ai kuwa zatonsa ya tabbata.
Cikin ɓacin rai ya ɗaka mata duka “Tashi kiyi sallah”
Kamar daga sama ta jiyo muryarsa ai kuwa zubur ta miƙe, wallahi har cikin ranta tana ƙaunar Captain Alee.
Hugging nashi tayi zata kai masa peck ya ja gefe “See You, ko salla baki yi ba kina shirin taɓa ni, oya go and pray, ki Kuma same ni a bedroom ɗina” ya faɗa cike da taƙama tare da yamutsa fuska.
Baki Pretty ta sake tana ganin ikon Allah. Tsawon aurensu bai taɓa yi mata magana da irin wannan sigar ba duk da cewa tasan a jininsa ne, kai ta karkatar tana faɗin Allah yasa ba aiki na bane ya ɓaci ba”
Daga haka ta nufi toilet ta ɗauro wanka da alwala. Ko sallar bata yi bata sheƙa kwalliya kamar mai zuwa gasar kyau.
Kitchen ta nufa ta buɗe fridge tare da ɗauko sauran abincin da tayi order jiya, warming tayi sannan ta ɗauka ta wuce Bedroom ɗinsa.
Kwance ta tarar da shi yana lallatsa wayarsa ga kuma wani irin kwarjini da yayi mata. Sai ta tsinci kanta da faɗin “Good morning sweetheart” idan da wayar da yake dannawa tayi magana la'alla ta amsa mata. Kusa da shi ta zauna tana ajiye abincin bisa side drawer. Ba tare da ya tanka mata ba yaci gaba da uzurinsa. Ganin ma ba kulata zai yi ba yasa ta miƙe jiki a saɓule zata fita. Muryarsa ce ta daki dodon kunnenta “Wa ya baki izinin fita?”
Cike da takaicin sauyin halin nasa ta juyo rai babu daɗi. Cikin ranta tana ayyana “Ba zai saɓu ba, dole ne ka dawo ƙarƙashina Captain. You're mine alone”.
Ba tare da ya juyo ya kalle ta ba yace “Ki haɗa kayan da zaki buƙata, in a day time zamu wuce Adamawa”
Baki sake take kallonsa ta ma kasa furta komai. “Me mutumin nan yake nufi?”. Cikin ƙarfin hali tace “Sweetheart kwana nawa zamu yi?”
Har ta cire ran samun amsar sa taji yace “Can zamu koma da zama”
“Kutumar uba!, Wallahi ba zata saɓu ba”
Ta faɗa tana riƙe kunkumi tare da jijjiga jiki irin ta tsumu da bala'in nan..
Bai kalle ta bare tayi tunanin yasan me take, saboda haka ta fice a fusace cikin ranta tana tabbatarwa kanta aikinsu ya ɓaci.
“Dole kuwa nasan yadda zanyi”
Mami ta ƙira take sanar da ita komai. Wani Ashar da ta kututtumo kamar bamagujiya.
“Amma wannan Allah yayi ƴan abu ta kazar uba, karki damu Daughter, yanzu ki nuna masa babu komai ki lallaɓa shi tunda ya dawo hankalinsa, ko bayan tafiyarki zan koma wurin bokan yayi masa babban aiki ke harda iyayen nasa ma”
Da haka ta fara haɗa trolleyn ta, komai na buƙata ta saka, ga yanzu damuwarta ma ɗaya itace ta cikin dake jikinta. Tana ayyana dole Captain ya amshi cikin ko kuma tayi aborting nasa.
Da haka ta haɗa komai ta zauna cike da zulumin komawarta Adamawa.
Washegari da safe ma sai da ya tashe ta tukun ta tashi, daga nan ya fita yana jin takaicin wannan aure nasa, sai da ya kammala komai tukun ya wuce yayi musu booking flight. Abinci ya biya ya siya daga nan ya ƙarasa gidan. Bai bi ta kanta ba har washegari. Ƙarfe bakwai dai-dai yaje ya tasheta saboda Flight ɗin 8 zasu bi, shi kam already ya gama shirinsa cike da haɗuwa da burgewa. A daddafe ta kammala shirin saboda zazzaɓi zazzaɓin da ya sauƙa mata. Tare suka wuce zuwa airport ɗin ba tare da wani ya cewa ɗan uwansa ƙala ba.
Ɓangaren Khairy kwana biyun nan bata san me ake yi ba, kowa tausayin halin da take ciki yake, Adda Salma Kam ta taro part ɗin granny tare da ita ake kula da Khairyn.
Flight ɗinsu na landing suka ƙarasa zuwa motar Hamma Salim da yazo ɗaukarsu. Kallo ɗaya yayi mata ya gano tana ɗauke da juna biyu, cike da barkwanci yace “Ke amarya zuwan farko da tsaraba”
Cike da duburburcewa tace “Ehm ah ehm yayan mu..” Bata Kai ga ƙarasawa ba ya katseta yana dariya “Kinga ba wani abu bane, baki ga basaraken mijin naki ma bai ce komai ba”
In banda ƙyaƙƙyafta ido babu abunda pretty keyi har suka iso. Shi dai Hamma Zaki ko kallo basu ishe shi ba. Bayan sun isa a part ɗin Mom suka sauƙa, babu yabo babu Mom ta tarebe su, Laraba aka sa ta kai trolleyn su Bedroom ɗin Hamma Zaki dake upstairs.Dawowar su Fauzah daga school yasa Mom ta umarce ta taje su raka ta ta gaida sauran mutanen gidan.
Sai dai suka je kowanne sashi sai dai gaisuwar mutunci basu samu daga wurin Pretty ba, daga ƙarshe sashen granny suka wuce. A lokacin granny na gaban Khairy wacce ta farka, abinci take bata sai gocewa take ita kuma granny sai famar sannu take aika mata.
Isowarsu ko sallama babu, ita kanta granny Bata san da shigowarsu ba har sai da Fauzah tace Granny Khairyn ta tashi?”
Juyowa granny tayi yayin da idonta ya kai kan Pretty da ta hakimce tana wani hura hanci.
A faɗace granny ta dubi Pretty tace “Ke Kuma fa Malama? Daga ina?”
Fauzah ce ta rufe bakinta da hannu cikin ranta tace “Shikenan granny ta ɓata” a zahiri kuma tace “Granny Aunty Nabila CE fa matar Hamma Zaki”
Baki granny ta kama tace “Ah ai dole, ashe dai kece, zakiyi fiye da haka, to rasa kunya tashi ki bani waje tunda ba'a koya miki ɗaa a gidanku ba”
Daga haka ta juya tana maida dubanta ga Khairy tana ƙara jera mata sannu. Sai da ta saisaita kanta kafin tace “Yi haƙuri Hajiya naga kina bawa yarinya abinci ne shiyasa, ina wuni mun same ku lafiya?”
Ɗan sanyi granny taji ta juyo babu yabo babu fallasa tace “Shikenan lafiya ƙalau” sannan ta maida dubanta ga Fauzah “Ke fauziyya raka ta ina kula da yarinyar nan, sa dawo ita da mijin nata ai”.
Pretty Kam danne fushinta tayi ta wuce ta koma part ɗin granny tana tunanin yaya zamanta zai kasance a wannan gidan? Dole ne tayiwa tufkar hanci don ba zata juri iskancin wannan ahalin nasu ba. Tunawa da wannan yarinyar da tsohuwar ke wani tarairaya kamar jaririya tayi “Tsaki taja tana shigewa cikin Bedroom ɗin da aka ajiyeta.
“Wow!” ta furta, “Kai komai nasa daban